Showing 174001 words to 177000 words out of 236327 words

Chapter 59 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45302

nake da kunƴa a yanzu, after all what i did to you, you decided to forgive me so soon, you will surely make a great King Son" ya faɗa yana sake rungume ɗan nasa cikin tsantsar farin cikin da yake ciki.

Ɗagowa sukayi suna kallon juna nan ZEEYAD ya duƙar da kai yace "But..." shiru yayi bai iya iddawa ba.

"Talk Son, faɗi dukkanin abin dake ranka."

"Am not ready to be a King."

Murmushi mai Martaba yayi yace "You don't have to be ready in order to be a King, ka sanƴawa ranka cewar dukkanin wani abu da zai shige maka gaba zaka iya dealing ɗinsa komin nauyin sa, sannan kuma ka kasance mai yawan addu'a addini da neman jagorar Ubangiji a duk wani abu da zaka sanƴa a gaba, ka kuma kasance mutum mai nutsuwa da sanin yakamata, ka kuma kasance mai adali da gaskiya, indai ka riƙe wadannan abubuwan then you're good to go Son, and am sure ka tara dukkanin wadannan abubuwan da na lissafa, kai matashi ne na tabbata zakayi shugaban ci mai kyau sannan kuma Al'umma zata soka, it's time that i step down, kada ka manta da cewa that i will always be there to guide you har zuwa ran da rai zaiyi halin sa and your Grandma is also here to support you, i know fargabar ba bai wuce ta ina zaka fara ba, do not worry Son we are here for you" ya ƙarashe cikin patting shoulders ɗin ZEEYAD ɗin.

Shiru ZEEYAD yayi kafin yace "But i don't have any passion for ruling, i mean duk wani abu da yakamata ace Sarki ya tara ni banida wannan, ban iya faɗa da takobi ba, ban iya riding doki ba, and i...i don't even have a wife" ya ƙarashe cikin sunkuyar da kai.

Murmushi mai Martaba yayi yace "Duk wannan abu mai sauƙi ne, zaka iya koyon takobi da tuƙa doki a ƙalilan lokaci, and besides ka tara dukkanin qualities da ake buƙata dan gane da Sarki, and a wife, da akwai yaran Abokai na Sarakuna ba zaka rasa wacce tayi maka a..."

"No" ya katse mahaifin nasa kafin yace "Ina da wacce nakeso."

"Masha Allah, tell me who she is, and ƴar ina ce?" ya faɗa yana kallon ɗan nasa.

Cikin duƙar da kai ZEEYAD yace "I know ban ta6a sanar da kai wani abu dangane da rayuwar da nayi bayan na bar MASARAUTA ba, but the girl and her Family have done alot for me, itace mace ta Farko da ta fara nuna min ƙauna da kulawa bayan Ummie na so tanada matuƙar muhimmanci a zuciya ta and i respect her for that, and above all i love her..."

"Just tell me where she is, nikuma nayi maka alƙawarin nemo maka auren ta cikin lokaci ƙalilan muddin hakan zai sanƴa ka farin ciki, labarin rayuwar da kayi bayan barin ka nan kuwa i know komin daren daɗewa zaka zo ka same ni sannan ka sanar dani dan kuwa ba zan tilasta maka abinda bakayi niyya ba, tell me Son, a ina ita wannan yarinƴar take?."

"She is a Nigerian, and am afraid kada kace dole sai ƴar ƙasa ta zan aura."

"Is she a Muslim?."

Kai ya jinjina masa yace "Yeah she is, a pious one."

Murmushi mai Martaba yayi yace "Then you've nothing to worry of Son, ba dai kanason ta ba, then you will Marry her, i will make a formal annoucement zanje dani da ƙalilan daga cikin ministoci na dan zuwa neman maka auren yarinƴar."

Wani irin tsantsar farin ciki ne ya mamaye zuciyar ZEEYAD ɗin, rungume mahaifin nasa yayi yace "Thank you so much Abhi, you're the best."

Ɗan dariyar manƴan ta mai Martaba yayi yana ɗan buga bayan ɗan nasa.

