Showing 201001 words to 204000 words out of 236327 words
taka ƙafar sa yaje, sai dai koh Aljani kokuma babban matsafi, ina ne wurin Grandma, nasan ba zaki rasa masaniya akai ba."
Shiru Grandma tayi tana kallon sa kafin tace "Boy kana lafiya kuwa maiyasa kake tambaya ta wurin, wani abin ne ya faru?."
Kai yake girgiza mata yace "Grandma please, its so urgent just tell me idan kin sani please Grandma" ya faɗa cikin riƙo ta.
Kai ta girgiza masa tace "Ban ta6a jin wuri makamancin hakan ba Boy, ka sanar dani meke faruwa mana."
Kai ya girgiza cike da tashin hankali, ba zai iya sanarwa da Grandma ba dan kuwa bayason hankalin ta ya tashi, dukda kuwa yasan she can be of help."
Sakin ta yayi kawai yana barin falon nata cikin gudu, da sauri ta mara masa baya tana kiran sunan sa.
Part ɗin Nazeerah ya nufa dukda kuwa yasan babu wata jituwa tsakanin su, but ganin yadda take nunawa fake DEENAH kulawa cikin ƴan kwanakin nan yasan maybe she can be of help.
Bangaje kuyangun ta kawai yake yana ratsawa ciki har ya iso cikin fankacecen falon nata, karon farko kenan da ya taka ƙafar sa zuwa cikin part ɗinta.
Nazeerah dake kishingiɗe gaban ta ɗauke da fruit miƙewa tayi tsaye cike da mamaki ganin ZEEYAD ya faɗo mata kamar wanda ake korar sa.
Ƙarasowa gaban ta yayi yana riƙo kafaɗun ta yace "Please, please Big Mom, can you help me?."
Mamaki ne ya cika Nazeerah tana kallon ZEEYAD ɗin ganin yadda ya firgice nan tace dashi "What's wrong with you?."
Kamar wanda zaiyi kuka yace "DEENAH..."
Zaro idanu tayi tace "What's wrong with her, kada kacemin Hafeezah taci galaba akanta."
Kai yake girgiza mata nan yace da ita "Ba Hafeezah bace wannan karon, i know that ban ta6a zuwa wurin ki neman wani abu ba but can you please tell me..."
"ZEEYAD?" cewar Grandma cikin katse shi tana ƙarasowa ta fizgo shi tace "Mai kake yi anan, mai ya kawo ka nan wurin, i thought duk wani abu da ya shafe ka kana iya faɗamin sannan na kan baka shawara mai kyau, but this time ka tsallake ni kazo nan wurin Nazeerah mai kake tunanin zata iya yi maka wanda ni ba zan yi maka ba" ta faɗa cikin 6acin rai.
"Grandma please..."
"Banason jin wani abu, wuce muje" ta faɗa tana nuna masa hanƴa.
"Grandma DEENAH, i can't find her" ya faɗa cike da tashin hankali yana kallon Grandma ɗin.
Kallon sa Grandma take kafin tace "Mai kake faɗa ne haka Boy, ya zakace min baka ga DEENAH ba, ba ɗazun nan da safe kuka zo gaida ni ba."
"Grandma, that wasn't DEENAH."
"Ban...bangane ba, mai kake nufi da ba DEENAH bace."
Riƙo Grandma yayi yana jan hannun ta yace "Come with me."
"Don't you need my help anymore?" cewar Nazeerah.
Dakatawa yayi yana juyowa ya kalleta, duk wani gulma na PALACE ɗinnan ta sani so maybe ta san wani abu akan Naseeba dama kuma abubuwan da take aikatawa, nan yace "You should come too" yana faɗin haka yaja hannun Grandma sukayi gaba.
Da kallo Nazeerah ta bi su kafin kuma ta mara musu baya koh da bata samar da wani alfanuwa a wurin ba ta samarwa idanun ta da kunnuwan ta abinci.
Part ɗinsa ya kawo su tare da buɗe ƙofar ɗakin da ya rufe Naseeba suna shigewa ciki.
Kwance suka ganta duk suna ƙarasowa wurin ta inda duk suka zaro idanu cike da tashin hankali duk suka furta "Naseeba!."
Juyowa Grandma tayi tana kallon ZEEYAD nan tace "Mai ya kawo nasee cikin ɗakin ku, sannan kuma ina DEENAH?."
