Showing 135001 words to 138000 words out of 182745 words

Chapter 46 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

129

zamo abinta ta zauna. Taj ya shagala da kallonta ta nuna masa ledojin da ido.

"Ba za ki taimaka min ba?"

"Amarya nake. Yau Waya ina zaune kayi min komai."

"Burina ma kullum na taimaka miki." Ya wuce kitchen ya samo tray da kofuna.

Tana zaune ya buWe ledojin ya ajiye tray Win a tsakiyarsu. Akwai youghurt da juice, sai snacks irin su doughnut, croissant da pizza. Ga kwali madaidaici a ciki akwai cake da aka rubuta beautiful beginning Happy and Mrs Happy.

"Allah Sarki Happiness mai sona da gaskiya." Taj ya yi magana yana kallon Hamdi a kaikaice.

Ta gane da biyu yayi magana shi yasa ta ce "Wallahi kuwa, Allah dai ya ?aro aminci."

Taj ya yi ?wafa kawai ya buWe ledar gasashshiyar kaza da gurasa.

"Wanne za ki ci?"

"Mene ne wannan?" Ta nuna croissant Win.

"Abincin maza ne." Ya tsokaneta.

Yana rufe baki ta Wauka ta gutsira harda lumshe ido ta ce da daWi.

"Na ce miki na maza ne."

"Nima ai ta mazan ce"

Hamdi is just too cute. Yadda take maganar kaWai ya gama hargitsa masa tunani.

"Har mu nawa?"

"Ga Abbana, ga Halifa sannan..."

Ya zuba mata idanu. Dole taji kunya ta saki murmushi.

"Sannan kuma ga Happy nawa."

"Happy naki." Ya maimaita da murmushin jindaWin. Ture tray Win ya yi ya dawo kusa da ita kamar zai mayar da ita jikinsa ya ce "saboda Allah da gaske kike to akan maganar nan?"

"Da gaske nake."

"Amma in banda ke wa yake kama wani da laifin da ba nasa ba?" Ya marairaice mata.

Yadda komai tayi yake taSa masa zuciya bai san ita ma haka yake a wajenta ba.

HaSarta ta Wora akan tafin hannunta Waya tana kallonsa ta ce "Yanzu ya kake so ayi?"

Kalmomi neman Sace masa suka yi saboda har cikin zuciyarsa yake jinta.

"Stop acting all coy..."

"Meye coy?" Tambayar ma a yangance tayi ta.

Ba kuma wani abu bane yasa take yi masa haka sai don kada ya Wauki zafi akan shawarar da ta yankewa zamansu. Soyayyarsa tana jinta kamar da ita ta rayu. ?ata masa rai is the last thing on her mind. To amma me zai faru idan zama yayi zama sai kawai Alhaji ya yiwa Abbanta abin da zata ji ha?urinta ya ?are? Idan wataran ta kasa ri?e bakinta ta rama fa? Da wane ido za su kalli juna ita da Taj?

"Acting all lovey dovey,.. and shy...and bold, and...."

"This?" Hamdi ta sa?ala hannuwanta a wuyansa.

GabaWaya su ka tafi. Sai da ya kaita kan kafet Win. Fuskokinsu na kallon juna. Numfashinsu na gauraya sannan zu?atansu na bugawa lokaci guda.

"Hamdiyya"

"Taaajjj" sunansa ya fito da wani irin shau?i kwatankwacin yadda ya kirata.

"Duk abin da za ki yi, ki ji tsoron Allah kada ki Wauki alhakina."

Murmushi mai kama da dariya tayi "Ba zan Wauka ba."

Tausayi ya bata ta danno wuyansa ya ?ara yin ?asa. Ta Wago kanta a hankali su ka haWu. Bata sani ba ko don yau a gidansu suke babu fargabar da yake barinta da ita ta tunanin wani zai gansu. Sakin jiki tayi ta bari yana kissing Winta kamar ranar ya fara. Sai da zancen ya fara fin ?arfinta ta shiga neman ?watar kanta.

"Yunwa...yunwa nake ji Allah."

?arfin hali ya yi ya sake turo mata tray Win da su ka ture da ?afa. Kallon duk motsinta yake yi ta rufe ido.

"Ni gaskiya kunyarka nake ji. Ka daina kallona."

"Ji min gulma. Ki gama tumurmu..."

Hannu tasa ta toshe masa baki "ba ni bace."

Taj ya kama dariya "haka ne. Mrs Happy ce."

?in kallonsa tayi. Saboda kunyar da ta rufar mata bata san ta loda abinci da yawa a gabanta ba.

"Ni fa ba ci zanyi ba." Ya yi maganar yana bin gefen kunnenta da wuya da bakinsa.

