Showing 144001 words to 147000 words out of 182745 words

Chapter 49 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

132

da Firdaus suna ?us?us. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar.

"Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaWai ce ban san da tafiyar ba?"

"Bana son jin kowa na faWin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani." Taj ya faWa da damuwa a tare da shi "kamar wani abu ake Soyewa."

"Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai Soye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta."

"Amma ta kasa faWa a Home group?"

Waya Yaya Hajiyayye ta Wauko ta dubi Taj "zan yi sanarwa yanzu. Duk mai ?an matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su."

"Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa."

"Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?" Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son Sata lokaci idan aka ce za ayi abu.

Taj ya bata amsa da cewa "Alfarma na nema" yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu.

Basu gama hirar ba Salwa ta ?wan?wasa ?ofa. Taj ya tashi zai buWe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen.

Ita kuwa Firdaus hannun ?ofar ta kama da murnarta tana cewa "Ko ?an gidanmu ne?"

Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taSa ganinta da ita ba.

"Anti Salwa ke kaWai? Ina Anti Zahra da su Hayat?"

"Ni kaWai ce. Ya Taj yana nan?"

"Eh, shigo ciki."

?amshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita.

"Ya Taj ina wuni?" Tayi magana da wata zu?a??iyar murya.

"Lafiya ?alau."

"Ka ganni sai yau ko?"

Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce "mun yi dake za ki zo ne?"

Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce "Noooo, I thought you want to see me. Miss me?"

"Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba." Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara "akwai wani abu a tsakaninku ne?"

Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri.
"Me ki ka gani?"

"Me ta zo yi gidanka a haka?" Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ?asa.

Danne Sacin ranta tayi ta Wauke kai ta dubi Taj.

"Ya Taj a ina za mu yi magana?"

Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ?ofar kitchen Win inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faWa mata ba?uwar da aka yi.

"Ga hanyar Wakinsa can ku je can ku yi."

"Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa." Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara.

Zuciyar Hamdi kamar ta fashe ta juya za ta bar wajen Taj ya dam?o hannunta. Ta ja za ta fizge ya janyota gabaWaya jikinsa yayi mata wata irin kyakkyawar runguma a gabansu. Ta kuwa fashe da kukan da Anti Labiba ta faWa mata a gida ana yiwa miji. Da gatanki da tarin soyayya a zuciyarsa ake yinsa don kawai an isa. Kissa adon mata! Da aka faWa tayi zaton shegantaka ce za ta sa mace kuka babu duka ba zagi daga miji. Ashe ba haka bane. Shi ma kukan yana sanin lokacin zuwansa yayi.

Tayi nasara fiye da tunani. Taj ya shiga tashin hankali sosai. Bayanta kawai yake shafawa yana faWa mata kalaman kwantar da hankali.

Wannan abu ya tayar da hankalin Salwa fiye da ?ima. Me yake faruwa ne? Ya dace zuwa yanzu hankalin Taj ya koma gareta. Ko zuwan nan, tayi ne don son ganin rigimar da take sa ran sun fara.

"Ya Taj..." shiru bai waigo ba, yadda ka san Hamdi ce kaWai a duniya. ?irjinta ya kama hawa da sauka cikin kiWima ta ce "magana nake fa."

"Kana ji tana kiranka. Ni gidanmu zani. Da na sani ban..." Hamdi ta soma faWi cikin kuka.

Yaya Hajiyayye ta hanata ?arasawa da cewa "Hamdiyya ki yi ha?uri kinji ko. Taj ya ci albarkacina kada ki yarda ki Waga masa hankali akan Salwa. ?a na Wauke ki ba matar ?ani ba. In har na isa to don Allah ki barni da ita."

Hamdi ta Waga kai ta ture Taj da ta farga da yadda su ke ta ce "Kin isa Yaya. Wallahi kin isa."

"Salwa baki da lafiya ne ko me? Haka kike dama ko kuwa wani abu ne ya same ki?" Yaya Hajiyayye tayi tambayar tana kallon ta.

