Showing 231001 words to 234000 words out of 236327 words

Chapter 78 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45329

ɗansa suma ki kashe toh insha Allah kin gama yawo a duniyar nan, ya zama dole ne ki girbi abinda kika daɗe kina shukawa, miye ribar ki yanzu, ribar mai kikaci a aikata sharri cikin rayuwar ki Hafeezah,gashi nan ke da kanki kinzo kina tonawa kanki asiri, ai dama Allah ba zai ta6a barin ki ba, mutuwa ta tabbata akanki Hafeezah, a rayuwa sharri kaɗai kika maida abinci da shan ki dama kuma suturar ki, kaicon ka YAZEED bawan Allah bakayi dacen uwa ba kaga abinda uwar ka ta janƴowa kanta, Allah ne kaɗai yasan dalilin sa na jarabtar ka da uwa kamar Hafeezah yaron kirki ɗan albarka" ta ƙarashe tana goge hawayen fuskar ta da bakin mayafin jikin ta.

YAZEED komawa yayi ya zauna tare da sadda kansa dake barazanar tarwatse wa, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi masa zarya jin kayan kunƴar da mahaifiyar sa ta aikata, sosai yake ƙarajin tsanar ta na ninkuwa cikin zuciyar sa, da wane irin ido zai dubi ɗan uwan sa, shi kaɗai yasan mai yakeji cikin zuciyar shi, ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse, wani irin ciwon kai mai tsanani ne yaji ya kama shi gashi dama yanzu yake farfaɗowa daga rashin lafiyar da yake.

Saurin riƙo sa JALILAH tayi tanajin wani irin tausayin sa na ratsa dukkanin zuciyar ta, tabbas Allah ya jarabce shi, Allah ne kaɗai yasan irin halin da yake ciki sannan mai yakeji a yanzu.

Runtse idanun sa dake yi masa zugi ZEEYAD yayi, maganganun Hafeezah jinsu yake tamkar ana feshe zuciyar sa da tafasasshen ruwan zafi.

Mai Martaba zubewa yayi kan kujerar da yake dan kuwa idan ya cigaba da tsayuwa toh tabbas zai iya zubewa anan koh a ɗauki gawar sa ma.

Guards ɗin dake tsaye ne suka zo suka tafi da Hafeezah, dukda iriyar ihun sai ta kashe ZEEYAD da iyalan sa da take tana neman kwacewa basu sake ta ba.

Fadar ce ta ɗau shiru sai shessheƙar Grandma kawai akeji, DEENAH rasa nayi tayi tama rasa wurin wa zata fara zuwa tayi comforting, tsaye ita ɗinma tayi hawaye sun gama wanke mata fuska.

Da kyar ZEEYAD ya iya motsa ƙafar sa yaa fara tafiya dan barin cikin fadar.

Kallon sauran tayi kafin tayi saurin mara masa baya.

Ja tayi ta tsaya bakin ƙofar ɗakin su durƙushe ta ganshi kan guiwowin sa bayan sa take kallo kafin ta shiga takawa a hankali dukda kuwa tsoron tunkarar tasa take.

Zagayowa tayi gaban sa tana ta6a shi tare da kiran shi a hankali "Abyad?."

Ɗago da jajayen idanun sa da suka ƙanƙance yayi yana zuba mata su kamar jira yake ta shigo ya rungume ta sosai yana runtse idanun sa, sosai takejin yadda zuciyar sa ke gudu da sauri-sauri kamar zata 6allo ƙirjin sa ta fito, sake ƙanƙame shi tayi a jikin ta wani irin tausayin sa na ratsa zuciyar ta, a hankali take hura masa iskan bakin ta a kunne tana patting bayan sa gently dan ganin ya sauƙo daga fushin da yake ciki.

Hawayen da yayi shekaru da shekaru yana jiran fitowar su ne suka shiga yi masa zarya a fuska yana sake ƙanƙame DEENAH, sosai jikin sa ke rawa zuciyar sa na sake yi masa zafi, sun jima a haka ƙanƙame da juna har izuwa lokacin da taji gudun zuciyar tasa ta sassauta.

Lumshe idanu tayi tana cigaba da rubbing bayan sa gently, ɗago da fuskar sa da tayi jaa sosai tayi tana kallon sa, haɗe bakin su tayi tana basa cool kiss kafin ta ɗago tana sake rungume shi a jikin ta, a hankali ta shiga faɗin "It's alright" tana ɗan bubbuga bayan shi.