Shiru yayi kafin ya ƙaraso yana kallon Grandma yake nuna Naseeba dake kwance yace "This witch here have been fooling us all a matsayin itace DEENAH, she have DEENAH in captivity and took her shape duk dan ta biyawa kanta buƙatar da ta daɗe tana nema a wuri na, DEENAH have been away for 2weeks Grandma yayin da wannan matar ke pretending a matsayin ita, i have been living with her wanda duk a tunani na she is my DEENAH."
Hankali tashe Grandma ke maimaita kalmar "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un."
"Kana nufin kace ka kusanci Naseeba a matsayin matar ka DEENAH?" ta faɗa cike da tashin hankali tana kallon sa.
Kai ya girgiza mata yace "No Grandma, but tayi duk wani ƙoƙarin ta na ganin hakan ya faru, but ban bata haɗin kai ba, sabida naji sam hankali na bai kwanta da ita ba duba da wasu irin halaye da ta tsiro dasu, i have been blaming innocent DEENAH akan halayen wannan witch ɗin."
"Where is DEENAH then, ina ta kai ƴar mutane?."
"I don't know, i don't know where to start Grandma, i don't know where to find her, she gave me a clue ɗin inda zan same ta and kince bakisan wurin ba, what do i do now Grandma?."
Shiru Grandma tayi babu abina take sai salallami tana jero tsarkakan sunayen Allah.
"Where did she said DEENAH take?" cewar Nazeerah tana kallon sa.
Ba tare da ya kalleta ba yace "Tace wani wuri ne da babu wani mahaluƙi da ya ta6a taka ƙafarsa yaje wurin except idan ba matsafi koh Aljani bane."
Shiru Nazeerah tayi tana nazari idanun ta kan Naseeba.
Shiru duk ɗakin ya ɗauka babu abinda kakeji sai muryar Grandma dake ta jawa Naseeba tsinuwa cikin muryar kuka tana haɗa wa da addu'a da kiran sunan Allah.
Nazeerah ce tayi caraff tace "I don't know the place but seems like Naseeba na neman yi maka wasa da hankali ne, ba abin mamaki bane idan DEENAH na cikin gidan nan."
Sai a sannan ya ɗago yana kallon ta, kai ta jinjina masa kafin tace "Tun kana yaro Naseeba ke bibiyar ka take kuma son cimma manufar ta akanka, hakan ya sanƴa ba zata yi ƙasa a guiwa ba har sai taga burin ta ya cika, da akwai wata Maid ɗinta Kiki tare suke shirya duk wani makirci da ƙulli, na tabbata idan aka nemo Kiki zata faɗi inda DEENAH take dan kuwa ba zata rasa masaniya ba."
"Where is this Kiki?" ya faɗa yana kallon ta.
Shiru tayi kafin tace "Bana ma tunanin idan idan ƴar garin nan ce, koh tantama bana yi ta koma chan garin su idan Naseeba ta cika burin ta sai ta dawo a zumar cewa duk tafiya sukayi kamar yadda Naseeba ta sanar."
Kai ya jinjina kafin kuma yayi saurin ficewa daga ɗakin inda duk suka bisa da kallo.
Grandma dake cikin tsananin tashin hankali kallon Nazeerah tayi tace "Tunda nake ban ta6a yarda dake ba, wa ya sani ma koh bakin ku ɗaya da wannan iftila'in dake kwance, duk kun bi kun takurawa rayuwar yaro kun hana shi sukuni, duk abubuwan da kukayi masa a baya bai isheku ba, ku shikenan ba zaku sarara ba har sai kunga bayan shi, yayi auren ma kun soma bibiyar matar sa, yarinƴa ashe koh kwana ɗaya batayi cikin gidan nan ba wannan tsinanniyar ta kar6e gurbin ta, insha Allah Naseeba ƙaryar ki ta ƙare yau, azzaluma insha Allah wannan ƙatoton kan naki sai an guntule shi yau sai naga ta tsiya, tsinanniya kawai mai bakin iyaye" ta ƙarashe tana sharce hawaye.
Ɗan ta6e baki Nazeerah tayi kafin tace "Ni ba wannan ba tukun Hajiya, mu kama Naseeba mu ɗaure ta dan kar ma ta samu damar tserewa idan ta farka, ke kanki kinsan bana shiga sabgar da ba tawa ba, ZEEYAD ne ya gayyato ni da kansa idan ba haka ba ai koh murya ta ba zakiji ba har a gama case ɗinnan."
