Showing 147001 words to 150000 words out of 182745 words

Chapter 50 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

124

kirana su ka yi mu ka gaisa."

"To kun gani ko..." Abba ya ce da murna.

Suna wannan hirar Halifa ya buWe passport Win Yaya yana gani.

"Laah Yaya wane irin blood group ne wannan O minus?"

Hamdi ta karSe ta kalla " ya kamata in Wan yi studying bambancin blood group Winnan. Nima anyi min test Winsa amma ban duba ba da shi da geno type."

"Da aka yi min sai da mutumin ya ce min wai jinina na musamman ne don yana wahala."

Zee da Halifa sai cewa su ka yi su ma Win za su je ayi musu. Daga wannan hirar Abba ya ce,

"Hamdi ki bamu numbar Kamal ta can, idan ta isa sai ta kira shi su gaisa."

"Idan bamu da nisa in je dai mu gaisa zai fi." Yaya ta faWi tana murmushi.
RAYUWA DA GI?I 35





Batul Mamman=ؖ?





***

Kwana biyu a ?irgen Hamdi tana lura da duk wani motsin Taj. Ta riga taji a jikinta tun randa ya koma Happy Taj bai dawo gidan da irin jovial spirit Win da ya fita dashi ba. Aura Winsa gabaWaya is down amma a zahiri babu wata alama ta ciwo. Ta tambaye shi me ya faru tun a lokacin ya nuna babu komai. Da dare kafin su kwanta ta sake maimaita tambayar sai ya shashantar da zancen.

Jiya ma haka aka yi, domin da ya dawo bai sake fita daga Waki ba. Ya ce mata mura yake ji tana neman kama shi. Tayi iya yinta ta rabu dashi. Haka su ka kwana kowa ya juyawa Wan uwansa baya. Sai da asuba da farka ne ta ganta tayi matashi da ?irjinsa ya rungumeta sosai. Shi kenan aka cigaba da ranar lafiya ?alau kafin ya fita. Da ya dawo

Yau dai yana fita ta kira Abba Habibu. Kunya ta so hanata tambaya. Tana ta juya zancen a zuci. Kamar ya sani sai ya Wauko maganar komawar Taj Win aiki.

"Ance maigidan naki ya soma fita ko?"

"Eh, ashe ba ku haWu ba." Ta amsa da sauri.

"Satin nan ban fita ba. Kin san yana ta matsa min da na ajiye aikin. Ni kuma ban saba zaman haka kawai ba. Na fahimci saboda yana aurenki kamar zai takura idan ina ?ar?ashinsa...duk da tun a baya bai taSa ci min fuska ba. Na rasa shawarar yankewa Hamdi."

Hamdi tayi murmushi "Abba indai ka san wani aikin za ka nema idan ka bar Happy Taj Win gara kayi zamanka."

"Ba za ki ji komai ba?"

Numfasawa tayi da rawar murya "ba zan ji ba. Wanda nayi a baya ma don Allah ka yafe min Abba."

Kafin ta karyar masa da zuciya har ya kai ga kasa Soye rauninsa ya ce "ba ki min komai ba. Har abada babu ri?o tsakani na daku in sha Allah. Allah Ya yi muku albarka."

"Amin Abbana" tayi maganar cikin farinciki.

Hira ce ta kankama tsakaninsu wadda duk akan tafiyar Yaya ce. Kafin su yi sallama ne ta daure tayi masa tambayar duk da gudun kada yaga rashin kunyarta.

"Abba wani abu yana faruwa a Happy Taj ne?"

"Me ki ka gani? Me ya faru?" Ya tambayeta da sauri kuma cikin tashin hankali. Ba komai ya janyo hakan ba sai lura da yayi yanzu kullum Baba Maje sai ya yi masa tambayar da ta shafi Happy Taj da kuma lafiyar Hamdi da Taj Win.

Amsar tasa ta ishe ta samun gamsuwa "Kullum idan ya dawo yanayinsa babu daWi. Na fahimci kamar daga can ne matsalar."

Wayancewa Abba Habibu yayi tunda bai san mene ne manufar tambayoyin Baba Maje ba. Shi yasa bai sanar da ita ba.

"Anya kuwa? Da wani abu ya faru zan ji. Amma ki bari zan tambaya."