Kasa magana tayi. Idanunta na bin Hamdi da kallon tsana. At the same time tana jifan Taj da nasa salon kallon na bege. Ta kasa gane ya aka haihu a ragaya. Yardar da tayi da aikin yasa bata kawo haka zai iya faruwa ba. A karo na uku dai ta sake gwada sa'arta ta gani ko akwai dama.

"Ka bani minti biyar mu yi magana Ya Taj. Wurinka na zo don Allah."

HaSa Yaya Hajiyayye ta kama tsabar mamakin wannan ?arfin hali. Muryarta a kausashe kuwa ta ce,

"Wuce ciki da matarka yanzun nan." Ta dubi Firdaus "koma kitchen ki kula da girkin." Sannan ta dawo da dubanta ga Salwa "ke kuma kama gabanki yanzun nan kafin in gwada miki ni wace ce."

"Allah na tuba sani kuma na nawa zan yi miki Yaya Hajiyayye? Kishiya ta hanaki zama a gidanki na farko. Alhajinku ya ?a?aba wa yaronsa ke aka haifi waWannan" Salwa ta nuna Firdaus tana yatsina fuska.

Wani kukan kura Firdaus tayi, tayi kan Salwa. Kafin ta kai mata duka Hamdi ta ri?eta da iya ?arfinta. Firdaus na ?o?arin ?wacewa Taj ya Waga hannu zai kai mata mari shi ma Yaya Hajiyayye ta ri?e nasa hannun.

"Jinin Alh. Hayatu da dukan mace? Allah Ya kiyaye."

Maganarta ta farko yaji ta jan hannun Hamdi domin su bar falon. Zamansa tabbas zai janyowa gidansu abin faWa. Da Firdaus ya haWa su ka shiga Wakin Hamdi ya ce su zauna shi kuma ya sake fitowa. Daidai lokacin Yaya Hajiyayye tana yiwa Salwa magana.

"Ki tafi gida Salwa. Wannan abin da kike yi ba zai taSa baki abin da ki ke nema a mutumce ba."

Taj gaban Salwa ya ?arasa ya tsaya fuskarsa a murtuke
"Salwa na taSa cewa ina son ki?"

Shiru tayi. Zuciyarta cike taf da uwar kunya sai dai son zuciya ya riga yaci ?arfinta. Sunanta kawai da ya kira sau da ya saukar mata da kasala da ?arin son sa.

"Tunda baki da amsa to ina ro?onki this should realy be the last time. Ina raga miki ne kawai saboda Yaya Ahmad."

'Ko dai shafa masa turaren zan yi in kuma yi masa magana a lokacin?' Salwa ta raya a ranta. Wanda yake hannunta da ta shafa a bakin ?ofar falon ta duba ta hanyar mitstsika yatsunta. Tana Waga hannuwa ita kuma Yaya Hajiyayye tayi tunanin rungumarsa za ta yi shi yasa tayi saurin shiga tsakani ta tsinketa da mari tasss. Kunnuwan Salwa sai da su ka Wauke wuta na wucin gadi.

"Ke jakar ina ce kike ?o?arin rungumar baligin namiji mai aure?"

Caraf maganar a kunnuwan Hamdi. Ta yun?ura za ta tashi Firdaus ta ce ko ta fita kada ta saka baki.

"Ki barta da Mama. Wallahi yau ko me take ji dashi ta tara ta samu."

Hannuwa duka biyu ri?e da kumatu su ka sameta. Taj ya kasa kallonta. Zama kawai yayi ya dafe kansa.

"Bata da lafiya Yaya Hajiyayye. Wannan ba abin da mai lafiyayyar ?wa?walwa zai yi bane."

"Babu wani hauka a tare da ita. A nono ta zu?a kuma in sha Allahu gidanmu nan gani nan bari."

Tana rufe bakinta ta dannawa Ahmad kira.

"Yaya please zan kira ki anjima kaWan..." rashin samun Salwa a waya ne ya kiWima shi. Ya rasa wa zai kira ya tafi asibitin. Mami da danginta amma tamkar wadda ta faWo ita kaWai saboda ba?in halinta ya kori kowa.