"Nima na ?oshi." Ta matsar da tray Win. Abin da yake mata ya toshe duka senses Winta.

"Cikinki duk ya cushe ko? Tashi kawai muje mu kwanta." Ya tayar da ita jikinsa.

Harararsa tayi tana magana da shagwaSa "Amma dai a tarihin angwaye kai ne ka fara hana matarka cin abinci ranar da aka kawota. Duk labarin da nake ji tura musu abinci ake yi ko basa so."

"Cewa za ki yi duk na fi sauran son matata. Ba zan takuraki ba but I promise you komai dare ki ka ji yunwa ki tada ni. Zan kawo miki abinci."

Da gaske...ba a taSa cinye Taj da magana. Hankali kwance ya lauya zancen ya fitar da kansa.

Abincin da ba a ci ba kenan. ?akinta ya rakata wanda yake da ?ar tazara da nashi ta shiga wanka shi kuma ya koma falo. Yana kwashe abincin nasu yana rausaya. A fridge ya ajiye komai inda ba za su lalace ba. Ya Wauki robar youghurt Waya ya kai Wakin Hamdi da kofi sannan ya tafi nasa Wakin.

Youghurt Win ta fara sha tana mamakin yadda aka yi yunwar da take ji ta Sace. Ta gama shirinta tsaf yadda aka yi mata huWuba a gida. Sassanyan ?amshi yana tashi koina a jikinta. Ta kawo hijabinta har ?asa ta Wora akan rigar baccin da ta saka mai santsi wadda ta tsaya mata a gwiwa.

Taj ma nutsuwa ya yi ya gama shirin bacci sannan ya taho Wakinta. Wani abu ne ya bashi mamaki da yana shiryawar har ya kashe masa dukkan karsashi da Wokinsa.

Da ya saka kaya ya fesa turaruka da body spray sosai amma sam bai ji ?amshin ko guda ba. Ya Wauki turaren ya kara a hancinsa amma har lokacin babu. Ya koma toilet ya aga sabulunsa wanda yanzu da yana wanka yake sake yaba ?amshinsa sai yaji yanzu baya jin komai.

Zuciyarsa wani irin harbawa tayi. Yaje ya buWe fridge nan ma babu komai. Hankalinsa a tashe ya Wauki kwalin juice ya kafa kai don yana son jin sanyi a zuciyarsa. Sai dai me??? Harshensa kwata-kwata babu WanWano.



Afuwan =?O?=?O?=?O?
Its late, I know.
RAYUWA DA GI?I 32




Batul Mamman=ؖ?




This page is sponsored by NAFS-BEDDINGS (Nafisa Tofa 08034581454). A trusted and reliable plug for bedsheets and duvets. A trial is all it takes to get conviced. ?ar uwa a yar da Wan yagwalgwalin zanin gadon nan da ya gama tashi daga wanki Waya a sayi garanti!








*

Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daWi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daWi ba? Idan sun haWa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaWai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun Wazu shi ne a ransa?

Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taSa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a ma?era sai aka sameta a masa?a. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu.

Muryarta a tausashe ta ce "Wani abu ne ya faru?"

"Me ki ka gani?" Taj ya faWi yana mi?e ?afafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaWarta ya dawo da ita jikinsa.

"Babu komai tunda baka son faWa min."

"Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai."

"Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sau?i in sha Allah." Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faWa ya san bata yarda ba Win.

Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ?a??arfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah.

Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ?amshin Wakin da na jikin Hamdi sun cika ?ofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah.

Shi dai tunda yaji wannan ?amshin ya tashi da ?arfinsa ya sungumi Hamdi yana faWin Alhamdulillah.

"Wai don Allah me ya faru?"

Hancinsa ya Wora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce "its nothing" ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaWai.

***

Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faWawa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text Winsa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta

(Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.)

Bacci Sarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faWawa komai a hali na tashin hankali.

"Wallahi ba ya son Soye Soye. Goben nan ban san me zai yi min ba."

"Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faWa da wuri."

Wannan magana ?ara dagula mata lissafi tayi. Washegari a daddafe ta jira ?arfe bakwai da rabi tayi ta kama hanya ta tafi gida. Waya ta Wauka ta kira Alhaji. Yayi mamakin sammakonta.

"Idan kina da aikin safe ne ki wuce Kubra sai na same ki a office idan na shirya."

"A'a Alhaji. Na san akan abin da kake nemana. Babu aikin da zan iya idan baka fahimceni ba."

Katseta yayi da ya gane me take nufi.
"Jira ni a Wakin Kamal."

"To Alhaji. Kayi ha?uri don Allah." Ta faWi da rawar murya.

Ko amsata bai yi ba ya kashe wayarsa. Ya?i jinin ?umbiya ?umbiya. Shi yasa yake jan su a jiki tun basu da wayo. Ko fensir wannan bai yarda wani ya zo ya ce wane na bu?ata ba. Ya fi son ka je da kanka ka faWa.

