Showing 222001 words to 225000 words out of 236327 words
na YAZEED "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" take ta nanatawa a ranta.
************************
_________Sosai likitoci suka rufu akan YAZEED suna iya bakin ƙoƙarin su na ganin sun ceto rayuwar shi.
Mai Martaba gabaki ɗaya ya rikice ya zangwame lokaci guda, hankalin sa a matuƙar tashe yake, Abhi ɗin Sadeeq ne ke ta ganin ya kwantar masa da hankali amma kamar sake ƙara masa damuwa yake, ya kasa zaune ya kasa tsaye, damuwa da fargaba sunyi masa ƙatutu a cikin zuciya bai ma damu da tasa lafiyar ba, burin sa shine YAZEED ya samu lafiya nan ne kaɗai hankalin sa zai kwanta.
Fitowar wani likita daga ɗakin tiyatar ne ya sanƴa mai Martaba iyo masa wani irin riƙo yana faɗin "How is he, how is my Son?."
"Calm down your Highness, muna iya bakin ƙoƙarin mu ne na ganin mun ceto shi, zai fi kyau ka sarara haka muyi aikin mu cikin kwanciyar hankali" yana faɗin haka yayi gaba da sauri.
A takaice dai sun ɗau awanni da dama akan YAZEED kafin su fito daga ɗakin tiyatar kusan likitoci shida ciki harda Sadeeq.
Duban idanun Sadeeq Abhi yayi kafin ya kalli mai Martaba da shima shi yake kallo.
"How is YAZEED?, sannan zuwa yaushe zai samu lafiya mu tafi dashi gida?."
Kallon Abhi ɗinsa Sadeeq yayi cikin sanƴi yace "I'm sorry..."
Kallon da mai Martaba yayi masa ne ya sanƴa sa kasa idda maganar tasa.
"Yes, tell me."
"YAZEED have only 30% chance of survival munyi nasarar cire takobin daga cikin sa wanda yayi nasarar huda small intestine ɗinsa, so munyi masa dukkanin wani ƙoƙarin ma na likitoci but..."
"Kana nufin kacemin kana tantama zai rayu koh ba zai rayu ba kenan?" cewar mai Martaba ɗin.
Kai Sadeeq ya jinjina masa, nan mai Martaba ya sake faɗin "Zancen banza ne wannan likita, ran YAZEED ba a hannun ka yake ba, you have no gut to tell me ba zai rayu ba, ni nasan insha Allah ɗana zai rayu na rasa na farko ba zan iya jurar rasa wannan ba, our kingdom needs someone very trusthworthy da zai mulke ta, YAZEED is the only person da nake sa ran zai cika min buri na, this kingdom will fall apart muddin YAZEED ya mutu..." hawayen da suka zubo masa ne ya sanƴa maganar tasa ƙaƙarewa.
Ido Abhi yayi wa Sadeeq akan ya wuce yaje kafin kuma shi ya shiga baiwa mai Martaba ɗin baki.
Sadeeq Office ɗinsa ya koma, kifa kansa yayi akan table ɗin ofishin nasa, wasu hawaye masu zafi na wanko masa fuska, he can't believe iriyar ƙaddarar wannan MASARAUTAR yana tsoron rasa YAZEED tabbas idan YAZEED ya mutu then komai lalacewa zaiyi, and ZEEYAD kuma har yanzu babu wani labarin cigaba a fannin lafiyar shi.
Yasan rai ba a hannun sa yake ba but zaiyi dukkanin ƙoƙarin sa tare da addu'ar ganin YAZEED ya rayu haka ma ZEEYAD, su ɗin abokai ne amana a gareshi dan haka it's a must for him ya dage da yi musu addu'a dukkanin su, kowa nasu tausayi suke basa DEENAH, JALILAH Grandma dama kuma Mai Martaba, ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya tashi ya fice daga office ɗin.
*************************
*6 MONTHS LATER*
_________Hafeezah na hango cikin Katuwar cell hannayen ta dama kuma duka ƙafafun ta ɗaure da chain, sosai tayi kaca-kaca tayi jina-jina da ita, sosai ta koma wata iriyar shiru-shiru tamkar ba Hafeezah marar imanin nan ba.
