Showing 189001 words to 192000 words out of 236327 words
kuma yace "Mai kike faɗa ne haka?, you should know your limits."
"Yakamata ka fahimci cewa ina ƙoƙarin kare ƴaƴan ka ne daga tuggun wannan yarinƴar, ni na tabbata ba haka kurum ta bar ɗanka ba, babu ta yadda za'ayi ZEEYAD yaso kamar ta, na tabbata asirce shi tayi dan ta samu damar biyan dukkanin buƙatun ta..."
"Enough of this, i can't take this anymore" faɗin ZEEYAD da ransa ya soma 6aci sosai.
"Hold it there Young boy, ba da kai nake ba so don't you dare try to interrupt me, am doing this for my children's Peace, ba zan ta6a bari wannan abar da ka ɗauko a matsayin mata ta nemi lalata mana MASARAUTA akanka ba, ƴar talakawa irin ta, she is not even from a royal family so then how on earth zaka amince da auren sa da yarinƴar da ba ma ƴar ƙasar sa bane, itace zaku ɗauko a matsayin wacce zata zamto future Queen na wannan MASARAUTAR, i can't believe you guys, yakamata ka sake tunanin ranka ya daɗe this girl here doesn't deserve to be the Queen of this kingdom."
"Ya isheki haka Hafeezah."
"Let me talk your Highness, let me said my mind, kodai kai ɗinma ta asirce ka ne, kada ka bari son da kake yiwa ɗanka ya rufe maka ido ka kasa ganin gaskiya, nasan ni ba wacce zaka yarda da ita bane sabida baka ɗauke ni da muhimmanci ba, but atleast yakamata kayi nazarin kalamai na, yarinƴar nan sam ba haka nan ta bar wannan yaron ba, she has something bad in her mind trust me."
"Enough of this Hafeezah, i won't let you said something bad about DEENAH again" faɗin Grandma itama cikin 6acin rai.
"Am not saying anything bad about your in-law face gaskiyar abinda na sani kuma na gani, this girl here is using a spell against all of you shiyasa ba zaku ta6a ganin laifin ta ba, kuma kuke ƙoƙarin kare ta, sannan duk mun sani amfani da sihiri mummunan laifi ce a dokar MASARAUTA..."
Sosai ZEEYAD yake neman tanka mata sai dai ganin YAZEED ya sanƴa shi jin ba zai iya tozarta mahaifiyar sa a gaban sa ba, komin ƙin ta da yake yi dole ne yaji babu daɗi game da abinda zai iya yi mata a yanzun.
"Hafeezah stop accusing an innocent girl, she just arrived to the PALACE yesterday, how on earth kuma kike zargin ta da aikata wannan mummunar laifin?."
"Ba zargin ta nake ba, bata kai matsayin da zan zarge ta kokuma na ɗaura mata sharri ba."
"Then wacce shaida kike dashi kan batun da kike faɗin ta aikata?."
Shiru tayi wani irin farin ciki na lullu6e mata zuci na ganin plan ɗinta is about to be achieved, nan tace "Ofcourse ina da shaidu bama shaida ba."
Duk tsaya kallon ta sukayi cike da mamaki kafin ta juyo ga DEENAH da hawaye ya gama wanke mata fuska tace "What happened young lady, kina tsoron tonuwar asirin ki ne?, muddin kinsan kina da gaskiya baikamata kike zubda kwalla haka nan ba, ai duk wani mai gaskiya bayajin tsoron tonuwar abinda bai aikata ba."
Janƴo DEENAH ZEEYAD yayi jikin sa yana wullawa Hafeezah mugun kallo, murmushin gefen baki Hafeezah ta saki kafin ta tsinkayo muryar mai Martaba na faɗin "Hafeezah, kinsan da cewa duk wanda aka kama da aikata aikin asiri dumu-dumu hukuncin sa ba mai sauƙi bane, inason ki gabatar min da shaidun da kike dashi yanzun nan anan."
Kallon mai Martaba ZEEYAD yayi cike da mamaki kafin yace "Your Highness what are you saying?, matata ba zata ta6a aikata abinda ake zargin ta dashi ba, she is innocent and i trust her."