Ɗagowa ZEEYAD yayi yace "Zanje na sanar wa Grandma" ya faɗa yana shirin ficewa mai Martaba ya kira sunan shi, dakatawa yayi yana kallom sa nan yace "Don't forget, daga gobe zaka fara koyon dukkanin wasu abubuwa da bakada masaniya a kai, so be ready."

Kai ZEEYAD ya jinjina masa cikin murmushi yace "Yes Abhi" yana ficewa daga ɗakin.

Murmushi mai Martaba yayi yana komawa ya zauna.


***********************


__________Cike fadar take da manƴa-manƴan mutane wadanda kai tsaye za'a iya kiran su da na hannun damar mai Martaba wato su ne wadanda yake zantawa kafin ya yanke shawarar komai.

Kowannen su sanƴe yake cikin shigar sa ta alfarma inda kowanne ke haƙimce kan kujerar sa wanda akalla zasu kai su ashirin da biyar.

Shiru fadar ta ɗauka kafin wani dattijo daga cikin su ya miƙe tsaye, hannun sa riƙe da wani kundin littafi da alama dai irin litattafan nan ne na dah.

Cikin gyarar murya ya fara magana kamar haka "Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'alah Wabarakatuhu" tsagaitawa yayi yayin da suke amsa sallamar sa kafin kuma ya cigaba da faɗin "Kamar yadda kuka sani, ni sunana Abdulbasid Ibn Omar shugaba kuma wakilin gidan tarihi na wannan MASARAUTA, kamar yadda mai Martaba sarki ABBAS ya umarta a yau za'a canza dukkanin wani ƙa'idoji da aka sani a dangane da wannan MASARAUTA sakamakon sabon mamulki da zata samu wato babban ɗa gun Sarki Abbas wanda aka fi sani da Yarima ZEEYAD, a yau zamu zanta daku mutanen amana kuma na hannun daman sarki dangane da wannan batu, sai dai kafin na kai ga lissafo dukkanin wasu sharuɗa dama kuma sabbin dokoki na wannan MASARAUTA ina so naji daga gareku idan akwai mai wata ingantacciyar shawara kan wannan batu, idan kuwa babu kai tsaye sai mu tafi ga abunda ya tara mu anan" ya faɗa yana mai bin mutanen cikin fadar da kallo.

Ganin babu wanda yake da ta cewa ne a cikin su ya sanƴa shi cigaba da faɗin "Masha Allah, toh kamar yadda dai kuka sani wannan daddaɗiyar MASARAUTAR tamu wanda aƙalla zata kai shekaru ɗari biyu da tamanin da kafuwa sannan kuma Sarakuna daban-daban suka mulke ta har izuwa kan Sarkin mu na wannan zamani wato Sarki Abbas muna fata tare da addu'ar wannan MASARAUTA zata cigaba tafiya tare da ginuwa kan gaskiya da adalci kamar yadda ya samo asali daga Kakannin mu da suka mulke ta suka shuɗe, dayawa daga cikin ƙa'idojin wannan MASARAUTA ta dah sun shuɗe sakamakon yanayin da zamani yazo mana dashi, sai dai a yau kamar yadda mai Martaba kuma Adalin shugaban mu sarki Abbas ya umarta, tsarin wannan MASARAUTA zata canza ne izuwa ta Kakan sa Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM" dakatawa yayi sakamakon murmuring ɗin mutane dake tashi ƙasa-ƙasa.

Da ɗan ƙarfi yayi gyaran murya kafin kuma yayi shiru yana kallon su duka, kallon mai Martaba dake kishingiɗe kan Throne ɗinsa yayi kai ya jinjina masa alamar ya cigaba, nan ya cigaba da faɗin "Dayawa daga cikin mu muna ƴan ƙanana Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM yayi mulkin sa, nasan kuma da akwai abubuwan da wasu daga cikin mu zasu iya tunatowa lokacin da yayi mulki..."

