Showing 6001 words to 9000 words out of 236327 words

Chapter 3 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45376

ya Kalli Sadeeq yace "Ku saki abokin nasa, shi kuma da ya aikata laifin ku tabbatar da kun yi masa hukunci mai tsanani ta hanƴar horar dashi."



Kallon sarkin Dakaru yayi yace "Wannan aikin naka ne Najeeb, ka tabbatar ya fuskanci hukunci dai dai da abinda ya aikata."



Kai wanda aka kira da Najeeb ya sunkuyar alamun amsa maganar sarkin, kafin kuma ya bada Umarnin fitar da ZEEYAD ɗin.



Bayan Fadar ta watse ne ya saura daga mai Martaba sai kuma Uwargidar sa *Sarauniya Nazeerah*.



Cike da tsantsar makircin da tayi course akai ta kalle shi tare da faɗin "Allah yaja ran Sarki, amma nace kana ganin wannan hukunci da kakeyi wa ZEEYAD baya yin tsanani kuwa, ka tuna fah ɗanka ne kuma...."



"Ya ishe ki haka Nazeerah" ya faɗa cikin ɗaga mata hannu kafin kuma yace "Ina buƙatar ke6ancewa ni kaɗai."



Sum-sum ta tashi daga kishingiɗen da take ta fice, nan dakarun ta suka take mata baya zuwa Side ɗinta.



Ajiyar zuciya sarki ya sauƙe kafin kuma ya tashi daga kan Throne ɗinsa ya fara yin safa da marwa a cikin fadar.



Sosai da sosai har chan cikin ƙololuwar zuciyar sa yake Ƙaunar ZEEYAD wanda ya samo asali ne daga ƙaunar da yakeyi wa Mahaifiyar sa.



Lokacin da Mahaifiyar ZEEYAD keda rai babu abinda yafi so da Ƙauna bayan su,sai dai yanzu ganin ZEEYAD ɗin da yake ba ƙaramin baƙan ta masa rai da sanƴa shi fushin da baiyi niyya ba yake.



Tsanar da yakeyi wa ZEEYAD ɗin koh maƙiyin sa baya yi masa shi wanda har cikin zuciyar sa ba haka bane ba,sai dai kawai ba zai iya controlling anger ɗinsa bane aduk sadda ya ɗaura idanu akansa.



Yayin da ya kasance baya kusa dashi kuma babu abinda yake muraɗi da kwaɗayin gani kamar sa.



Ajiyar zuciya ya sauƙe inda kuma wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa akan ƙunci,kai ya jinjina kafin kuma ya bar cikin fadar zuwa ɗakin sa.......




**********



.........."Stop being nice to me General, kayi abinda aka umarce ka a kaina, coz that won't change things."



Kallon sa sarkin Dakaru yayi kafin ya furzar da iska yace "ZEEYAD, kaci abincin nan tukun, koh da zan hukunta ka ɗin ya zamto da ƙarfin ka."



Kallon tray ɗin abincin da akayi serving ɗinsa yayi kamar wani ɗan gidan yari, kafin kuma ya ture yace "Am not eating it, just let me be" ya faɗa cikin rawar murya.



Zama sarkin dakaru yayi a gaban shi yace "Look ZEEYAD, being always bored won't make things right, ka rigada ka saba da wannan rayuwar tun kana ɗan shekara goma, dan haka it's now high time da yakamata kayi accepting ƙaddarar ka, babu wani abu da zakayi dan canza ra'ayin mahaifin ka akanka, ba cewa nake ka cire rai da samun sauƙin rayuwa ba, amma yakamata ka kasance cikin farin ciki kullum koh da kuwa kana cikin bad mood ne, ganin ka kullum cikin ƙunci shike baiwa maƙiyan ka damar cigaba da munana maka dan kuwa shi maƙiyi babu abinda yafi tsana kamar ganin farin cikin wanda ya tsana ɗin, shawara ce ZEEYAD kada ka ta6a bari maƙiyan ka su gano weak point naka dan kuwa dashi ne zasu cigaba da muzanta maka kullum, try and change your way of life ZEEYAD and stop being bored always" ya faɗa yana buga kafaɗun sa kafin kuma ya tashi ya fice ba tare da ya jira cewar sa ba.



