Showing 171001 words to 174000 words out of 236327 words

Chapter 58 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45332

are they?" ta faɗa tana ƙarewa wurin kallo ganin babu su.

"Maybe in there" ya faɗa yana nuna mata wata ƙofa.

"Anan za'ayi taron?" ta tambaya tana kallon sa.

Kai ya jinjina mata yana yin gaba nan ta mara masa baya.

Buɗe ƙofar yayi ya shiga kafin ita ma ta mara masa baya.

Cak taja ta tsaya ganin wani irin duhu mamaye cikin ɗakin gabaɗaya.

Idanu ta fara rarrabawa tare da yin lalume tana yin gaba "Abyad?" ta ƙira sunan nasa a hankali.

"Where are you, why is it so dark in here?."


"Abyad?" ta sake faɗa cikin ɗan tsoron da ya fara darsar mata tana cigaba da laluma hannayen ta.

"Ab..." bata kai ga ƙarasar maganar tata ba taji an saki ihun _Happy Birthday to you_ dai-dai lokacin da wutar wurin ya kawo wasu flowers suka shiga zubo mata akai.

Sosai ta tsorata da yadda sukayi mata ɗin dan haka hannaye tasa ta rufe fuskar ta ta fara kuka a hankali, inda kuma wurin ya cika da sautin flute ɗin happy birthday.

Fuskar kowa washe yake da murmushi, Jafar ne ya fara tafa hannayen sa yana yi mata waƙar _Happy birthday to you_
_Happy birthday to you_
_Happy birthday dear DEENAH_
_Happy birthday to youuuuu_

Zuwa tayi da ɗan gudu tana rungume shi cike da farin cikin da take ciki.

_How old are you now?_ cewar Anty Khadija cikin ɗan waƙa.
_She is 20yrs old now_ Amirah ta amsa.

Duk ɗan dariya ƴan wurin sukayi suna kallon Jafar da DEENAH ɗin.

Ɗagota yayi yana share mata hawayen yace "Why the cry?."

"Actually you guys scared me" ta faɗa cikin ɗan dariya.

Kallon ZEEYAD da yayi folding hannaye a gefe tayi tana ƙarasawa wurin sa tace "Thank you."

Cike da ɗan mamaki yace "For what?."

Wurin ta ƙarewa kallo wanda daga gani ba ƙaramin naira aka zuba masa ba tace "This is all your doing, isn't it?."

Murmushi yayi yace "Actually, you deserve anything, more than this."

Murmushi tayi tana sadda kai ƙasa.

"It's getting late, muyi abinda ya kawo mu mu tafi, let's cut the cake" faɗin Jafar.

Duk nufar inda ƙaton kyakkyawan cake ɗin yake sukayi, Jafar ne ya kallesu yace "Am eager naji cake ɗinnan cikin baki na."

Murmushi duk sukayi kafin tace "Muje."
Murmushi yayi ya mara mata baya, tsakiya duk suka sanƴa ta.

Anty Khadija ce ta ɗau ƴar ƙaramar knife ɗin yanka cake ɗin tana miƙawa DEENAH.

Amsa tayi cikin murmushi tana saita shi kan inda zata yanka, waƙar happy birthday ɗin suka cigaba da yi mata har ta yanka cake ɗin suna cigaba da tafa mata.

Slice ta ɗauko tana sanƴawa Jafar a baki inda shima ya gutsuro da niyyar bata sai dai ya fuzge yana sanƴawa girlfriend ɗinsa tare da barin DEENAH da sakakken baki, juyowa yayi tare da ɗaga mata gira yace "Wife first."

Turo baki tayi tana juyawa ta kalli ZEEYAD dake gefen ta.

Murmushi yayi yace "Don't mind him" ya faɗa yana ɗaukar knife ɗin ya yanka ɗan madaidaicin slice, kallon ta yayi yace "Haa."
Buɗe baki tayi nan ya sanƴa mata cake ɗin, yana goge cream ɗin da ya ɗan 6ata mata gefen baki da tissue, duk tafi suka sanƴa, DEENAH kuwa sosai zuciyar ta ke cike da tsantsar farin ciki marar misaltuwa.

Wani yanka ta sake iyowa tana baiwa Anty Khadija a baki, kafin duk ƴan wurin ta bisu ta basu suma.

Amirah ce tace "Toh shi ba zaki bashi bane?."