"Ai koma mene ne uzurin indai ba sallah bace to ka saurare ni. Batun wannan yarinyar ne Salwa..."

Katse ta yayi da saurin sa "gidan ki ta zo?"

"Ina fa. Gata a gidan Taj."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yaya Hajiyayye tun Wazu nake kiranta ina nemanta." Ya ce a sanyaye gwanin ban tausayi.

"Ta ina za ta Wauka bayan ta fito yawon zubar da mutumci?"

A tsiwace Salwa ta ce "ni da aure nake son shi ba..."

"Rufe bakin ki" Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da zuciyarta ta kaWa. Firdaus kuwa ta san halin mahaifiyarta dama. Akwai ban dariya da iya zolaya amma kada ka shiga huruminta. Yanzun nan za ta birkice.

"Kana ji na Ahmad? Albarkacin ka zan sassauta mata. Amma lallai ka ja mata kunne. Idan ma hauka ne to tayi a wani wajen."

Bai ji daWi ba amma kuma bai ji haushin yayar tasa ba saboda ya san gaskiya ce take faWa. Kuma Salwa ce ta jawo wa kanta
"?alau take wallahi. Tsabar son zuciya ne da rashin tawakkali. Idan tana da zuciya ko aurenta ya ce zai yi ai ta ce bata so a yanzu. Saka ni a speaker"

Yaya Hajiyayye ta saka. Ahmad ya kalli inda Kamal yake kwance ya ?ara jin nauyi a zuciyarsa. Ga damuwar gaske amma haka kawai Salwa tana tayar masa da hankali.

"Idan kin fita ki koma asibiti ko ki wuce gidan ubanki kin ji ko. Na gaji. Ba ni na haife ki ba saboda haka ba za ki saka min hawan jini ba. Duk abin da ki ka zaSarwa kan ki daga yau ya rage naki. Kada ki yarda ki koma gidana."

Bai jira jin ta bakin kowa ba ya katse call Win. Salwa ta bi su da kallo WaiWai. Ta muzanta ajin ?arshe. Haka ta mi?e ta yi ?wafa da ?arfi ta fita.

"?ar banzar yarinya. A dalilin ki yau har rungume rungumen ango da amarya sai da na gani." Yaya Hajiyayye ta cigaba da mita.

Taj ya kama dariya. Hamdi kuwa hanyar Waki ta nufa, Firdaus na yi mata dariya. A lokaci guda falon ya mamaye da ?aurin girkin da ya rasa kulawar waWanda su ka Wora shi. Su huWun dake falo a tare su ka yi hanyar kitchen Win.

***

Tsinuwa da zagi da mummunar addu'a babu irin wanda Salwa bata yiwa Ummi ba da ta fito. Ta tari adaidaita sahu amma ta rasa ina za ta ce ya kaita. Sai da ya yi shirin tafiya tayi saurin faWin sunan unguwar da za ta. Suna tafe a hanya tayi mamaki ?warai da ta gane gidan. Sau Waya ta taSa biyo Ummi a baya bayan sun tashi daga wata haWuwa da su ka yi kafin bikin su Hamdi.

Zuciya tana ta ingiza ta. Ba?inciki da Sacin ran da take ciki ya yi yawa. Da ta ?wan?wasa ?ofa Siyama ce ta buWe.

"Ummi nake nema."

"Wa zan ce mata?" Siyama ta tambaya a tsorace. Fuskar Salwa abin tsoro. Kana ganinta ka san ba da alkhairi ta zo ba.

Daga tambayar Salwa ta gane Ummi tana ciki. Bata Sata lokaci ba ta hankaWe Siyama gefe ta faWa cikin gidan tana ?wala kira.

"Ummi. Ummi. Ummi..."

A firgice Ummi ta fito daga Wakin Iyaa inda aka saka ta gyaran wardrobe. Gabanta ya faWi da ta tabbatar Salwa ce ba muryar ke mata gizo ba.