"Ban faWa masa komai ba."
Kamal ya tabbatar mata da ta shiga Wakin.

"Nafi tunanin gaya min zai yi. Gara da na faWa masa gaskiya a waya don ban san yadda zanyi na fidda kaina a gabansa ba."

Sai bayan kimanin minti sha biyar Alhaji ya shigo tare da Bishir da Abba. Kana ganinsu ka san basu san me yake faruwa ba. Sun dai kama bakinsu tunda sun san koma mene ne yanza za su ji. Ita dai Yaya Kubra tana haWa ido da Alhaji ta sunkuyar da kai. Daga daren shekaranjiya zuwa yau ya faWa. Dakakkiyar shadda ce a jikin shi ruwan toka. Babbar rigar a ninke Abba ya rataya a hannunsa. Kwarjini iya kwarjini sai Alh. Hayatu.

Da kakkausar murya ya ce mata "Kin kyauta."

"Alhaji don Allah..." ta fara cewa tana zamowa daga kan gado.

"Ya isa." Ya zauna a inda ta tashi. Yaran nasa su ka zagaye shi a ?asa banda Kamal da ya hana motsawa daga kan kujera.

"Wace gudunmawa shirunki ya sama min?"

Iya bincikenta na ?an uwansu na kurkusa (gidansu Alhaji da Hajiya) ta sanar dashi. Abin al'ajabi cikinsu babu mai blood group AB(-). Ana bikin Taj ta tura musu survey link na google form inda ta bu?aci su cike da cewar research (bincike) ne take yi da ya shafi aikinta. A ciki tayi tambayar da mutum sai ya saka sunan dangin da ya fito. Ta haka ta rarrabe kowa.

"An sami masu rhesus negative mutum huWu."

Alhaji ran?wafowa yayi kamar da haka ne zai ji me za ta ce sosai.

"Biyu ba za su iya yi masa amfani ba domin Waya A ne, Wayar kuma B."

"Ina jin ki Kubra."

"Masu O negative biyu da za su iya taimaka masa, Waya Wiyar ?anwar Hajiya ce."

"Mata suna iya bayarwa ne?" Alhaji ya tambayeta hankalinsa a tashe. Bishir da Abba su ka sake shiga duhu.

"Eh, amma...amma da wuya a samu nata. Widad ce. Yaranta biyu tana da cikin na uku" Yaya Kubra ta faWi, ita ma kanta tana cikin jin ciwon hakan.

Kamal ya dube su. Irin wannan abin yake gudu.
"Alhaji don Allah..."

"Ka rufe bakinka Kamal" ya tsawatar masa. Ya juya ga Yaya Kubra "Sai wa kuma?"

"?an Widad Win na farko mai shekara biyar. Yayi ?an?anta."

"Wai me ake bu?ata ne Yaya Kubra?" Abba ya gaji da jin maganar da bai fahimta ba kuma yana ganin masu yinta cikin rashin nutsuwa.

"?oda ce Abba. Duka ?odojin Kamal ciwo ya cinye su." Alhaji ya bashi amsa da kansa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Abba da Bishir kuka su ka fashe dashi. Alhaji ko hanasu bai yi ba. Kowanne yana cewa a cire tashi. Da su ka ji ba da ka za a Wauka ba nan ma sun sake shiga tashin hankali. Kamal mai ciwon shi ya koma rarrashinsu.

"Amma fa ni ban gane ba. Me yasa masu A da B ba za su iya bashi ba, bayan kuma su ma Win negative ne? Jiya fa nayi ta bincike Kubra. A da B duka donors ne." Cewar Alhaji da sanyin jiki.

"Haka ne Alhaji. Mai B Win sickler ce."

Alhaji ya ce "Ita ma mace? Bana ma son a kai ga Waukar na mace. A Win fa?"

"?an Kawu Sayyadi ne (?anin Hajiya). Shi kaWai ne bayan mu nan wanda ya san da ciwon Kamal. Naje na same shi. Ban ko ro?a ba ya ce a shirye yake da aje a cire tasa. Shekaranjiya kafin naje wajen bikin test muka fara zuwa aka yi masa." Ta ja numfashi sannan ta ce "yana da Hepatitis."

"A ta?aice dai ...Ya Rabbi....Allah na" Alhaji ya danne ?irjinsa da ya kama wani irin ciwo.

Duka su ka rufar masa. Yaya Kubra ta tashi zata koma mota don motar likita ba ta rabuwa da kayan bada kulawar gaggawa.