*****************************


*THE NEXT DAY........*







*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[9/10, 2:30 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *FINALE🤸🏽‍♀️*
*(FINAL)*




*Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


*055*


_______Kai da komowa mai Martaba keyi cikin ɗakin sa, kansa a matuƙar ƙulle yake, ya rasa ta ina zai fara 6ullowa wannan lamari na Hafeezah, babu wanda yafi tausayawa kamar YAZEED ɗan albarka, tayaya zai fara yankewa mahaifiyar da hukuncin kisa a gaban sa, sai dai kuma wani 6angaren na zuciyar sa na umartar sa da ya shashashantar da lamarin YAZEED ya yanke mata hukunci a bisa dokar Allah (SWT), ya sauƙe mata dokar MASARAUTA koh dan albarkacin YAZEED ma, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana maida duban sa kan hoton QUEEN MOTHER, ya jima yana kallon hoton nata kafin kuma ya sauƙe numfashi tare da ɗaukar sandar tafiyar sa a hankali cikin takun ƙasaita ya bar cikin ɗakin nashi.

A fadar sa ya yaɗa zango inda ministocin sa ke zaune suna jiran fitowar sa, tattaunawa sukayi sosai kafin kuma duk su miƙe su nufi filin da aka ware dan yankewa masu laifi hukunci.

Sosai mutane suka hallara tsofi da manƴa dama kuma ƙananun dan shaidawa idanun su irin hukuncin da za'a yankewa matar sarki Hafeezah.

Inda aka ware na zaman mai Martaba ya nufa ya zauna sai dai ya gama wulla idanun sa bai hango ZEEYAD da YAZEED ba anan wurin.

Bafaden dake tsaye a kansa yayi wa magana kan ya dubo masa su, cike da girmamawa ya amsa masa kafin ya bar wurin kafin wani yayi saurin replacing wurin tsayuwar sa yana ƙamewa.

***************

_______Zaune YAZEED ɗin yake yayi jugum dashi, kwakwalwar sa cunkushe take da tunanika kala-kala, he can't believe wai uwar da ta haife sa za'a yankewa hukuncin kisa a gaban ɗumbin mutanen gari, sosai yakejin wani iri a ransa, baya tunanin zai iya fita zuwa wurin taron nan, dan kuwa ba zai iya shaida irin hukuncin da za'a yi mata ba, sosai zuciyar sa ke rawa tana karyewa, shi kaɗai ya san abinda yakeji.

Knocking yaji daga bakin ƙofar ɗakin nasa ba tare da ya bada izinin shigowa ba JALILAH ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo, tsaye tayi tana kallon sa cike da tausayawa, ɗagowa yayi ya kalleta kafin kuma ya kauda kansa ƙasa.

Idda shigowa tayi tana zama kusa dashi tare da dafa kafaɗun sa tace "Inaso ka sani cewa, Allah ya ɗaura maka wannan ƙaddarar ne ba dan bayason ka koh baya ƙaunar ka ba, koh wane bawa mai imani Allah na jarabtar sa ta fanni daban-daban dan ganin ƙarfin imanin sa, haƙiƙa kai mai imani ne hakan yasa ka iya tsallake duk wani tuggu da mahaifiyar tayi ƙoƙarin cusa maka a baya haka kuma Allah na son ka da rahama hakan ya sanƴa shaiɗan baiyi galaba akanka ka biye mata ba dukda cewa ita ɗin mahaifiya ce mai iya umarta ayi ba tare da musawa ba, Allah na sonka da rahama YAZEED kada ka ta6a manta wannan, dah ace bayason ka na tabbata da kai za'a yankewa wannan hukunci ba iya mahaifiyar ka kaɗai ba, ka godewa Allah da ya sanƴa ka zamtowa mai tsarkakakkiyar zuciya, irin ƙaddarar mahaifiyar ka kenan babu wanda ya isa ya gujewa hakan koh ya canza shi, kayi haƙuri, kayi haƙuri YAZEED ka rungumi jarabawa, ba zaka ta6a iya canza ran sarki ba akan hukuncin da zai aiwatar, koh ka manta faɗin Allah ne na cewa duk wanda ya kashe shima a kashe shi, da akwai mutane da dama da suka shuɗe da tasu jarabawar tafi taka tsarkakiya da wahala amma sunyi haƙuri sun jure gashi komai ya zamto labari su kansu sun zamto labari, inaso ka sani cewa ZEEYAD ma bayida mahaifiya amma yana da mata, Kaka, mahaifi dama kuma ɗa, kaima kuma hakan take a wurin ka, kana da mahaifi, Grandma ta ɗauke ka tamkar ZEEYAD ne, kanada mata sannan kada ka cire ran zaka samu ɗa wataran kaima, mai yafi samun wadannan abubuwa farin ciki a rayuwa?, har yanzu kana da family ZEEYAD, Grandma, Mai Martaba, DEENAH, Rahinah, little ZEEYAD, Ayaan dama kuma ni, na tabbata wadannan sun isa su samar maka da farin cikin da kakeso na har abada, kayi haƙuri haka nan, ka sani rayuwar da ZEEYAD yayi fama da ita a baya ta wuce ƙuncin da kake ciki a yanzu, yanzu kuma da ya gano mahaifiyar ka ce tayi sanadiyyar mutuwar tasa mahaifiyar ya kuma ganka cikin halin ƙunci sabida za'a yankewa mahaifiyar ka hukunci mai kake tunanin zaiji cikin ransa cewar bakason a ɗaukar wa mahaifiyar sa haƙƙin ranta komiye?."

Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana sanƴawa cikin nata da take kallon sa, murmushin kan le6e ta saki tana riƙo hannun sa cikin nata kafin ta cigaba da faɗin "Nasan ba zaka so yaji wani abu game da hakan ba, ka ɗauki QUEEN MOTHER tamkar mahaifiyar ka ne, dan haka ka ɗauka cewa mahaifiyar ka ta daɗe da mutuwa kaima tamkar ZEEYAD, sannan ka sanƴa a ranka cewar fansar ranta za'a ɗauka yanzu tamkar yadda Ubangiji ya halatta, kada ka kuskura ka bari ɗan uwanka ya gano kanajin ƙunci game da wannan lamari, nasan it will be hard for you, sabida har yanzu jinin ta ne ke yawo a jikin ka amma daurewa zakayi, daurewa zakayi YAZEED ka maida komai ba komai ba, ka toshe idanuwan ka da kunnuwan ka ka cire damuwar hakan tattare da kai idan kayi hakan then with time zakaji komai ya zamto tarihi cikin rayuwar ka lokacin da ka buɗi ido ka ganka zagaye da family ɗinka masu sonka kuma kullum suke ƙoƙarin ganin sun sanƴa ka farin ciki, bin hukuncin Allah shi kaɗai zai haifar da zaman lafiya cikin zuri'a dama kuma ƙasa baki ɗaya, ƙuncin da zakaji na lokaci ƙanƙani ne nayi maka alƙawarin hakan da zaran kaga kowa cike da farin ciki da walwala ba zaka san sadda kaima zaka warware al'amura su cigaba da tafiya dai-dai tare da kai ba, i know it's hard YAZEED but na ƙanƙanin lokaci ne bi-iznillah" ta ƙarashe tana kallon sa kamar yadda yake kallon nata.

Sosai yaji kalaman ta sunyi matuƙar tasiri tare da sanƴaƴa masa zuciyar sa, ya ɗauka ba zai ta6a samun sanƴi cikin zuciyar sa nan kusa ba, sai dai kuma cikin ƙanƙanin lokaci kalaman JALILAH suka sanƴaƴa masa zuciya tare da bashi hope ɗin tabbas watarana komai zai zamto tarihi tamkar ba'ayi ba haka kuma farin ciki marar yankewa zata darsu cikin wannan family nasu, gusar da gur6atattun mutane kamar mahaifiyar sa daga cikin ahali dama kuma ƙasa baki ɗaya shi kaɗai ne hanƴar wanzar da farin ciki marar yankewa, shima damƙe hannun ta yayi cikin nashi yana jinjina mata kai yayin da murmushi ke wanzuwa kan fuskar sa.

Maida masa martanin murmushin JALILAH tayi tanajin daɗi sosai a ranta na yadda ta kwantar masa da hankali, sun daɗe suna kallon juna kafin kuma yayi saurin kauda kansa yana miƙewa tsaye.

Tsaye itama ta miƙe kafin tace "Nasan abu mai wuya ne kaje wurin taron nan, zaka iya kwanciya ka huta koh zaka sami ƙarfin jikin ka."

