Showing 192001 words to 195000 words out of 236327 words
"Hu..hukunci, toh akan mai?, akan nayi ƙoƙarin ceto ku daga faɗawa halaka sabida an zo min da zancen kuma har mutane uku na tabbatar da hakan daga garesu, shine kake cewa hukunci ya hau kaina ai a doka ma banida laifi, sabida ba ƙarya nayi na cewar na ganta da idanu na tana aikata sihiri ba, koh da akwai wadanda za'a hukunta bai wuci wadannan bayin bane, ba kai kaɗai aka raina wa wayo anan ba hatta ni nan sun maida ni ƙaramar mutum sabida yadda na dage akan gaskiya suke faɗi, sai gashi kuma ba haka bane."
"Dan girman Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri kayi mana rai, mu mun tabbatar da abinda idanuwan mu suka gani ne, sai dai koh idan basu duba bane da kyau."
Grandma ce tace "Kai ku dakata haka nan, ai daman nasan sai an kai ga haka wannan ne dalilin da ya sanƴa ni tanadar shaida sabida nasan tsinannen makirci irin taku, yanzu sai ku haɗa ƙarya tuburan duk sabida ku sanƴa wani cikin gagarumar matsala toh ahir ɗinku dan kuwa tundaga sama har ƙasa na tofe ƴata da turaren da addu'ar masu mugun hali ire-iren ku, ku ba'a tauye muku komai ba amma ku kunfi kowa tsanar mutum, Allah yayi wa Boy ɗina albarka da saya min ƴar wayar zamanin nan da yayi ai koh bakomai yau tayi rana, dama jira nake naga iya gudun ruwan ku, daga shigowar yarinƴa jiya har kun fara kai mata hari, ku abin ma yayi muku yawa, ga talauci ga kuma hassada da ta mamaye maku zuci tayi muku naƙe-naƙe, ai daman jira nake naga iya gudun ruwan ku, tunda kuka ɗaurawa DEENAH sharrin abinda bata aikata ba toh kuwa kun buɗo wa kanku ƙofar wahalar da bata da ranar yankewa har ku mutu shegu masu kama da ƴaƴan 6era."
Shiru duk fadar tayi kowa ya tsaya kallon Grandma da ta ciro wayar ta cikin aljihun rigar ta tana latsawa, inda ta haɗa da faɗin "Ni za'a nunawa tantiran ci na daɗe da gano akwai munafukai a 6angare na, sai gashi yau asirin biyu ya tonu da izinin Allah na sauran da nake targetting zai tonu dan kuwa ba'a jini na bane zama da munafukai, duk inda munafuki yake kusa dani toh tabbas sai naji a jiki na, miƙawa mai Martaba wannan wayar yaga abin dake ciki da idanun sa" ta faɗa tana miƙa wayar wa ɗaya daga cikin guards ɗin da suka je binciken.
Mai Martaba aka baiwa wayar inda ya kafe ta da idanu yana ganin lokacin da suke sanƴa abin a ƙarƙashin gado suna ɗan waige-waige kamar yadda suka ce DEENAH tayi, kafin su sanƴa ɗaya cikin ƙasan rug ɗin dake shimfiɗe a ɗakin, sai da suka gama kafin su sake waigawa suna ficewa daga ɗakin da sauri, nan Grandma kuwa ta shigo tana cire abubuwan da suka sanƴa ɗin mai kamar wasu manƴan layoyi.
Sosai ran mai Martaba ya 6aci da ganin video ɗin, dan haka maidawa Grandma wayar ta akayi, ba tare da ya kalli ministocin sa ba yace "Menene hukuncin wanda yayi wa wani ƙazafin asiri alhalin shine mai aikata hakan ya ɗaurawa wani?."
Shiru fadar ta ɗauka kafin ɗaya daga cikin ministocin yace "Bisa ga dokar marigayi hukuncin sa shine, horo mai tsanani na watanni biyu kafin kuma azo a rataye shi sabida shima ya aikata asirin ne koh da kuwa sanƴa shi akayi ba yin kansa bane."