Cikin ɗaya daga cikin ministocin ne ya katse shi da faɗin "Kowa yasan lokacin da Marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM yayi mulki, mulkin da yayi cike take da ɗumbin tsanani da takura, tabbas iyayen mu sun bamu labarin lokacin da yayi mulki, dawo da irin tsarin mulkin sa a yanzu tamkar takurawa rayuwar Al'umma ne duba da yadda duniyar ta canza a yanzu dama kuma yanayin rayuwar da ake a yanzu sam bashida wani kamanceceniya da ta dah, mutanen mu na yanzu sun kasance masu rauni ne, bakomai ne zasu iya ɗauka da jura ba muddin aka dawo da iriyar mulkin Marigayi Sarki ZAYYAD."

"Tabbas kayi gaskiya Hisham, ba abu ne mai sauƙi ga Al'ummar mu ba, dukda munsan cewa ba'a yi Adalin sarki kamar sa ba, sai dai fah mu sani ya Al'ummar mu zasu ji da wannan sabuwar salon mulkin da basu ta6a fuskantar ta ba?."

"A hankali zasu saba dashi, you've made the right decision Abhi, mulki irin na Marigayi Sarki ZAYYAD shine ya kamaci mutanen mu na yanzu, be it hakan zai zamto takura a garesu koh jindaɗi that doesn't count, muddin mutum ya yarda da kansa mai gaskiya ne sannan yana aikata alkhairi then baikamata hankalin sa ya tashi dan yaji an ambaci mulki irin ta Marigayi ba, there is no need aji shawarar wani daga cikin ku, the decision is been concluded, i will rule like my great-grandfather and no one dares to stop it from happening" ya ƙarashe cikin dafa teburin dake gaban sa.

Duk speechless suka tsaya kallon ZEEYAD ɗin wanda shigowar sa kenan yaji suna maganar.

"Am totally against this, there is no way da zamu yarda da wannan juyin mulkin and besides, ZEEYAD is too Young to rule us, i guess a al'adar wannan masarautar sai yaro ya kai shekaru talatin da biyar kafin a miƙa masa ragamar mulki, why then za'a canza tsarin komai haka kurum ba tare da dalilin komai ba?" cewar wani daga cikin ministocin cikin miƙewa tsaye.

"Abdulrashid yayi gaskiya, there is certain age da idan mutum ya kai ake basa ragamar mulki, haka kuma bamu yarda da dawo da tsarin mulkin Marigayi ba, a kullum cigaba ake nema ba ci baya ba, dawo da tsarin mulki irin na Marigayi tamkar faɗuwar wannan MASARAUTAR ne, yakamata ka sake nazari kan wannan batu Mai Martaba."

Ɗaga sandar sa mai Martaba yayi alamun yana son kowa yayi shiru kafin kuma ya fara magana cikin kakkausar murya "Ban kira ku nan bane dan neman shawarar ku goyon bayan ku, ku kanku kunsan bana jaye dukkanin wani abu da na yanke, ZEEYAD here shine wanda zai zamto shugaba a gareku, be it you like it or not, duk wani wanda yaga hakan baiyi masa ba zai iya zame kansa daga cikin membobin wannan fadar, i have made up my mind and so be it."

Shiru fadar ta ɗauka kafin ɗaya daga cikin ministocin ya tashi tsaye yana faɗin "There is no way ƙaramin yaro zai dinga umurtar mu, so am stepping down muddin wannan yaron ne zai zamto wanda zai mulke mu."

"Then so be it, anyone else willing to step down?" faɗin ZEEYAD yana bin kowannen su da kallo.

Biyu daga ciki ne suka tashi tsaye, murmushin gefen baki ya saki kafin yace "Well then this kingdom will do it's great without you, who else?."

Duk miris sauran sukayi basu tashi ba, dan kuwa sunsan wannan MASARAUTAR ita kaɗai ce hope ɗinsu, muddin sukayi kuskuren barin wata muƙami da suke dashi a cikin ta toh tabbas sun gama ne.

