Showing 69001 words to 72000 words out of 236327 words
na kawo tata harin, ita kanta tasan idan ta mallaki ZEEDAN toh tabbas ta gama cirar tuta ne a cikin ƙawayen ta dama kuma abokan ta, dole ne su bata award ɗin mallakar wannan santalelen saurayin.
Duk tana tunanin nan ne cikin murmushi sabida burin ta na daf da cikewa.
Idanun ta ne suka faɗa kan wani ɗan ƙaramin gift da akayi wrapping ɗinsa.
Hannu ta kai ta ɗaukaka tana jujjuya shi tana kallo kafin kuma ta yaga ledar gift ɗin ta ciro kwalin tare da buɗe shi.
Idanu ta waro tare da furta "Wowww" tana ciro abin hannun dake ciki tana kallo.
Duk abinda take ZEEDAN bai kula ta ba dan kuwa idan yana yi mata magana ji yake haushi da takaicin kansa na kama sa.
"Is this for me?" ta faɗa tana kallon sa.
Ajiyar abin ta ya bata ba tare da ya koh kalle ta ba idanun sa na kan tuƙin da yakeyi.
Murmushi tayi tace "Am definitely sure nawa ne, ka saya ne dan kayimin gifting ɗinshi a Engagement ɗinmu, am sure nawa ne coz it's diamond and the design is so beautiful kai ne ka zana shi akayi maka irin sa?."
Da ƙarfi ya danna parking ɗin motar zuciyar sa na tafarfasa, hannu yasa ya warce bracelet ɗin a hannun ta yana maida shi cikin kwalin sa tare da ajiyewa a gaban sa.
Da kallo ta bisa cike da jin haushin abinda yayi mata tace "How dare you?."
Shiru yayi kafin yace "Get out of my Car."
Murmushi tayi tace "Your car?, kokuma motar da Daddy na yayi maka hanƴar samun kuɗin sayar ta?."
Juyowa yayi ya kalle ta kafin ya saki murmushin kan le6e yace "Your Dad?, Yes Dad ɗinki ne yayi min hanƴar samun aiki but don't forget cewa da gumi na nayi aiki na samu kuɗin da koh Dad ɗin naki bai mallaki irin su ba, you know what?, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda Dad naki da kuma Mom naki da suka kasance mutanen kirki, banaso nayi abinda zai 6ata musu rai, but tunda kince ba zaki gyara halayen ki ba then there is no way da zan dinga haɗa inuwa ɗaya dake, and this diamond bracelet here, not even your family can afford it, so there is no way da zan bar ki ki sanƴa shi coz it's not made for you, it's for someone so very special and dear to me, so now get the hell out of my car" ya faɗa yana kallon ta cikin tsukewar fuska.
Sosai ta sha jinin jikin ta da yadda yayi mata magana kuma yake kallon ta, sai dai tayi ƙarfin hali tace "Someone so dear and special to you, who the hell is she?" ta faɗa cikin rawar murya alamun ranta yayi mugun 6aci zuciyar ta na tafarfasa.
Scoffing yayi tare da maida duban sa kan box ɗin yace "Knowing who she is won't do you any good, out of my car....now" ya faɗa yana juyowa ya kalle ta.
"Am not going out, babu inda zanje har sai ka faɗamin wacece ita, you can't love someone idan ba ni ba, no one deserves to be loved by you except me Okay?, am not going out until you tell me who she is" ta faɗa idanun ta na kawo hawaye.
Cize baki yayi kafin ya buɗe motar ya fita yana zagayowa inda take ya buɗe yace "Get your fucking body out of my car."
Maƙe kafaɗa tayi tana harɗe hannaye a ƙirji tace "Babu inda zanje, taya zaka sauƙe ni a local area ɗinnan, and baka ga irin shigar dake jiki na bane, babu inda zanje ni."