Kallon ZEEYAD tayi duk sai taji babu daɗi, kafin a hankali tace "Baya ci."

"Ohh" duk suka faɗa.

Murmushi tayi tana samun wuri ta zauna tare da rufe idanu tace "Alright, am waiting for my presents."

"Happiest birthday DEENAH, Allah ya ƙarawa rayuwar ki albarka" cewar budurwar Jafar tana miƙa mata wani box da akayi wrapping nashi.

Buɗe idanu DEENAH tayi tana amsar gift ɗin cikin murmushi tace "Thank you so much Sweetheart."

Anty Khadija ce ta ƙaraso ita ma tana miƙa mata nata gift ɗin tace "Happy birthday babyn Abyad, Allah yayi wa rayuwar ki albarka ya cika miki dukkanin burikan ki na alkhairi."

"Aameen Yaa Rabb Bestest, thank you so very much" ta faɗa tana ajiye shi a gefe.

Jafar ne ya ƙaraso shima da ƴar tashi madaidaiciyar gift ɗin yace "Barka da murnar zagayowar ranar haihuwar ki lil sis, i love you so much."

Amsa tayi tare da faɗin "Wow, thank you Blood, i love you more" ta faɗa tana ajiye nashi shima.

Kallon Amirah da ƙannen Ruqayyah girlfriend ɗin Jafar da sukayi tsaye suna bin kowa da ido tayi tace "Am waiting guys."

Dariya ƴan biyun sukayi suna 6oye fuskokin su, Amirah dake ta rarraba idanu ne ta sanƴa hannu cikin Jakar ta tare da ciro wani ɗan ƙaramin kwali da akayi wrapping nasa tana zuwa ta miƙawa DEENAH.

Amsa DEENAH tayi tana jujjuya ɗan ƙaramin kwalin a hannu kafin tace "Miye a ciki?."

Ɗan ta6e baki Amirah tayi tace "Kibiya ce da mataji, dan Allah ki dinga kitsa kanki" tana faɗin haka tayi gefe abin ta.

Duk dariya ƴan wurin suka sanƴa, kwafa DEENAH tayi tana ajiye box ɗin a gefe.

Ƴan biyun ne suka ƙaraso gaban ta nan suka ce "Bamu da abinda zamu baki, sai wannan" suka faɗa kowanne na kai mata kiss a kumatu.

"Aww" ta faɗa cike da jindaɗi tana rungume su tace "Thank you so much cuties."

"Allah ya ƙarawa rayuwar ki albarka" suka faɗa.

"Aameen Yaa Rabb" ta amsa musu cikin murmushi.

Kallon ZEEYAD tayi cikin murmushi nan ya ƙaraso da bunch of flowers ɗin dake hannun sa tare da durƙushewa a gaban ta yace "Happy Birthday Wifey, i love you."

Hannu tasa ta amshi fulawar cike da farin ciki tana kaiwa saitin hancin ta ta shinshina kafin tace "Thank you so much Abyad Darling."

Murmushi yayi yace "This isn't gift ɗin da zanyi miki."

"Really, where is it then?" ta faɗa tana kallon sa.

Miƙewa tsaye yayi kafin yace da ita "Up."

Tashi tayi nan ya ciro farar kyalle yana zagayawa ta bayan ta yayi blindfold ɗinta.

Murmushi tayi tana ta6a kyallen tace "Why did you blindfolded me?."

"You will see" ya faɗa yana riƙo hannun ta su fara tafiya.

Duk mara musu baya su Jafar sukayi suma dan ganewa idanun su abinda zai bata.

Waje suka fito still hannun sa jaye da ita inda yake controlling duk wani step nata dan ganin bata sami matsala wurin tafiyar tata ba.

A haka har suka ƙarasa wani gu, nan yaja ya tsaya, duk waro idanu sukayi ganin abin dake gaban su.

"Inalillahi" cewar Amirah cikin waro idanu, nan Anty Khadija tayi saurin gwa6e mata baki.

Jafar ma baki ya sake cike da mamaki yana bin ZEEYAD ɗin da kallo.

"Mun iso?" faɗin DEENAH ɗin dan kuwa ta ƙosa ya buɗe mata idanun dan ganin kyautar abinda zaiyi mata.

"Yes babe" ya amsa mata cikin murmushi.

"Alright, menene mu ganshi" ta faɗa tana miƙa masa hannun ta.

