Showing 69001 words to 72000 words out of 182745 words

Chapter 24 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

104

Sai ka faWa min inda maganar ?anwarka ta kwana tunda naji ance mahaifin amaryar Wan daudu ne."

A take fuskarsa ta canja da furucin Hajja. Ta kalli Amma da mamakinta ya fi na Anti.

"Kada ku ce min baku san Wan daudu bane baban nata?"

Amma ta kalli Taj tana neman ?arin bayani a tsorace.

?oye Soye dama can ba halinsa bane. Balle kuma yanzu da ya riga ya yi aure. In ya rufe yau anjima ko gobe magana za ta fito. Saboda haka a ta?aice ya labarta musu yana aiki da Abba da kuma abin da ya faru lokacin auren Sajida har zuwa jiyan.

"A ta?aice dai ba auren soyayya bane. Yarinya mai asali girSatacce irin wannan dama sai dai auren alfarma." Cewar Anti.

Hajja kuwa cewa tayi "kakarta ce kawai ta yanke sa?a. Wannan kishi da ita ma Sata lokaci ne Anisa. Kawai ki sa a ranki ke kaWai ce."

"A'a fa Hajja" Taj ya katse musu hanzari kafin a kai matakin da zai faWi ba?a.

"A'a me?"

"Ina sonta."

"Taj" Amma ta kira shi don ta san hali.

"Am serious Amma. Ina ro?onku don Allah kada a sake tada zancen mahaifinta ko yanayin auren. Nema nayi ba bani aka yi ba. Please" ya kallesu Waya bayan Waya.

For once sai jikin Hajja ya yi sanyi. Magiya Taj yake amma irin wadda mai yinta yake fata da tsananin burin samun biyan bu?ata.

Tashi Hajja tayi ba tare da tayi magana ba. Ta dai ?arewa Taj kallo sai taji babu adalci idan ta cigaba da sanya shi a kwana.

"Ina Wan uwanka Kamalu"

Taj ya dubeta girarsa a cure "yana gida."

"Idan ka koma ka ce ina nemansa. Shi sai ya zo su daidaita da Anisa idan bashi da wata."

"Hajja!!!"

Anisa, Taj da Anti su ka kirata lokaci guda. Ta taSe baki.

"Ku bar Hayatu da halinsa. Ban taSa ganin wanda Allah Ya azurta da iyali masu kyakkyawar mu'amala da Wabi'a kamar nasa ba. Shi yasa nake kwaWayin haWa zuri'a dashi ba wani abu ba."

Bata jira jin me za su ce ba ta fita. Anti ma fita tayi da niyyar yiwa Daddy magana. Bata maraba da tumbling Win ?arta da Hajja take yi. Ita ma Anisa bayansu ta bi. Sai dai kafin ta fita ta tsaya tayi masa magana.

"Allah Ya sanya alkhairi Ya Taj."

"Nagode Anisa. Kuma don Allah kada ya zama reason na lalacewar zumuncinmu."

"Tun farko dama kayi min bayani. Babu wani abu. Sai mun zo ganin amarya."

Da ya rage su biyu a falon Taj ya kalli Amma "that went well right?"

"I think so." Ta bashi amsa da fatan hakan ne.

Breakfast ta kawo musu. Bayan sun gama ya faWa mata komai ds komai da ya danganci Abba da aurensa.

"Yaron nan da a Wan daba ka tashi sai an wahala da kai. Banda rigima ka rasa ?ar wanda za ka auro sai Simagade? Kai yanzu ka yarda Yaya Hayatu ba zai kawo matsala a gaba ba?"

"Da Allah na dogara Amma. Bana son yin wannan tunanin saboda ban hango abin da zai rabani da Hamdi ba."

"Sunanta ya min daWi fa. Hamdiyya. ?azu da ka faWa har zan magana na kama bakina kafin Hajja ta zageni."