Sai a sannan yama san irin shigar dake jikin ta, doguwar riga ce mai hannun vest irin ta turawa wanda koh guiwa bai kai mata ba duk fararen cinƴoƴin ta a waje, kanta kuma head-band kawai tasa tare da kama gashin ta da ɗan ƙaramin ribbon.
Kauda idanun sa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke tafarfasa, tabbas idan ya bar ta a haka bai kyautawa iyayen ta ba, sometimes kana yiwa mutum abu ne sabida irin halaye masu kyau da na kusa dashi kuma wadanda kakejin kunƴar su suka tara, idan ba haka ba wasu mutanen halin su ma kaɗai ya isa idan suna daf da faɗawa wuta basu sani ba,ka kauda idon ka a zumar cewa kai ɗinma bakasan da wutar ba.
Zagayawa yayi ya koma cikin motar tare da fizgar ta a tsiyace kai kace zai ɗauke kan kwaltar ne.................
_*Idan kuka jini shiru ku dinga yi min uzuri, duk ranar da baku ga posting da safe ba, toh kuyi haƙuri zuwa dare zaku gani, duk ranar da baku gani da dare ba toh kuyi haƙuri zuwa wayewar gari, yin typing da posting ba shi kaɗai ne aiki na a matsayi na ta ƴa mace kuma budurwa wacce ke gaban iyayen ta ba, dole ne da akwai abubuwan da sai anayi wa mutum uzuri, masu cewa har kun gaji da jira kun cire rai, ku daina faɗar haka please, banajin daɗi wlh👏🏽🥹*_
*Yawan Comment, Yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*023...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
_Ina Masoyan Amjad da Mhizz jidderh?, zamu fara sabon novel, wanda ba'a ta6a kawo muku irin shi ba, namu salon na daban ne, ya ƙunshi tausayi, ƙin biyayyah ga iyaye da Sauran su, kude ku kasance damu a wannan tafiya da zamuyi cikin littafin *BANI DA ZAB’I*, salon na daban ne, inaso ku nuna mana soyayya fiye da yadda kuka nuna mana a cikin ZEEYAD dama kuma TAREEQ👏🏽🥰_
*Wannan Page ɗin maimakon na jiya ne da banyi posting ba😆*
A matuƙar fusace yayi parking motar ya fito ba tare da yabi ta kanta ba ya nufi ƙatuwar ƙofar da zai sada shi cikin office nasa.
Murmushi Khairat ta saki tare da buɗo ƙofar ta fito kafin ta mara masa baya cikin takun ta ɗai-ɗai hannayen ta sarƙe a ƙirjin ta.
Lifter ya shige kafin ya sada shi da flour ɗin office ɗinsa.
Ba tare da yabi ta kan masu yi masa gaisuwa ba ya buɗe ta ya shige ƙofar ta rufu.
Ja yayi ya tsaya yana ƙare mata kallo ransa na matuƙar sake 6aci.
Zagayowa yayi tare da zama kan seat ɗin sa yana lumshe idanu.
"Babe?" ta kira shi.
Jin yayi mata shiru yasa ta cigaba da faɗin "Babe, yaushe rabon da ka ganni yanzu, amma koh nema na bakayi ba afterall ina chan hospital banida lafiya sai jiya aka sallame ni, but you didn't even bother to know my whereabout, ka kyauta da hakan kenan?" ta faɗa tana kallon sa.
Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta cike da haushi yace "Bakida lafiya ai ba mutuwa kikayi ba, sannan maiyasa zan neme ki ai tun da chan ma kece kike nema na, i thought kin.saduda kuma kin rabu dani ne but i can see har yanzu kina kan bakar ki."
"Babe please maiyasa kakeyi min haka ne, maiyasa ba zaka soni ba koh da bai kai wanda nakeyi maka ba, dan Allah kaji tausayi na mana...."
