Showing 45001 words to 48000 words out of 236327 words

Chapter 16 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45361

wallahi" cewar Aisha.


"Kiyi ta addu'a maybe ke ki zama."


Shigowar MADEENAH yasa su duk maida duban su gareta kowacce cikin sakin fuska.



Ɗan murmusawa tayi tana kallon su kafin tace "Ina wunin ku?."

Duk amsa mata sukayi da "Lafiya ƙalau."


Kallon Anty Khadija tayi tace "Dan Allah anty Khadija kinga headphone ɗina?."



Shiru tayi bata kula ta ba sai ma cigaba da zana kwalliyar ta da take.



"Anty Khadija magana fah nake, kodai fushi kike dani ne?."



"Ɗaga min kanki" cewar Anty Khadija tana faɗawa wacce take yiwa kwalliyar.



"Anty Khadija dan nace ba zan biki bane kike fushi dani?."



"Kai Khadija ba dake ake magana bane wai?" cewar ɗaya daga cikin ƙawayen nata.



Suma ƙin kula su tayi ta cigaba da harkar gaban ta, DEENAH kuwa ficewa tayi hawaye na kawo mata na rashin jindaɗin manna mata da Khadija tayi.



"Nikam, dakyar nake iya ɗauke idanu na akan yarinƴar nan" cewar ɗaya daga cikin su.



"Aikuwa dai wallahi nima, ta haɗu ta koh ina dama nice" cewar Aisha.


Duka ɗaya ta zuba mata tace "Cha6 idan kece da wannan kyawun ai mun boni a cikin garin Sokoto wallahi."


Dariya sukayi kafin ɗaya tace "Wallahi babu saurayin da ba zai santa ba,bama cikin garin Sokoto kaɗai ba kaf Nigeria."



Haka nan sukayi ta hirar su har aka gama yi wa kowace kwalliya masha Allah dukkan su sunyi kyau sosai sun sha anko abin su gwanin ban sha'awa.


Duk fitowa sukayi zuwa falon gidan anan suka tadda su Mami, Amirah da ma kuma MADEENAH.


Duk sake gaida Mami sukayi kafin Khadija tace da ita "Mami sai na dawo."



"Zo nan" cewar Mami ɗin.


Zuwa tayi ta zauna kusada ita tace "Gani Mami."



"Mai MADEENAH tayi miki tana yi miki magana kin share ta?."



Kallon DEENAH tayi kafin tace "Babu abinda tayimin Mami."


"Ƙarya kike, babu abinda tayi miki kuma tana yi miki magana kina share ta, hakan ya kyautu kenan Khadija, mutum yazo muku hutu amma kina nuna mata halin nan, ƴar uwarki ce fah miye amfanin hakan toh?, bana fah son irin abin nan na faɗamiki."


"Mami dan fah kawai MADEENAH tace ba zata bita dinner ɗin ƙawar su bane yasa take ta nuna mata halin koh inkula" cewar Amirah.



"Toh dinner ɗin na ƙanwar uwarta ne da zakice sai kin tilasta ta ta tafi?" cewar Mami cike da mamaki.


"Mami ni fah kawai gani nayi yawan zaman ta cikin ƙunci yayi yawa shiyasa na kawo idea ɗin tafiya da ita koh zata rage shiga damuwa, amma tunda tace bata so ai shikenan" cewar anty Khadija.


"Toh ana dole ne, kema sai na hana ki tafiyar yanzu iskanci kawai" cikin faɗa Mami ta faɗi hakan.



"Mami zanje" cewar MADEENAH.


Kallon ta Mami tayi tace "Aa MADEENAH, babu inda zaki tunda bakya so."



"Allah Mami zanje, gaskiya Anty Khadija ta faɗa idan naje ni ɗin maybe na samu sassaucin abinda ke damu na."



"Kin tabbata?."


Kai ta jinjina mata nan Anty Khadija tace "Yauwa kaji ƴar albarka, zo muje na shirya ki" ta faɗa tana kamo hannun DEENAH kafin tace da ƙawayen ta "Kuzo ku zauna ku jira ni, yanzu zamu fito mu tafi."



Ɗaki suka koma, kasancewar tayi wanka kawai kayan ta ta ciro set ɗin komai baƙi hatta takalmin da zata sanƴa.


"Ke kam bakida wani kaya ne sai baƙi?" cewar Anty Khadija.


Murmushi kawai tayi kafin Anty Khadija tace "Toh zo ki zauna na gyara miki face ɗin naki tunda bakya son kwalliya."


