Showing 135001 words to 138000 words out of 236327 words
cikin faɗa kamar zai ham6are su.
Tunda ya fara magana Umma ke ta hawayen da ta kasa controlling ɗinsu, shiru office ɗin ya ɗauka kafin kuma likitan ya sake cewa "Well i guess banida wani abu da zan iya yi muku yanzu wanda ya wuce nace muku ku maida ta wurin likitan da kuka gani farko tun kafin rayuwar ta ta gama faɗawa cikin illa ta koma gidan jiya or fiye da hakan ma."
"Yes Doctor, zuwa yaushe kake ganin yakamata ace an maida ta ɗin?."
"Today, tomorrow, Next Tomorrow, but indai ya wuce sati koh kuka ɗau wani dogon time then the risk is yours to take."
"Alright, Thank you" ya faɗa kafin ya kalli Umma yace "Umma muje."
Kamata yayi ta tashi tsaye kafin su fice a office ɗin yana rarrashin ta.
Ɗakin da aka kwantar da DEENAH suka shiga, inda suka ganta kwance unconcious an laƙa mata abin shaƙar numfashi, ga kuma drip da aka jona mata da sauran abubuwa.
Kuka Umma ta fashe dashi tana faɗin "Kaico na!, ki yafe ni DEENAH nasan duk nice dalilin faɗawar ki wannan hali, kinyi gaskiya da kika ce bamusan abinda kike ji ba, ya Allah ka yafe ni."
Patting ɗinta Jafar keyi a baya yana faɗin "It's alright Umma, ki bar faɗin haka, dukkanin wani abu dake faruwa nada dalilin faruwar sa, stop blaming yourself for all this please, kin ta6a ganin inda uwa ke ƙoƙarin kai ƴar ta halaka ne, bale kuma ke da kullum kike fatan rayuwa mai inganci wa DEENAH?, dan Allah ki bar sawa kanki damuwa and DEENAH insha Allah zata tashi in good health har tafi dah ma, just keep praying."
Kai ta jinjina tana share hawayen fuskar ta kafin yace "Zanje na fara shirye-shiryen komawar ku Egypt, DEENAH will be fine insha Allah, yakamata ace zuwa jibi dai kuna chan."
Kai kawai ta iya jinjina masa, kafin yaja mata kujera ta zauna shi kuma yana ficewa.
************************
__________B'angaren ZEEYAD yau 3days da barin sa Nigeria zuwa wata ƙasar, ayyukan sa yake gudanar wa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Yayin da kullum kuma suna cikin waya da Grandma ɗinsa 24\7, inda sauran masa 1month ya ƙarashe abubuwan da suka kaisa ya dawo.
Yau ma zaune yake cikin wani ƙayataccen madaidaicin falo mai ɗan karen kyau, ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana mai daddana wayar sa.
After some seconds ya kai wayar kunnen sa, murmushi ya saki bayan an ɗau kiran yace "Grandma?."
"Habiby, ya kake?."
"Am food Grandma, and you?."
"Alhamdulillah, Alhamdulillah Habiby sai kewar ka kawai, ka duba fah yau watan ka ɗaya baka nan, kada kaso kaga yadda duk na rame."
Murmushi mai ɗan sauti yayi yace "Grandma kenan, kada ki damu maybe na gama abubuwan da suka kaini zuwa next two weeks, so bana tunanin zan cike sauran wata ɗayan."
"Toh alhamdulillah, naji daɗi sosai Boy, Allah yasa dai hakan ta yiwu."
"Insha Allah Grandma" ya faɗa cikin murmushi.
"Toh ga Jalilah nan na son magana da kai, tace tunda ka tafi baku gaisa ba."
"Yeah" ya ɗan faɗa.
"Assalamu Alaikum" yaji ta faɗa.
"Wa'alaiki Assalam" ya amsa mata.
"Ina wuni Akhi?."
"Lafiya, am good, and you?."
"Lafiya ƙalau alhamdulillah, ya ayyuka?."
"Alhamdulillah" ya amsa a takaice.
"Masha Allah, Allah ya taimaka, dama gaisuwa ce."
"Aameen, Thank you" ya faɗa kafin yace "Grandma?."
Muryar Grandma yaji a wayar tana faɗin "Masha Allah Boy, Allah ya taimaka yayi maka Albarka."
"Aameen Yaa Rabb Grandma."
"Toh sai anjima koh?."
"Yeah" ya faɗa kafin kuma ta katse kiran.
Murmushi ne yayi forming kan fuskar sa yana komawa da ya jingina da kujerar da yake kai yana lumshe idanu.
