Showing 174001 words to 177000 words out of 182745 words

Chapter 59 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

123

?eya.

"Ba na faWa miki sai da na sa Happy ya canja min kaya ba?"

"Yesss"

"Kaya dai har sai da su Alhaji su ka shigo yi min sai da safe su ka ganni da su, na kasa cirewa. Shi da Abba Habibu ne su ka cire min. It took more than 10 minutes saboda su na tsoron fama min Winki."

"Ya Rahman" Mubina kanta sai da taji kunya.

"Da su ka gama ne Alhaji ya ce sai na biya ladan wahalar da jikin girma. A gabana su ka cinye naman nan. Harda cewa ranar da za ki tare zai biya mu." Ya Wan cije baki "Saboda Allah me zai sa ya yi min zancen tariya? Don na Wan yi kwalliya shikenan sai a fassara ni? Ko ni na kawo fitina duniya ai dole in jira nayi healing ko?"

"Ni dai na shiga uku."

"Wallahi kin shiga. Kazar amarci surukan ki maza sun cinye. An barwa ?a?a tarihi."

Kamar za ta yi kuka ta ce "to ni yanzu yaya zan yi?"

Kamal ya ware hannuwansa yana kallon cikin idanunta.
"You can start by giving me that first halal hug."

Bata san abin da zai ce ba kenan da ba za ta zauna a kurkusa yadda kunyarsa za ta kama ta da yawa haka ba.

"Idan ka warke kayi da kan ka." Ta faWa a ciki-ciki.

"Mubina" ya tsare ta da ido.

"Na'am."

"Now please."

Magiya ce ko umarni? Ita dai bata gane ba. Abin da ta fahimta kawai shi ne zuciyarta tana muradin yin abin da mamallakinta yake so. She gave him the warmest hug. Zuciya da gangan jiki su ka sami kyakkyawar nutsuwa.

A lokacin da Kamal yake tunanin Mubina ta gama biyansa da alkhairi, she brushed his lips lightly da nata. Tsokana ta so yi, reshe sai ya juye da mujiya. Happiness got his happiness and he wasn't willing to let go easily.

Kamal da Mubina Allah Ya ?ara lafiya da zaman lafiya!

***

Wani irin kuka Inna Luba ta fasa daga Waki mai firgitarwa. Malam da yake ririta ta tun jin Yaya ta tafi Saudiyya ya fito daga banWaki da zariyar wando a hannu.

"Luba me ya faru? Mutuwa aka yi?"

Inna Luba kuka kawai take yi babu ?a??autawa. Amarya duk jarabarta jikinta ya Wan yi sanyi. Shi yasa bata faWi magana mara daWi ba da ta fito. Banda haka da tuni ta fara domin tsufa bai rage mata komai ba. Da ?yar Malam ya samu cikin kuka Inna Luba ta faWa masa wayar da aka kira ta daga Kano.

"Surukar Abdul?adir ce ta kira yanzu wai za ta yi min jaje."

"Waye kuma Abdul?adir?"

"?anin Habibu mana."

"To, sata aka yi ko gobara wani cikinsu ya yi?" Amarya ta tambaya tana jin haushin tsurkun da ta fito kuma da alama labarin ba zai ?ayatar da ita ba.

"Yarinyar nan ce..."

Malam ya dafa bango jiki na rawa. Sai ka rantse bai taSa nunawa Yaya ?yama ba. Ya marairaice sosai gwanin ban tausayi.
"Lubabatu bar zancen nan haka. Zuciyata ba za ta iya Waukar zancen mara daWi akan gudan jini na ba."

"Wannan kam dole sai ka ji. Wai anyi mata aiki an cire mata ?oda guda Waya an dasawa wani yaro."

Da wani irin zafin nama Malam ya zabura kamar ba tsohon da yake taku da ?yar ba saboda ciwon ?afa.

"Me???"

Yadda taji ta maimaita. Dama su kan gaisa a waya da ita a matsayin surukai. Ashe duk gargaWin ds Abdul?adir ya yiwa matar tasa akan Soye zancen sai da ta sanarwa ?an gidansu kaf. Ita kuwa Mamansu da bata san Soye zancen ake yi ba ta kira Inna Luba domin ta jajanta mata. Jinjin ta bayar da ?oda an dasawa wani Wan balarabe a Makka.

"Jar uba! Kin ga kira ?andaudun nan ki haWa mu kawai. " Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki "Ni za a ha'inta? ?iyar tawa za a feWe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuWin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ?uda ba zai iya kashewa ba ashe ja'irin ?odar Wiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!"

To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani Wan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta mi?a masa wayarta ko zama bai yi ba.

"Ya'u maza lalubo min lambar Sajida ka kira."

Ya'u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya mi?a mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karSe ya manna a kunne yana masifa.

"Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan."

"Baba Malam me a ka faWa muku?" Sajida ta fahimci ba lafiya ba "don Allah ka tsaya nayi maka bayani."

"?al ?wal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi" ya yi ?wafa "wato kun haWa kai da baban ku za a kawo muku kuWin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin Wiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ?odarta."