"Dan girman Allah ranka ya daɗe kayimin rai, wallahi nayi nadamar aikata hakan, kayi min rai" cewar ɗaya daga cikin su cikin ihu da ƙururuwa .
"Kuje dasu sannan ku yanke musu hukunci dai-dai da abinda suka aikata."
Sosai Sarauniya Hafeezah taji haushin rashin cikawar plan ɗinta, tsoron ta ɗaya kada su buɗi baki suce itace wacce ta sanƴa su, duk da kuwa ba ƙaramin warning da barazana tayi musu ba.
"Wait" cewar ZEEYAD.
Tsayawa guards ɗin sukayi daga fitar da matan waje nan yace "They can't leave without apologising to my wife."
"Haka ne they should apologise for there misdeeds" cewar mai Martaba.
Tunkuɗa su guards ɗin sukayi suna zubewa gaban ƙafafun DEENAH dake rungume a jikin ZEEYAD, cikin riƙo ƙafafuwan ta suke cewa ta yafe musu ta kuma sa a janƴe hukuncin da aka yanke musu ba zasu sake ba.
Ɗauke kanta tayi daga kansu tana shigarwa jikin ZEEYAD tare da janƴe ƙafafun ta.
"The future Queen batada niyyar yafe musu."
"Then they should be executed, let this serve as a lesson to those having the intention ɗin aikata abinda sukayi" cewar mai Martaba.
Ɗago su guards ɗin sukayi tare da fitar dasu daga fadar suna ihun ayi musu rai.
Tsaye mai Martaba ya tashi tare da ƙarewa ƴan fadar kallo yace "Let this serve as a sound warning to you all, duk wani wanda ya aikata abinda wadannan mutanen sukayi toh babu shakka irin hukuncin da za'a yi masa kenan, Hafeezah" ya kira cikin Kakkausar murya.
Tsorata tayi da yadda ya kira sunan nata nan ya cigaba da faɗin "You must be punished for believing your maids against an innocent girl, hukuncin ki shine zaki fita daga fada ki koma zama cikin bayi na tsawon sati biyu, the next time da na sake kama ki da irin wannan laifin i won't spare you, and i want you to apologise for your mistake."
Shiru Hafeezah tayi tana kallon mai Martaba har ya kai zancen sa, there is no way da zata baiwa DEENAH haƙuri ba zai ma yiwu bane ba.
"Yes i made a mistake but that doesn't mean i should bow infront of this little girl da sunan neman yafiya."
"But you hurt her, so you must Apologise."
"It's Okay, we're fine, we don't need her apology" cewar ZEEYAD kafin ya ɗaura da faɗin "Just tell her to be careful, and mind her own business with my wife, coz i won't take a single shit from her next time" yana faɗin haka yaja hannun DEENAH sukayi gaba.
Da kallon tuhuma Grandma tabi Hafeezah da tayi tsuru-tsuru da idanu kafin itama ta mara musu baya tana faɗin "Just be careful next time Hafeezah."
Da mugun kallo Hafeezah tabi ta zuciyar ta fal cike da baƙin ciki.
******************
_______"Kiyi haƙuri DEENAH, i know you're hurt da abinda Hafeezah tayi miki but tunda har gaskiya tayi halin ta ki godewa Allah sannan kiyi haƙuri ki daina kuka" cewar Grandma cikin rarrashin ta.
Ita dai DEENAH sai kuka take bata ƙi ta ganta a gidan su yanzun ba, duk taji zaman nan ɗin baiyi mata ba, koh 24hrs bata cika a gidan ba amma gashi har an fara kawo mata hari kamar dama jiran ta ake.
"Grandma she needs to rest so am taking her to my part" cewar ZEEYAD.
Harara Grandma ta wulla masa tana faɗin "Mai kake nufi da zaka kai ta part ɗinka, leave her here ka kaita ɗaki na ta huta."
"Ahm...actually she would like it more a part ɗina, she is even scared da zama a part naki yanzun."
