Showing 66001 words to 69000 words out of 236327 words
kwakwalwa sai
_"Masha Allah, nima goben nan zanyi tafiya zuwa London dan samo muku engagement ring mai kyau da tsada, domin ƴaƴan nawa na musamman ne"_
Rufa bargon tayi har kanta tana fashewa da kuka..............
*Yawan Comment, Yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*022...*
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
_"Surely with every hardship there is ease" (Q94:5)._
```May Almighty ALLAH (SWT) justify your efforts, purify your faith, beautify your character, satisfy your needs and make things easy for you and your entire family now and always, Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Juma'at Mubarakah```
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
..............6angaren ZEEDAN kuwa mai gadi kawai ya baiwa saƙon nata ya wuce ba tare da ya bita ɗin ba............
*********************
..............Masauƙin sa ya nufa yayi wanka sannan yayi shirin zuwa masallaci, sai da yayi sallar Isha'i anan kafin ya dawo.
Bayan ya dawo ne already yayi ordern abinci aka kawo masa yaci sannan kuma ya ɗauko Laptop ɗinsa ya kama aiki.
Sosai yayi abubuwan da yakamata yayi a ciki kafin kuma ya rufe ta.
Wayar sa ya ɗauka nan dai yaga missed call kaca-kaca, nan ya fara bin masu amfanin yana kiran su.
"Assalamu Alaikum Dad" ya faɗa bayan yayi dialing number ɗinda ya gani a ƙarshen yi masa missed call.
"Wa'alaikumusalam, ZEEYAD, dafatan kana lafiya?."
"Alhamdulillah Dad."
"Naji Mom naku tace kayi tafiya koh, yaushe ne zaka dawo?."
Shiru yayi yana tunani kafin yace "Dad da zaran na gama abinda ya kawo ni, but idan akwai wani abinda kakeson nayi maka ne zan dawo koh gobe ma."
"A'a kada ka damu, ka bari idan har ka gama abinda ya kai ka, duk ranar da ka dawo sai mu tattauna game da maganar ka dama kuma Khairat."
"Yeah sure" ya faɗa.
"Madallah, sai anjima koh, take care."
"Thank you sir" ya faɗa yana ajiye wayar.
Komawa da baya yayi ya jinginu da kujerar da yake kai yana dafe goshi.
Sosai yake tunanin haɗin auren sa da na Khairat da iyayen ta ke son yi musu, Khairat sam batada irin qualities ɗin da ake buƙata a wurin mace ta gari, batasan darajar kanta ba balle kuma na wasu, ta ɗauki rayuwar yahudawa ba a bakin komai ba, dan kuwa a cewar ta hakan shine wayewa.
Sosai ya shiga cikin damuwa, sam ba zai iya rayuwa da mace kamar Khairat ba, dole ne yayi dukkanin yadda zaiyi na ganin ya dakatar da wannan haɗin nasu, amma tayaya, tayaya zai fara hakan iyayen ta sunyi masa halacci, kenan buɗar baki zaiyi yace musu bayason ƴar su komiye?
Wannan shine tunanin dake ta yi masa yawa a zuciya da kwakwalwa sannan kuma ya hana sa samun sukuni.
Wayar ya sake ɗaukawa ya shiga kiran lambar ta, jin sa a kashe yasa duk yaji babu daɗi a zuciyar sa, hakan na nufin yau ba zaiyi bacci mai daɗi ba kenan...............
***********************
...........Da misalin ƙarfe goma na safe aka kawo masa abinda yayi ordering.
Amsa yayi ya dawo cikin Apartment ɗinshi kafin ya zauna tare da ciro wata ƴar madaidaiciyar kwali.
Buɗe ta yayi take wani abin hannu mai kyau na mata golden colour ya bayyana sai sheƙi da yalƙi yake yi.
Murmushi yayi tare da ciro ta yana ƙare mata kallo.
"I just do hope she accept this gift" ya faɗa kafin kuma ya maida ta cikin kwalin ta ya rufe.
Wrapping ɗinta yayi a cikin ledar gift mai kyau mai zanen love a jiki kafin kuma ya miƙe yayi shirin wanka.
Bayan ya fito ne ya shirya cikin ash colour ɗin suit mai kyau, gashin kansa da ya sha gyara mai kyau sai sheƙi yake yi, sosai yayi kyau kamar kullum.
Tsayawa yayi a gaban mirror yana ƙarewa kansa kallo inda yaga baiyi ba sai ya gyara duk dan kawai ya burge ta ta kasa ɗauke idanun ta a kansa.
Atlast murmushi yayi yana gyara tsayuwar zaman coat ɗinsa kafin kuma ya ɗau makullin motar sa da Gift ɗin ya fice sai ƙamshi yake tayi.