Cikin kuka tace "Eh kuma kinyi gaskiya" tana goge hawayen idanun ta.
***************
________Cikin abinda bai fi awanni biyu ba aka nemo Kiki da ta gudu ƙauyen su kamar yadda sukayi da Naseeba.
Durƙushe take gaban mai Martaba fadar cike da mutane kamar kullum, da kaga idanun ta kaga sun raina fata sai jujjuya su take yawa warwaro a langa, tsabar munafurci da yayi mata ƙatutu cikin zuciya.
"Gata kamar yadda akace itace Jakadiyar Sarauniya Naseeba, sannan da sanin ta take aiwatar da duk wasu hukunce-hukuncen ta" cewar ɗaya daga cikin ministocin.
Tsaye ɗaya ya tashi bisa ga Umarnin mai Martaba nan ya hau tambayar Kiki "Menene ainihin sunan ki, sannan daga wace ƙabilar kike, sannan kuma menene gaskiyar abinda Yarima YAZEED yake faɗa har ya sanƴa aka kamo ki daga chan garin da kika gudu..."
"Wait, wait, sake tambayar ta kake do you think i can lie to you or something?" kafin kuma cikin tsawa ya ɗaura da faɗin "My wife is in their captivity and you're here asking her koh abinda na faɗa akansu is true, just ask her where my wife is or else i will take action in my own."
"Calm down Prince, komai cikin ruwan sanƴi akeyin..."
"What kind of ruwan sanƴi, irin wadannan mutanen ba'a binsu ta lallama, what about my wife then, do you have any idea yadda rayuwar ta ya kasance tare dasu tsawon makonni biyun da tayi a wurin su, and you expect me to calm down, calm down on what, my wife being captured or what?" ya faɗa cikin tada jijiyoyin wuya yana iyowa kan minista ɗin.
Maganar mai Martaba ce ta dakatar dashi, sai hura hanci yake cike da tsantsar 6acin rai yana fidda huci mai tsananin zafi, juyawa yayi ga mai Martaba ɗinma ya hau faɗin "Are you trying to stop me or what your Highness?, why would he tell me to calm down, does he have any idea ɗin halin da nake ciki...? Shiru yayi ya kasa iddawa sakamakon wani tululun baƙin cikin da yazo masa maƙoshi.
Tasowa mai Martaba yayi daga inda yake zaune yana takowa inda ZEEYAD ke tsaye ya hau buga kafaɗun sa yace "We should take everything easy Son, insha Allah matar ka zata bayyana."
"If anything happens to her then... then i don't know ya tawa rayuwar zata kasance nima."
"Don't say that, i promise you zata dawo cikin gidan nan yau."
Juyawa yayi ga ministan nan yace "The Prince don't want her to be confronted like this, ku kai ta ku garƙame sannan a haɗa mata da horo mai tsanani har sai ta faɗi gaskiya akan dukkanin abinda suke shukawa da ita da Naseeba, sannan ta faɗi inda matar Yarima take, take her."
Cikin ƙururuwa tace "Kuyimin rai, wallahi zan faɗi komai dan kuwa nasan koh da nayi shiru azaba zan sha sannan kuma nazo na faɗi gaskiyar da banason faɗa ɗin, wallahi nasan inda take kuma shirye nake da na faɗi gaskiyar komai."
Kai sarki ya Jinjina yana komawa wurin zaman sa, nan ministan yace "We are all ears."
"Wallahi amaryar Yarima tana nan da ranta, sannan tana chan ƙarƙashin kulawar kaka ta ne."
"Kulawa kokuma azabtarwa?" ya sake tambayar ta.
"Azabtarwa nakeson faɗa, ayimin rai."
"Wacece kakar taki sannan a ina take da zama?."
"A chan wani ƙauye ne wanda tafiyar awanni sha biyu ne tsakanin sa da wannan MASARAUTA, sannan Kaka ta ta kasance tsohuwar matsafiya ce wacce ba'a ta6a yin irinta duk ƙauyen ba, haka ma batada ɗigon imani koh kaɗan muddin an biya ta makuɗan kuɗaɗe, sai dai wannan karon bata kar6i kuɗi ba sakamakon cewar jinin amaryar Yarima ZEEYAD yayi mata dan kuwa irin sa ta daɗe tana nema dan cikar wani burin ta, maganar da nakeyi maka yanzu ma a yau ɗinnan take niyyar sadaukar da ita ga ƴan ruwa sakamakon wani matsayi da zasu bata."