Cikin farincikin shiryawa da Amma ya bar gidan da yamma. Ta so ya kwana amma ya dage gara yaje hotel. Zaman nasa a ganinsa tamkar rashin kunya ne. Zai kyautu ya bawa mutanen gidan damar sake karSarsa idan ciwon abin da su ke tunanin laifi ne ya ragu.

***

A yau sha'anin biki ya ?are. Kakan Safwan ya wakilta masu Wauko amarya Sajida zuwa gidansa. Dama Umman Safwan Win bata da damuwa ko kaWan. Babansa ne baya so. Bayan koke koken amarya da ?an uwanta da kuma Yaya, gidan kakannin Safwan aka wuce da ita.

Tsohon nan ya yi musu nasiha sosai da jan kunne.

"Sai kun ji kon ?i ji. Ku gani kuma ku ?i gani sannan auren zai yi ?arko. Musamman gareki jikata" Sajida ta kalle shi da jan ido "duk wanda ya sami dama a dangin nan zai faWa miki magana son rai akan asalinki. Wannan ko ka hana wani sai ya yi. Saboda haka ki koyi kawar da kai. Inda ba za ki iya ba kuma ki kare martabar mahaifinki. Ina mai tabbatar miki da an kwana biyu zai bi jiki. Kowa zai ha?ura matu?ar kun zauna lafiya. Kun bawa maraWa kunya."

Safwan ne kaWai ya iya yi masa godiya. Sajida kuwa in banda sharar hawaye babu abin da take yi.

*

Ana can ana ?arasa guntattakin gyara a gidan amarya Zee ta fice daga Wakin da Hamdi take yiwa turaren wuta ta koma wajen gate ta kira Taj. Yamma ce li?is. Tana ta addu'ar samunsa a wayar. Tayi sa'a kuwa bugun farko ya Wauka. Sai kuma ya kashe ya kirata.

"Zee amarya."

Sake tsokanarta ya yi "to uwargida. Tun yanzu har an fara kishi kenan."

"Don Allah ka bari"

Yanayin muryarta ba yadda ya saba ji bane. Shi yasa bai ja wasan ba ya nemi ta sanar dashi dalilin kiran. Muryarta rawa ta fara, sai kuma ta kama kuka. A haka ta faWa masa maganganun da taji Abba yana faWawa Hamdi jiya ba tare da sun san ta biyo su ba.

Ashe tun shigowar Hamdi cikin gidan ta taso za ta tsokaneta akan me taje yi a waje sai taga Abba ya ja ta zuwa soro. Fuskarsa da ta gani da damuwa ita tayi sanadin binsu da tayi. Tana gama jin abin da ya ce tayi saurin komawa ciki.

Jijiyar kansa tashi tayi sosai. ?acin rai ya rufar masa. Ya rasa dalilin da yasa Alhaji yake yi masa haka.

"Ya Taj don Allah ka saketa ba sai tayi maka abin da zai Satawa Abbs suna ba."

"Yi shiru Zee. Maganar nan da wa kika yi bayan ni?"

"Babu kowa." Ta ja hanci.

"To don Allah ki yi min al?awarin ri?eta a ranki kin ji."

"Sakin fa?"

"Hamdi ta zo kenan. Idan ku ka yi wasa ma duk sai ta riga ku haihuwa."

Wayar ta cire daga kunnenta saboda kunyar kalamansa. Kamar ya sani ya ce

"Oh sorry, ?anwa ce fa ke."

"Idan tayi maka laifin da zai sa ka saketa fa?"

"Kada ki damu. Just focus on yourself. Ki gama karatunki ki kuma ri?e mutumcin aurenki. Ni da Hamdi in sha Allah anyi auren kenan."

"Tsoro nake ji kada babanka ya yiwa Abba wani abu."

"In sha Allah babu abin da zai faru. Ina son sister Winki. Zan kuma tsare mutumcinta da na duka family Winku."