Sauƙar marin da taji a ƙuncin ta ne yasa ta saurin dafe kumatu tana, hannayen ta riƙe da ƙunci tana ɗagowa ta kalli Khairat dake ta huci kamar zata haɗiƴe ta.
Tashi Surayya tayi tsaye hannayen ta har yanzu dafe da ƙunci tana kallon Khairat cike da mamaki.
Hannu Khairat ta ɗaga da niyyar kai mata wani marin tayi saurin riƙe hannun nata.
Daddagewa tayi itama tare da baiwa Khairat wani irin zazzafar mari a fuska.
"How dare you?" cewar Khairat cike da mamaki tana kallon Surayya.
"Kokuma how dare you ba, who gave you the gut da zaki faɗo from nowhere ki mare ni har ma kike ƴunƙurin ƙarawa, dayake nikuma sakarya ce kike tunanin na barki ki mari banza kenan komiye, who the hell do you think you're?."
Sosai ran Khairat ya 6aci, nan kuma tace "He is my Man, so you better stay away from him indai kinason kanki da lafiya."
Riƙe kunkumi Surayya tayi tana kallon Khairat from head to toe tace "Hun, your Man or my Man?."
Kallon ZEEDAN da ya miƙe tsaye yana shirin ficewa Khairat tayi kafin tayi saurin shan gaban sa tana faɗin "Ina kake tunanin zakaje, ya zama dole ne ka tsaya ka warware ƙullin da ka haɗa sannan kuma kayi min bayanin wacece wannan karyar dama kuma matsayin ta a wurin ka, idan kuma ba haka ba sai na tabbatar da nayi mata mugun illa anan wurin."
"Alright go ahead then, tunda ke Mahaukaciya ce" ya faɗa yana ra6a ta ya wuce.
Da sauri ta riƙo kwalar rigar sa ta baya tana shan gaban sa tace "Na faɗamaka babu inda zakaje ka, ya zama dole ne ka faɗamin koh wacece ita" ta faɗa cike da 6acin rai idanun ta na yin jaa sabida irin muguwar kishin dake cinta.
Kallon Surayya yayi yace "Try to defend yourself from her, dukkanin ku bakuda wani value a gare ni, so why would i waste my time wurin ganin haukan ku, after all i have alot of important things to do" ya faɗa yana maido duban sa kan Khairat.
"ZEEDAN, wacece wannan ɗin wai, maiyasa take abu kamar mahaukata?."
"Kece mahaukaciya, jaka kuma akuya mai maƙalewa mazan mutane, toh bara kiji na gayamiki ZEEDAN nawa ne gara kinyi gaggawar zuwa kin samu wani saurayin, amma aure tsakani na dashi tamkar an ɗaura ne."
Kallon ta kawai Surayya take kafin kuma tayi murmushi tace "Au ashe ma dai kice layi ɗaya muke dukkanin mu ɗin akuyoyi ne tunda kema binsa kike tsirara, GOD forbid ZEEDAN ya auri mahaukaciya irin ki, ai baikamata kice ni ina binsa ba tunda kema ba wai an ɗaura auren naki dashi bane, bale ma kuma ba auran naki zaiyi ba."
Zuwa tayi zata riƙo Surayya nan tayi saurin ja da baya tace "GOD forbid bad things, wai kina nufin faɗa zakiyi dani, ashe ma bakida aji koh kaɗan gaki nan dai kamar wayayyiya amma kwakwalwar babu saiti, naji ZEEDAN baya sona amma koh bakomai yafi sona akanki koh dan hauka da rashin kamun kai dake tattare dake, jaka kawai" ta ƙarashe haɗi da jan dogon tsaki tare da fuzgar jakar ta ta bar cikin office ɗin, dan kuwa ZEEYAD tuni ya daɗe da ficewa ya bar su.
Daskarewa khairat tayi tsaye anan hawayen baƙin ciki na kawo mata, ta lura idan ba tsaye tayi akan wannan banzar Surayya ɗin ba, ba zata rabu da ZEEDAN cikin sauƙi da kwanciyar hankali ba.