School ɗinsu ya nufa yana zaman jiran ta har aka fito first period bai ganta ba, haka kuma koh ɗuriyar ta bai gani ba, bayan ya leƙa class ɗin nasu.
Bai tsaya tambayar kowa ba ya nufi gidan su.
A bakin gate ɗin gidan ya danna horn, take mai gadi ya leƙo da kansa dan ganin koh wanene.
Fitowa yayi tare da zuwa kusa da window ɗin motar, sauƙe glass yayi nan yaga ZEEDAN ne.
Haƙora ya washe yace "Kai mai gida ashe dai kai ne, barka da zuwa bari na buɗe maka gate ɗin."
Kai ZEEDAN ya jinjina masa dan kuwa har yanzu ba wai Hausar ya iya sosai ba balle ya biye masa.
Buɗe gate ɗin keda wuya ya kutsa kan motar tasa cikin gidan.
"Ohh this Mother-fucker is here again" ya faɗa cikin cize haƙora yana kallon motar Abdul dake fake a parking space ɗin gidan.
Parking tasa motar yayi ya fito zuciyar sa kamar zata tarwatso waje tsabar haushi.
Inda ya gansu zaune ya nufa tare da janƴo kujera ɗaya ya zauna fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure.
DEENAH kallon sa tayi kafin kuma ta kauda idanun ta tana mamakin mai yake nema da ita haka, bayan duk ƴan matan da yake dashi.
Kallon sa Abdul yayi cike da mamaki kafin yace "Excuse me, Malam lafiya?."
Kallo ɗaya ZEEDAN yayi masa ya ɗauke kai tare da sauƙe idanun sa kan DEENAH yace "I want to have a word with you."
Ba tare da ta ɗago ba tace "Maybe later, amma yanzu ina tare da baƙo ne."
Ta gefen ido ya kalli Abdul kafin a zuciyar sa yace _"Har wannan abin yana da wani value a wurin ta?."_
Kafin kuma yace "Yanzu nakeson muyi maganar."
Ɗagowa tayi ta kallesa kafin tace "No not now..."
"I want it now" ya faɗa a ƙufule yana katse ta.
"Sweetheart, waye shi, why is he talking to you like this?" cewar Abdul yana kallon DEENAH.
"Ka rabu dashi dear, aiki ne bai ishe shi ba."
Dunƙule hannu ZEEDAN yayi yana jin yadda zuciyar sa ke tafarfasa "MADEENAH?" ya faɗa.
Kallon sa tayi nan yace "I want to talk to you."
"Nikuma nace ba zanyi magana da kai ba, just let me be please, maiyasa kake shisshigewa rayuwa ta haka ne?" ta faɗa cike da jin haushi tana kallon sa.
Sosai yaji zafin yadda tayi masa magana a gaban wannan ga6on kalan kawai ya raina shi take so.
"Wanene shi, kuma miye tsakanin ki dashi?."
"I don't even know, kawai ya bi ya takura min ne, babu komai tsakani na dashi."
Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon ta, kafin kuma yace "Let's talk, for GOD's Sake please."
Shiru tayi ba tare da ta ɗago ta kallesa ba, dan kuwa ta gane so yake yayi Playing da feelings ɗinta kamar yadda yayi wa ƴan matan sa, daga baya kuma yayi dumping nata yaje yayi auren shi, dukda batasan koh Surayya kaɗai bace budurwar sa but ta tausaya mata dan kuwa sai da ya gama lalata mata rayuwa tukun yake shirin yin aure yanzu, shiyasa koh kaɗan ba zata sakar masa fuskar yi mata wasa da hankali ba.
"MADEENAH?."
"Just let me be please, just stay away from me, ka bar bibiya ta haka nan, babu komai tsakani na da kai why then kake neman takurawa rayuwa ta ne, bana binka bashin komai haka kaima, toh mai kuma kake sake nema daga gare ni, i thought tunda na sauƙe nauyin dake kaina mun rabu kenan, but you kept pursuing me, mai kake nema ne daga gareni haka?" ta faɗa bayan ta miƙe tsaye tana kallon shi.
Tsaye ya tashi shima yanajin zafin yadda take yi masa magana sosai a ranshi but haka nan ya daure, abinda yasa ransa ke 6aci bai wuci ganin Abdul ɗinnan da ya kafe su da ido yana kallo bane, shi kuma ba zai ta6a yarda bane ta yarfa sa a gaban shi.
Shiru yayi kawai yana kallon ta ba tare da ya iya cewa komai ba.
Abdul ne ya miƙe tsaye tare da dafa kafaɗun ZEEYAD yace "Look bro bansan koh menene alaƙar dake tsakanin ku ba, but the best thing you can do shine ka rabu da ita, since hakan take da buƙata, you can't just keep pursuing a girl that doesn't like you, i can clearly see that you've feelings for her, but am sorry to say you're late..."