"Me ya kawo ki gidan mu? Wa ma ya nuna miki?" Ummi ta ja hannunta su ka koma ?ofar gida.

Iyaa da Baba Maje fitowa su ka yi daga Wakinsa da Baballe inda su ke tattaunawa akan ginin gidansa inda Zee za ta tare. Wajen su ka je amma Ummi da Salwa basu ankare da su ba.

Salwa ta cakumi wuyan Ummi "Ni za ki ha'inta? Turaren da ku ka bani dama ba wanda zai sa Ya Taj ya saki wannan ?ar Wan daudun bane ya aure ni?"

Tsohuwar bully an saba dambe. Ummi mantawa tayi da inda take ta doke hannun Salwa ita ma ta ri?e mata wuyan riga.

"Banza a banza...duk soyayyar da za a siya da asiri wallahi na raina ta. Turare kuma ba na kashe aure bane."

Don ba?in ciki Salwa harda kuka ta ce "Na mene ne? Me ku ka sa nayi?"

"Ummi..."

Iyaa ta fara kiranta horrified da jin abin da su ke cewa. Sai dai da wuri Baba Maje ya yi mata nuni da tayi shiru. Abin kunya har mutane sun fara taruwa.

"Ki jira ki gani amma tabbas soyayyarsa ba ta ciki."

"Wani aikin ku ka saka ni?"

"Alh. Usaini dai ya saka ki. Ni mene ne nawa a ciki?"

Cikin karaji Salwa ta ce "Waye Alh. Usaini? Me nayi Ummi? Turaren mene ne?"

"Turaren kassara sana'ar mijin Hamdi." Ta amsa mata da yanayin tsokana.

Ai tana rufe baki Salwa ta daddage ta kai mata wawura. Kan kace meye wannan dambe ya kacame a tsakaninsu. Duka harda yaga riguna a gaban mutane. Iyaa hawaye kawai take zubarwa. Baba Maje kuwa cikin gida ya koma yana mai jin kunyar abin da ?arsa tayi na zubar musu da mutumci. Baballe duk zafinsa akan Ummi shi ma komawa yayi yana mai jan hannun Siyama. ?an unguwa su ka yi ?o?arin rabasu abu yaci tura. Wani kawai sai ya kira ?an sanda. Daga cikin gidan su ka ji jiniyar motar. Baba Maje ya ce kada wanda ya fita.

Aka tattara su sai Police station. Nambar Baba Maje Ummi ta bayar. Da aka kira shi akan case Win ya ce zai zo. Suna gama magana ya kashe wayarsa gabaWaya. Ya kuma ce da su iyalinsa kada wanda ya amsa kiran ba?uwar namba. Ummi ta zauna ta koyi hankali.

Salwa ta fi Ummi tsurewa. Kwana a nan abu ne da ba za ta iya ba. Gashi ita Win mai laifi ce. Ta kasa bada numbar Zahra saboda gudun tashin hankalin da za su yi da Ahmad. Garin Kano cike yake da dangin Mami, yau ga ranarsu amma babu wanda za ta iya kira kai tsaye saboda ba ayi mu'amalar arzi?i ba. ?arshe nambar babanta ta bayar. Aka kira shi sau biyar baya kusa bai Wauka ba.

"Tunda baku da kowa mu bamu rasa masaukin ba?i. A wuce dasu su shiga su huta." Cewar DPO ya na barin inda su ke.

Hankali a tashe Salwa ta ce "Don Allah ka sa a sake kiran Babana. Ni wallahi ba zan iya kwana a nan ba."

Ummi kuwa ko gezau. Bata shaida ta shiga one chance ba sai da aka haWa su cell Waya da wasu yan daban mata. Ashe damben su da Salwa wasa ne. Irin dukan da aka yi musu a cell in ya ?azanta. Babu wadda jikinta bai amsa ba. Kafin wani lokaci kowacce fa kama kukan gaske.