Zuwa yayi ta bayan ta tare da sunce mata ɗaurin da yayi mata ɗin yana zagayowa ta gefen ta ya tsaya.

Murmushi tayi idanun ta da takejin sunyi mata duhu a runtse tace "Na buɗe?."

"Yeah."

"Okayyy" ta faɗa tana buɗe idanun nata a hankali har ta gama ware su tarr.

Side hug ya ɗan bata yace "Here is your gift baby."

She was stunned for some moments as she stared at the car speechlessly inda kuma murmushin kan fuskar ta ya shiga gushewa.

"W...wha...what is this?" ta faɗa still idanun ta kan baƙar *Toyota venza 2010* dake gaban ta.

"It's your birthday gift" ya faɗa shima idanun sa kan motar.

Shiru DEENAH tayi idanun ta na tara hawaye tace "This... this... why will you gift me such an expensive car?, i mean how much did you bought it?."

"Yes please... this car is worth #7million, it's to expensive for DEENAH, kuma as a birthday gift" cewar Jafar yana kallon sa.

Murmushi ZEEYAD yayi yace "No it's not expensive as far as she likes it."

Lumshe idanu tayi hawayen fuskar ta na samun damar sauƙowa, she can't believe her eyes, wai yau ita aka yiwa kyautar mota as birthday gift, and yayi hakan ne just to make her happy.

"You don't have to do this" ta faɗa cikin kuka.

Kallon ta yayi yace "Why are you crying, you should be happy, idan ma baiyi miki bane then i will change it na saya miki wani wanda kike so" ya ƙarashe cikin share mata hawayen fuskar tata.

Kallon sa take tace "I...bansan ta yadda zan fara gode maka ba."

Murmushi yayi yace "You like it?."

"I love it" ta faɗa cikin murmushi.

"Well then you don't have to thank me, farin cikin ki is worth everything."

Cike da murna ta rungume shi tana faɗin "Thank you so much."

Murmushi yayi yana ɗan bubbuga bayan ta, nan ta ɗago tana kallon sa tace "I don't know what to repay you back."

Cike da ɗan mamaki yace "Ofcourse you do."

"Really, how?."

Murmushi yayi yace "By marrying me."

Rufe fuskar ta tayi tana murmushi.

"So will you Marry me?."

Shiru tayi tana kallon sa cikin murmushi kafin kuma tace "Maybe" tana gimtse fuska.

"Congratulations lil sis" faɗin Jafar cikin murmushi.

Zuwa tayi shima tana rungumar shi tace "Thank you."

Duk congratulations sauran sukayi mata ta amsa musu cike da murna.

"So i think we should get going dare nayi."

"Yeah sure" cewar ZEEYAD.

Key ɗin motar ya ciro yana miƙa wa Jafar yace "It will be safe a hannun ka, muje na baka documents ɗin."

"Yes, Sire" ya faɗa suna jerawa tare.


**********************


*3 DAYS AFTER*


________"Am not happy you're living" ta faɗa cikin turo baki gaba.

Murmushi yayi yana kallon ta yace "Am not happy as well, but you know Grandma, she missed me and i missed her too."

Murmushi tayi tace "Hakane, so now tell me, yaushe zaka sake dawowa?."

"To do what exactly?" ya tambaye ta.

"To see me" ta faɗa tana kallon sa.

"No, i won't only come back just to see you, but to take you away with me."

Murmushi tayi tace "And when is that?."

"Maybe in the next two weeks."

"2 weeks, but how can you Marry me in the next two weeks?."

"Well you just wait and see."

"Uhm, alright we will see then."

Murmushi yayi yana buɗe motar sa ya shige.

Sauƙe glasses ɗin motar tasa yayi yana kallon ta yace "I can't wait to have you as my wife baby."

Hannu ta kai ta ɗan mari fuskar sa tace "Let's see then, ka rama Marin ka ranar auren, bye" tana faɗin haka ta juya ta koma cikin gida.

Da kallo ya bita murmushi ɗauke akan fuskar sa yace "Sure zan rama" kafin ya tada motar tare da janta ya bar wurin.


*GUDU, GUDU, SAURI, SAURI🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️*


______"Grandma i have never loved JALILAH, please don't force me to marry her."

"But the girl loves you boy, why ba zaka tausaya mata ka haɗa da ita ɗin ka aura ba?."