Cike da tashin hankali duk suke kallon Kiki, Sarauniya Hafeezah kuwa wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya, koh bakomai Naseeba ta kawo mata sauƙi yanzu saura ita da ZEEYAD ne, dan kuwa babu shakka kafin mu su isa ga kar6o DEENAH an riga da an sadaukar da ruhin ta ga aljanun ruwan, sai dai suje su sami gawar ta.
A matuƙar ruɗe sarki ya tashi tsaye cikin tsawa yace "Find her."
Duk fadawan dake cikin fadar ficewa sukayi cike da girmamawa cikin bin umarnin sarkin suka je suka fara shirye-shiryen kaiwa Ƙauyen farmaki, inda aka tafi da Kiki dan yin jagora.
ZEEYAD kuwa tsaye yayi kamar wanda aka ɗauke masa dukkanin wasu ƙuzarin jikin sa.
Dafa shi YAZEED yayi yace "We will find her."
Runtse jajayen idanun sa da suke yi masa yaji sosai yayi yanajin sa kamar ma ba a duniyar yake ba.
He can't believe wai DEENAHr sa za'a yi wa sacrificing soul nata wa ƴan ruwa, this is odd.
Juyawa kawai yayi ya fara tafiya kafin YAZEED ma yayi saurin mara masa baya.
Komawa mai Martaba yayi ya zauna yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, kallon ministocin sa yayi yace "Naseeba, Jakadiyar ta dama kuma duk wasu masu sanƴa hannu cikin wannan lamari duk a yau za'a yanke musu hukuncin da aka tanadawa masu laifi irin nasu."
Amsawa sukayi cike da girmamawa kowanne zuciyar sa cike da al'ajabin wannan lamari.
*********************
________Ƴar ƙofar karar da aka buɗo ne ya sami damar baiwa haske gurbin shiga cikin ɗakin.
A hankali take motsa nannauyar idanun ta da hasken ranar ya dallo mata shi da bakin ta da ya bushe ƙaƙarau kamar wacce ta ɗau tsawon kwanaki bata sha ruwa ba.
Kutsa kai akayi aka shigo cikin ɗan ƙararramin ɗakin wanda kai tsaye za'a iya kiran sa da kurkuku tsabar matsi da ƙanƙantar sa, ga kuma tarin wasu tsoffin abubuwa da aka rufe su cikin buhu da alamu dai sun daɗe duba da yadda spiders suka zagaye shi da gine-ginen su.
Turo mata tray ɗin silver akayi wanda ke ɗauke da busasshiyar slice bread guda ɗaya kafin tsohuwar ta fara magana cikin muryar da ba fahimtar komai take ba "Ina mai gargaɗin ki da kici wannan abincin dan kuwa shine zai kasance abinci na ƙarshe da zakici a duniya, ƙin cin sa dai-dai yake da rasa ranki nan da ƙanƙanin lokaci, nikuma ba zanso hakan ya faru ba kafin ki mutu dole naje na sadaukar da ruhin ki koh dan samun cikar buri na."
DEENAH dai saurarar ta take ba dan tana gane wani abin da take cewa bane, gashi kuma a mugun galabaice take, sau ɗaya take bata busasshiyar bread a rana ɗaya matsayin abinci ruwa kuwa, idan ta bata cikin wani ɗan madaidaicin kofi a rana ɗaya shikenan, shima dai tana bata ne dan kar ta mutu kafin lokacin da zata bayar da ita yayi.
DEENAH dai kawai da idanu take bin ta, har ta fice daga cikin ɗakin tana rufo ɗakin take ya gauraye da wani irin duhu kai kace dare ne yayi.
Jan ɗuwawu tayi daga inda take zaune zuwa inda taga ta ajiye tray ɗin kasancewar hannayen ta da ƙafafuwan ta da akayi musu ɗaurin goro.