**********************
*EGYPT*
________Yau kwanan su Umma ɗaya a asibitin sai dai tunda aka shiga da DEENAH ba'a bari ta ganta ba har yanzun, sosai ta nesa da tunanin da ta lula.
Dafa ta akayi nan ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula ta ɗago tana kallon nurses ɗinnan tsaye akanta.
Murmushi suka sakar mata suna zama gefen ta.
Wacce ta dafa ta mai suna Marwa ce tace "You look so disturbed Aunt, ki kwantar da hankalin ki DEENAH will be alright, ashe kun dawo ma sai yanzu da muka fito muke ganin ki."
Ɗayar mai suna Azeemah ce tace "Please Aunt, kada ki wani sawa ranki damuwa, DEENAH zata samu lafiya ta tashi kamar bata ta6a yi ba."
Kai kawai Umma ta jinjina musu, nan suka cigaba da rarrashin ta tare da kwantar mata da hankali.
******************
_______Sai Ƙarfe goman dare aka barta taga DEENAH.
Kwance take kan bed tayi nisa cikin tunani, shigowar Umma ne ya sanƴa ta maida duban ta gun ƙofa tana kallon ta.
Kallon ta Umma tayi tana ƙarasowa ta zauna gefen ta.
"DEENAH?" ta faɗa tana shafo fuskar ta.
Da idanu kawai DEENAH ke binta ba tare da tace mata komai ba.
Hannun ta Umma ta kama tana cigaba da kallon ta, DEENAH zame hannayen ta tayi daga cikin na Umma tana kauda kanta zuwa ɗayan 6angaren.
"DEENAH, akwai abinda kike buƙata ne nasa a kawo miki?."
Kai kawai ta girgiza mata alamun A'a ba tare da ta juyo ta kalle ta ba.
"Kin tabbata bakyajin ƴunwa, tun fah shekaran jiya baki sanƴa komai a cikin ki ba, sai ruwan nan da ake ƙara miki."
"Bana jin ƴunwa" ta faɗa.
Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe kawai ba tare da tace komai ba ta buga tagumi tana kallon wuri guda.
Ba'a jima ba aka buɗo ƙofar aka shigo, nan duk suka maida duban su kan YAZEED dake tsaye.
Sallama yayi yana ƙarasowa ciki, inda duk suka bisa da idanu Umma na amsa sallamar tasa.
Zuwa yayi ya gaida Umma cikin girmamawa yana tambayar mai jiki.
"Alhamdulillah, she is much better now" ta faɗa.
Ɗan murmusawa yayi yana kallon DEENAH da ita ma shi take kallo.
"Hi DEENAH" ya faɗa.
"Hi" kawai ta basa amsa.
"How are you feeling now, how is your health?."
"Alhamdulillah" ta bashi amsa.
"Masha Allah" kawai ya faɗa.
Sadeeq ne ya shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin sa, amsa masa sukayi yana ƙarasowa ciki.
Buga kafaɗun YAZEED yayi yana yi masa murmushi, murmushin shima YAZEED yayi yana kauda kai zuwa kan DEENAH.
"Well done Aunt" cewar Sadeeq.
"Thank you Doctor" ta faɗa.
"Sadeeq" ya faɗa.
Ɗan murmusawa kawai tayi kafin ya kalli DEENAH da ta kasa ɗauke idanun ta kan YAZEED, gyaran murya Sadeeq yayi yace "Hello patient, ya jikin ki?."
Kallon sa tayi tace "Alhamdulillah."
"Good, akwai wani abin da kikeji ne kuma?."
Kai ta girgiza masa alamun a'a, kafin tace "I just want to be alone."
Duk kallon ta sukayi kafin yace "Alone?, ofcourse you need some rest, and in the other hand you need something to cheer you up."
Kallon sa take kafin yace "Maybe a kunna miki TV ɗinnan a sanƴa miki Cartoon ɗin Tom&Jerry, i know it would surely cheer you up."
Ɗan murmusawa tayi a zuciyar ta, Tom&Jerry sai kace wata yarinƴa ƙarama, Ofcourse shine best cartoon ɗinta lokacin da take ƙarama but yanzu bata tunanin tana ma da lokacin kallo.
"A kunna?."
"Ofcourse ka kunna what are you still waiting for, she needs something to cheer her up, right DEENAH?" cewar YAZEED yana kallon ta.
Kallon fuskar sa da yanayin maganar sa kawai take, sosai yaso yayi mata shige da ZEEYAD sai dai idan ta tuna fuskar ZEEYAD ɗin sai taga basu wani shige, ɗauke duban ta tayi daga kansa tana lumshe idanun ta.