Babu musu taje ta zauna, taje mata gashin kanta tayi ta kama mata shi sannan ta sanƴa mata jel a kai tare da fidda mata style mai kyau ta gaban, simple make-up kawai tayi mata ta gyara mata face ɗin, amma kyawun da tayi ba'a magana sai wanda ya gani.


Bayan ta gama mata ne ta shirya cikin kayan ta, kallon ta Anty Khadija tayi tace "Nikam wannan dressing ɗin naki bansan ma da wane suna zan kira shi ba, gashi dai ke ba ƴar Turkey ba kuma ba ƴar Korean ba Kuma ba balarabiyar dubai ba, amma kuma kinason yin shiga irin tasu."



Kallon kanta tayi a mirror tayi murmushi dan kuwa ita kanta ta san ba ƙaramin kyau tayi ba, nan tace "Inajin daɗi idan nayi dressing irin wannan sannan kuma inason baƙin color shiyasa dukkanin kayayyaki na suke baƙi."



"Uhmm no wonder, wannan kyanta ace kin zama Fashion blogger."


Kallon Anty Khadija tayi tace "Muje dare yana yi."


"Wallahi fah ƙarfe takwas fah za'a fara dukda nasan sai anyi african time an kai tara kafin a fara event ɗin amma kuje da wuri kam yafi mutunci."



Fitowa sukayi nan duk idanu ya dawo kansu, Mami ce tace "Kai masha Allah, ƴata tayi kyau" ta faɗa cikin murmushi.


Amirah kuwa baki kawai ta saki tana kallon DEENAH haka ma ƙawayen Anty Khadija sai binta da ido suke suna kallo.


"Toh Mami mu zamu wuce sai mun dawo."


"Adawo lafiya, Allah ya tsare dan Allah Khadija kada kuje ku zauna kinga dai dare ne koh?."



"Insha Allah Mami" ta faɗa suna ficewa.


"Yanzu fah duk wankan nan da muka ci Taxi zamu hau koh?" cewar Aisha.


"Taxi zaku hau dai amma banda mu" ta faɗa tana nufar wata danƙareriyar mota chan gaba da gidan su.


"Kutt, kar dai Aliyu ne zai kai ki?."


"Toh miye amfanin shi, yana da mota kuma naje ungwa a Taxi ƙarya ne wallahi, kunga gara fah kunje kun nemi abin hawan ku, kuma ba rasa samari kukayi ba, ni da DEENAH ce kaɗai zamuje a motar sa, wallahi babu ƙatuwar da zata bini a cikin ku, kuna da kuɗi ba wai bakuda shi bane."


Sun san sarai Khadija batada mutunci indai ta wurin Aliyu saurayin ta ne, sun san koh mutuwa zasuyi ba zata bar su su bisu ba, Aisha ce tace "Dallah kuzo mu tafi wa zata yiwa wulaƙanci, dukkanin mu nan babu mai saurayi matsiyaci kema kin sani, kuma ai tun farko baki ce mana Saurayin ki ne zai zo ɗaukar ki ba, dah tuni munyi tafiyar mu wallahi."



"Kwaji dashi" ta faɗa tana riƙo hannun DEENAH suyi gaba.


Da kallo duk suka bisu nan ɗaya tace "Wallahi Khadija ƙarshe ce wurin iya rashin mutunci, sai muje mu tari Taxi ɗin ai ya muka iya?."


"Mtssww Allah ta ƙular dani, ni matsala ta ma yarinƴar nan da ta ɗauko tsaf zata kashe mana kasuwa a wannan wurin."


Dariya sukayi ɗaya tace "Kyaji dashi, idan kinga dama ki biyo mu, idan kin ga dama kuma kyayi ta tsayuwa anan" ta faɗa sunayin gaba.



Taxi suka tara suka faɗa masa inda zasu kafin su shiga yaja ya bar wurin, dan tuni su Anty Khadija sun tafi................



************************


..............Ƙaton hotel ne da ya amsa sunan sa wurin haɗuwa da tsaruwa, haske gauraye ta koh ina.



Babu abinda kakeji sai karar sauƙar motoci da tashin su, ga kuma ƴan mata da samari kowanne cikin shigar sa ta alfarma, da alamu dai party ɗin ba na biki ɗaya bane.



Duk fitowa sukayi daga cikin motar bayan yayi parking, sallama sukayi kafin ya wuce.


Dafa DEENAH da duk takejin ta a takure tayi tace "Ki saki jikin ki, bari na jira zuwan su Aisha sai mu shiga."



Kai kawai ta jinjina mata but sam haka kurum take jinta so remorsed, bata da wata walwala ga kuma sanƴi da wani irin karkarwa da zuciyar ta takeyi, har cikin tafin ƙafar ta takejin sanƴin.