A matuƙar fusace ta fice daga office ɗin itama zuciyar ta na matuƙar ƙuna sosai.
Koh da ta fita farfajiyar Company ɗin, bata hango motar ZEEDAN a parking space ba, hakan na nufin tafiya yayi ya barta kenan.
***********************
Zaune suke dukkanin su a ƙatuwar falon gidan da ya ƙawatu da kayan alatu da more rayuwa iri-iri, tsaya musalta girman falon da kyawun sa 6ata lokaci ne.
Khairat ce rungume jikin wata kyakkyawar mata sai kuka take kamar ranta zai fita, inda kuma matar ke ta rarrashin ta.
ZEEDAN kuwa a ƙasa yake zaune kusa da wani babban mutum falon ta ɗau shiru babu abinda kakeji sai sautin kukan Khairat.
Numfasawa mutumin yayi tare da gyaran murya yace "ZEEYAD ɗana, kaji dai bayanin da Khairat tayi, shin dagaske ne kana kula wata daban a waje?."
Shiru ZEEDAN yayi kafin kuma ya saita nutsuw sa yace "Hakane, amma maganar gaskiya shi ne yarinƴar itace take bibiya ta, babu soyayyar ta koh kaɗan a cikin zuciya ta, nayi dukkanin iya ƙoƙari na na ganin ta rabu dani sai dai taƙi yin hakan."
Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe kafin yace "ZEEYAD nasan ba zakayi min ƙarya ba, amma inaso ka faɗamin tsakani da Allah, akwai soyayyar Khairat a zuciyar ka koh babu?."
Shiru ZEEDAN yayi yaji tambayar tayi masa mugun nauyi da tsauri, tayaya zai fara buɗar baki a gaban su yace bayason ƴar su?, bayan su kuma sun nuna masa so da ƙauna tamkar su suka haife shi, idan yace yanason Khairat then ya cuci kansa, idan kuma yace bayason ta baisan wane irin kallo zasuyi masa ba.
"Kayi shiru ZEEYAD, ka faɗi ra'ayin ka, babu wanda zai tilasta maka, koh dai akwai wacce kakeso ne daban, ka faɗamin nikuma nayimaka alƙawarin nemo maka auran ta."
_"MADEENAH, but bataso na, she loves someone else, ba zai iya raba ta da abinda takeso ba muddin hakan ne zai sanƴa ta farin ciki, she seems so happy with that guy, she would never be happy with me, sai ma burin ta kaɗai da mafarkin ta da zan ruguza"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma cikin dauriya yace "No."
Haɗa ido Momy da Daddy sukayi tare da yin murmushin jindaɗi, nan Daddy yace "Masha Allah, kana nufin a shirye kake da ka auri Khairat, sannan kuma kanason ta?."
Kai ya jinjina kawai ba tare da ya iya cewa komai ba.
Murmushi sukayi kafin duk su furta "Alhamdulillah."
Momy ce tace "Toh ai sai ki share hawayen naki hakanan koh tunda kinji abinda ya faɗa, ki bar sanƴawa kanki damuwa hakanan" ta faɗa tana sharewa Khairat ma dake murmushi hawaye.
"Masha Allah, kasan nan da kwana uku ne Ranar sa ranar auren ku, zamu tattauna batun da kawunan ta dama kuma mahaifiyar ta dan ganin yaushe yakamata a sanƴa ranar auren."
Kai ya jinjina kafin yace "I need to go, inada aiki a office."
"Bakomai, zaka iya tafiya."
Miƙewa yayi idanun sa sunyi matuƙar yin duhu yanajin kansa na sara masa ya fice daga cikin falon.
Motar sa ya shiga yana kifa kai akan steering zuciyar sa nayi masa zafi sosai.