Da kallo ZEEYAD ɗin ya bishi kafin ya maida duban sa kan abincin dake gaban sa, tabbas yana jin ƴunwa sai dai ba zai ci abincin nan ba, dan kuwa ba yarda yayi da sarkin dakarun ba shima.



Bayan kamar mintina sha-biyar Sarkin Dakaru ya dawo ɗakin, murmushi yayi ganin koh ta6a abincin baiyi ba, lallai ba ƙaramin jinjinawa taurin rai irin na ZEEYAD yake ba.



"So, lokacin hukunta ka yayi ZEEYAD."



Ba tare da yace komai ba ya miƙe ,chain aka ɗaura masa a hannaye kafin a tusa ƙeyar sa zuwa waje.



Fili ne ƙato aka kawo shi, kafin kuma a kaisa kan wani abu kamar mumbari aka ɗaure masa hannaye a sama.



Mutane da dama sun halarci wannan wuri dan ganin wane irin hukunci za'a yiwa Yarima ZEEYAD da yayi faɗa da babban dakare kamar Mulah,a gaban mahaifin sa sarki.



Wata Ƙatuwar dorina mai baki uku aka ɗauko,wacce take da tsayi da kauri.



Kafin kuma aje ta bayan sa a shiga shauɗa masa ita bisa ga umarnin mahaifin sa.



Lafiyayyun bulala ɗaɗɗaya har zuwa Hamsin akayi masa, amma koh gezau baiyi ba balle idanun sa su tara hawaye, zuciyar sa ce kaɗai ke mugun yi masa tafarfasa, dan kuwa yayi alƙawarin ba zai sake yin kuka ba a duk hukuncin da za'a yi masa,dan idan da sabo ya saba.



Sunce sa akayi nan ya faɗi a wurin hannayen sa dafe da ƙasa, da idanun sa da sukayi mugun jaa ya ɗago ya kalli mahaifin nasa da shima shi yake kallo.



Saurin kauda kai yayi daga kallon da ZEEYAD ɗin keyi masa kafin kuma ya tashi dogaran sa suna mai gyara masa hanƴa tare da yi masa kirare-kirare ya bar wurin............




*TWO DAYS AFTER*




Zaune yake yana gasa bayan nasa da yaji shatin bulalar da akayi masa, kasancewar bashida wani mai taimaka masa.



Bayan ya gama ne yayi wanka sannan ya shirya cikin ƴar tsofaffiyar kayan sa, kafin ya kama hanƴar zuwa cikin gida, kasancewar ɗakin sa ma a chan bayan gidan yake wurin arean Bayi Mata.



A hanƴar sa ta zuwa ne ya haɗu da wata Dattijuwar mata, da kallo ta bisa har ya ɗan wuce kafin tace "Hmm,Yaro kana ganin Rayuwa kai da Masarautar Ubanka."



Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba, ita ɗinma tsayuwa tayi ganin koh zai kula ta, juyowa yayi tare da sake mata murmushin da ya sanƴa ta daskare wa a wurin tana kallon sa har ya 6acewa ganin ta.



Cike da mugun sauri ta nufi 6angaren *Sarauniya Hafeezah* dan shaida mata abinda idanuwan ta suka gani.



Zubewa tayi a gaban ta tana kwasar gaisuwa.


Wani irin Kallo ta watsa mata cike da ƙasƙanci kafin tace "Lafiyar ki kika faɗomin ɗaki haka kamar wacce aka jefo, bayan kinsan yanzu lokacin hutu na ne?" cewar Sarauniya Hafeezah.



Cikin 6arin jiki da mugun gulmar dake cinta tace "Allah ya taimake ki Sarauniya ta,mata mafi soyuwa ga sarki *Abbas Ibn Qazeem*, nazo miki ne da wani babban labari yake Sarauniya ta.



Murmushi tayi tace "Shiyasa nake Ƙaunar ki Jakadiya Nadiya, domin kuwa a kullum kina kawomin labarin dake sanƴa ni cikin nishaɗi na tsawon kwanaki, ina jinki wane labari kuma kika zo min dashi yau?" ta ƙarashe tana 6antarar Apple ɗin dake hannun ta.



"Ai Sarauniya ta yau nazo miki da abun ban mamaki, yau idanu na sun ganemin abinda zai hana ni sukuni ya kuma hanaki kema, a yau dai da wadannan idanuwan nawa naga yaron nan Yarima ZEEYAD yana murmushi."