Ta?aita zancen yayi cikin sauri da su ka gama wayar ya kira Waya daga cikin ma'aikatan kitchen Win Happy Taj. Babu wani Soye Soye ya ce ya faa masa abin da yake son ji. Yaron bai musu ba. Don ya ce dama sun yi niyar kiransa da kansu ma.

Labarin da yaji bai yi masa daWi ba. Kwana uku a jere girkin Taj ba ya ciwuwa. Duk abin da zai Wora sai an sami matsala. Haka nan indai ya taimaka musu da nasu aikin su ma ba ya tafiya daidai.

"Yau bai saka mana hannu a girki ba. Da za ayi serving wasu ba?i sake yin taro a ?aramin conference room wallahi Abba Habibu baka ga Sarin da yayi ba. Trolley (food trolley) Win gabaWaya ya kifar a gabansu."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yanzu yana ina?"

"Ya ce kwastoman ?arshe na fita mu tashi. Idan akwai sauran abinci a bayar."

Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ce "Nagode."

Allah Ya taimake shi Yaya bata nan. Ita da bata da son fita yau ta nemi Zee ta rakata unguwa...gidan Baba Maje ta tafi yi musu bangajiya na musamman duk da an riga anyi a waya. Ta sayi atamfa da shadda masu kyau da tsada za ta basu na kyautatawa.

***

"Wai ni ina Ummi ne? Ba za ta fito mu gaisa ba?"

Cewar Yaya bayan an sami kimanin awa gida suna hira da Iyaa. A ?ofar gidan daga cikin adaidaita su ka rabu da Zee don ta ce ba za ta shiga ba. Cikin gari gidan ?anwar kakansu ta gudu. Idan Yayan ta gama za ta dawo su tafi.

Iyaa ta numfasa "tun Wazu nake ta addu'ar kada ki yi cigiyarta."

"Allah Yasa lafiya. Indai ?alau take ba sai kin yi min bayani ba." Yaya ta faWi tana murmushi.

"Jinjin kenan. Kina da kawaici sosai. Yanzu idan na?i faWa miki ba za ki ji haushi ba?"

"Banda abin ki ai ba ayi ciki domin tuwo ba kaWai. Kuma idan bamu zama murfin sirrin ?a?anmu na farko ba to wa zai zama? Kada ki ji komai. Allah Ya dafa mana akan yaran nan kawai."

Daga bayansu su ka muryar Baba Maje "sirrin Ummi ba zai rufu ba saboda lokacin bankaWo shi ya yi."

Kallonsa Iyaa tayi tana girgiza kai. Duk lalacewar Ummi ba za ta so hakan ba. Ba kuma don tana goyon bayan abin da tayi ba. Ko kusa! Duk duniya ko Baba Maje bai kai ta son shiryuwar Ummi ba. Kuma ta yarda da Yaya Wari bisa Wari amma dole tayi kwaWayin sakayawa indai ba ya zama dole ba.

"Sakaya kan ki Habibu zai shigo."

Jin haka Yaya ta juya ba shiri ta kalle shi. Murmushi ya yi kawai mai tarin ma'anoni ya fita.

Me zai kawo Abba a wannan lokacin? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta kafin su shigo tare da Baba Maje.

Babu zancen gaishe gaishe. Kai tsaye Baba Maje ya soma magana.

"A waya kayi min tambayar me yasa kwanakin nan kullum sai na tuntuSeka game da lafiyar Hamdi da mijinta."

"Shi ne kuma za ka ce in zo gida na same ka?" Abba ya tambaye shi domin shi ma Win ya shiga duhu.

"Inda zamu je yafi kusa da nan shi yasa. Kafin mu tafi amma zan so sanin me ya ankarar da kai har kayi min tambayar. Na san don ina yawan tambayar lafiyarsu ba zai zama abin tuhuma ba."

"?warai kuwa. Sai dai keSe Hamdi ba tare da yawan bibiyar lafiyar su Sajida ba shi ne yasa da naji wata magana game da Taj na neme ka. Amma ka sani ban yi da wata mamufa ba sai son jin ko kana Soye min wani abu ne don kada na shiga damuwa."

Hankalin Iyaa sai yafi na Baba Maje tashi. So kawai take taji me yake faruwa da Taj Win. Abba Habibu ya faWa musu abin da yaji daga Hamdi da ma'aikacin Happy Taj.