Sosai takejin baƙin cikin kashe YAZEED da tayi, sai dai ta dangana laifin ne akan DEENAH wanda har yanzu bata cire ran kashe ta ba da ita da abinda ta haifa ɗin bayan ta fito daga kurkuku, dukda batasan dalilin da ya sanƴa ba'a yanke mata hukunci har yanzu ba but batada wata damuwa tunda akwai Sairah da Rahinah su zasu ƙarasar mata da sauran aikin da batayi ba.
"Chill out DEENAH, soon dake da abin da kika haifa ɗin zaku baƙunci lahira, i don't care yadda makoma ta zata kasance all i want and need is your death, i won't stop at nothing until a avenge my Son's death dama kuma Ayaan da kikayi sanadiyyar naƙasar masa da halitta, i hate you DEENAH yadda ban ta6a tsanar wani mahaluƙi a duniya ba, ba zan ta6a samun Peace of mind ba har sai naga gawar ki da ta ɗan da kika haifa da idanu na, i have spent six months cikin wannan kurkukun duk saboda ke, i swear... i swear DEENAH dole ne ki mutu only then i can be happy" ta ƙarashe idanun ta na kaɗawa suyi jazir.
**********************
________Zaune DEENAH take akan dukda ba sallar takeyi ba sai dai bakin ta ɗauke yake da tasbih dama kuma kiran sunan Allah tare da nemawa YAZEED dake kwance har yanzu lafiya, yayin da 6angare guda kuma take yiwa mijin ta addu'ar da kullum bata gajiya dayi masa.
Ƙananan kukan da Jaririn dake kan gado yayi ne ya sanƴa ta miƙewa tana zuwa kan gadon tare da ɗaukar sa, a hankali ta shiga jijjiga shi tana faɗin "It's Okay Baby, Momy is here banyi nisa da kai ba" ta faɗa tana rungume shi a ƙirjin ta.
Lumshe idanu tayi hawaye na sauƙo mata tace "You left us a lokacin da babu wanda ya ta6a tsanmani, a lokacin Allah ya ɗau ranka, but gashi Allah ya dawomin da photocopy ɗinka, wanda dashi ne zan dinga tuna ka sannan dashi ne nakejin present ɗinka a kusa dani, you may not be here with us but we were always with you and we will forever be Abyad" ta ƙarashe tana zama kan bed ɗin kafin ta kwantar da yaron da alamu dai ya koma bacci, yaye fuskar sa da tayi daga cikin towel ɗinne ya sanƴa wayar hannu na kusan su6ucewa da ganin kyakkyawar halittar yaron mai kama da mahaifin sa sak tamkar an tsaga kara.
Murmushi DEENAH tayi tana sake kallon fuskar yaron, kishingiɗa tayi kusa dashi tana a haka har Asuba tayi.
Kiran farko ta farka tana sauƙe idanun ta kan fuskar kyakkyawan Baby boy ɗin nata.
Murmushi tayi tana miƙewa tare da gyara masa kwanciya kafin ta tashi ta nufi bathroom, Alwala tayi ta fito kafin ta tada sallah, bayan ta idar ne kuma tayi azhkar da Tasbih ɗinta, ta daɗe akan sallayar tana addu'a kafin kuma tayi karatun Al'ƙurani mai girma, bayan ta idda ne ta miƙe tare da nannaɗe sallayar tana maida shi gurbin zaman sa.
Yaron da taga idanun sa a buɗe ne ya sanƴa ta yin murmushi kafin ta ɗauke sa tana yin ɗakin Grandma dashi.
Akan sallaya ta tadda ta dan haka shimfiɗe shi tayi akan gadon Grandma kafin ita kuma ta fice.
Wanka ta iyo tayi shirin ta mai kyau tamkar kullum kafin ta dawo ɗakin Grandma nan ta tadda har ta yiwa jaririn wanka, gaida Grandma tayi kafin DEENAH ta kar6i yaron tana dawowa ɗaki dashi.
Tana cikin shirya shi JALILAH ta shigo ɗakin fuskar ta ɗauke da murmushi take faɗin "Mai raino tazo."
Murmushi DEENAH tayi tana miƙa sa wa JALILAH bayan ta shirya shi.
Kallon sa JALILAH take kafin tace "Har gobe ba zan daina cewa fuskar mahaifin sa nake gani tattare dashi ba."
Murmushin yaƙe kawai DEENAH ta iya yi, ita kaɗai tasan abinda takeji cikin zuciyar ta, abin akwai ciwo ciwon da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake koh da kuwa ya ta6a shiga irin halin sai dai kawai yayi ta 6oye damuwar dake cikin zuciyar sa da murmushi, but tabon da hakan ke yiwa zuciyar mutum ba ƙarami bane.