Jan sandar su sukayi duka sukayi hanƴar ficewa, ɗaya ne ya tsaya daga cikin su yana kallon ZEEYAD kafin yace "I just hope ka iya mulkar wannan ƙasar da kyau young Boy, sabida babu abinda nake hangowa sai faɗuwar ta warwas" yana faɗin haka ya wuce yana baza alkyabar jikin sa tamkar zai tashi sama.

Kallon sauran dake zaune Wakilin gidan Tarihi yayi kafin yace "Shin akwai mai magana?."

"Ka lissafo musu dokokin" cewar mai Martaba.

Cike da girmamawa ya duƙa kafin yayi gyaran murya yace "Sorry for the inconveniences, kamar yadda mai Martaba sarki ya umarta ga sabbin dokokin wannan MASARAUTA kamar haka."

"Doka ta Farko zamu ɗauko ta ne daga kan matsalar tsaro, matsalar rashin tsaro kowa ya sani babu ita a lokacin mulkin marigayi, a yanzu mutane dayawa, talakawa, matafiya, makiyaya, manoma, matsinta, ƴan kasuwa da dai sauran su na ƙorafi akan fama da rashin tsaro da suke a wuraren biyan buƙatar su da samar wa kansu da iyalan su abinci, dan haka matsalar rashin tsaro a wancan lokacin babu ita sakamakon zuba jami'an tsaro ƙarfafa wadanda akayi musu horo mai kyau a kowanne lungu da saƙo na, tare da ajiye na'urorin da zasuyi alarming ɗin mutane aduk inda wani mummunan abu ke gab da afkuwa, wanda a wancan lokacin ana amfani ne da ƙararrawa mai ƙarfin ƙara wacce zatayi alarming dukkanin wasu sojoji dake kusa da wannan wuri dan kai taimakon gaggawa, wanda kuwa aka kama shi da aikata laifi wurin kwatar haƙƙin mutane, wanda kai tsaye za'a iya kira da sata, hukuncin sa shine za'a yanke masa hannuwa duka biyu tare da yi masa horo mai tsanani, wannan hukunci yayi tasiri sosai a wancan lokacin domin kuwa an samu raguwar rashin matsalar tsaro sosai da sosai dan kuwa cikin kaso dari bai wuci kaso goma bane wanda suma sun fi aikata hakan ne ta hanƴar amfani da asiri koh wani abu makamancin shi, wanda shima hukuncin amfani da tsafi a wancan lokacin shine kisa, duk wanda aka kama yayi amfani da tsafi koh asiri wurin cutar da wani Marigayi ya bada umarnin a yanke masa hukunci ta hanƴar rataye sa har lahira, domin hakan ya zamto izina ga ƴan baya masu aikata shirka a doron ƙasa."

Idanu kawai ZEEYAD ya zuba masa yana kallo kafin ya cigaba da faɗin "Doka ta biyu kuwa itace Tsaftace muhalli, ya halarta ga duk wani ɗan ƙasa be it cikin MASARAUTA yake koh wajen ta, be it cikin garin CAIRO yake koh wajen ta, duk wani wanda aka kama koh da ƙofar gidan sa ce da datti toh tabbas za'a hukunta shi ta hanƴar yi masa bulala zafafa kwaya hamsin kacal, idan ya kuma ƙarawa aka kama sa a karo na biyu za'a yi masa bulala sittin har izuwa ranar da zai gyara ya daina muddin kuma bai daina ba toh kuwa kullum goma zata dinga ƙaruwa kan wannan hamsin ɗinnan, tsafta na daga cikin koyarwar Manzon Allah haka kuma cikon imani ce, Marigayi bai lamunce wa rashin tsafta ba a ƙasar sa komin ƙanƙantar ta."