Umma ta san sarai ita ce DEENAH bata so kusa da ita shiyasa ta faɗin tana son kasancewa ita kaɗai.
Miƙewa tayi daga zaunen da take tare da kallon Sadeeq tace "Tana son Cartoon ɗin Tom&Jerry, ka kunna mata shi am sure it will cheer her up kamar yadda ka faɗa, i will be outside so that tayi enjoying kallon ta" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin.
Har ta fice DEENAH bata buɗe idanun ta ba, muryar YAZEED taji yana faɗin "Alright DEENAH, ni zan wuce ina da patient ɗin da zan duba, take care Okay?."
Kai kawai ta jinjina masa tana kallon sa, murmushi yayi tare da ɗan baiwa Sadeeq blow ta baya yana ficewa daga ɗakin.
Sadeeq kamar yadda ya faɗa jona mata kallon yayi tare da kaiwa tashar da akeyin Cartoon ɗin, juyowa yayi yana kallon ta yace "Alright DEENAH, Enjoy" ya faɗa cikin murmushi yana ficewa.
Da kallo ta bisa kafin kuma ta maido duban ta kan TV ɗin da takejin ƙarar fashe-fashen da Tom da Jerry ɗinsa keyi tana kallo.
Ta kai kusan 20mins tana kallo, sai dai babu wani murmushi koh dariya da yayi forming kan fuskar ta, sosai ita kanta tayi mamakin hakan ba kamar dah da idan tana kallo tayi ta kyakyata dariya yawa mahaukaciya sabuwar kamu ba, har sai Umma tayi mata magana kafin ta rage, tuno da irin yadda takeyi a wancan lokacin idan tana kallon ne ya sanƴa ta sakin light smile wannan moments ɗin na Playing cikin memories ɗinta.
Lumshe idanu tayi tana cigaba da sakin murmushin.
*******
"I told you right, just look at yadda take smiling" cewar Sadeeq da idanun sa ke kan System suna kallon DEENAH wanda da alama seta camera sukayi a ɗakin.
Murmushin farin ciki Umma ta saki, kallon ta YAZEED yayi yace "Don't worry Aunt, she will be fine insha Allah."
Kai Umma ta jinjina tana share hawayen farin cikin da suka zubo mata.
"Oh wait... what makes her sad again?" cewar Sadeeq yana kallon cikin system ɗin ganin ta bar yin murmushin fuskar ta ta koma kamar dah.
Umma ji tayi farin cikin da take ciki ya fara gushewa.
DEENAH dake kwance so bored ka ƙarar katun ɗin da ya cika mata kunne, idanu ta lumshe tare da sanƴa hannu ta toshe kunnuwan ta kafin kuma in a calm voice cikin zazzaƙar muryar ta ta fara rero waƙa
_Here's to the ones that we got_
_Cheers to the wish you were here,but you're not_
_Cause the Drinks bring back all the memories_
_Of Everything we've been through_
_Toast to the ones here today_
_Toast to the ones that we lost on the way 'cause the drink bring back all the memories, and the memories bring back, memories bring back you_
_There is a time that i remember_
_When i did not know no pain_
_When i believe in forever_
_And now everything would stay the same_
_Now my heart feel like December_
_When somebody say your name_
_'Cause i can't reach out to call you, but i know i will one day, yeah_
_Everybody hurts sometimes_
_Everybody hurts someday, Ayy-Ayy
_But everything gon' be alright, go and raise a glass and say, Ayy_
_Here's to the ones that we got_
_Cheers to the wish you were here but you're not_
_'Cause the drink bring back all the memories_
_Of Everything we've been through_
_Toast to the ones here today_
_Toast to the ones that we lost on the way 'cause the drink bring back all the memories, and the memories bring back, memories bring back you_
_Doo-Doo, Doo-Doo-Doo-Doo_
_Doo-Doo, _Doo-Doo-Doo_
_Memories bring back memories bring back you..._
Buɗe idanun ta tayi shiru lokacin da aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo.
Maida duban ta tayi kan Sadeeq da YAZEED dake tsaye suna kallon ta.
"Aren't you enjoying the show?" cewar Sadeeq.
Cire hannayen ta tayi daga kunnuwan ta tana maida duban ta kan TV ɗin, kafin kuma ta kalle shi ta jinjina masa kai.
"Oh strange" ya faɗa yana idda shigowa ɗakin tare da zuwa ya kashe kallon.