"Dawo ki zauna." Alhaji ya tashi ya dafa kafaWar Kamal "akwai Allah kaji ko." Ya dubi Abba "ka haWa muku kaya kai da Kamal akwai jirgi gobe. Yanzu zan sa Ahmad ya sayi ticket ku tafi Saudiyya."

"Alhaji ni fa? Me zan yi?" Bishir ya tashi tsaye da zafin nama yana goge ?walla.

"Tare zamu bisu jibi da Ahmad. Bana son iyayenku su gane komai. Kawai zan ce musu Umra zamu ni da yarana maza."

"A nan za ku barni Alhaji?" Yaya Kubra ta soma sabon kuka.

"Kina da visa ne?" Da sauri da amsa cewa akwai "ki tattaro komai na asibitinsa a wajen Dr. Mubina jibin sai mu tafi. Ki san me za ki faWawa iyayenki tunda kin ?ware a rufa-rufa." Kai ta sunkuyar.

"Me zan faWawa Taj?" Kamal ya yi tambayar ga Alhaji.

"Zai yi zargin baka ha?ura ba shi yasa baka haWa da shi ba." Inji Bishir.

Alhaji wayarsa ya Wauko daga aljihun gaban rigarsa ya dubi lokaci. Yayi wuri ya kira mai sabon aure. Sai ya ce da Kamal,

"Ka faWa masa zamu je Umra amma ba da shi ba. Yaje ya yiwa matarsa passport a nemi visa a sanar dani sai su tafi daga baya."

Da ya fita ya kulle musu ?ofar Wakin sai ya sami damar barin zazzafar ?wallar da ya danne a gaban ?a?ansa saukowa. Sau Waya ya haWa ido da Kamal yaga yayi masa murmushi na wanda ya karSi ?addararsa hannu biyu.

"Ya Allah ban isa ba. Ba iyawata bace ta bani ?a?an nan. Allah nagodewa ni'imominKa gareni. Da rauni da gazawata na zo gareKa cikin ?an?antar da kai. Ka ceci rayuwar Wana Ya Ubangijina." Bayan shekaru masu Wimbin yawa ya sami kansa da fashewa da kuka mai ciwo da cin zuciya. Yana ?aunar ?a?ansa kamar rai. WaWanda ya rasa a Sari da biyu da su ka tafi da ?ananun shekaru har yau yana jin abin a ransa.

Tsayuwarsa ya yi a wajen yana neman nutsuwa amma idan ya tuna ha?uri irin na Kamal sai yaji zuciyarsa tana zafi. Duk gidan shi ne yafi kowa damunsa akan maganar Taj. A dalilinsa ya ha?ura ya bar iyalinsa suna mu'amala da Taj Win. Domin da fari niyarsa ya yanke shi daga jikinsa gabaWaya.

?ofar Wakin Yaya Kubra ta zo da shirin fita taji sautin da mahaifinta yake dannewa. Bata san lokacin da ta koma da baya ta Wora kukan ba. Abba da Bishir su ka kara kunnuwa su ka ji. Kowa ya koma ya zauna da kuka. Shi kuma ya koma ciki ya shige Waki ya rufe ?ofa.

"Magana ake ta Kamal yana da rai har yanzu. To me hwaru?" Kamal ya faWi yana dariya.

"Ni ban taSa tsanar wannan kalmar ba sai kamar yau." Abba ya sha kunu.

Yaya Kubra tayi murmushi "dole ka sako wasa kafin Taj yaji wannan maganar."

"Don Allah ki bar tayar min da hankali. Da me kike so in ji? Ciwon ko tararrabin abin da zai zo yayi?"

***

"Siyama kin tabbatar duk abin da Iyaa ta faWa min gaskiya ne?"

Yadda Baba Maje ya Wauki zafi sai da gaban Siyama ya faWi. Ta dai san cewa ba gulma ta kawo ba tunda cutar da mutum taji za ayi take son hanawa da ikon da Allah Ya bata.

"Da gaske ne Baba."

"Kirawo min Ummin"

Tashin muryar iyayen nata ne ya fito da ita daga Waki inda taji Baba Maje na rantsuwar sai ya karya Ummi. Iyaa kuma tana tare shi. Da ?yar ta samu ya nutsu shi ne ta ce masa,

"Taurin kai gareta ka sani. Idan baka bi komai a hankali ba wallahi ko me zai faru ba faWin gaskiya zata yi ba."

Bai daina faWan ba sai dai ya ha?ura da zancen zuwa ya tasheta da duka. Hankalin Siyama sai ya tashi shi ne ta fito yake tambayarta.

"Ita hayaniyar nan bata tasheta ba?" Ya faWi yana girgiza ?afa da kallon ?ofa.

"Yanzu zan taso maka ita. Amma don Allah ka bi komai a sannu."

?akin nasu Iyaa ta shiga ta taso Ummi. Har ta fara kiran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login