Da yake Yaya akwai dauriya idan ka kalli fuskarta ba za ka fahimci yadda wannan zance ya kaWa ta ba. Iyaa kuwa kukan ba?inciki take yi. Wannan abin da yake faruwa akwai hannun Ummi. Wace uwa ce za ta yi alfahari da haka?

Baba Maje ya labarta musu rigimar da ta faru tsakanin Ummi da Salwa.
"Tun ranar babu wanda yaje a cikinmu. Rayuwar da ta zaSa ce take yi mata horo tun yanzu. Gara a barta da duniya ta koya mata hankali."

"Kada ka ce haka. Babu Wan da aka taba barwa duniya aka ga daidai. Kuma ita ma yanzu da ka ?yaleta idan ta haWu da waWanda su ka fita fitina fa?"

"Ummi ce fa! Babu wanda ya lalata ta sama da biyewa ruWin zuciyarta. Indai bata Sata Wan wani ba, to kuwa babu wanda zai Sata ta. Da kanta ta mayar da halayenta irin wanda mutane ke gudun yaransu su yi abota da ita."

Su huWu su ka rankaya police station Win da aka rufe su Ummi. Wani tsamurmurin Kofur ya fara yi musu surutu akan rashin zuwa tun ranar da aka kawo su. Baba Maje ya ce barinta yayi a ladabtar da ita. Kuma ko yanzu ba beli ya zo yi ba.

"?akin da muke tsaron nasu fa a cunkushe yake. Tunda rigima ce kawai ta mata za a iya baku su."

?auke kai daga gare shi Baba Maje yayi. Ya ce yana son ganin wanda ya dace domin a fito da Ummi su yi magana. Aka dangana su da ofishin DPO inda a nan ne aka fito musu da Ummi.

Kwanaki uku kacal!
Ummi ta zuge ta fita hayyacinta. Babu wanka babu wanki. Kayan jikinta kamar tsummokara. Kumatunta sun yi shatin hawaye dabbara dabbara. GabaWayanta babu kyawun gani. Haka ta ?araso gabansu tana Wingishi. Wananda su ka tarar a cell Winsu sun yi musu duka ita da Salwa.

Kamar haWin baki. Babu wanda ya nuna damuwa akan ciwukanta. A gaban DPO Win dai Baba Maje ya Wauko zancen Taj.

"Ki faWa min gaskiya Ummi. Me ki ka yiwa mijin Hamdi har ya fara fuskantar irin waWannan matsaloli daga komawa aiki?"

Allah Ya sani ta gaji da wajen nan don haka ba za ta wahalar da kanta wurin Soye Soye ba. Abin gudun ya riga ya faru. Kwana uku babu baccin kirki, ta fannin abinci ma sai addu'a. Wurin zagayawa kuwa tun tana amai har ta daina. Gashi don bala'i cikinta ya rasa lokacin lalacewa sai a nan. Bugu da ?ari ?an cell Win nasu sun Wora mata karan tsana. Daga ita har Salwa sun daku amma nata yafi yawa saboda ita ce mai ramawa da farko.

"Salwa ce ba ni ba."

"Wace ce Salwa?"

Kofur Win Wazu ya ce "ita ce aka kawo su nan tare. Ace ?ar mutum tana sakaye amma bai san ma ita da waye ba sannan babu waiwaye."

Fuska a haWe DPO ya kalle shi ya ce "Kofur ?anliti yaya haka ne? Me ma kake yi a nan?"

"YallaSai wasu iyayen ne sam ba sa gane illar barin ?a?ansu mata a station."

"Kai dai naka ?a?an suna gida ko?" DPO ya ce a harzu?e.

"La shakka."

"To jeka ka kawo Salwa Win ka kama gabanka."

Wani sassanyan murmushi Kofur ?anliti ya yiwa Ummi da zai fita. Harda cewa ta kwantar da hankalinta. Yanzu gaskiya za ta yi halinta. ?ila ma a yau ta sami damar tafiya.

Tsawar da DPO ya daka masa ce tasa shi gaggawar fita yana ?ananun surutai akan ?ulle mutane ba bisa ha??i ba. Ita kuwa Ummi wata muguwar harara ta galla masa da ya juya. Tun zuwansu yake ta rawar ?afa a kanta. Matan da suka yi mata duka ma ya so basu horo irin yadda ake yiwa masu laifi saidai yana ganin shugabarsu ya fita yana Allah Ya isa. Matar regular ce kuma tantiriya. A tsaye ta fishi nesa ba kusa ba.

