Showing 9001 words to 12000 words out of 236327 words

Chapter 4 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45371

ya juyo ya kallesa sama da ƙasa kafin yace "Yeah, i guess you need new clothes, Abdulhakeem ka basa kuɗi yaje ya saya dukkanin abinda yake buƙata bana kuma son ya dame ni akan maganar wata kuɗi, bana ƙaunar ganin fuskar sa, ka bashi kuɗin da zai ishe sa yayi komai dashi bama sayan kaya kaɗai ba na shekara ɗaya" yana faɗin haka ya shige motar aka rufe.



Kallon sa Wanda aka kira da Abdulhakeem yayi yace "How lucky of you!...anyways yanzu fita zamuyi ka jira idan mun dawo sai na baka kuɗin."



"No i need the money right now."



"What, rashin kunƴa zakayi min, alright then mai zai hana kawai ka zama ƙuda ka shige cikin aljihu na ka ɗau kuɗin ka fito, you scoundrel" bai jira cewar ZEEYAD ɗin ba yayi gaba tare da shigewa ɗaya daga cikin motocin da aka jera ɗin.



"Kai ƙasƙantacce ba zaka matsa bane koh dai sai an kwashe maka ƙafafu ka rasa na tafiya" ya jiyo muryar Mulah ta bayan sa.



Juyawa yayi ya kallesa fuskar nan duk tasha Bandage da plaster, ƙarasowa gaban sa Mulah yayi yace "I can't believe kai ne kayimin wannan abin, anƴa ma bakada Aljanu kuwa kokuma dai nace fatalwar uwarka ce ta taso ta shige jikin ka ka aikata min hakan."



Sosai ran ZEEYAD ya 6aci hannu ya kai da niyar bugun Mulah sai dai yayi nasarar cafke hannun nasa tare da faɗin "Kayi kaɗan yaro bansan dai koh nangaba idan ka ƙara girma ba, wancan ranar ma tsautsayi ce ta faɗa min, hukuncin da mahaifin ka yayi maka koh kaɗan bai faranta min rai ba, a yanzu kuwa inada damar yi maka duk wani abinda naga dama sabida babu mai kar6ar ka" dogon gashin kansa ya damƙo yace "Wannan gashin naka naga kamar tana buƙatar gyara, muje mu na gyara maka shi yanzun nan" ya faɗa yana ture shi da ƙarfi ya faɗi.



Nan hankalin mutanen wurin ya fara dawowa kansu, fizgo sa yayi tsaye ta baya tare da tusa sa gaba suka bar arear cikin gidan.



Buɗe ƙofar ɗakin yayi tare da tura sa ciki yace "Ba zaka fito ba har sai sauron dake jibge a cikin ɗakin nan sunyi min yaga-yaga da naman jikin ka, koh da jinin jikin ka zasu zuƙe gabaɗaya ba zan damu ba, dan dama bakada wata amfani da mutuwar ka da rayuwar ka duk ɗaya ce" ya faɗa yana garƙame ƙofar da ƙatuwar sakata ta waje.



"Oh no!, Mosquitor bites are so dangerous to health" faɗin ZEEYAD ɗin kafin kuma ya ankare yaji mil wani irin zazzafan cizon sauro a gefen kumatun shi, da sauri ya kai hannu tare da marin fuskar sai dai da alamu bai sami sauron ba.



Kukan sauro ne suka cika masa kunne kafin ya ankara kuwa tuni sun mamaye shi sun fara cizon sa, cikin ɗagun murya yace "Get me out of here Mulah."



"Hahahahahaha, so nake suyi gunduwa-gunduwa da naman jikin ka kafin na fitar da kai, koh an gayamaka ka bugi banza ne?" cewar Mulah tare da ɗaukar bowl ɗin barasa ya kafa akansa, gyatsa mai ƙarfi yayi tare da goge bakin sa yana lumshe idanu.



ZEEYAD abu goma ya haɗu yayi masa yawa, tsananin duhun ɗakin, zafi, kukan sauro dama kuma cizon su, irin cizo mai zafin gasken nan.



Zubewa yayi wurin tare da fara lalume koh zai sami abinda zai kori sauron dashi sai dai ɗakin babu komai sai ƙasa da yake ta shafawa.