Doka ta Uku itace, Girmama juna musamman ma mata, sau tari rahoto na zuwan wa marigayi akan Maza dake harassing mata, koh ci musu mutunci da zarafi a idanun Jama'a kokuwa dai wani abu makamancin haka, duk wanda aka kama da wannan laifin hukuncin sa shine zaman gidan kaso na watanni shida tare aikin horo mai wahala dan gane kuren sa tare da fahimtar cewa mata na da matuƙar daraja dan haka girmama su ya zame dole ga jama'a,

Doka ta huɗu itace Fyaɗe, kowa ya san fyaɗe mummunar laifi ce a musulunci, dan haka duk wani wanda aka kama sa da laifin fyaɗe hukuncin sa shine za'a yanke masa mazaƙuta ta hanƴar dandaƙa, koh da kuwa ya kasance ɗan cikin gidan Masarautar kanta ne, dan kuwa Marigayi baya nuna bambanci tsakanin bayin sa da mutanen cikin gidan sa,

Doka ta biyar itace ya zama wajibi ne a baiwa kowane mahaluƙi damar aiwatar da abinda yaso muddin ba wai ta sa6awa koyarwar addinin musulunci bane, kowane mahaluƙi koh da kuwa bawa koh baiwa ce suna da freedom na kansu, tunda suma mutane ne ba wai injina ba, ya zama dole idan lokacin hutu yayi a bar su su hutu sannan a daina tsanan ta musu aiki musamman ma bayi mata,

Doka ta shida ita ce kamar yadda na faɗa, duk wani wanda aka kama da aikin asiri koh tsafi toh lallai hukuncin sa shine kisa ta hanƴar rataya..."

Magana zai sake ZEEYAD yayi saurin katse shi da faɗin "It's Okay, zan kar6i kundin naje na karanta dukkanin wata doka da kaina."

Duƙar da kai yayi cike da girmama kafin ya kalli mai Martaba yace "Your Highness, kaɗan daga cikin dokokin kenan, Yarima yace zai idda karanta sauran da kansa."

"Tunda yace haka, hakan za'ayi zaka iya basa kundin dama kuma dukkanin wasu litattafai masu muhimmanci."

Cike da girmama ya amsa yace "Insha Allah, ranka ya daɗe" ya faɗa yana samun wuri ya zauna.

Gyaran murya sarki yayi kafin yace "Dafatan dukkanin ku kunji wadannan dokoki sannan kunyi na'am dashi?."

"Insha Allah Ranka ya daɗe" duk suka amsa.

"Masha Allah" ya faɗa a hankali kafin ya kalli inda ZEEYAD ke tsaye yace "A Man needs a Woman to support him in other to achieve something great in life, dan haka dani da kai Liman, Waziri dama kuma likitan gargajiya, ku shirya zuwa jibi zamu je neman wa Yarima ZEEYAD aure a wata ƙasar daban, dan haka ku tabbatar kun shirya duk wani abu da za'a buƙata wurin zuwa neman aure, za'a gudanar da komai ne tamkar yadda ake zuwa tambayar aure a wannan ƙasa."

"Masha Allah" shine abinda ya karaɗe ilahirin fadar.

ZEEYAD bai san sadda ya saki wani irin ƙayataccen murmushi ba yana duƙar da kai.

Tsinkayo muryar mai Martaba yayi yana faɗin "Ku barmu haka nan, inason zantawa da dukkanin Family na, kowa da kowa da muka haɗa alaƙa ta jini dasu ina buƙatar su anan hatta ƴaƴa da jikokin su kada a bar kowa."

Duk miƙewa sukayi tsaye suna gyara zaman alkyabar jikin su, cike da girmama wa sukayi masa sallama suna mai ficewa daga fadar.

Miƙewa tsaye mai Martaba yayi yana sauƙowa daga kan kujerar sa, ƙarasa wurin sa ZEEYAD yayi yana riƙo sa, kallon ɗan nasa yayi yace "I can see how happy you're Son, da alama kanason yarinƴar sosai, how lucky she is da samun kamar ka."

Murmushi yayi kafin yace "Am so proud of you" yana rungume mahaifin nasa.

Ɗan bubbuga bayan sa mai Martaba yayi kafin ya ɗago sa yace "Bari na wuce ɗaki na ɗan kwanta."

"But... kace kana neman kowane family member."

"Yeah, ban manta ba, kafin su iso ni zanyi baccin na tashi."

"Alright, muje na raka ka" ya faɗa cikin hannayen sa kan kafaɗun mahaifin nasa.





*TALLAH*


Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻

_*infection*_
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login