Ba a jima ba su ka shigo da Salwa. Ta tsaya musu ?erere tana harararsu. Ta gane iyayen Hamdi ta kuma gane iyayen Ummi daga kamanninsu.

"Dur?usa" Kofur ?anladi ya ce da tsawa saboda haushinta da yake ji.

DPO kai ya girgiza kawai don ya Wago shi ya ce Ummi ta maimaita abin da ta ce. Nan kuwa ta nuna sam bata san komai akan Taj ba. Salwa ke son shi kuma ita ce tayi masa asiri.

"Lallai ma. To a ina na samo turaren? Ba ke bace ki ka bani?" Salwa ta kalli DPO "Wallahi cewa tayi idan na shafa masa zai saki Hamdi ya aure ni."

"To yanzu me ya haWa ku faWa?"

Salwa ta ce tayi amfani da turaren yadda aka ce amma Taj wula?anta ta ma yayi fiye da yadda yake yi a baya.

"Ummi har kin san bin bokaye kuma?" Iyaa ta fashe da kuka.

"Nima bani aka yi Iyaa. Don Allah ku tafi dani gida."

Ba a wani sha wahala ba ta faWi cewa Alh. Usaini ne ya bata. Kuma a zahiri ga abin da ya ce mata zai faru da Taj saSanin yadda su ka faWawa Salwa.

"Aikin ku nayi muku kenan? Kin san mutanen da na rabu dasu saboda tunanin zan sami Taj?" Salwa tayi kan Ummi cikin Sacin rai.

Kofur ?anliti yayi saurin anjige ta kafin ta cakumi Ummi ta faWi a ?asa. Abba Habibu da Yaya sun ga ikon Allah. Bayan Ummi ta kwatanta inda za a sami Alh. Usaini. Ta tabbatar musu da cewa akwai chats Winsu harma da recording Win wayoyinsu a wayarta.

"Damma kin shiryawa rana irin wannan ne?"

"A'a, na dai kula idan muka gama chatting yana bin duka abin da ya turo ya goge. Shi yasa na soma yin screenshot saboda kada a gaba wani abu ya faru ya zame ya barni."

"Allah ma Ya sa kina da wayonki. Irinsu haka su ke amfani da marasa wayo su cuce su."

Ayyanawa Ummi tayi a ranta cewa indai Kofur ?anliti yayi gigin cewa yana sonta, za ta nuna masa rashin mutumcin da zai jima yana yi masa ciwo. Idan ba karambani ba ai shi ma daga gani ya san su ba sa'annin juna ba. Duka duka bai fi rabinta ba a faWi. Tsayi kuwa ba zai wuceta ba.

Gida Abba Habibu ya bu?aci Yaya ta koma tunda kawo Alh. Usaini zai Wauki lokaci. Babu musu ta tashi. Jikinta yayi matu?ar sanyi. Ka haifi a ya zama silar zubar mutumcin mutum babu ruwansa da gazawar tarbiyya. Wani duk ?o?arin iyayensa sai ya janyo musu magana hankalinsa yake kwanciya.

Baba Maje ma ya ce Iyaa ta tafi ta nuna zama za ta yi. So take taji ?arshen wannan abu da Ummi ta zama sakarya wajen jagosarsa.

Minti ashirin bayan tafiyar Yaya sannan aka zo da Alh. Usaini. Tun a waje yake ta bala'i da zage zage. Da yaga Ummi sai ya taSe baki.

"Kina da shaidar nunawa kice da hannuna?" Ya kalli Salwa "ke kin sanni ne?"

"Kaga ka ajiye wannan surutun zai amfane ka a kotu."in ji DPO

"Kotu??" Salwa da Ummi su ka maimaita cikin tashin hankali.

"?warai kuwa. Kafin lokacin muna bu?atar shi Taj Win a nan."