Toshe kunnuwan sa yayi kawai tare da ƙanƙame jikin sa,dan kuwa babu yadda ya iya face ya bari su cize sa ɗin.


Sai da yayi mintina ashirin a cikin ɗakin nan kafin Mulah ya buɗe shi, dariyar mugunta ya saki yace "Koh bakomai yanzu ka horu, nangaba ba zaka sake gigin kwatanta abinnan akan wani bama balle ni, au ashe fah na manta nace zan aske gashin nan koh?, kai maza kuzo ku riƙemin shi ku kaisa wurin Hakim yayi masa aski da kwalba, kai ba mace ba ka tara wannan uban gashin, kodai ka fara yawo da ƴan iskan gari ne bansaniba?."



Tahowa sukayi tare da kama ZEEYAD ɗin da jikin sa baki ɗaya kama daga kan fuskar sa duk yayi jan tabo sakamakon cizon sauron, haka nan suka ja shi kamar kayan wanki suka kaisa wurin wanda Mulah ya umurce su.



"Kai Hakim gashi nan Mulah yace mu kawo maka shi ka mule masa kai, askin kwalba zakayi masa kada ka bar gashi koh kaɗan akansa."



Dariya wanda aka kira da Hakim yayi yace "Madallah, madallah da wannan rana, na daɗe ina farautar ka sai kuma gashi yau Allah ya kawomin kai har cikin fada ta ba tare da na sha wata wahala ba, ku miƙa saƙon gaisuwa ta ga Mulah sannan kuma kuce dashi ina mai gayyatar sa liyafa yau da daddare a gida na" ya ƙarashe yana tamƙe fuska tare da kallon ZEEYAD.



"Masha Allah, maza ka tashi yanzun nan na aske maka wannan gashi da ka tara kamar ɗan bokaye, sai dai babu laifi kuma yayi maka kyau, amma fah hakan ba zai sanƴa naƙi aiwatar da nufi na akanka ba" ya ƙarashe yana washe yellow ɗin haƙoran sa.



Miƙewa yayi daga zaunen da yake tare da zuwa wani lungu daga cikin shagon sa ya ɗauko wata ƙatuwar kwalba.



Zuwa yayi ya fasa ta yana dariya kafin yace "Wannan zai yi matuƙar taimakawa wurin kammala askin da wuri kuma sakamako ya fito da kyau, koh ya kace hahaha."



Da idanu kawai ZEEYAD ke bin sa da kallo dan kuwa babu ta yadda zai yarda ne a sanƴa masa kwalba a kai da sunan aski.



Takowa yayi zuwa inda ZEEYAD ke durƙushe tare da kama bakin doguwar gashin nasa da niyar yankewa.



Shigar abu mai kaifi a gefen cikin sa ne ya sanƴa sa yar da kwalbar hannun nasa yana faɗi zaune riƙe da gefen cikin sa, idanun sa na sauƙa akan ma'askar dake riƙe a hannun ZEEYAD.



Miƙewa yayi tsaye ya tako inda Hakim yake ya tsuguna yace "Aski kakeson kayimin?, you don't have that right, yes i would became so very bad since naga kamar hakan kukeso, you would be my first victim, i promise i will make sure kayi nadamar shiga gona ta, i have suffered alot for the past 20years, dan haka yanzu lokaci yayi da yakamata nima na tsayawa kaina, but before i vanished without a trace i would make sure i killed you first Hakim" ya faɗa in a serious tone yana kallon Hakim da ya haɗa wani irin uban gumi yana zaro idanu waje.



Jefar da askar askin yayi kafin ya miƙe tsaye ya fice yana mai kama gashin nasa ya ɗaure ta wuri guda.........




********



..........Zaune yake bakin famfo yana wanke fuskar sa, jikin sa yabi da kallo wanda duk yayi tabo yana yi masa zafi, kafin kuma ya miƙe tsaye yana gyara hannun rigar sa.


Hango Abdulhakeem yayi da wasu dogarai hannun su riƙe da ƙatuwar ghana must go suna ƙarasowa wurin sa.