"Shikenan ai sai ka ɗauke ta ku tafi, sannan ka tabbatar da ka dawo da ita cin abincin rana, kuma ban ce kayi mata wani abin ba."
Kallon ta yayi kafin kuma ya riƙo hannun DEENAH da har yanzu bata bar kuka ba suka fice.
Zaunar da ita yayi bakin bed yana tsungunnawa a gaban ta tare da ƙura mata idanu yana kallo, he can see how deeply she is in pain.
Tashi yayi tare da zuwa ya buɗe wani kyakkyawan ƙofa cikin ɗakin yana kutsa kai ciki, bai wani jima sosai ba ya fito hannun sa ɗauke da wata baƙar Abaya yana ƙarasowa kusa da ita yace "Get up let's get your dress changed."
Tsagaitawa tayi da kukan tana ɗago da idanun ta ta kalle shi.
Gira ya ɗaga mata yace "Bakya jin nauyin sa ne?, we should change it right?."
Sauƙe idanun ta tayi tana share hawaye kafin ta miƙe tsaye tace "I will change it myself."
Placing hannu yayi around her waist yana jawo ta jikin sa yace "I can see how tired you're, so let me help" ya faɗa yana kai hannu ya fara unzipping ɗin zip ɗin bayan rigar tata.
Saurin kwacewa tayi tana ja da baya tare da faɗin "What are you doing?" zuciyar ta na racing, kafin kuma ta ɗau kayan tayi saurin shigewa inda taga ya shiga ya ɗauko kayan tana rufowa.
Murmushi yayi haɗi da ɗan cize lips yana zama bakin bed ɗin.
Da kallo taƙe ƙarewa inda ta shiga ɗin ganin kayayyakin sawa a jere kowanne da wurin zaman sa kai kace wani shopping mall ne na kayan sawa, ajiyar zuciya ta sauƙe tana sake jinjina kai a karo na ba adadi.
Muryar sa ta jiyo yana faɗin "Am coming in."
Waro idanu tayi, kafin da sauri tace "No" ta faɗa cikin ɗagun murya, kafin kuma ta ƙarasa bakin door ɗin wurin tare da sanƴa masa lock tana sauƙe ajiyar zuciya.
Sanƴa kyakkyawar abayar tayi tare da naɗa gyalen sa, ƙarewa kanta kallo tayi cikin mirror ɗin wurin kafin kuma ta buɗe ƙofar tana fitowa, tsaye ta gansa bakin ƙofar nan tace "You're peeping on me again?."
"No, what are you saying?, you should be glad the door isn't transparent."
Rolling idanu tayi tana ƙarasawa bakin mirror ɗin ɗakin.
Kujera taja ta zauna, tana gyara fuskar ta, kafin ta ɗau turare masu ƙamshi ta ɗan feffesa sama-sama a jikin ta.
Harar sa tayi ta cikin mirror ɗin ganin yadda yayi tsaye akanta yana kallon ta.
Knocking akayi a bakin ƙofar ɗakin, tsuke fuska yayi kafin kuma ya ƙarasa ga bakin ƙofar yana buɗewa ya leƙo da kansa.
Wata baiwa ya gani tsaye hannun ta riƙe da tray, nan tace "Afuwan ranka ya daɗe, Hajiya babba ce ta aikowa Gimbiya da wannan."
Kallo ya ƙare mata tsaf kafin ya sanƴa hannu ya kar6i tray ɗin yana shigowa ciki.
Kallon DEENAH dake kwance kan bed yayi kafin ya dire tray ɗin yana ƙarasawa ya zauna kusa da ita yace "Grandma ta aiko miki da abu."
Buɗe idanun ta dake a lumshe tayi tana kallon sa.
"But wait, let me call her first and confirm whether itace ta aiko ɗin."
Maida idanu DEENAH tayi ta lumshe, inda shi kuma ya kira Grandma dan tabbatar da koh itace ta aiko da abin.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yace "Tace itace, so stand up and eat."