A matuƙar razane ta ɗago tana kallon Jakadiya kafin ta ɗau hannu ta wanke ta da wani irin azababben mari tace "Tashi ki bani wuri matsiyaciyar banza da wofi wacce bata gaji arziki ba, ni zaki zo wa da wannan mummunar labarin da koh a mafarki wani yazo min dashi toh tabbas sai naga bayan sa?, Useless old hag, wannan mummunar labari ce, how dare you ruined my happy mood?."



"Allah ya huci zuciyar ki, sarauniya ta, ba dan na ɓata miki rai na Kawo miki labarin nan ba, ina ganin Kamar zaki ɗau mataki akai ne tunda babu abinda kika fi tsana kamar farin cikin shi, Allah ya huci zuciyar ki yake Sarauniya ta" tana faɗin haka taja jikin ta ta baro wurin riƙe da ƙunci.




Nazarin maganar Jakadiya ta shiga yi kafin Kuma taja dogon tsaki tare da dakawa bayin nata tsawa take suka watse daga wurin.



Tashi tsaye tayi tana fidda wani irin huci mai zafi dake tasowa daga chan ƙasar zuciyar ta dake yi mata ƙuna tace "Baikamata ka kasance cikin farin ciki ba ZEEYAD, yakamata ka ƙare rayuwar ka ne cikin ƙunci,wahala dama kuma baƙin ciki, kamar yadda naga bayan Mahaifiyar ka kaima haka nakeson ganin bayan ka, sai dai taurin rai irin naka yasa har yanzu na kasa aiwatar da ƙudiri na akanka, kasancewa cikin farin ciki sam ba naka bane ZEEYAD ya zama dole nayi gaggawar yiwa wannan lamari tufkar hanci, tun kafin sirrin da nake 6oyewa shekaru da shekaru ya tone" ta faɗa tana tattare doguwar gown ɗin dake jikin ta tayi hanƴar ficewa da sauri..........



*************




............Tundaga inda take ta hango ZEEYAD ɗin tsaye a bakin ƙofar shiga fada, wanda da alama dakaru ne suka hana sa shiga, hakan ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba dan kuwa burin ta shine a kullum ya kasance cikin ƙunci da wahala.



Ƙarasowa wurin tayi nan kuwa dakarun nan suka shiga kwasar gaisuwa kafin su buɗa mata, kallon ZEEYAD da koh da wanzuwar ta baisan dashi bane tayi kafin ta gyara tsayuwar ta tana juyowa gareshi tare da harɗe hannaye a ƙirji tace "ZEEYAD my Boy, shin ba zaka durƙusa a gaba na ka roƙe ni na sanƴa wadannan ƙasƙantattun bayin barin ka ka shiga izuwa wurin mahaifin ka ba?, au koh dayake ashe ma fah Mahaifin naka ya tsani ganin ka toh akan mai kuma kake son nuna masa fuskar ka?."



Hannu tasa ta ɗago ha6ar sa tace "Wannan kyakkyawar fuskar taka kamata yayi ace duk sadda akayi arba da ita mutum ya kasance cikin farin ciki ba baƙin ciki ba, amma abin mamaki kowa ya tsane ka a wannan nahiyar koh maiyasa hakan oho" ta faɗa tana ƙiƙƙifta idanu cikin makirci.



"ZEEYAD, a matsayi na ta mata ta biyu ga mai martaba Sarki, Mahaifiya ga Babban Yarima kuma ɗa mafi soyuwa ga sarki wato *YAZEED* ina mai umartar ka da ka durƙusa a gaba na yanzun nan kayimin gaisuwar safiya koh hakan zai sanƴa naji tausayin ka a matsayin ka na ƙasƙantaccen ɗan da ya rasa Mahaifiyar sa, koh hakan zai faranta min rai na sanƴa a buɗa maka wannan ƙofar ka shiga ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba" ta ƙarashe cikin ƙuntume fuska dake nuna tsantsar tsanar sa tana kallon sa.