"Are you Okay?" cewar Anty Khadija tana kallon ta.


"Am fine" ta bata amsa.


"Naga kamar kina karkarwa ne."


"No, am fine."


Ƙarasowar ƙawayen Anty Khadija ne yasa su nufar cikin ƙaton hotel ɗin.


Motoci ne a ciki birjik kowanne na ƙece raini, nan Aisha tace "Um bari mu natsu koh Allah zai sa muyi kamu" ta faɗa tana gyara nutsuwar tafiyar ta.


"Toh wannan kuma wanene haka?, naga bodyguards koh ta ina" cewar ɗaya daga cikin su.


"Maybe wani babban ne, kema kinsan auren nan na manƴan mutane ne, amma kuma kina wata tambayar daban dan kinga securities."


"Kuma fah."


Juyawa Anty Khadija tayi ga DEENAH dake chan baya tana tafiya kamar wacce kejin tsoro "kuyi gaba ina zuwa" ta faɗa tana komawa wurin DEENAH.


"DEENAH put yourself together, kinji?."



"Anty Khadija zuciya ta rawa takeyi,tsikar jiki na tashi yake, bansan meke damuna ba."



"Duk sabida baki saba shiga cikin jama'a bane yasa kike jin hakan, but da zaran mun shiga ciki zaki dawo normal, Okay?."


Kai ta jinjina mata kafin ta kama hannun ta suyi ciki.



Hawa huɗu ne wajen, dan haka hall ɗin da za'ayi nasu Event ɗin shine a hawa na huɗun.



Stairs suka hau ya kai su har bakin ƙofar hall ɗin.



Ƙaton hall ne sosai wanda aƙalla zai ɗauki mutane ɗari-biyar koh sama da haka, sai dai iya mutanen dake ciki ba zasu haura ɗari zuwa ɗari da hamsin ba.



Sosai hall ɗin ya ƙawatu da kwalliya wanda da ka gani kasan bikin na masu hannu da shuni ne.



Ja tayi ta tsaya tana girgiza kai, kallon ta tayi tace "Menene?."



"Ba zan iya shiga ba, akwai mutane dayawa."



"Ina mutanen suke, come on DEENAH karki ba dani mana, a hakan ma fah kaɗan aka gayyata sabida party ɗin ya bada ma'ana, baki ma ga kowa na harkar gaban shi ba, babu wanda hankalin sa ke kanki, yanzu muje chan na bada ticket ɗin gayyatar mu sai mu shiga koh?."



Shiga sukayi ta bada ticket ɗin gayyata kafin a bar su su shiga, riƙo hannun DEENAH tayi suka shige main hall ɗin bikin.


Wani irin shock ne taji ya ɗebe ta wanda sauran kaɗan ta faɗi Anty Khadija ta taro ta "DEENAH" ta faɗa.



Wani haɗaɗɗen table ne daga chan gefe wanda aka ƙawata shi yafi kowane table haɗuwa ta kai ta ta zaunar tace "Ki zauna anan ina zuwa kada ki tashi fah, kuma kada ki kula kowa."



Kai ta jinjina mata kafin Anty Khadija ta juya ta tafi.


Gyara zaman ta tayi tana bin mutanen cikin hall ɗin da kallo, inda kowa sanƴe da anko ya kai kala biyar ƴan matan nan kansu sai rawa yake.


*****************


.........."So you made me wear this kaftan just for your wedding?" ya faɗa yana kallon cikin madubi yana gyara zaman hular kansa.


"Yes sir, baka ga yadda kayi kyau ba, Allah yasa dai kar amarya ta tace ta fasa daga ganin ka" cewar Mansoor yana dariya.



Murmushi ZEEDAN yayi yace "Alright ango, muje kada amaryar taka ta fara gajiya da jiran ka."



Fitowa sukayi kamar yadda Mansoor ke sanƴe da farar shadda haka shima ZEEDAN ke sanƴe dashi yasha binjima kai ka rantse shine angon sabida yadda kayan ta zauna tayi masa kyau ba'a magana sai wanda ya gani kawai.



Hall ɗin suka nufa direct, suna cikin tafiya ne yaji an kira sunan sa "ZEEDAN?."


Ja yayi ya tsaya kafin yace da Mansoor yayi gaba yana zuwa.


Surayya ce ya gani itama cikin shigar atamfa ɗinkin fitted gown sosai tayi kyau, ƙarasowa wurin sa tayi tana murmushi tace "Dama kaima wannan auren zakayi attending?, Oh my GOD i just couldn't take my eyes off of you, shigar nan tayi maka kyau sosai Oh my GOD" ta faɗa kamar ta ɗauke sa ta haɗiye.