Kallon YAZEED dake tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannaye a ƙirji tayi, murmushi ya sakar mata kafin kuma tayi saurin kauda kanta tana maida idanun ta lumshe.
Ƙarasowa inda YAZEED ke tsaye Sadeeq yayi kafin cikin harshen larabci yace dashi "Why are you staring at her like this?, go on maybe ta saki jiki da kai kuyi hira."
Kallon sa YAZEED yayi kafin yace "Tana yi like bata sanni ba, she will be like, _"hey, who are you?"_, _"Do you know me?."_, _"Have we shared any relationship before."_ Irin tambayoyin da zata jero min kenan, and what answer should i gave her, tell her that we met lokacin da bata dawo hayyacin ta ba or what?."
Dariya Sadeeq yayi yana jawo sa suyi waje tare da rufo ƙofar.
Buɗe idanun ta tayi tana bin ƙofar da kallo.
***********************
________Duk inda ka zaga lungu da saƙon part ɗin Grandma toh kuyangu mata ne ke ta kai komo kowacce na busy da aikin da aka sanƴa ta.
Sosai akayi decorating part ɗin da flowers masu ɗan karen kyau da ɗaukar hankali, ga kuma wutar lantarki da ta haska koh ina na part ɗin, sai kuma wani irin fitinannen ƙamshi mai sanƴaƴa ruhi ɗan Adam dake tashi ta kowane lungu da saƙo.
Magana Grandma dake sauƙowa kan beni keyi cikin ɗan faɗa take cewa "Wai mai kukeyi ne har yanzu baku idda gyaran nan ba?, Prince na kan hanƴa zai iya isowa kowane lokaci yanzu, amma ku nan kunzo kuna aiki simi-simi yawa wadanda basuda jini a jiki, ku kuma da kuka zuba min ido kuna kallo yawa wacce suka ga sabuwar halitta fah, zaku wuce ne koh sai ranku ya 6aci yanzun, iyayen tsegumi kawai."
Da ɗan gudu Jalilah tazo tana kamo hannun Grandma tare da ɗanyin juyi da ita tace "Grandma?, irin wannan kyau ɗin da kikayi yau ba dole kowa ya tsaya kallon ki ba" ta faɗa cikin ɗan dariya.
"Ohh ni yarinƴar nan ai sai ki sanƴa ni jin hajijiya da wannan juyi, yoh toh ba dole nayi kyau ba abin ka da kyakkyawa" ta faɗa cikin murmushi.
Murmushi itama Jalilah tayi kafin Grandma tace "Toh maza kema jeki ki shirya dawuri kafin ya iso kada ya raina ki tunda kin kammala girkin."
"Toh Grandma" ta faɗa cike da farin ciki tana hawa kan matattakalar benin cikin gudu.
Murmushi Grandma da tasha kyau cikin shigar ta ta alfarma tayi tana cigaba da masifar ayi sauri a gyara komai yayi steady prince ya kusa ƙarasowa.
6angaren Jalilah kuwa tunda ta haura sama ta shige cikin ɗaya daga cikin ɗakunan dake jere a corridor ɗin.
Sosai ɗakin yake da bala'in kyau da ɗaukar hankali.
Cikin farin ciki ta nufi haɗaɗɗen closet tare da ciro wasu gown dresses kala huɗu masu matuƙar kyau da ɗaukar ido.
Zuwa tayi ta tsaya gaban mirror ta shiga gwaggwada su a jikin ta ba tare da ta sanƴa su ba ganin koh wanne ne zaiyi mata kyau.
Ta kai minti goma a tsaya ta kasa za6ar ɗaya a ciki, knocking taji a bakin ƙofar ɗakin dan haka ba tare da nuna wani tsanani ba ta bada izinin shigowa.
Buɗe ƙofar akayi aka shigo inda wata mata da ba zata wuci shekaru arba'in da biyar ba ta shigo bayan ta wasu kuyangun ƴan mata biyu biye da ita.
Kallon su Jalilah tayi tana ƙanƙance cikin mamaki kafin tace "Hanifa Humairah, mai kuka zo yi anan, and wacece wannan?" ta faɗa tana kallon matar.
Dariya matar wacce tunda suka shigo take ta bin ɗakin da kallo tace "Come on Jalilah, kina nufin baki gane ni bane, babu wanda bai sanni ba cikin MASARAUTAR nan, kodai baki ta6a jin labarin Kiki bane, ai nice nan Kiki" ta ƙarashe cikin dariya.
Ɗan murmusawa Jalilah tayi tace "Kiki!, wane irin suna ne haka?, yi haƙuri amma bangane ki ba."