ZEEYAD sam bai damu da maganganun da take faɗa masa ba dan kuwa idan da sabo toh yaci ace ya saba da baƙaƙen maganganu irin na *Sarauniya Hafeezah da Nazeerah*



Ganin yaƙi kulata kuma koh kallon gefen ta baiyi bane yasa ta jin wani irin ƙululun abu ya tokare mata maƙoshi, da kyar ta haɗiye ƴawu tsabar baƙin ciki tace "Tsayawa magana da ƙasƙantaccen yaro kamar kai ba ƙaramin zubar min da mutunci da ƙima zaiyi ba, ina ƙoƙarin fitar da kai daga ƙunci amma kuma kai kana sake tsoma kanka a ciki, hakan ma yayi dai-dai dan kuwa zama wuri ɗaya da irin ka babu abinda zai haifarwa mutum sai cuta sabida ƙazantar dake tattare da kai" tana faɗin haka ta wuce fuuu kamar wacce iska ke turawa ta faɗa cikin fadar nan kuwa aka maida ƙofar aka rufe.



Juyawa yayi da niyyar komawa inda ya fito nan idanun sa suka faɗa cikin nata tana yi masa wani irin kallo.


"Subhanallah" ya faɗa a zuciyar sa yana kauda kai, dan kuwa idan akwai wacce yake mugun tsoron haɗuwa da ita bata wuce *Sarauniya Naseeba* ba, itace matar sarki ta uku sannan kuma tun mutuwar Mahaifiyar sa sarki bai ƙaro wani auren ba.



Ƙarasowa tayi wurin kuyangin ta na taka mata baya kafin tace "Ku buɗe masa ya shiga."



Juyowa yayi ya kalle ta kafin kuma ya sake kauda kai,dan kuwa kwata-kwata baya ƙaunar haɗa idanu da ita.



"ZEEYAD my dear, come on zo mu shiga daga ciki" ta faɗa tana sakin masa wani irin tsadadden murmushin da ita kaɗai tasan ma'anar sa.


"No thanks" ya faɗa yana ƙoƙarin wuce ta.


Riƙo hannun sa da tayi ne yasa shi faɗin "Alright" cikin rawar murya kafin kuma ya wuce ya shiga, dan kuwa sam baya ƙaunar abinda zai haɗa shi da ita.



Da kallo ta bisa tana mai kintsa abubuwa dayawa a cikin zuciyar ta game dashi, kafin ta take masa baya suna shigewa da ita da kuyangun nata..........



***************



..........Dining ne haɗaɗɗe dogo mai faɗi wanda a ƙalla zai ɗau mutane Talatin.



Duk zaune suke inda kowacce idanun ta da hankalin ta na kan ZEEYAD ɗin, sai dai kowacce da nata ƙudirin da yasa take kallon sa.



Sarauniya Naseeba ce a saitin sa, shiyasa duk ya kasa samun sukuni, babu damar ya ɗago da kansa zai tsinci tana kallon sa, hakan ba ƙaramin takura sa yake ba tunda ya fahimci manufar ta akansa, yasa yake kiyaye duk wata hanƴa da zai sanƴa sa haɗuwa da ita.



Sarauniya Hafeezah da sam bata fahimci zaman ZEEYAD ɗin a cikin su bane tace "What's this pathetic shit of trash doing here?."



Kallon ta Sarauniya Naseeba da taji haushin maganar tata tayi tace "Enough of this, ya isheki haka Hafeezah, maiyasa zakiji haushin zaman sa a nan wurin koh kin manta shima ɗa ne ga mai Martaba?."



Kallon ta Hafeezah tayi tace "Kada ki nemi ki gayamin maganar banza akan wannan yaron Naseeba, wai ma tukun dakata maiyasa akoda yaushe kike ƙoƙarin karesa a duk sadda wani daga cikin mu ya nemi gaya masa magana, baikamata ki dinga karesa ba sabida that is what he actually deserves."



Ido Naseeba ta haɗa da Sarauniya Nazeerah dake jinsu tana sakin murmushin gefen baki wacce da alamu tasan komai, kafin kuma tayi saurin faɗin "Ba wai ina ƙoƙarin karesa bane ba, amma yakamata ki gane cewa ZEEYAD dai-dai yake da kowane ɗa a cikin gidan nan."



A zafafe ta miƙe tsaye tana nuna ta da yatsa tace "Kul! Kada ki kuskura ki sake haɗa ƴaƴa na da wannan abin, idan ba haka ba toh tabbas zaki fuskanci fushi na, koh dayake dama juya kamar ki mai ta sani gameda ƴaƴa shiyasa kike haɗa ƴaƴan da na haifa dashi."