"Two wives at same time?, no i can't do that Grandma" ya faɗa yana samun wuri ya zauna.

"Boy..."

"Grandma, i feel bad for her, i know it's not easy wanda kakeso turns out to be akwai wata a ransa, but what can i do to help?, tayi haƙuri kawai."

Zama Grandma tayi kusa dashi tana dafa kafaɗun sa tace "Ofcourse you can help boy, kai fah Namiji ne, zaka iya auren mata har huɗu, what is the big deal idan ka haɗa JALILAH da ita DEENAH ɗin ka aura, i know ba zaka sami wata matsala daga garesu ba, tunda they are all decent, think about the poor girl boy, ta kwallafa rai sosai akanka, baikamata ka watsa mata ƙasa a ido ba."

"But Grandma..."

"Listen Boy, ba zan tursasa maka auren JALILAH ba, but zan baka time kayi nazari akai ka gani, kaji?."

Shiru yayi bai amsa mata ba, dan kuwa baya tunanin wannan karon ƙorafin Grandma ɗin zata kar6u a wurin sa, he only loves DEENAH, muddin ya kuskura ya amince da auren JALILAH then ba zata ta6a samun kanshi ba.

"Kaje ka gun mahaifin naka, he must be waiting kaga tunɗazu ya aiko."

Tashi yayi kawai yana ficewa.

Ƙofar fadar aka buɗe masa ya shigo, kai tsaye wurin zaman mai Martaba ya nufa ganin bai fito bane, ya sanƴa shi nufar hanƴar Babban falon fadar dan zuwa ɗakin sa.

Ganin su zaune akan dining suna karin kumallo ne ya sanƴa shi juyawa da niyyar komawa.
"ZEEYAD?" cewar mai Martaba ɗin, hakan ya sanƴa shi ja ya tsaya.

"Ka ƙaraso nan mana."

Kallo ya ƙarewa ƴan rainin hankalin kan dining ɗin kafin kuma cikin tsukewar fuska ya ƙarasa wurin ba tare da yabi ta kan kowannen su da kallo ba.

"Yes your Highness" ya faɗa bayan ya ƙarasa wurin.

Cikin kulawa mai Martaba ya kallesa yace "It's been decades da muka zauna tare da niyyar cin abinci, come on please have a seat and have breakfast with me."

"No, am full naci abinci a wurin Grandma."

"You only consider your Grandma as your family isn't it?, it's alright banga laifin ka ba" faɗin mai Martaba ɗin cikin rashin jindaɗin maganar ZEEYAD ɗin.

Tsayawa kallon sa ZEEYAD yayi kafin kuma yaja kujera ya zauna yana faɗin "Actually, you're also my family, you're my father, it's just that things were not as it was before."

"Yeah and it's all my fault."

"No please, stop blaming yourself for everything, let by-gone be by-gone" ya faɗa cikin dafa hannun mahaifin nasa.

Murmushi kawai mai Martaba yayi yana kallon ɗan nasa.

"I will dine with you someday" cewar ZEEYAD yana kallon sa.

Kallon sauran yaran dake zaune a dining ɗin mai Martaba yayi yace "Seems like duk kuna buƙatar a dawo da old rules na cikin MASARAUTAR nan, and this is exactly abinda zai faru ɗin kenan, ZEEYAD here is your eldest brother and you must show him respect where ever you see him."

Ɗagowa Ayaan yayi yace "But he should respect our mothers too, before he gain some respect from us."

"Ayaan" cewar mai Martaba ɗin a tsawace.

Tsaye Ayaan ya miƙe yana faɗin "Your Favorite boy here will never gain any respect from me, he should respect my Mom before na girmama shi."

"Guards" cewar mai Martaba ɗin.
Karasowa guards sukayi kafin yace dasu "Take him away."

A fusace Sarauniya Hafeezah ta tashi tace "Hold it right there" kafin kuma ta juyo gun mai Martaba tana faɗin "You can't get your son arrested sabida ya faɗi abin dake ransa."

"He should know how to respect his elders a duk inda ya gansu..."

"There is nothing to be respected here, everyone knows yadda ka tsani yaron nan..."