Kai kawai ya iya jinjina mata, murmushi tayi ta nufi hanƴar ficewa.

"JALILAH" ya kira sunan ta, tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon sa "Thank you" yace da ita, murmushi tayi masa kawai kafin ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice.


********************

_______Cikin mutane tayi ta ratsawa cike da tashin hankali har ta iso inda mahaifin nata ke zaune da gudu tazo zata isa garesa wani dogari yayi saurin tare mata hanƴa da takobin hannun sa.

A tsawace tace dashi "Get out of my sight you stinking being" ta ƙarashe cikin wulla masa mugun kallo da idanun ta da sukayi jazir alamun tasha kuka ta gaji ne.

Hankalin sarki ne ya dawo kansu, fuskar sa ya sake ɗinkewa ganin Rahinah ce tsaye tana yiwa dogarin rashin kunƴa.

Cikin tsukewar fuska wannan dogarin yace da ita "Mai Martaba baya buƙatar ganin kowa yanzu har sai bayan an aiwatar da abinda ya tara jama'a anan wurin."

Hannu ta ɗauke ta wanke fuskar sa da mari kafin ta nuna sa da yatsa tace "How dare you, uba na ne shi dan haka babu wanda ya isa ya hane ni daga zuwa ganin sa a duk lokacin da naso, ƙasƙantaccen bawa kamar ka bai isa ya taremin hanƴa da sunan tsare ni daga zuwa wani wuri ba musamman ma wurin mahaifi na, so get your ugly face out of my sight now."

Sosai dogarin yaji zafi cikin zuciyar sa, sa'ar ta ɗaya ita ɗin ƴa ce ga sarki dah kuwa babu abinda sai hana shi tattaka ƴar banza ƙaramar yarinƴa da ita.

Hanƴa ya buɗa mata nan tayi saurin wucewa tana aika masa da mugun kallo, kafin ta isa ga mahaifin nata tana zubewa a gaban shi tare da riƙo ƙafafun sa.

Cikin kuka take faɗin "Abhi dan Allah, dan Allah ka kyale Ummie kada ka yanke mata wannan tsattsauran hukuncin, ka tuna fah mahaifiyar mu ce tayaya zaka yanke mata hukunci gaban mu?, Abhi gashi Ayaan ma yana chan asibiti kwance rai a hannun Allah, hannun sa sai ƙara ciwo yake infection ya shiga likitoci sun ce zasu sake yanke masa hannun, dan Allah Abhi kayi haƙuri kada kayi mana haka, ina zamu sanƴa ranmu idan ka ɗauke mana Ummie, ita kaɗai ce gatan mu kuma ita kaɗai ce mai son mu, dan Allah kayi haƙuri ka janƴe maganar hukuncin nan" ta ƙarashe cikin fashewa da wani irin matsanancin kuka.

Sosai jikin mai Martaba yayi sanƴi, yana tausayin yaran nasa sai dai hakan ba zai hane shi daga aiwatar da abinda ya zamto wajibi a gareshi ba, dukkanin wani baƙin hali daga gun mahaifiyar su suka ɗauko shi, shiyasa kaf cikin ƴaƴan sa yafi ƙaunar ZEEYAD da YAZEED sai kuma ƴaƴan Nazeerah wadanda kowacce ya aurar da ita tun suna 18yrs kuma alhamdulillah suna nan zaune gidan mazajen su lafiya ba tare da sun ta6a kawo masa rahoton wata matsala ba dan kuwa yasan halin mahaifiyar su suka biyo wacce bata shiga sabgar da bata shafe ta ba take kuma ɗauke ido akan dukkanin wani abu da ta gani muddin ba wai ka tambaye ta bane ba, sa6anin Ayaan da Rahinah da koh kaɗan basu ɗauko hali mai kyau ba sai karatun da uwar su Hafeezah ta koyar dasu, yanajin tausayin wannan rayuwar tasu sai dai ya zama dole ya yankewa Hafeezah hukunci koh suma sa samu su gyara halayen su dan kada hakan ya faru a kansu nangaba.

"Take her away" kawai ya iya faɗa, sake riƙo ƙafar sa tayi tana kuka tare da kiran sunan sa amma yayi mata biris har aka fitar da ita daga wannan wurin.