***

Saboda yawan kiran waya sai da kunnen Ahmad ya yi zafi. Duk wasu ?an uwa Mami na kusa da na nesa ya dinga kira yana neman taimakonsu akan kula da itaa asibiti. Duk wanda ya kira suna yabon yadda ya kiyaye zumunci amma kowa da irin labarin cin kashin da Mami tayi masa a baya. Bottom line dai babu mai zuwa. Ya shiga damuwa sosai. Kamar ya faWawa Alhaji sai dai yana tsoron me zai faru. DaWin daWawa ga Kamal a kwance sai na'u'rori. Kansa ya ?ulle.

Lokaci guda wata shawara ta zo masa. Ya kira likitan Mami ya ce a bashi Nos guda da za ta zauna da Mami tsahon sati Waya kafin ya dawo. Zai biya ko nawa ne. Aka tsadance ya tura kuWin a take su kuma su ka tura wadda za ta iya Wakin. Sai lokacin ya sami nutsuwa ya kira Baban Salwa ya tambayi ko ta koma.

"Bata dawo ba amma zan kira ta. Ina so ka zare hannunka a kanta. Zan yi maganin abin da kaina."

***

Kwanaki huWu bayan nan Taj ya shirya zai koma Happy Taj. Hamdi ta dasa masa rigima kala kala. Rarrashi iri daban daban yayi mata. ?arshe ba shi ya fita ba sai ?arfe goma da minti kusan arba'in. Ya fara kaita gida saboda suna sa ran tafiyar Yaya ta samu nan da kwana biyar. Yana zuwa yaran kitchen Winsa su ka ce yau gwaji za su yi masa su tabbatar aure bai mantar dashi girki ba.

"Kada daWin abincin amarya yasa ka manta naka."

Kowa yayi dariya kuwa. Shi kuma ya ?arSi ragamar dafa chicken kabsa. A lokacin ne kuma aikin su Alh. Usaini ya yi tasirin gaske. Ya haWa spices Winsa tunda abin da zai dafa dama spices ne sinadarin sa. Komai ya ajiye a gefe yayi marinating kazar. Bai
anWana ba tunda hannu ya gama sabawa. Cikin ?warewarsa ya gama haa komai saura jiran dahuwar abinci. Yana duba list Win abubuwan da aka ?aro da baya nan yaga wasu cikin ma'aikatansa sun shigo kitchen Win a guje.

"Sir baka ji ?auri ba?" Wani ya tambaye shi da ya ce me ya faru.

Ya juya ya bu
e tukunyar. ?auri ya sake cika kitchen Win. Kowa na tari banda shi. Shinkfar tayi Saki ta ?one babu abin mora a ciki. Abin ya Waure masa kai. Ya faki idonsu ya da dangwali gishiri ya lasa. Ko Wigo bai ji WanWanon sa ba. Ya sake Wora wata shinkafar ita kuma da ya gama aka yi serving ga masu saye babu wanda yaci rabi. Haka aka dinga dawo da plates Win cike da abinci. Bakinsa still babu taste. Yasa yaran kitchen Win WanWawa. Kowa ya kai baki sai ya gumtse abinsa ya dangana bakin shara ya tofar. Akwai wanda ya soma amai a gabansa ma.

"Me kuke ji?" Yayi tambayar calmly.

"Gishiri da garlic sun yi yawa sosai. Yawan daido duk dauriya mutum ba zai iya rufe ya ci ba."

Hankalinsa sayiwani irin tashi yayi. Bai yiwa kowa sallama ba ya fita. Yana zuwa gida ya buWe fridge ya Wauki mixed fruit juice Win da ya haWa da hannunsa jiya. Nan ma shiru baki da hanci bai ji komai ba.

***

Abba Habibu da iyalinsa suna tattaunawa game da waWanda Yaya za ta bi saboda ta sami muharrami.

"Abba dama dai ka jira ka samu wasu kuWin kun tafi tare." Cewar Zee

"Yanzu Allah Ya kirata. Ku dai ku yi mata addu'a. Banda abin ku mijin Labiba ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ai ya zama Wan gida. Yan uwan nasa da zai yi tafiyar dasu jiya har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login