"No am not late, but maybe you're" ya faɗa yana cire hannun Abdul daga dafa shi da yayi, kafin yace "Do you really thinks she liked you, No she is just pretending to be inlove with you, but the one who she truly loves is....Me" ya faɗa yana juyawa ya kalli DEENAH da idanun ta ke ƙasa ta harɗe hannayen ta a ƙirji.
Ɗagowa tayi tana kallon sa cike da mamakin abinda ya faɗa.
"W..wha..what are you saying?" ta faɗa still idanun ta akansa.
Murmushi yayi tare da sarƙe hannaye cikin aljihu yana ƙarasowa gaban ta yace "Isn't that true, you like me don't you?."
Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "No..i don't like you, and babu abinda zai sa na so mutum kamar ka, koh da kuwa kai ne kaɗai namijin da ya saura a duniyar."
"Lies."
"Am not lying, gaskiya nake faɗamaka, baka kai matsayin da zanyi maka ƙarya ba, idan ma kana tunanin inason ka ne yasa kullum kake bibiya ta then you're wrong, coz am inlove with someone else, and you know what?, yana da halaye masu kyau, sannan kuma ya tara dukkanin qualities ɗin da ake nema a wurin miji na gari, Unlike you da bakasan koh ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, wanda bakada aiki sai kula matan banza sannan kuma kayi dukkanin abinda kaso dasu, kana tunanin ni irin matan nan ne da har zaka dinga bibiya ta dan kawai ka samu damar shawo kaina ka kuma yaudare ni da kalaman ka, ka cika mummunar manufar ka a kaina?" kai ta girgiza tana kallon sa kafin ta cigaba da faɗin "Ba zaka ta6a samun hakan ba, idan kana tunanin kuɗin ka dama kuma kyawun ka zasu ruɗe ni then you're mistaken, dan ni ba su ne a gaba na ba, samun miji na gari wanda yasan darajar mace yake kuma girmama ta tare da sauƙe dukkanin haƙoƙin da ya rataya a kansa irin sa nake biɗa kuma Alhamdulillah na riga da na samu, ba irin ka mai tara matan banza kana lalata musu rayuwa ba, ni Abdul shi ne za6i na kuma shi nakeso, kuma shi zan aura ba kai ba, ban ta6a sonka ba kuma ba zan ta6a son naka ba, idan ma kana tunanin inada interest akanka ne gara kayi gaggawar farkawa domin kuwa mafarki kakeyi, ni ba zan ta6a zama taka ba, keep that at the back of your mind, i will never be yours, never....ever" ta ƙarashe hawaye na gangaro mata idanun ta cikin nasa.
Sosai da Sosai maganganun ta sukayi mugun tasiri wa zuciyar sa dama kuma gangar jikin sa, da kyar ya iya motsa ƴar yatsar sa tare da wiping ɗin fuskar sa, sosai jikin sa yayi matuƙar sanƴi da maganganun da ta faɗa masa, he can't believe ganin sa da Surayya ne yasa ta ɗauke shi mutumin banza kuma take yi masa kallon hakan.
He can't believe DEENAH zata iya buɗar baki ta iya faɗa masa magana haka, sosai yaji dukkanin wani ƙuzarin dake tattare dashi ya gudu, he was stunned sosai kalaman ta sukayi matuƙar shigar sa, he was heartbroken for loving the wrong person cikin shekaru goma na rayuwar sa, he loves DEENAH but yau guda tayi turning ɗinshi down, tayi refusing nasa tun kafin ya bayyana mata abinda yakeji game da ita, sosai da sosai yakejin zafin hakan a ransa.
"Get out of my house, sannan kuma kada ka sake dawowa, yakamata ka fita daga cikin rayuwar mu dukkanin mu haka nan, dan kuwa hakan ba zai sa ka same ni ba" ya jiyo ta faɗi hakan.
Kai ya girgiza cike da dauriyar abinda yakeji a ransa yace _"You won't easily get me out of your life, and maganar bibiyar ki kuma yanzu na fara shi koh da kuwa hakan na nufin zan rasa dukkanin wani abinda na mallaka ne"_ kafin kuma yayi murmushi a fili yace "Oh come on girl, ban furta cewa inason ki ba tukun why then kika ɗau abin da zafi haka, koh kin ta6a ji a bakin wani cewa ni ZEEYAD inason ki ne?, well then forget, dama abinda ya kawo ni wurin ki shine, nazo nayi wa Mom naki sallama ne akan i will be going back tomorrow and just to check on how you're doing, nothing else, so relax please" ya faɗa yana kallon ta.
Juyawa yayi ga Abdul da ya zama ɗan kallo yace "And you, i just hope dukkanin abinda ta faɗa akan ka turns out to be the truth, coz you doesn't seem innocent."