Juyawa kiki tayi ta kalli ƴan mata biyun dake tsaye a bayan ta tace "Ku kuyi mata bayani mana."
Kallon ta ɗaya daga cikin su tayi tace "Ranki ya daɗe, ita ɗin mahaifiyar Rumaisa ce, tazo ne dan maye gurbin aikin da Rumaisa keyi miki kafin ta samu lafiya ta dawo bakin aiki."
Tunda ta fara magana Kiki ke jinjina kai tana washe haƙora.
Murmushi Jalilah tayi tana zuwa ta kamo hannayen ta tace "Ke mahaifiyar Rumaisa ce?, gaskiya ƴarki nada matuƙar kirki da iya aiki mai kyau, tana da juriya da ƙoƙari sosai wurin yi min dukkanin abinda nake buƙata, itace kuyanga mafi soyuwa a gareni, sai dai ba zan bari kiyi aiki a gurbin ta ba, kinga kin haife ni baikamata ace kinyi min wasu abubuwan ba, Hanifa da Humairah sun maye gurbin aikin da Rumaisa keyi kada ki wani ji damu kinji?."
6ata rai Kiki tayi alamun bataji daɗin hakan ba kafin kuma tace "Haba ranki ya daɗe, Rumaisa da kanta ta turo ni nan dan kulawa dake, duk wani aiki da kika ga tana yi miki duk a wuri na ta gaje shi ni na koya mata komai, naji ance yau Yarima ZEEYAD zai dawo kina ganin baikamata ace kinyi shiri mai matuƙar kyau wanda zai siye zuciyar sa bane?."
Blushing Jalilah tayi kafin tace "Hakane..."
"Toh kada ki wani ji damuwa ni nan zan kula dake sannan nayi miki shiri mai kyau wanda zai sanƴa shi kasa ɗauke idanu akanki" cewar kiki cikin katse ta.
Murmushi tayi tace "Toh Nagode sosai."
Kallon kayayyakin dake ajiye Kan bed tayi kafin tace "A cikin wadannan zaki sanƴa?."
Kai Jalilah ta jinjina mata kafin tace "Eh amma tunɗazu na kasa za6ar guda ɗaya da yayi min kyau" ta faɗa cikin ɗan frowning face tana turo baki.
"Kada ki damu ranki ya daɗe, nazo miki da wani kaya mai kyau da tsada nasan zaki soshi sosai sannan zaiyi miki kyau ba kaɗan ba, ku bani jakar nan" ta faɗa tana amsar jakar dake hannun ɗayar.
Buɗe shi tayi kafin ta ciro wani kyakkyawan gown dress ash colour jikin sa wasu duwatsu ne masu kyau da kyalli, ya dai haɗu sosai.
Amsa Jalilah tayi tana furta "Wow yayi kyau sosai, amma a ina kika same shi haka dan kuwa daga gani yana da tsada sosai."
Rarraba idanu Kiki ta fara kafin idea yayi saurin faɗo mata kasancewar ta mace mai wayo da kaifin basira nan tayi murmushi tace "Ai a kasuwa na kar6o miki ita ki gani koh zatayi miki kyau, kinga sai ki bani kuɗin na kai musu, yanzu ki gwada shi ki gani idan yayi miki sai ki saya idan kuma baiyi miki ba sai ki za6i wanda kika ga yafi Kwanciya miki a cikin wadannan."
"Bashi?, amma dai ba da sunana kika kar6i bashin ba koh?."
"Aa koh kaɗan tayaya ma zasu fara yarda cewar zaki kar6i bashi, na riga da na biya musu kuɗin, yanzu kinga idan kika bani sai na riƙe abu na."
Mamaki ne ya kama Jalilah tayaya kamar ita zata samu kuɗin sayen kayan nan, kauda tunanin hakan tayi a ranta kafin tayi murmushi tace "Toh shikenan hakan yayi kyau, lokaci na ƙurewa yakamata mu gaggauta koh?."
"Kwarai kuwa ranki ya daɗe, ku shiga ku haɗa mata ruwan wankan, nikuma zanji da sauran."
Kamar yadda ta faɗa sukayi, ruwan wanka suka haɗawa Jalilah, nan ta shiga tayi ba tare da ta bari an taya ta ba.
Bayan ta fito ne kuma suka hau shirya ta, inda ƴan matan sukayi mata light make up wanda ya kar6i fuskar ta yayi mata kyau sosai haɗi da yi mata gyaran gashi mai ɗaukar hankali.
Taya ta sukayi ta shirya cikin haɗaɗɗen gown ɗin, wanda yayi