"Bana jin ƴunwa."
"Are you kidding me?."
"But naci abinci kafin muje fada so har yanzu ciki na a cike yake."
Zuwa yayi ya zauna kusa da ita kafin kuma ya ɗan ja mata bargon yana rufa mata shi da kyau yace "Sleep then."
Ɗan murmusawa tayi tana maida idanun ta ta rufe.
Murmushi yayi yana kallon ta, a hankali ya sumbaci lips ɗinta kafin kuma ya tashi ya bar ɗakin.
*Yawan Comment, Yawan Typing*
07061979284
*MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽*
[8/30, 12:14 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*049...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
_________Razana tayi cikin baccin da take tana ware idanun ta.
Addu'a tayi cikin zuciyar ta kafin kuma ta miƙe zaune tana sauƙar da ƙafafun ta daga kan bed ɗin.
Shiru ta zauna tana jinta so lonely, kewar gida na nuƙurƙusar zuciyar ta.
A hankali ta miƙe tayi ƙofar da take tunanin toilet ne ta tura tana shiga, kamar yadda tayi hasashen kuwa Toilet ne, baki DEENAH ta saki tana ƙarewa cikin ƙaton bathroom ɗin da yake kamar ɗaki kallo, komai is neat and tidy kamar mutum yayi bacci a ciki, abubuwan zamanin da aka ƙawata bathroom ɗin dashi kuwa su kansu abun kallo ne, ficewa tayi daga bathroom ɗin ta wuce ɗakin closet inda anan taga akwatinan ta da sauran abubuwan ta.
Abubuwan da ta san zatayi amfani dasu ta hau cirowa kafin ta fito ɗakin ta jere wadanda tasan zata ke amfani dasu a ɗakin, na toilet ma haka ta kai ta jere su.
Ficewa tayi daga ɗakin zuwa falo tana sake ƙarewa ƙaton falon kallo, wani ƙofa da ta gani ta tura nan dai taga wani ɗakin ne shima komai steady a cikin sa, haka ma na kusa dashi duk.
Wani ƙofa ne ta gani kusa da ta Balcony ɗin cikin falon, tura shi tayi nan dai taga ɗakin Gym ne, rufo shi tayi kafin ta sake bin wani lungu da ta gani, ɗakuna biyu ta gani a jere ɗaya na kallon ɗaya, tura na left handside ɗinta tayi nan taga wani irin ƙaton kitchen haɗaɗɗe hakan ya sanƴa ta sakin baki tana bin kitchen ɗin da kallo, shigewa tayi nanma wani ƙofa ne ta gani ta tura shi food storage ne shima babba komai na kayan abinci kowanne jere a mazaunin sa.
Fitowa tayi daga kitchen ɗin ta tura ƙofar dake facing ɗinsa, wannan ɗin wayam yake ɗaki guda babu komai a ciki sai dai sosai yake so neat dashi, rufo ƙofar tayi ta fito falo kafin ta kama hanƴar sauƙa daga stairs, irin abinda yake a sama shine anan ƙasa ɗin, sannan kowanne da furnitures a ciki.
Sama ta dawo ta koma cikin ɗaki agogon dake manne jikin bango taga har sha biyu ya ɗan wuce, dan haka toilet kayan da ta sanƴa ta shiga ragewa, kafin ta wuce toilet ɗin.
Turarukan wanka masu daddaɗar ƙamshin da aka haɗa mata a gida ta zuba cikin ruwan wankan nata.
Sosai tayi wanka ta tsaftace jikin ta tare da ɗaura alwala ta fito.
Kayan ta ɗinkin leshi fitted gown ta sanƴa, dogon Hijab ta sanƴa ganin har an fara kiraye-kirayen sallah, dan haka tada sallah tayi bayan ta iddar ne tayi addu'oin ta kafin kuma ta naɗe sallayar tana maida shi wurin zaman sa.
Gaban mirror tazo ta zauna fuskar ta da yake fresh dashi ta ɗan gyara tare da sanƴa kwalli sai lip balm sannan ta ɗaura ɗankwalin kayan.