Ranar har dare suna station dai. Taj da Hamdi su ka zo aka maimaita komai. Ya dubi Alh. Usaini ya ce masa da shi da su Salwa duk ya yafe musu ya juya ya fita. Fitarsu ke da wuya mahaifin Alh. Usaini ya je. Bayan ya gama zagi da ci masa mutumci a gaban mutane yace ba zai bashi shugabancin komai cikin kadarorinsa ba. Gado ma ba don Allah ne Yayi da Kansa ba tabbas da ya ce ba zai gaje shi ba. A ?arshe ya fice. Su Baba Maje ma su ka kama gabansu. Abba Habibu ne ya karSi Ummi albarkacin iyayenta. Salwa ma an saketa amma ko da ta fito ta rasa inda za ta tafi.

***

Da Hamdi ta shiga Waki a kwance ta sami Taj amma ya juya mata baya. A hankali ta lallaSa ta hau gadon ta kwanta a bayansa. Hannunta Waya ta zura ta ?ar?ashin jikinsa, Wayan kuma ta gaba ta haWe su ta rungume shi.

"Kuka kake yi ne?"

"Tsokana ta ma kike yi?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba.

"?orafi dai na zo yi. Ta yaya zan aureka kuma ace safe, rana da dare duk ni ce a kitchen. Gaskiya da sake."

Tashin da bai yi niyya ba yayi.
"Kin manta halin da nake ciki ko kuwa da gaske tsokanar ce?"

Hamdi ta ce "Ka faWa min damuwarka ne? Ba da kaina na nemo amsar ba?"

"Da ki ka nemo ba ki ji tausayina ba?"

"Girkin ne ba za ka tayani ba kake tada zancen?" Ta kyaSe fuska.

Taj ya ri?e baki da yaga da gaske idanunta suna neman zubo da ?walla "Abu ya same ni amma saboda ?arfin hali ke ce da Sata rai da shirin kuka?"

"Na fi ka shiga tashin hankali. Ka da aka mana aure hancin ka da baki duk suna aiki. Yanzu da haka ta faru sai anyi min cikon sadaki." Tayi kicin kicin da fuska.

Taj bai san lokacin da ya soma dariya ba "cikon sadaki fa kika ce?"

Ta goge ?wallar ?arya "Eh mana. Na baka tausayi ko?"

"Ha??un."

"Zan iya yafewa in za ka yarda ka fito daga Wakin nan mu shiga kitchen."

"Hamdi..."

"I'll be your nose" ta tsaya akan gwiyoyinta akan gadon ta goga hancinta da nasa "and your tongue." Ta rataya hannuwanta a wuyansa ta sumbace shi "I'll be you har ka sami lafiya."

?an?ameta Taj yayi. Ta dage ta ?i barin raunin zuciyarta ya bayyana balle tayi kukan da take ta dannewa.

"I love you."

"Me too" ta faWi har lokacin wuyanta na kafaWarsa.

A ranar bata yarda sun sake komawa wannan zancen ba. Sai ma mitar da take yi wai ta rasa sunan da za ta dinga kiransa. Ya Taj Win da take jindaWin faWa shi taji Salwa na kiransa dashi. Yana dariya ya ce

"Ki kirani Malam kawai?"

Ita ma dariyar tayi ta ce "Happy ya ishe ni. "

***

Washegari Taj yaje gida ya faWawa su Inna abin da ya faru. Da Salwa ta san illar baki da bata janyowa kanta abin da zai sa ta shiga bakin mutane ba. Hajiya bata yi ?asa a gwiwa ba ta kira Alhaji ta faWa masa. Hankalinsa ya sake tashi fiye da baya. Bayan sun gama jajantawa juna ya kira sauran matansa. Sun jima suna magana da Inna yana kwantar mata da hankali. Ya ce su dage da yin addu'a. Shi kuma zai san yadda yayi da Alh. Usaini. Yadda su ka ?ulla abin su za su kwance in sha Allah.

"Kun sa ranar dawowa ne?"

"A'a. Za mu yi magana daga baya."

Ajiye wayar yayi yana ta juyayin abubuwa. Case Win Taj da Kamal ba Waya bane amma a ?alla mahaifiyar Taj ta san abin da ya shafi Wanta. Addu'arta tana kai masa. Hajiya fa? Ta ina zai fara? Duk da haka dole ta sani zuciyarsa ta faWa masa.

Kamar haWin baki a daren ranar Yaya Hajiyayye ta kira shi tana tambayar saura kwana nawa su dawo.

"Mene ne?"

"Alfarma zan ro?a ku ?ara lokaci. Nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login