Fitowar mai Martaba ya sanƴa Sarauniya Naseeba yin shiru ba tare da ta furta abinda tayi niyya ba.............





*Share Fisabillah👏🏽*




*MHIZZ JIDDHERR.........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*005...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





..............Tsaye yake akan ƙatuwar bridge inda ruwa ke ta gudana yana wucewa da gudu ta ƙarƙashin sa, he feels so very empty, ji yake komai na rayuwa ya fitan masa a kai, he wishes ina ma ba'a halicce shi ba, rayuwa tayi masa mugun zafi, babu wanda yake sonsa except family ɗin mahaifiyar sa, sai dai su ma mai Martaba yayi musu iyaka dashi, bashida kowa bashida komai sai Allah.



Ajiyar zuciya ya sauƙe yana lumshe idanun sa sakamakon sassanƴar iska mai shiga jiki dake busawa a wurin yana ratsa cikin jikin sa.



Idanun sa ya buɗe tare da sauƙe su kan wani Ƙaton jirgin ruwa dake tafiya akan ruwan, idanu ya zubawa jirgin har yayi nisa, kafin kuma ya furzar da iska a bakin sa.



Necklace ɗin wuyar sa ya ciro daga cikin rigar sa yana kallo kafin kuma ya ɗan saki murmushin da ta tsaya masa saman le6e yana maida ta.



Juyawa yayi ya fara tafiya a hankali dan komawa inda ya fito, ya ɗanyi tafiya mai nisan gaske kafin ya shigo cikin Masarautar tasu.



Tsadaddun manƴan Baƙaƙen Motoci ne da aƙalla zasu kai ashirin ya gani jibge an fito dasu sun sha wanki sai ɗaukar idanu suke wanda da alama fita za'a yi dasu.



Wani ɗan dakali ya samu daga ɗan nesa da farfajiyar wurin parking space ɗin ya zauna.



"Kai mai kakeyi zaune anan?" ya jiyo an faɗi hakan ta bayan sa.



Juyawa yayi tare da kallon mutumin da yayi maganar, nan ya sake cewa "Au ashe kaine, ai na ɗauka koh almajiran da suka saba shigowa ne suka shigo dah sai nace musu yau babu sadaka, miye ka wani ƙure ni da idanu koh dama bakayi kama da almajiran bane iye?" ya faɗa kamar wanda zai buge shi.



Kauda kai ZEEYAD yayi daga kallon sa, dan kuwa idan yace zai biye masa tsaf zasuyi faɗa anan wurin, bakomai ya sanƴa shi zama anan ba sai jiran fitowar mai Martaba.



Ganin ZEEYAD ɗin bai tanka masa bane yasa shi jan ƙatuwar jikin sa yayi gaba yana surutai.



"You will all reap what you sow oneday.....i promise" ya faɗa a hankali yana bin mutumin da kallo har ya 6acewa ganin sa.



Ya ɗan jima zaune a wurin kafin Mai Martaba ɗin ya fito tare da dakarun sa dama kuma wasu manƴan mutane wanda daga gani suma jinin sarautar ne.



Tashi yayi daga zaunen da yake ba tare da wata fargaba ba ya doshi wurin su.



Ƙofa aka buɗewa mai Martaba yana shirin shiga ne ya tsinkayo muryar da yafi tsana ya kira shi "Your Highness" ya faɗa.



Runtse idanu mai Martaba yayi na wasu ƴan seconds ba tare da ya juyo ya kallesa ba yace "What do you want?."



"I need to talk to you."



"You can't talk to him right now, he have an important meeting to attend" cewar ɗaya daga cikin mutanen dake tare da mai Martaba ɗin.



"It's urgent..." bai ƙarasar ba wannan mutumin ya sake cewa "Get him out of here."



Zuwa sukayi zasu kama shi nan mai Martaba yace "Let him talk" nan duk suka ja baya dan cika umarnin mai Martaba ɗin.



"What do you want?" Cewar Mai Martaba.



"I want some Money to buy new clothes."



Duk idanu ƴan wurin suka zuba masa jin abinda ya tambaya, sai a sannan mai Martaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login