Ya Wauki lokaci sosai wajen kwantar mata da hankali. Sannan ya yi mata godiya da ta tunkare shi da zancen. Wayar Kamal ya nema da su ka gama don ya faWa masa yaji a kashe. Ya yi Wan tsaki. Tun asuba fa Kamal ba yadda ya saba yake ba. Komai daina yi masa daWi yake saboda yana jin tamkar wani Sangare na jikinsa baya tare dashi.
Jirgin tara na safe ya yi booking ta waya kafin ya kwanta.

***

Hannuwa da ?afafunsa ya kalla hankalinsa ya sake tashi. A kumbure suke. Fuskarsa kuwa kamar an hura balloon. Magungunan jiya ya Wauko yayi ta dubawa ko akwai wanda ya sha ba daidai ba amma babu. Gabansa ya dinga faWuwa da tunanin me zai faru idan yanayinsa ya cigaba a haka. Babbar matsalarsa ma ita ce yadda zai samu ya bar gidan ba tare da kowa ya gan shi ba. Daga daren jiya zuwa yanzu ya fita hayyacinsa baki Waya. Wayarsa ya nema ya kunna domin magana da likitarsa sai yaji ana taSa ?ofar Wakinsa.

Hankalinsa ya sake tashi da ya kalli kansa a madubi.

"Waye?" Ya furta da Wan ?arfi.

Shiru yaji babu amsa. Sai zura mu?ullai da ake tayi a ?ofar. A gwaji na biyar aka buWe ?ofar Wakin wanda bai taSa zaton akwai spare key ba. Idanunsa da ?yar su ke buWuwa saboda hasken fitilun waje da su ka shigo.

"Abba? Bishir?"

Fitilar Wakinsa aka kunna gami da rufe ?ofar Wakin nasa.

"Kamal? Shaye shaye kake yi?"

A gigice ya Wago idanunsa da suke buWewa da ?yar saboda kumburi ya kalli wadda ke tsaye a kansa.

"Umma?"
RAYUWA DA GI?I 20


Batul Mamman=ؖ?




_Gaisuwa ta musamman ga baiwar Allah da ta tura sa?o OpenDiaries. Ina fata kin sami sau?i. Allah Ya inganta Ya raba lafiya. Abba Habibu Simagade yace a baki ha?uri ba niyyarsa kenan ba. Shafin yau naki ne._


Ina ?ara tunatar da masu karatu posts weekdays ne kawai don Allah. Nagode sosai. SonSo


***

Na Wan ta?in lokaci ?wa?walwarsa ta so ?ullewa har ma ya faWi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faWawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya Waga hannuwa da ?afafunsa yadda za ta gansu sosai.

"Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ?arasa inda yake tana tattaSa shi.

"Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai."

"Subhanallahi" ta matsa hannunsa na dama "akwai zafi?"

Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ?anzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba.

"Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?"

Gaban Kamal ya faWi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar Sangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono.

"Ita da take gynae? Wannan ba Sangarenta bane."

"Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani ba?i naga kayi."

"Kai Umma, idonki ne." Ya wayance.

Da ?yar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ?wararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti.

"Amma me ya sa ka Soye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ?waya ka fara sha."

Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba.

"Abin da ban yi da ?uruciya ba Umma?"

"Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri'ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin Sata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika."

Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sau?i ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ?arasa ya tura mata sa?o ta bashi amsa. Ro?onta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba.

Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ?arfinsa sun soma ?arewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce.

Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da ba?ar abaya da ?aramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai Wan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ?ibar ba mai yawa bace. ?akin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado.

Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce "Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ?araso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye."

"?an bamu wuri" ta ce idanunta akan Kamal. Patient Winta mai Wan banzan taurin kai.

Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu'ar a shawo kan matsalar da wuri.

Yana fita Mubina ta rufe ?ofar emergency Win ta shiga bawa Kamal taimakon da ya kamata. Kimanin minti talatin kafin jikin nasa ya fara daidaita. Ya buWe ido a hankali ya sauka cikin nata.