Sajida ta sake kwantar da murya
"Baba Malam ka yi ha?uri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai."

"Da ?odarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ?auye. Tun Kaka da Kakanni ban taSa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai Wauka ba."

Ha?urin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karSe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu.

"Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam." Ta katse kiran.

Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sau?in da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ?aramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen.

"Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu Wokin zama ?an yaWa labari mara daWi. Suna rawar jikin zama farkon waWanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?"

"Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?"

Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar Wanta ce ta janyo mu su.

Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaWai ya dinga faWa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taSa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faWa yake yi iya ?arfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karSi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin Wakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin.

Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karSa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaWinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara.

"Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu Sullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?"

"Hajiya turo min numbar da zan same su."

"Bari na karSa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye."

Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su Wauka son zuciya ba.

"Mu bata dama tunda Sangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace."

*

Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaSi ya rufe ta yayinda ma?ota su ke ta zaraf-zaraftu a ?ofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ?waf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waWanda ta san za su tayata yaWawa. Kafin wani lokaci gari ya Wauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ?oda sukutum kuma yana nan da rai.

Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta Wauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta bu?aci Innar ta haWa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa.

"Yarinya ko me za ki ce ki faWa min kawai."

"Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka."

Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa'a tayi kiciSis da Ya'u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana Wasawa da kowa a gidan.

"Inna kina bu?atar wani abu ne?" Ya matso kusa da ita da sauri.

"Gashi" ta bashi wayar ta koma cikin Wakinta.

Ya'u ya saka waya a kunne ya ce "hyalo?"

Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da bu?atarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga Sangarensa. Yadda take magana kaWai ya yi masa kwarjini don jikinsa har rawa yake wajen amsa mata.

"Aiki ka ke yi ko karatu?"

"Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu."

"Masha Allah. Mal. Ya'u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?"

"Et fife (8,500) ne." Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi Win cima zaune ne.

"To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan bu?ata ta ta biya."

Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf.

"Me ki ke so nayi?"

"So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp."

"Shike nan?" Ya tambayeta da mamaki.

"?warai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya Waukar lokaci."

Ya'u baki har kunne don farinciki ya ce "wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof Win ma ya yi ispiya."

"Wannan layin?"

"Eh."

Cikin minti biyar Ya'u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira Wari zuwa Wari biyu sa'i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya dur?usa har ?asa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya'u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ?odar da ma zuwan Abba Habibu.

Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe.

"Yanzu ?ar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?"

"In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu'a da kulawa kawai take bu?ata."

Baba Malam kuwa cewa ya yi "Idan gudan ?odar ta sami matsala fa?"

Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi.
"Komai na Allah ne Baba. Addu'a da kulawa kaWai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maWaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taSa barin wanda Ya fawwala Masa al'amuransa ya taSe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya."

"Allah Ya sa ?ar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya."

Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matu?a.
"Inna na san Yaya a ?alla za ta yi wata a ?asar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haWa jaka. Zan yi magana da ?annena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa."

"Allahu Akbar. Ni Win?" Ta kalli Baba Malam "wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ?ar nan?"

Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Ya?e kawai yake yi.

Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya'u ta ce ya kira ya haWa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daWin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu'o'i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da al?awarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah.

***

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ?oda. Sau?i ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ?asar domin suna bu?atar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku.

"Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba" Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huWun tare da shi a Wakin hotel.

Inna ta ce "Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama Wan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan."

"Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum" cewar Mama.

"Kamawa fa tayi." Umma mai Wan sau?in ta ce tana murmushi.

"Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?"

"Wannan shawarar ku ce. Ni dai ?afata-?afar Habibu da iyalinsa." Ya gyara zama yana sauraron su.

Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ?an uwanta su ka yi na'am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faWa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida.

"Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su."

*

Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi.

"Habibu ba ce wani abu mana."

Abba Habibu ya girgiza kai "wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karSa kuwa?"

Alh. Hayatu ya ce "me zai hana? Ro?a kayi?" Ya yi gyaran murya "ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?"

"Har na isa a bani abu makamancin wannan?"

"Kada ka yi saSo mana. Kowane bawa da arzi?insa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taSa wuce shi. Ko dai ka je da ?afarka ko ya biyo ka har inda kake."

"Haka ne. Allah Ya zaSa mana abin da yafi alkhairi."

"Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau."

Abba Habibu ya yi murmushi "Zan yi istihara in Allah Ya yarda."

*
Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matu?a, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taSa sana'ar abinci a nan.

A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaWan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa al?awarin yi musu igama shi da Yaya da duka ?a?ansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama.

"Ku buWe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya." Ita ce shawarar da ya bashi.

Kamar haWin baki duka shawararzu guda. Ya karSa. To dai ya karSa Win ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka.

A gida ma ?an uwa da su Zee anata murna da rawar jiki.

"Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa."

"To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4."

Daga cikin Waki Anti Zinatu ta Wago murya "to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saSon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi."

Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ?ya?yatawa.

***

Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa.

"Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta."

"Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna."

"Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ?an uwan juna bane?"

Tayi dariya "ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka Wauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane."

"Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min."

"Lokaci Waya mu ka yi da kai." Ta zolaye shi.

*

Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta Wauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba'u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la'ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login