Ganin yadda yanayin ta ya canza ne ya sanƴa JALILAH miƙewa tsaye tana faɗin "Toh mu mun wuce."
Kai kawai ta iya jinjina mata kafin kuma ta miƙe akan bed ta shiga kukan da batasan ranar dainawar ta ba.
***********************
*3 DAYS LATER*
________Zaune Sadeeq yake a ofishin shi kira ya shigo wayar sa, gaban sa ne ya faɗi ganin malamin nan ne mai kira.
Ɗagawa yayi tare da yin sallama cikin sanƴi.
Shiru yayi yana saurarar abinda mutumin ke cewa, hankali tashe ya miƙe tsaye yana faɗin "What do you mean...?."
"He is under your care, and kayi alƙawarin bashi dukkanin kulawa how comes kuma zakace baka ganshi ba yanzu."
"This is Nonsense, kai kacemin bai sami lafiya ba har yanzu, ya kuma zakace min ba sace sa akayi ba."
"Hold up, i will be right there yanzun nan, duk inda yake ka tabbatar kun nemo shi before i arrived" yana faɗin haka ya ajiye wayar tare da ficewa cikin kiɗima.
Sai da ya leƙa ya duba lafiyar YAZEED tukun kafin ya fice ba tare da ya sanarwa kowa ba.
*******************
______Daga cikin closet room ɗinsu take jin kishi-kishin ɗin yaron yana surutan su irin na jarirai inda ita kuma take amsa masa, kayan su take haɗawa kasancewar gobe da sassafe zasu koma Nigeria dan kuwa taga sam wannan zaman MASARAUTAR ba zata ta6a yiwuwa a garesu ba, muddin tana son ɗanta ya rayu ya zama dole ta tafi tayi nesa dasu dan kuwa kusan sau huɗu ana kawowa jaririn ta hari tana kamawa, hakan ya sanƴa ta zuwa part ɗinsa da ta mance yaushe rabon ta da ta shiga tana harhaɗa abubuwan ta.
A hankali yake tafiya har ya idda shigowa cikin ɗakin, turus yaja ya tsaya yana bin ɗakin da kallo kafin kuma ya shiga lalla6awa a hankali yana nufar jaririn da ya hango akan tsakiyar bed ɗin ɗakin.
Tsaye yaja yana ƙarewa kyakkyawar yaron kallon wanda ba zai wuci watanni biyu da haihuwa ba, wutsil-wutsil yaron keyi da ƙafarsa yana cigaba da surutun sa irin ta jariran.
Gyara rufar bargon jikin sa kamar kuma mai tsoro ya kai hannu tare da ɗaukar jaririn yana kallon sa.
Shiru yaron yayi tare da ƙure fuskar wanda ya ɗauke shi ɗin da idanu yana kallo.
Sosai suke kallon juna shi da jaririn, cikin wasa yaron ya kai hannu ya shiga jan doguwar gemun fuskar sa da tayi buzu-buzu da ita.
Murmushin kan le6e ya saki ganin yadda ɗan jaririn keyi masa wasa.
Rungume shi yayi a ƙirjin shi yana lumshe idanun sa.
Dai-dai lokacin DEENAH da taji shirun ɗan nata yayi yawa ta fito dan ganin meke faruwa, turus tayi taja tana kallon bayan mutumin da jikin sa ke rufe da bargo har zuwa kansa.
Batayi wata-wata ba ta hau dube-duben abin duka ganin 6arawo ya shigo yana neman satar mata ɗanta.
Idanun ta ne suka faɗa kan flower-vase dake ajiye a dan haka da sauri ta kai hannu tana ɗauko shi kafin ta shiga takawa a hankali zuwa bayan mutumin, a hankali tace "Stay away from my child."
Saurin buɗe idanun sa dake a lumshe yayi yayin da zuciyar sa ta shiga running very faster.
Ganin bai juyo ba kuma bai motsa bane ya sanƴa ta sanƴa hannu tana yaye rufin da yayiwa kansa, idanun ta kan doguwar gashin kansa da ya sauƙo har baya tace "Surrender yourself... now."
Ganin har yanzun bai motsa bane ya sake sanƴa ta faɗin "Please ka ajiye min ɗana, i will give you everything you want, just don't hurt my child please" ta faɗa dan so take ya ajiye mata ɗanta kafin ita kuma tayi maganin shi.