Ranta a Sace yake sosai. Kallon da tayi masa ya sanya shi murmushi. Ya aga hannunsa guda ba wanda take yi masa ?arin ruwa ba ya kama kunnensa.

"Sorry."

"Ya kake so nayi da kai? Ni a rayuwata babu abin da na tsana kamar Soye Soye."

Ya Wage gira Waya "a ta?aice dai kin tsaneni."

Shan kunu tayi "ban ce ba."

"Don Allah ki yi ha?uri." Ya tashi zaune "Zan iya tafiya?"

"Jikin naka..."

Sallama aka yi, kafin ta amsa Alhaji ya turo ?ofar ta buWe gabaWaya su ka shigo tare da Abba. Kai idan kaga fuskar shi sai ya baka tsoro. Hannuwan babbar rigarsa sun sauko amma yau ya manta da wani matsayi. ?ansa kawai yake son gani.

"Me ya same ka?" Ya kalli Dr. Mubina "Doctor me ya same shi?"

Kamal bai bari tayi magana ba don ya kula ganin Alhaji ya kiWima ta.

"Allergy ne Alhaji."

"Kai ne likitan?" Ya sake dubanta idanunsa na daWa firgita ta "ina jin ki."

"Allergy ne kamar yadda ya ce."

"To an gano mene ne jikin nasa baya so domin a kiyaye?"

"A'a, muna dai kan..."

KafaWarsa Alhaji ya ri?e "Kai tashi. Visar ina da ina gareka yanzu da ba su ?are ba?"

Mubina taga yadda bakinsa ya kasa tattaro amsa saboda sanin kafiyar Alhajin.

"Don Allah ka Wan ?ara mana lokaci Alhaji. Lifestyle changes muke ta gwadawa. In sha Allah a hankali zamu gane trigger Win."

"A hankali fa ki ka ce doctor. Jira zan yi har sai wani mummunan abu ya same shi?"

"Kayi ha?uri. Rashin bamu dama yana daga cikin abubuwan da ke sa a dinga ganin kamar bamu san aikinmu ba."

Yadda ta tare shi kai tsaye ta bashi wannan amsa sai ya sanya shi murmushi. Yana son mutane masu confidence.

"Ya sunanki ne?"

"Mubina...Mubina Sa'id Kibiya."

Fuskar Alhaji washewa tayi. Shi ne harda dariya irin tasu ta manya.

"Ikon Allah. Ke ?ar wajen Marigayi Dr. Sa'id ce?" Ta gyaWa kai a hankali "kai masha Allah. ?asar nan ba ?aramin rashi tayi ba. Arewa tayi rashin jajirtaccen likita. Allah Ya masa rahama."

Idanun Mubina da ?ar ?walla ta ce "amin."

Sakin jiki Alhaji ya yi su ka gama magana ya ce ya bata damar yiwa Kamal dukkan abin da ya dace domin samun sau?insa. Ya ?ara da cewa baya so ta sallame shi a yau. A kumbure gaSoSinsa su ke duk da a haka Abba ya ce wai ya saSe. Fita su ka yi da Abban zai raka shi. Kamal kuma Mubina ta ce lallai ya koma ya kwanta.

"Ai dole na. Idan na koma gida yau ba za mu ?are da daWi ba."

"Gaskiya yana son ka." Ta faWi tana murmushin yadda uban ya nuna kulawarsa akansa.

"Ai baki ga komai ba. Sai ?arsa na labour room ake gane waye Alhaji. Wallahi in dai ba baya gari ba da shi ake zaman asibiti daga lokacin da yaji an tafi haihuwar har a fito da baby."

"Kun ji daWi. Shi ne kake Soye masa halin da kake ciki?"

"Duk tsaurinsa yana da mugun rauni akan ?a?a. Sanin matsalata alhalin babu abin da zai iya yi min damunsa kawai zai yi."