Da kyar ta miƙa hannu ta lalumo busasshiyar bread ɗin wanda shima ya fara huhhuna ta kai bakin ta inda kuwa wasu irin siraran zafafan hawaye suka shiga yi mata zarya kan kumatu, a haka ta lunƙuma bredin a baki dan kuwa idan bata ci ba wani abincin take kawo mata daban wanda bata tunanin mutane ma suna cin sa, sannan ta sanƴa ta dole sai ta cinƴe shi.
Sosai zuciyar ta ke cike da baƙin ciki da ƙunci, babu wanda ya san da ita anan wurin sai Allah, Abyad ɗinta bai san tana nan wurin ba da ya daɗe da zuwa neman ta, yana zama da Naseeba ne a matsayin ita, babu ta yadda zaiyiwu ya gane cewa ba ita bace ba, shikenan ita kuma tata rayuwar tazo ƙarshe kenan dan kuwa she have no idea mai tsohuwar nan take shirin aikata mata, maybe dama chan Allah bai tsara zasuyi rayuwa tare dashi ba, maybe dama haka Allah ya tsara ƙaddarar rayuwar ta zata mutu ne ba tare da kowa nata ya san cewa ta mutu ba, ta san shikenan ƙarshen ta yazo kenan tunda har tsawon kwanakin nan babu labarin da taji na ana neman ta koh asirin Naseeba ya tonu, wani irin matsanancin kuka ta sanƴa da ƙarfi tana yi harda shessheƙa, sosai koh ina na jikin ta keyi mata zugi da raɗaɗi, musamman hannayen ta da ƙafafun ta da tunda ta tsinci kanta anan ba'a ta6a sunce mata su ba, except idan zata banɗaki ne, ba'a barin ta taje koh ina, kullum tana cikin wannan ɗaki mai matsanancin wari da duhu, ga kuma tarin kwari da cinnaku kamar ruwan su akeyi, bata ta6a runtsawa na awa ɗaya ƙwakkwara cinnaka bai gallaza mata cizo ba, ga kuma azababbiyar ƴunwa da ishi da kullum take cikin sa, ga ruwa tana gani amma a bata ta sha ya zama aiki.
**************************
_________Naseeba ce ta fara buɗa idanun ta a hankali tana ware su kan Grandma da Nazeerah da suka sanƴa ta a gaba, tuna abinda ya faru tsakanin ta da ZEEYAD ne ya sanƴa ta saurin waro idanun ta tana sake bin su da kallo.
Duk tsare ta sukayi da idanu duk suna bin ta da kallo, jijjiga kujerar da take ɗaure akai ta fara tana ihu cikin bakin ta dake a toshe sealing tape.
Grandma dake bin ta da mugun kallo ne ta taso inda take, cike da mugun ta ta ɗaye gum ɗin bakin nata take ta saki wani ƙara cike da azaba, kafin kuma ta hau faɗin "Let me go or else i will make you all regret it."
Mari Grandma ta ɗauke fuskar ta dashi tace "Mu daɗe bamuyi nadama ba Naseeba."
Sosai zuciyar Naseeba ke burning, juyo da fuska tayi tana kallon Grandma kafin cike da fusata tace "How dare you Old hag."
Wani marin Grandma ta sake ɗauke ta dashi wanda yafi na farkon.
Magana zata sake ta sak ɗebe ta da wasu tagwayen marin kafin ta ɗaura da faɗin "You said a word, you get a Slap."
Huci kawai Naseeba ke fitarwa zuciyar ta na wani irin tafarfasa.
"How dare you Naseeba, ke bakiji kunƴa ba, da girman ki kike neman ɗan mijin ki da Alfasha, how could you do such a thing, well koma dai menene ya faru yanzu ke kika jawa kanki, sabida mai Martaba dama kowa ya gano ki asirin ki ya tonu Naseeba, da zaran an ɗauko DEENAH yanzu babu 6ata lokaci zaki baƙunci lahira" cewar Grandma cikin tsananin fushi.
Baki ta buɗe tare da faɗin "You think you can find her so easily am pretty sure kafin aje gareta ta riga da ta mutu."
Wani azabbaben mari Grandma ta ɗauke fuskar ta dashi a karo na huɗu tana faɗin "Shut up and don't say a word..."
"What will you do old hag, are you going to kill me, fine then go ahead koh bakomai buri na na kusantar jikan ki ya cika."
Mari Grandma ta sake kai mata tana faɗin "We know everything, Boy ba zai