Murmushi Abdulhakeem yayi yace "ZEEYAD my boy kalli wannan kaya ne na kawo maka, ina ta gararin neman ka tunɗazu cikin PALACE ɗinnan sai dai ban sameka ba, banason ka kalle ni a matsayin macuci wanda ya cinƴe kuɗin da mahaifin ka ya bada a baka, hakan yasa na tako zuwa wannan arear da kaina dan kawo maka, sai dai gashi har jikina ya fara ɗaukar ƙaiƙayi i wonder yadda kake rayuwa anan wurin." ya faɗa cikin ɗan dariya yana ƙarewa wurin kallo.



ZEEYAD bai kula shi ba sai kallon sa kawai da yakeyi hakan ya sanƴa shi faɗin "Ohh kada kace na cika surutu, gashi nan ka buɗe kaga abin dake ciki" ya faɗa yana nunawa ZEEYAD bagco ɗin.



Kallon sa yayi sannan kuma ya duƙa tare da kai hannu ya buɗe ta, kaya ne birjik a ciki sai dai daga ganin su an sanƴa su.



Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa nan ya sakar masa murmushi yace "Sunyi kyau koh?."



"What Nonsense, already kayan nan an rigada an sanƴa su."



Tamƙe fuska yayi yace "Mai kake nufi, kai kasan nawa ne kuɗin kayayyakin nan kuwa, kai koh godewa Allah ba zakayi ba da ya kawo maka wannan ɗin?."



"I don't want it, kuɗi mai Martaba yace ka bani ba wadannan tsofaffin kayan da ƴaƴan ka suka sanƴa ba."



Dariya yayi yace "Naji daɗi da ka fahimci cewa ragowar kayan da ƴaƴa na masu daraja suka sanƴa ne, yakamata ka amshe su hannu bibbiyu ba wai ka raina ba dan kuwa na tabbata koh nan da shekaru ɗari ne ba zaka iya sanƴa irin su ba."



Murmushi ZEEYAD yayi yace "Really?, kana nufin haka zan ƙarashe rayuwa ta?."



"Babu tantama kuwa" ya faɗa cikin ɗan dariya.



"OK then, we will see to that, but i just need my money now."



"No, ba zan baka kuɗin ba sabida.....na cinƴeee" ya faɗa saitin kunnen sa kafin kuma ya fashe da dariya.



"Ka cinƴe?" ya faɗa yana kallon sa.


"Kwarai kuwa, koh akwai abinda zakayi ne ZEEYAD?."



Kai ya girgiza masa yace "Not now though" kafin kuma yayi murmushi haɗi da ɗaga kafaɗu yace "Alright then shikenan tunda ka cinƴe, i will keep managing with the little i have."



"Come on ZEEYAD, tayaya zakayi manage da wadannan tsofaffin kayayyakin har zuwa wani shekara kana tunanin kallon mutum ma kaɗai ba zai yaga su ba tun ba'a ta6a su ba, ka ɗauki wadannan kaje kayi ta amfani dasu sabida sun zama tsofaffin yayi baikamata a gansu a jikin yara na jinin sarauta ba, but kaga kai nasan zasuyi matuƙar kar6ar ka suyi maka kyau sabida sam baka ta6a sanƴa irin su ba, don't be shy Okay, ba wanda zaiyi gulmar ka zan tabbatar da na rufe bakin kowa daga yin maganar ka, koh ya kace?" ya faɗa yana dafa kafaɗar ZEEYAD ɗin.



Jinjina masa kai yayi kawai yace "Okay, but wait please" ya faɗa yana juyawa zuwa cikin ɗakin sa.



Ashana ya ɗauko ya fito dashi ya kalli Abdulhakeem yace "Uncle Abdulhakeem you want me to wear these don't you?."



"Ofcourse ZEEYAD" ya faɗa cikin murmushi yana kallon sa.



"Sun zama mallaki na yanzu, right?."



"Ofcourse, miye kuma kake sake tambaya, nacemaka sun zama naka yan..." bai ƙarasar da maganar ba ganin ZEEYAD ya kyarta ashana tare da jefawa kan kayan, take expression na fuskar sa ta sauya.



"What the hell..." ya faɗa.