Tunanin family ɗinsa ya shiga, tayaya yana da family kuma wasu suzo su ɗaura masa aure da ƴar su?, yana tunanin yanzu lokaci yayi da zai koma garesu, bayason ɗaura wata damuwa koh nauyi akansa, dan kuwa har yanzu zuciyar sa bata bar ƙuna tare da kwaɗayin ɗaukar fansar abinda sukayi masa ba, a duk sadda ya tuna dasu yanajin wutar tsanar su na sake ruruwa masa ne a zuciya, especially mahaifin sa da ya kasance Sarki ya kuma kasa kula dashi, baya tunanin zai yafewa kowanne daga cikin su, dukkanin su sai sun ɗanɗani guɗar su ne, yayi alƙawarin ba zai bar kowa ba, sannan kuma zaiyi mulkin da ba'a ta6a yin irin sa a ƙasar ba, bayason tunowa dasu shiyasa ya toshe dukkanin wata hanƴa da zai sanƴa sa yin kasuwanci da ƴan ƙasar kokuma yaji wani labari da ta shafi ƙasar, hakan yasa bayason kallon News dan gudun ma kada ya kalli wani abu game da ƙasar da zai sanƴa sa cikin damuwa ya hana shi sukuni, balle kuma ya tuna masa da cewa shi ɗin ɗan Sarki ne.
Hannun sa ya nausa akan steering ɗin idanun sa na matuƙar yin jaa sosai, fuskar sa ta canza launi zuwa jaa, sosai baƙin ciki da 6acin rai suka sake samun gurbin zama a cikin zuciyar sa.
Wacce yake tunanin zata zame masa waraka kuma wani daban takeso, wani chan daban da baikamata ace shi zata so ba, amma ta bar zuciyar ta ta rinjaye ta ta fara sonsa.
A haka yaja motar tasa ya bar cikin gidan zuwa gidan sa.
********************
Tsaye yayi a gaban ƙatuwar hoton ta da ya zana yanajin baƙin ciki sosai ganin ba shine zai mallaki DEENAH ba.
Zuciyar sa DEENAH takeso ba Khairat ba, sai dai sun kasa gane hakan, tayaya suke tunanin zai iya buɗar bakin sa yace musu wata daban yakeso ba ƴar su ba, bayan irin halarcin da sukayi masa a rayuwa?.
Sauƙe jajayen idanun sa yayi cikin nata yana kallo, maganganun da ta faɗa masa ne suka shiga dawo masa cikin kwakwalwa.
_"Am not lying, gaskiya nake faɗamaka, baka kai matsayin da zanyi maka ƙarya ba, idan ma kana tunanin inason ka ne yasa kullum kake bibiya ta then you're wrong, coz am inlove with someone else, and you know what?, yana da halaye masu kyau, sannan kuma ya tara dukkanin qualities ɗin da ake nema a wurin miji na gari, Unlike you da bakasan koh ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, wanda bakada aiki sai kula matan banza sannan kuma kayi dukkanin abinda kaso dasu, kana tunanin ni irin matan nan ne da har zaka dinga bibiya ta dan kawai ka samu damar shawo kaina ka kuma yaudare ni da kalaman ka, ka cika mummunar manufar ka a kaina?"_
Zubewa yayi akan couch yana runtse idanun sa "Please don't do this to me" ya faɗa cikin rawar murya.
Wayarsa dake kan center table ce ta ɗau ringing ɗin da ya tsinkar masa da zuciya tare da faɗar masa da gaba.
Kallon wayar ya tsaya yi har ta tsinke bai iya ɗagawa ba.
Sosai yaji gaban sa na wani irin mummunar faɗuwa har wani kiran ya sake shigowa.
Hannu ya kai ya ɗau kiran yana kafawa a kunne.
Muryar Jafar yaji cikin kuka, hakan yasa shi miƙewa tsaye yace "Tell me."
Bansan mai Jafar ya faɗa masa ba, wanda ya sanƴa