"OK" kawai ya faɗa ya juya ya fara tafiya.


Saurin mara masa tayi suka jera dashi suna tafiya, duk inda suka gitta kuwa idanu ne ke binsu both maza da matan kowa sai yaba shi yake, yayin da zuciyar wasu mazan ya cika da kishin ganin ZEEDAN sosai.


Surayya kuwa ji take kanta na yin ƙato sabida kowa ganin budurwar ZEEDAN yakeyi mata.



"Sir this way" faɗin wani bodyguard yana yi masa iso da shigowa cikin hall ɗin.



Kafarsa da ya sanƴa ya shigo cikin hall ɗin shine ya faɗaɗa bugun zuciyar ta, damƙe jakar hannun ta tayi da ƙarfi tana jin kamar ta 6ace ta ganta a gida.


"Excuse me ma'am" taji an faɗa.


A ɗan tsorace ta ɗago tana kallon sa nan yace "Wannan seat ɗin is not for regular guests, it's made for someone special, please change your seat."


Tsayawa tayi kallon sa dan kuwa idan tace zata tashi toh babu makawa zata iya zubewa anan wurin.



"Ma'am" ya sake faɗa yana yi mata alama da hannu akan ta tashi.


Kai ta jinjina masa tana niyyar tashi ne kuma akace "Let her be."


Juyawa yayi ga ZEEDAN yace "but sir..."


Bai ƙarasar ba ya ɗaga masa hannu hakan yasa shi yin shiru kafin yaja masa kujera cike da girmamawa ya zauna.



Tunda taji muryar sa ne kuma bugun zuciyar ta ya ƙaru sosai, runtse idanu tayi kanta a ƙasa dan kuwa bata iya ɗagowa ta kallesa ba.



Ƙamshin turaren sa kuwa duk yabi ya addabe ta, sosai taji kamar ta ta6a jin irin wannan ƙamshin a wani wuri sai dai ta mance koh a ina ne.



Kallon ta yayi dan kuwa gefen fuskar ta kawai yake iya gani sakamakon ta juya daga saitin sa kuma idanun ta a ƙasa.


_"Toh ita wannan kuma daga ina, why is she behaving so strange"_ ya faɗa a zuciyar sa.


Kan kace miye kuma an cika gaban su da abubuwan ci da sha dayawa dama kuma kalolin abinci ba'a magana.


Surayya dake ta jin kanta na ƙato ne ta jawo kujerar ta kusa dashi tace "Babe."


"Stop calling me that" ya faɗa ƙasa-ƙasa ta yadda babu wanda zai ji.


"Come on look around kowa da boyfriend nashi anan, let's stick together and be like them please."



Share ta yayi dan kuwa ya gama ganewa batada kunƴa ne.


Ji tayi an ta6a ta, nan ta ɗago daga tana sauƙe idanun ta kan Anty Khadija.


Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Anty Khadija ina kika je tunɗazu?."


"Ke kinsan waye a kusada ke kuwa?" ta faɗa ƙasa-ƙasa.


"Dan Allah mu bar nan wurin, bana jin daɗin zama anan."



"Cha6 ai ni ingayamiki ma zama nazo yi babu inda zani" kasancewar seat huɗu ne yasa ta faɗin "Excuse me can i?" ta faɗa tana nuna seat ɗin.



Bodyguard ɗaya ne yace da ita "No."



Kallon sa ZEEDAN yayi hakan yasa shi yin shiru ya cigaba da patrol ɗinsa.



Murmushi tayi ta zauna tare da furta "Thank you."



Rolling idanu Surayya tayi ganin kowace mace idanun ta na akan ZEEDAN hakan na ƙona mata rai matuƙa.



Kama hannun DEENAH tayi tace "ki saki jikin ki mana."


"Sir you have an important call" cewar wani bodyguard yana miƙa masa wayar.



Ba tare da ya ɗago ba yace "Who is that?."


"Your Mom."


"Mom?" ya faɗa yana amsar wayar kafin ya kara a kunnen sa.


Ganin surutu da kiɗa yayi yawa a wurin ne yasa shi tashi ya bar wurin ya fice daga cikin hall ɗin.



Da kallo kawai tabi bayan shi tana ɗan jin bugun zuciyar ta na raguwa.


Sai a sannan ta ɗago tana gyara zama tace "Anty Khadija mu bar nan wurin."


"Cha6 ke bakiga idanun su Aisha ba kamar zai fita, shegiya da zata samu wuri anan da da gudu zata zo ta zauna."