Ha?ura Mubina tayi. Ta kula da indai izinin Kamal take jira babu wani cigaba da za a samu wajen binciken sama masa waraka. ZaSi guda ya rage mata. Za kuma tayi amfani dashi in sha Allahu.

Bata tashi ?ara sanin wane irin gida ya fito ba sai da taga matan gidansu da ?an uwansa suna ta tururuwar shigowa. ?akin ba ma zai Wauki rabinsu ba domin kuwa harda jikoki. Wannan yasa ta tunani akan hanyarta ta gida. Yanzu a ce duk yawan nan nasu babu wanda jininsa da na Kamal ya zo daidai?

***

Taj bai tashi sanin a asibiti Kamal ya kwana ba sai da safe. Da fari ya yi niyyar komawa gidan Amma domin su gaisa da Daddy. Sai ga wayar Naja tana sanar dashi labarin da ta samu daga gida. Ya duba wayarsa babu wanda ya kira shi. Jinjina kai ya yi ya Wauki jakarsa ya fita. Allah Ya taimake shi bai haWu da Sacin rana ba. Jirgin ya tashi akan lokaci. Kai tsaye asibitin ya wuce daga airport. Ya samu ana ta rikici a bakin ?ofa tsakanin wata nos da ?an uwansu mata. Ta tare ?ofar ta hana mutum biyar shiga. Na ciki su bakwai su ma tayi tayi sun ?i fitowa. Ana ?orafin sun yi yawa a Wakin, su kuma sun ce babu wanda ya isa yasa su fita daga wajen Wan uwansu.

"Ga wani ma nan ya shigo. Shi daga wani garin ma yake." Autar gidan ta faWi a tsiwace.

"To ko ma dai waye zuwa za ku yi ku fita. Idan ba haka ba zan sanar da na gaba dani. Doka ce ba a son a wuce mutum uku a Wakin mara lafiya." Nos Win ta ce da takaicin waWannan mutane. BakiWayansu kamar masu kan dutse. An rasa mai lallaSata ta ha?ura ko kuma yasa baki su fita.

Wata ma cewa tayi "ku sallame shi mana. Muma yayarmu likita ce. Allah na tuba don dai ?arin ruwa da allura wanne ne ba za ta iya ba?"

Ran Nos Winnan ya Saci matu?a. Idan an zo ita za a yiwa faWan barinsu a Wakin. Da taga Taj ne ma ta Wan saki rai. Ta san dai duk yadda za ayi namiji daban yake da mata.

"Kai ma Wan gidansu ne?"

Caraf wata mai tsohon ciki ta ce "Baki ga kama da mara lafiyan ba?"

"Don Allah ka faWa musu su ragu. A bakin aikina nake. In kowa bai min magana ba wallahi likitarsa sai tayi. Ta ce baya bu?atar hayaniya."

"Ya Taj barni da ita. So take ta nuna mana ta fi mu son Wan uwanmu. Ba fa surutu zamu yi ba."

Kamal ba jin an ambaci Taj ya yi hamdala. Shi ma sun ?i sauraronsa. Kansa har ya fara ciwo. A tunaninsu allergy Win ne shi yasa su ka dage. Basu san halin da yake ciki magana ma dauriya kawai yake yi ba.

"Happy. Don Allah kasa su bi dokar asibitin. Ni kaina doctor Win ba za ta barni ba idan ta gansu."

Nos dai tana jin sunan da aka kira Taj daga waje da wanda mara lafiyan nan ya kira shi, bata san lokacin da ta ce "Happy Taj? Kai ne mai HappyTaj don Allah?"

?an bani na iyan gidan Alh. Hayatu ne su ka amsa mata. Harda mai cewa da ta Wauka su Win local mutane ne take son wula?anta su.

"A bakin aikina nake." Ta nanata musu.

Da laluma da rarrashi Taj ya samu su ka bi tsarin asibitin. Da mutum bibbiyu aka dinga shiga ana fita. Nos Win tayi masa godiya bayan kowa ya tafi ta barshi ya shiga shi kaWai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login