Ganin ya motsa yana shirin juyowa ne ya sanƴa ta saurin ja da baya tana bada gap tsakanin su idanun ta akansa.
A hankali ya shiga juyowa still yaron rungume dashi yana sauƙe idanun sa cikin nata, kallon ta yake kafin kuma in a calm voice ɗinsa ya kira sunan ta "MADEENAH."
*Yawan Comment, Yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[9/8, 5:11 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*SEMI__FINAL*
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*054...*
_________A razane taja da baya tana yada vase ɗin hannun ta take ya tarwatse a ƙasa.
Manƴan idanun ta da ta waro tamkar zasu faɗi ƙasa ne ta kafa masa tana kallo cike da ɗimuwa da tashin hankali.
She can't believe her eyes, she can't believe mutumin da ya mutu kusan shekara ɗaya kenan shine tsaye a gaban ta, no inaa tayaya za'ayi hakan?, bayan kowa ya tabbatae da mutuwar sa har ma aka kai shi aka binne a idon ɗumbin jama'a, shine za'ace tsaye a gaban ta, toh kodai fatalwar sa ce?
Tasan tabbas ba shi bane ba, jikin ta ne ya kama rawa haka ma bakin ta da takeson buɗewa tayi magana sai dai ta kasa, a hankali kuma cike da tashin hankali ta shiga lalumar jikin bangon ɗakin still idanun ta akansa wanda shi ɗinma bai bar kallon nata ba har ta kai bakin ƙofar fita.
"DEENAH?" ya sake kiran ta.
Sake firgicewa DEENAH tayi jikin ta inbanda kyarma ba binda yakeyi, babban damuwar ta shine little ZEEYAD dake riƙe a hannun sa.
"DEENAH?" ya sake kiran ta yana taka ƙafarsa.
Ihun da ta saki ne ya sanƴa shi dakatawa daga tunkarar ta "Stay away from me, ka ajiye min ɗana ka tafi na roƙeka dan girman Allah kada ka cutar min da ɗana" ta faɗa cikin kuka dama kuma tsoron da ya cika mata ruhi.
Sake rungume yaron yayi a jikin sa yana mamakin abinda ya sanƴa DEENAH ke gudun sa, kodai bata gane sa bane ba, shine tambayar da yake wa kansa.
Sake takawa yayi zai tunkare ta ta sake sanƴa masa wani ihun tana ja da baya, bai tsaya ba ya cigaba da tunkarar tata, cikin kiɗima ta fice daga ɗakin cikin gudu, ZEEYAD baiyi ƙasa a guiwa ba ya mara mata baya shima.
Dai-dai tazo sauƙa daga stairs wani irin sul6i ya kwashe ta bata kai ga faɗuwa ba ya taddo ta yana riƙo hannun tare da fizgo ta tana faɗawa jikin sa.
Ƙara ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta ganin fatalwa ya riƙo ta.
Kamar wacce kuma wani abin ya gitta mata a kwakwalwa ta tsagaita da kukan nata cak na kusan seconds kafin kuma ta shiga buɗe fuskar ta da ta rufe da tafukan hannayen ta tana ware su akan shi.
Da hannu ta shiga tatta6a ƙirjin sa ganin tana iya ta6a sa ne ya sanƴa ta ɗago da kanta da sauri tana kallon sa.
"DEENAH?" ya sake kiran ta cikin calm voice ɗinsa.
Shiru tayi tana kallon sa da idanun ta dake tsiyayar da hawaye, kallon juna duk suke na kusan 2mins kafin cikin rawar murya tace "A... Ab... Abyad?."
"Baby" ya kira ta.
Kanta ta shiga girgizawa cikin kuka tana riƙo fuskarsa dake cike da gashi ta sake kiran sa "Abyad."
Kuka ta fashe dashi tana rungume sa take faɗin "I know it, i know it... nasan baka mutu ba ban ta6a yarda cewa ka mutu ba, wayyo Allah na nagode maka."
Da hannun sa ɗaya shima ya rungume ta ɗayan hannun nasa rungume da little ZEEYAD.
Sosai DEENAH ke kuka kamar zata shiɗe, bai iya hana ta ba sabida yasan mai takeji da shima zai sami damar kukan da babu abinda zai hana shi yin kukan, lumshe gajiyayyun idanun sa yayi yanajin wani irin kewa haɗi da so da ƙaunar ta na huda dukkanin wani sassa na jikin sa.