Kallon Surayya Khadija tayi tace "Hello."


Ɗan ɗagowa tayi ta kalle ta tace "Hi."


"Is he your boyfriend?."


Murmushi ta saki tace "Yeah, sannan ma we are about to get married soon."



"Wow, Congratulations."



"Thanks" ta faɗa cikin murmushi tana cigaba da danne-dannen wayar ta.



Cikin ƙasa da murya tace "Kinsan wani ana ce masa *ZEEDAN AL-ABBAS*, The most Famous and richest artist in the world to shine wannan, just look at how Handsome he is, koh sau ɗaya ki ɗago ki kalli face nasa am.definitely sure sai dukkanin damuwar ki ya yaye."


"Stop it Anty Khadija."



Tashi Surayya tayi da juice a hannun ta tana danne-dannen waya tazo wucewa ne cup ɗin hannun ta ya su6uce ya faɗa kan DEENAH inda gabaɗaya ya zube mata a kaya.


"Oh GOD!" ta faɗa tana ajiye wayar da sauri kafin tace "Sorry ban lura bane."



"It's Okay" ta faɗa tana tashi tsaye.


"Muje akwai toilet ta lungun chan ki shiga ki wanke jikin ki" cewar Anty Khadija tana kamo hannun ta.



Ajiye jakar ta tayi kafin su bar cikin hall ɗin.


Wayar Anty Khadija ne ya hau ringing nan tace "Ga chan hanƴar toilet ɗin a cikin corridor ɗinnan kije, bari na amsa kiran nan."



Wucewa tayi kawai da sauri tana tsane jikin ta.


Boooomm taji ta bugu da mutum inda wayar dake hannun sa ta faɗi ƙasa.


Da sauri ta sunkuya ta ɗago masa wayar tana faɗin "Sor.."


Maganar ta ce ta carke lokacin da idanun ta suka sauƙa cikin nashi.


Amsar wayar yayi yace "It's alright" ya faɗa yana wucewa.


Daskare wa tayi anan wurin ba tare da ta iya motsa koh da ƴar yatsar ta bace................





*Yawan Comment, yawan typing*





*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*016...*




...............Manƴan idanun ta da ta waro tun sadda ta haɗa idanu dashi ne ta kasa ƙiftawa har yanzu, sannan kuma ta kasa motsa koh da ƴar yatsar ta ne, haka nan ta tsaya in shock kamar wacce tayi sumar tsaye.



Tabbas shine, ta gane shi kallo ɗaya tayi masa ta gane kamannin sa, like a flash haka fuskar sa da kamannin sa suka faɗo mata cikin kwakwalwa.



"DEENAH!, DEENAH!!" cewar Anty Khadija tana girgiza ta.



A firgice ta ɗago tana kallon ta.


"Meke damun ki, bakije kin wanke bane?."



Dube-dube DEENAH ta fara ganin ya bar wurin bata gansa bane yasa ta nufar hanƴar cikin hall ɗin da gudu.



"DEENAH Stop" cewar Anty Khadija tana mara mata baya.



Tsaye DEENAH da takejin zuciyar ta kamar zata faso waje tayi a tsakiyar hall ɗin tana dube-dube, duk wanda ta gani da farin kaya kuwa sai taje ta duba fuskar sa taga koh shine.



Haka nan tayi ta yawo a cikin hall ɗin tana lelleƙa fuskar mutane cike da kiɗima, yayin da mamaki ke cike a fuskar kowa ganin yadda ta gigice ta daburce kamar wata zautacciya, nan duk kallo ya dawo kanta kuma.



Anty Khadija ce ta kamo ta tace "DEENAH miye hakan kike yi, bakiga kowa na kallon ki bane?."


"I saw him, i just saw him now" ta faɗa tana cigaba da bin mazan wurin tana leƙa fuskokin su.



Haka nan tayi ta zagaye hall ɗin baki ɗaya but bata ga ZEEYAD ba, batasan inda ya shiga ba.



Ficewa tayi daga cikin hall ɗin da gudun ta inda kowa ya bi ta da kallo Anty Khadija na mara mata baya.


Tsaye tayi ta sama stairs ɗin tana jejjefa idanun ta koh Allah zai sa ta ganshi a cikin mutanen nan.


Bata gan shi ba hakan yasa ta sauƙa zuwa hawa na uku tana duba shi bata gansa ba har ta fice zuwa waje.



Nan ma dube-dube ta fara tana waige-waigen neman sa, kamar a mafarki ta gansa yana shirin shiga motar sa da aka buɗe masa waya kare a kunnen sa.



Bata tsaya yin wata-wata ba kuma ta nufe shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login