"That is because you cast a spell on me Hafeezah" faɗin mai Martaba cikin 6acin rai yana miƙewa tsaye kafin ya ɗaura da faɗin "Ina raga miki ne dalilin ƴaƴan dake tsakanin mu, and most especially because of my lovely innocent Son YAZEED, he would never be happy aduk sadda yaji na rabu da mahaifiyar sa, i know all your doings and how you made me hate my Son here duk sabida son zuciya irin naki, kada ki kuskura ki kai ni maƙura or else abin ba zai ta6a yi miki kyau ba" ya faɗa yana nuna ta da sandar hannun sa.

Sosai idanun Sarauniya Hafeezah suka raina fata dan haka shiru tayi ba tare da ta iya cewa komai ba.

Murmushin gefen baki Nazeerah ta saki tana tsakurar abincin gaban ta a hankali dan ma kar ta cinƴe drama bai ƙare ba kallo ya bar ta.

Miƙewa ZEEYAD yayi kafin yace "Calm down Abhi, why don't you get some rest."

Cike da 6acin ran da yake ciki yace "No, inaso a kira min manƴan ministoci na, i have an urgent meeting with them, it's time we put an end to things here, and it's time da yakamata a sauya salon mulkin wannan ƙasa zuwa wata tsarin daban, my son is back and now lokaci yayi da yakamata mulkin wannan ƙasa ta dawo hannun sa, ba sai na jira har rai yayi halin sa ba, and you Hafeezah get ready to sow what you reap, take the arrogant boy away and make sure kun hukunta shi ya gane kuskuren sa" yana faɗin haka ya baza alkyabar jikin sa yayi gaba tare da barin kowa da buɗaɗɗen ido da sakakken baki, musamman Sarauniya Hafeezah da takejin maganganun nasa tamkar a mafarki, ga kuma wani irin hajijiya da taji na neman ɗibar ta, wanda bata ma bi ta kan Ayaan dake ta faman kiran sunan ta ba yana son kwacewa daga hannun guards ɗin ba.







*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR....................✍🏽*
[8/21, 9:58 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*045...*



________Duk jigum sukayi suna sake bin inda mai Martaba yabi da kallo, ZEEYAD da yaji maganar tayi masa banbarakwai saurin marawa mai Martaba baya yayi zuwa ɗakin sa.

Zaune ya iske shi kan bed ya ƙure hoton Masoyiyar sa da idanu yana kallon.

Shigowar ZEEYAD ne ya sanƴa shi ɗago da idanu yana kallon sa, kawar da kai yayi daga kallon ZEEYAD ɗin zuciyar sa babu daɗi.

"Abhi?" ZEEYAD ya kira shi yana ƙarasawa kusa da ƙafar mahaifin nasa ya zauna.

Kallon sa mai Martaba yakeyi kafin kuma ZEEYAD ɗin ya buɗi baki yace "Abhi sometimes we need to let go of our past domin ganin present dama kuma future ɗinmu yayi kyau, dukkanin wani abinda ya faru tsakani na da kai a baya let's forget it mu ɗau hakan a matsayin ƙaddara, you're my father and someone i will always be proud of, i realized that dukkanin wani abu da ka aikata a baya wasn't on your own doing, i know you will never treated me so different after Mom's demise muddin ba tilasta ka akayi ba, so stop thinking negative tare da tunanin cewa koh ban yafe maka bane, na yafe maka long ago am now your son wanda zaka iya juya shi and treated him like kowane ɗa a cikin gidan nan, wanda zaka ce masa bari ya bari, sannan kuma ka umurce shi, shi kuma zaiyi maka biyayya, Abhi let's change things between us mu gina sabuwar alaƙa, show me a fathers love that i have long been craving for, and nikuma zan mutunta ka tare da baka dukkanin girman ka a matsayin ka na mahaifi na" ya ƙarashe yana riƙo hannun mahaifin nasa cikin nashi ya damƙe.

Sosai jikin mai Martaba yayi sanƴi yayin da kuma zuciyar sa ke cike da tsantsar farin ciki jin kalaman ɗan nasa inda hawayen farin ciki, tausayi dama kuma nadamar abubuwan da ya aikatawa ɗan nasa suka shiga gangaro masa.

Rungume sa ZEEYAD yayi cikin patting bayan sa yace "It's alright Abhi, let's build a new world together."

Ɗagosa mai Martaba yayi suna miƙewa tsaye cike da tsantsar ƙaunar da yake yiwa ɗan nasa yace "GOD bless you Son, haƙiƙa cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login