Ganin Abdul ɗin ya haɗe fuska ne yasa shi yin murmushi yace "Relax Mehn, just don't try to break her heart, idan kuwa kayi hakan then i will make sure you regret it, Okay?" ya ƙarashe yana bubbuga kafaɗar Abdul ɗin.
Murmushi Abdul ɗin yayi yace "I won't break her heart, she deserves a pure relationship, idanma kana tunanin hakan zai faru then..."
Cike da basarwa ZEEYAD ya juya ga DEENAH yana ignoring maganar Abdul dan kuwa ba ƙaramin haushi yake bashi ba, koh kaɗan gayen baiyi masa ba, but ya rasa miye DEENAH ta gani tattare dashi har take ikirarin shi takeso, kafin yace "Is your Mom home?."
Kai ta girgiza masa alamun a'a.
Nan yace "Okay then tell me, ya jikin ki?."
"Am Okay" ta faɗa cikin sanƴi tana kauda kai.
Kai ya jinjina yace "Good, alright then i will take my leave, ki gaida Mom naki idan ta dawo."
Kallon sa tayi kafin kuma ya wuce trying so hard ganin yayi controlling abinda yakeji a cikin zuciyar sa.
Ƙarasawa wurin motar sa yayi ya buɗe ta ya shiga mai gadi na buɗe masa gate ya bar cikin gidan da mugun gudu kamar zai tashi sama, bai koh kula mai gadi dake ta faman ɗaga masa hannu yana washe haƙora ba.
Sosai DEENAH taji jikin ta yayi sanƴi, a haka ta sallami Abdul ɗinma ya tafi dan kuwa bata tunanin zata iya cigaba da hirar dashi.............
***********************
.............Juye-juye kawai takeyin akan gado ta rasa meke yi mata daɗi.
Sosai takejin ba daɗi tare da jin haushin kanta kan maganar da tayi masa ɗazu.
Haka ma 6angaren ZEEYAD he was heartbroken, bai iya runtsawa cikin dare ba, sabida jin DEENAH ba shi takeso ba sai wani daban.
The Next day ya bar garin Sokoto zuwa Kano..............
*******************
*******************
................"ZEEDAN wait" ta faɗa tana shan gaban sa.
Niyyar wucewa yake ta riƙo hannun sa tace "Ka faɗamin maganar da kukayi da Daddy."
Tsayawa yayi yana janƴe hannun ta cikin nasa, shiru yayi kafin kuma daga bisani yace "I can't refuse your Dad, coz i respect him, sannan inajin sa ne kamar mahaifina, ba zan iya ja da abinda ya faɗa ba, yayi min abinda koh Uban da ya haife ni ya gaza yi min shi, why do you think cewa zan iya buɗar baki na nace masa banason auren ki Khairat?."
Murmushi mai nuna tsantsar farin cikin da take ciki tayi tace "Wowww, so that means we are really getting ENGAGED within the next four days, what a good news."
Ra6a ta yayi ya wuce kafin kuma tayi saurin mara masa baya tana rungumo hannun sa tace "Don't you think we should go out for a romantic date since we are getting ENGAGED soon" ta faɗa tana kallon sa.
"No am not going."
"Well you have to, koh da kuwa bakaso hakan ba, zan koma ciki yanzu sannan na sanar da Daddy cewa tunda muke da kai baka ta6a nuna min kulawa ta musamman ba, idan ya tunkare ka da hakan kai kuma ba zaka iya yi masa ƙarya ba, dole ne ka faɗa masa abinda ke faruwa, daga nan kuma kaga dole ne dukkanin wani ƙimar ka da yake gani ya zube sabida ka kasa kula da ƴa ɗaya tal da ya haifa, bayan kuma irin halaccin da yayi maka ya fito da kai daga cikin ƙangin wuya"
Shiru ZEEDAN yayi yana jinjina makirci irin na Khairat.
Bai kula ta ba yayi gaba inda kuma ta mara masa baya, motar ya buɗe ya shiga ita ma ta shige, zuciyar ta cike da tsantsar farin ciki sabida zata mallaki irin mijin da ta daɗe kuma take mafarki tare da burin aura.
ZEEDAN ya haɗu ne koh ta ina, babu abinda yafi ɗauke mata hankali game dashi face sexy body ɗinsa, infact komai game dashi abin sha'awa ne dama kuma burgewa, shiyasa take mutuwar ƙaunar sa take kuma mutuwar kishin sa tare da kuma toshe duk wata hanƴa da zata bi dan haɗuwar sa da wata macen, koh da ta koma US karatu hankalin ta na kan ZEEDAN yayin da kuma zuciyar ta ke cike da mugun kishin sa, dan kuwa tasan yana chan ƴan mata kowacce