Taro ne ya sake cika mutane sai halarta suke, ganin ƴaƴan nasa basuda niyyar fitowa ya sanƴa shi bada umarnin a fito da Hafeezah dan yanke mata hukunci.

Ba'a jima ba aka kawo ta hannayen ta ɗaure da chain, kallo ɗaya zakayi mata ka hango tsantsar tashin hankali da firgici akan fuskarta, ganin yawan mutanen da suka hallara ne ya sake darsar mata da tsoro tare da gasgata mata cewar dagaske fah yau tata zata ƙare a duniyar.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi mata zarya akan kumatu, wani irin nadama, tsoro dama kuma fargaba na sake darsar mata cikin zuciya, sosai take nadamar abubuwan da ta aikata wanda daga ƙarshe bata ci kyakkyawar ribar komai daga cikin sharrin da ta aikata ribar ta kuwa shine hukuncin kisa a gaban ɗumbin jama'ar gari idon kowa na kallo, sosai ta shiga yin kuka tana ta shiga uku ta lalace a yafe mata ba zata ƙara ba.

Biris guards ɗin dake biye da ita sukayi har suka rakata zuwa inda zata hau a rataye ta ɗin.

Zubewa tayi a wannan wurin tana cigaba da kukan da ba zata amfanar da ita komai ba, babu abinda take tunani sai iriyar rayuwar da tayi a baya kamar ba zata mutu ba, tayi ta cutar da bayin Allahn da basuji ba basu gani ba dukda sunan ita mai mulki ce, ta kashe innocent baiwar Allah LATEEFAT duk dan son zuciyar, ta kuma wulaƙantar da rayuwar ZEEYAD sabida bata tsoron Allah bata tuna ranar ƙin dillanci, bata tuna cewar zata mutu fah wataran, gashi mai mulkin da babu irin sa a yau ya nuna mata iyakar ta, ya nuna mata cewa babu wani sarki koh mai mulki sai shi, ya nuna mata cewar duniyar a hannun sa yake, ya nuna mata cewa baya gyangyaɗi bale bacci, ya nuna mata cewa shi mai ji ne jin da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake, ya nuna mata cewa kowane ɗan adam nada iyakar sa a rayuwa sannan ya nuna mata cewa lokaci kowane ɗan Adam ke jira, lokacin da ya tanadar masa na ranar girbar abinda ya shuka walau alkhairi ne koh sharri.

Sosai take kuka kamar ranta zai fita, koh kaɗan babu wanda yaji tausayin ta a wannan wurin sai ma shewa da mutane ke tayi kan cewar _A kashe ta_, sosai wannan kalma da suke ambata ke sake firgitar da ruhin Hafeezah, ji take kamar ta nutse a wurin saboda kunƴa, sosai zuciyar ta ke mugun bada sauti mai cike da tsoro da firgici ganin dai tsakanin ta da mutuwa bai wuci taku ɗaya ba, mutuwa na jiran ta a gefe, babu damar tuba koh neman yafiyar Ubangiji, sabida bakin alƙalami ya riga ya bushe, sauƙin ta ɗaya a kashe ta kamar yadda ta kashe ta haka ne kaɗai zata ji sassauci cikin kabarin ta, though ta riga da yanke wa kanta cewar makomar ta ba mai kyau bace, sannan wannan hukunci da za'a yi mata yanzu ba hukunci bane hukunci sai taje cikin kabarin ta inda zata tadda babu kowa sai ita sai kuma halayen ta be it masu kyau ne koh munana.

Murya taji an bada umarnin a aiwatar da hukunci, nan fah ta sake ruɗewa har dasu sakin fitsari mai zafi da zawo a wando tsabar tsoron mutuwa da tsoron abinda zata tarar a rayuwar da zatayi har abada babu mutuwa nangaba, bata ankare ba taji a ɗaure mata hannaye ta baya an rufa mata baƙar hula akan fuska tare da saƙala mata igiya a wuya.

Kalmar shahada malamin dake kusa da ita ke bata amma inaaa Hafeezah koh jinsa bata yi tsabar fargaba da tsoron da ya rufe ta ga kuma harshen ta da yayi mugun nauyi, babu abinda take sai ihu kamar zata shiɗe tana kiran sunan mai Martaba da ƴaƴan ta musamman YAZEED akan ya taimake ta gasu nan zasu kashe ta, haka wannan malamin ya kyale ta yaja gefe, matse mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login