Katse sa ZEEYAD yayi da faɗin "Uncle Abdulhakeem, baikamata kayi fushi ba sabida ba kayan ƴaƴanka na ƙona ba, koh ka manta ne kai kace sun zama mallaki na yanzu, so i guess kamar yadda babu ruwan kowa da rayuwa ta baikamata kaji haushi ba dan na ƙona kayan da yake mallaki na ne, sabida bana buƙatar su."



Sosai Abdulhakeem yaji mugun haushi, nuna ZEEYAD yayi da yatsa yace "How dare you, ni zaka watsawa ƙasa a ido?, sai na tabbatar da kayi nadamar abinda ka aikata yanzun nan" yana faɗin haka ya juya fuu da ƙatuwar alkyabar dake jikin sa kamar zai tashi sama.



"Lallai yaro ka samu wuri" cewar ɗaya daga cikin dogaren sa kafin suyi saurin mara masa baya.



Da kallo ZEEYAD ya bisu har suka 6acewa ganin sa,kafin yaja Bagco ɗin kayan zuwa chan gefe yana ƙara mata wuta........



*****************


........"What!, bai sanƴa kayan ba?" ta faɗa cikin tashin hankali tana miƙewa tsaye daga kan kujerar ta.



"Ya kina magana kamar wacce bataji abinda na faɗa ba, koh so kike na ɗau lasifika nayi ta yawo a gari ina maimaitawa kafin kiji?."



Kallon Abdulhakeem tayi tace "Ya isheka haka nan,ka tsaya a matsayin ka na ƙanin ga mai Martaba, kada ka wuce iyakar ka ka nemi gayamin magana" ta faɗa cikin fushi.



Kallo ya ƙare mata tsaf sama da ƙasa yace "Mai kike nufi da na tsaya a matsayi na, kina nufin kice min shashasha kika ɗauke ni tsawon lokacin nan bansaniba koh miye?, kece yakamata ki tsaya a matsayin ki Hafeezah sannan kuma ki kiyayi dukkanin wani abu da zai 6ata min rai dan kuwa babu wani baƙin sirri naki da bansaniba."



Kallon sa tayi da idanun ta da kamar zasu faɗo daga ramin su kafin kuma ta haɗiyi ƴawu tana daidaita nutsuwar ta tace "Shikenan naji, amma ka sani ba zan ta6a samun kwanciyar hankali ba muddin banga bayan yaron nan ba."


"Ki bar komai hannu na Sarauniya Hafeezah, ni nan zanji dashi."...................





_Yau insha Allahu akwai shara, dan gaskiya comments ɗinku yana yin kaɗan, wasu sun bani shawarar maida shi na kuɗi dan haka indai banga comments ɗinda ya gamshe ni ba toh hakan zan aiwatar, kokuma na daina yi muku posting ɗinsa kullum, idan kuma littafin ne baiyi muku daɗi ba sai ku faɗamin na daina 6ata lokaci na wurin son faranta muku, tunda ku ba zaku iya faranta min wurin yimin zazzafan comment ba😑, dan Allah ku gyara comment ɗinku fah shine kwarin guiwar mu wlh, Masu turo sticker da Tnx ku bar abin ku dan Allah na yafe😑_





*Share Fisabillah*






*MHIZZ JIDDHERR..........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*006...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





..........Sosai dare ya ratsa yayin da kowanne ɗan Adam a wannan lokaci kafaɗun sa ke ƙasa yana bacci lokacin ne kuma ZEEYAD ya kasa koh da runtsawa ne sakamakon wani irin azababben zazza6i da ya rufa masa.



Sosai jikin sa ke karkarwa ji yake kamar ana yanka naman jikin sa koh ana hura masa wuta haka nan yakejin zafi na taso masa a jiki, yayin da kuma yake ta karkarwar sanƴi.



Fitowa yayi waje ya zauna gindin bishiya dan ya sha iska dan kuwa koh da kwan wuta babu a ɗakin sa balle kuma fanka.



Zaman sa gindin bishiyar nan babu abinda ya ƙara masa sai sanƴin da yakeji hakan ya sanƴa shi sake komawa ɗakin sa, sosai jikin sa da hannayen sa ke rawa haka nan ya zazzage kayayyakin dake cikin jakar sa baki ɗaya ya ciro tare da lullu6e jikin sa dashi kasancewar bashida bargon lullu6a.



Lullu6ar da yayi babu abinda ya rage masa daga jin sanƴi da karkarwar da jikin sa keyi.