Sun daɗe a haka zuciyar su cike da kewar juna, ƙishi-ƙishin ɗin kukan little ZEEYAD ne ya fargar dasu, ɗagowa tayi tana kallon sa kafin ta dubi yaron hannun sa inda shima ya ɗago yaron yana kallon sa.
Murmushi DEENAH tayi tana amsar sa shi dai ZEEYAD da kallo kawai yake binta dan kuwa ya rasa ɗan waye wannan ɗin.
Kallon idanun sa dake cike taf da alamun tambaya DEENAH tayi, kamo hannun sa tayi suka koma cikin ɗakin dan kuwa ta lura da akwai tarin stress da gajiyawa tattare dashi.
Rufe ƙofar tayi tana kwantar da little ZEEYAD kan bed kafin ta tunkaro ZEEYAD dake tsaye tana kallon sa.
Ganin tana sake shirin wani kukan ne ya sanƴa shi janƴo ta jikin sa yana bata tight hug mai kyau, sai dai har izuwa wannan lokacin babu koh burbuɗin murmushi akan fuskar sa, runtse jajayen idanun sa dake yi masa yaji yayi kamar wanda zai maida ta cikin sa ya huta da kewar ta dama kuma ƙaunar ta dake sake ninkuwa kullum cikin zuciyar sa, shi kaɗai yasan halin da ya shiga a wannan kwanciya ciwon da yayi na kusan shekara ɗaya.
DEENAH jin abinda take duka tamkar a mafarki, ta rasa da wasu irin kalamai zata kwatanta yadda takeji cikin zuciyar ta, she can't believe it, ta rasa ya akayi hakan ya kasance a raye bayan kowa ya shaida mutuwar sa, jana'izar sa dama kuma binnewar sa, ya kuma za'ayi ya dawo, sai anan ne kuma tunanin abinda YAZEED ke son faɗa mata lokacin da mahaifiyar sa tayi masa aika-aika ya shiga dawo mata kwanƴa, da alama sunan ZEEYAD yakeson kama mata a lokacin sai dai aka katse sa, kenan ya san wani abu ne dangane da hakan komiye?.
Ɗagowa tayi tana kallon sa, ɗan ɗagyal tayi tana manna masa long kiss a goshi kafin tace "I miss you" hawaye na biyo mata ƙunci.
Shi dai kawai da kallo yake bin ta yanajin wani irin ɗaci a zuciyar sa da maƙoshin sa, bakomai ke sanƴa shi jin hakan ba sai tsanar Hafeezah dama kuma wadanda take aiki tare dasu.
Cire masa bargon jikin sa tayi tana ajiyewa a gefe, kafin ta shiga rage masa kayan jikin sa, Bathroom ta nufa ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi yadda zaiji daɗin wankan.
Fitowa tayi da towel riƙe a hannun ta kafin ta nufe sa tana miƙa masa, amsa yayi daga hannun ta yana bin ta da kallo duk inda tayi, ji yake tamkar ya fashe da kuka sabida irin baƙin cikin da yake ciki, he can't believe kusan 1year baya tare da Family ɗinsa all because of Hafeezah da son zuciyar ta, sadda kai ƙasa yayi yana cize la6an sa sosai da sosai zuciyar sa ke wani irin bombing shi kaɗai yasan abinda yakeji dama kuma Iriyar abinda zaiyi mata.
Muryar DEENAH da ya tsinkayo tana yi masa magana tunɗazu ne ya sanƴa shi ɗago da kansa a hankali kafin ya tashi ya nufi bakin bathroom ɗin inda take tsaye.
Saurin tura shi ciki tayi lokacin da tajiyo muryar JALILAH a bakin ƙofa tana rufo shi cikin bathroom ɗin.
Juyowa tayi ga JALILAH da ta shigo tana sakin mata murmushin yaƙe.
Murmushi JALILAH tayi mata kafin tace "Grandma tace na dubo ki na taya ki haɗa kayan taga kin daɗe ne."
Murmushi DEENAH tayi kafin tace "A'a ki barshi nima zan ƙarasar, amma ga Abyad nan ki tafi dashi nima yanzun nan zan fito" ta faɗa tana ɗaukar little ZEEYAD.
Amsar sa JALILAH tayi cikin murmushi tace "Are