Sosai tayi kyau cikin shigar tata da ya zauna mata a jiki ɗarass, gyalen kayan ta ɗauko tana ɗan yafa shi kan kafaɗun ta kafin kuma ta tashi ta ficewa zuwa falo.
Turaren wuta mai dausar da nutsuwa da sanƴin cikin zuciyar mutum ta sake turare part ɗin dashi duk da kuwa a gyare yake hakan bai hana ta sake tsaftace shi ba.
Remote ɗin AC ta ɗauko tare da rage gudun sa kafin kuma ta miƙe kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman couchs ɗin dake zube a falon.
Shiru tayi tare da ƙure wuri guda da ido, so boring haka takejin ta gashi wayar tata kam ta manto shi a chan bale ta ɗanyi game, ga kuma tsoron gidan MASARAUTAR nan tasu ZEEYAD da yaƙi barin zuciyar ta har yanzun, idanu ta lumshe, sosai takejin kewar ƴan gidan su.
Ta kai kusan 10mins idanun ta a lumshe, motsa idanun ta fara a hankali jin kamar tsayuwar abu akanta.
Sosai zuciyar ta ta hau racing dan kuwa koh kaɗan batajin motsin shigowar mutum ba balle tace koh ZEEYAD ne ya shigo, jin feeling ɗin mutum na dab da ita ne ya sanƴa ta saurin ware manƴan idanun ta tana miƙewa zaune.
Waige-waige ta hau yi nan dai taga babu kowa, sosai zuciyar ta ta cika da tsantsar tsoro, a hankali ta koma ta tana ɗosana mazaunan ta kan couch ɗin.
Ji tayi an buɗo ƙofar ɗakin ɗaya daga cikin ɗakunan falon, a firgice tayi saurin maida duban ta gun bugun zuciyar ta na tsananta.
ZEEYAD taga ya fito daga cikin ɗakin wayar sa kare a kunne, hango DEENAH da yayi ne ya sanƴa shi sauƙe wayar yana ganin yadda tayi tsuru-tsuru da idanu kamar kace kyat ta arta a guje.
Ƙarasowa inda take zaune yayi yana kaɗa yatsun sa kan fuskar ta ganin yadda ta kafe sa da idanu tana kallo.
Zama yayi facing ɗinta yana faɗin "You're awake?."
Ita dai kallon sa take cikin tsoro kafin tace "Yaushe ka shigo?."
Kallon ta yayi kafin yace "Na shigo ina?, i didn't go anywhere."
Sake kallon ƙofar ɗakin da ya fito tayi kafin tace "But na duba dukkanin ɗakunan cikin gidan nan and koh kaɗan banji motsin ka a cikin gidan ba."
Murmushi yayi yace "What are you saying?, babu inda naje by the way why is it nake ganin kamar a tsorace kike."
Saita nutsuwar ta tayi kafin tace "No, kawai ina mamaki ne."
Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Alright, kinci abincin da Grandma ta aiko miki?."
Kai ta girgiza masa alamun a'a, nan yace "Why, you should eat it koh da ɗan kaɗan ne."
"No, ba tace ka kaini muci abincin rana a chan ba, muje ka kaini yanzu."
Idanu ya ƙure ta dashi kafin kuma ya miƙe yayi cikin ɗaki, bai jima ba ya fito ɗauke da tray ɗin abincin a hannun sa nan yace "Ba sai munje mu ba, you can eat this" ya faɗa cikin tsukewar fuska.
Hannu ta kai ta buɗe tray ɗin taga wani irin abinci ne ma da bata ta6a ganin irin sa ba, maidawa tayi ta rufe tana ɗagowa ta kallesa kafin tace "I... bansan yadda ake cin irin abincin nan ba."
Wani irin kallo yayi mata kafin kuma ya sanƴa hannu ya ɗau spoon yana ɗebo abincin a ciki, kallon ta ya sake kafin yace da