Sosai ya sha baƙar wahala cikin wannan dare dan kuwa koh runtsawa baiyi ba har wayewar gari bai iya samu ya dawo hayyacin sa ba.



Sosai gari ya waye sai dai koh taka ƙafar sa bai iya ya fito waje ba, hayaniyan da yaji a bakin ƙofar ɗakin sa ne yasa shi ɗago da gajiyayyun idanun sa yana kallon bakin ƙofar shigowa.



Da mugun bugu aka 6allo ƙofar ɗakin inda yayi saurin kare idanun sa sakamakon hasken rana da ya dallo masa idanu.



Bai ankara ba yaji anyi masa wata iriyar muguwar fuzga an miƙar dashi tsaye, inda kuma aka wullo sa waje.



Bai ankara ba kuma aka hau bugun sa ta koh ina, sosai sukayi masa lilis kafin ya basu umarnin dakatawa.



ZEEYAD dake kwance duk yabi ya galabaita dakyar yake iya motsa ƴar yatsar sa ne ya ɗago dan ganin koh wanene.



Durƙushewa ɗan Saurayin yayi wanda ba zai wuce sa'ar sa ba yayi yace "Hello Bro, long time no see."



"You.." ya faɗa cikin maida numfashi.



Murmushi ɗan Saurayin nan yayi kafin kuma ya damƙo gashin ZEEYAD ɗin yana zaunar dashi tare da kallon saitin idanun sa yace "Kai har ka isa, who the fuck do you think you are da har mahaifina zaiyi maka kyautar kaya na ka ƙona right infront of him?."



Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka masa ba inda kuma yake ta fitar da numfashin wahala yana runtse idanun sa cike da azabar da yakeji a jikin sa.



"Sooraj let go of him" ta faɗa tana zuwa ta ture shi daga riƙon da yayiwa ZEEYAD ɗin, kafin kuma ta ɗago da ZEEYAD ɗin tana shafa fuskar sa cikin kuka.



Daddagewa yayi tare da kwashe ta da wani irin azababben marin da sai da ya sanƴa ta ganin wasu irin taurari masu tsananin haske yace "Dan Ubanki mai ya kawo ki nan?."



Riƙe da ƙunci cikin kuka tace "Ai dama nasan zaka zo nan wurin tunda naji abinda Abhi ya faɗa maka akan ZEEYAD nasan sai ka biyo sa kayi masa illa, maiyasa wai ku bakuda imani ne?."



Kallo ya ƙare mata sama da ƙasa kafin ya ɗago ta tsaye yace "Ni kike faɗawa haka akan wannan bolan?, how the hell ma aka barki kika fito bayan ɗakin ki a rufe?."



"Eh ɗin na faɗamaka ɗin, mugu kawai azzalumi kuma wallahi sai kunyi nadamar abinda kukeyi masa dukkan ku."



Wani marin ya sake ɗebe ta dashi wanda ya sanƴa ta zubewa a wurin, nan ya kalli dogaran da yake tafe dasu yace "Ku sake yi masa dukan da yafi wanda kukayi masa yanzu, dukan da zai sanƴa sa guduwa da ƙafafuwan sa da zaran yaga dosowar wani daga cikin Family ɗin mu."



Ai kuwa kamar jira suke nan suka ha bugun sa da ƙafafuwan su, ita kuwa yarinƴar nan babu abinda takeyi sai kuka da ihun su sake shi inda yayan nata kuma ya riƙe ta gam yanajin wani irin tululun baƙin ciki ya tokare masa zuci, babu abinda yake fitarwa sai huci.



Sai da suka tabbatar da ya daina motsawa kafin su kyale shi, tusa ta gaba yayi yana janta suka bar wurin.



Barin su wurin keda wuya bayi matan dake harkokin su a wurin suka zo suka zagaye shi kowa na magana ƙasa-ƙasa suna tofa albarkacin bakin su "Ya mutu fah", "baya motsi", "Uhm nikam kunga tafiya ta", "Allah ya kyauta,lallai akwai hisabi ranar ƙiyama" Shine abinda wasu daga cikin su ke ta faɗa kafin duk su fara watsewa ɗaɗɗaya kowace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login