"Yardar da ka bata ne ya sanƴa ta samun damar aikata dukkanin wani abu da taga dama a gareka."
"We can't prove how innocent your wife is until an bincika an gano hakan kamar yadda doka ta tanada."
"What are you saying, wannan tozarci ne babu wanda ya isa yazo min kusa da mata da sunan bincika wani abu a jikin ta."
"Ba a jikin ta abin yake ba, but a ɗakin da aka sauƙe ta" cewar Hafeezah.
"I know you don't like me, but dukkanin wani abu da zaki aikata ya tsaya akaina, do not include my wife please" cewar ZEEYAD yana kallon Hafeezah dake kallon sa.
"Hafeezah kiji tsoron Allah, yaushe ne har kikaje ɗakin da aka sauƙe DEENAH kika gano tana aikata wani mummunan abin da sunan asiri?" faɗin Grandma.
Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Ba nice naje koh na gano hakan ba, bayin dake aiki a 6angaren ki ne suka gano hakan."
Wani irin mugun kallo Grandma ta watsa mata kafin tace "Kada ki nemi ki kawo mana rainin wayo anan Hafeezah, DEENAH ba zata ta6a aikata abinda kike zargin ta dashi ba..."
"Seriously, i can't believe har kin yarda da ita haka tun kafin ki zauna da ita ki san abinda zata iya aikatawa dama kuma wanda ba zata aikata ba, the girl is controlling you guys, by casting a spell on you."
"Enough, ina shaidun da kika ce kina dasu, ina buƙatar ganin su yanzun nan anan wurin."
"Kwarai kuwa nasan da cewa za'a neme su hakan yasa na umurce su da su kasance kusa" kafin kuma ta hau waige-waige tare da faɗin "Kuna ina?."
Wasu mata ne guda uku suka fito daga cikin crowd ɗin kansu rissine a ƙasa suka zube gaban sarki.
"Gasu nan, sune shaidun da nake dasu, sannan sune suka kawomin labarin."
Kallon su Grandma tayi kafin tace "Layuza, Rakiba, mai kukeyi anan?..."
"Sun zo bada shaida ne akan abinda idanun su suka gane musu" cewar Hafeezah cikin katse Grandma tana kallon ta.
Mai Martaba ne yace "Hafeezah, muddin dukkanin abinda kika faɗa ya zamto ba gaskiya bane, toh ki sani hukuncin ki sai ya cuna wanda akewa wadanda aka kama da aikin asiri, idan kuwa ya zamto abinda kika faɗa gaskiya ne toh tabbas za'a hukunta mai laifi dai-dai da abinda dokar MASARAUTA ta tanadar."
"You can't do this, and i won't let you do this, why will you even believe what she said?..."
"Son am sorry but kai kanka kasan sabuwar dokar MASARAUTAR and you approved it yourself, jin zance da ya shafi asiri koh da an san mutum ba zai iya aikata abinda ake zargin sa dashi ba ya zama dole a bincika a gano gaskiyar lamari, ni kaina ban yarda da maganar Hafeezah ba sai dai wajibi ne a gareni a matsayin adalin shugaba nayi duba akan abinda ta faɗa, zuwa gareku, kune kuka zo wa da Hafeezah da zancen kunga amaryar Yarima ZEEYAD na aikata wani abu da yayi kamanceceniya da asiri?" ya faɗa yana maida akalar tambayar sa kan bayi matan dake zube a gaban sa.
"Kwarai kuwa ranka ya daɗe, ni nan baiwa ce a sashin Sarauniya Hafeezah, su kuma wadannan ƙawaye na ne sannan suna aiki ne a sashin Hajiya babba sune suka zo min da wannan labarin, nikuma banyi ƙasa a guiwa ba naje na sanar da Sarauniya, shine ta yanke shawarar yiwa abin tufkar hanci tun da wuri."
"Hakane?."
Kai suka jinjina masa kafin ɗaya tace "Haka ne ranka ya daɗe, da idanun mu muka ganta jiya."
"They are lying, how dare them accuse my wife of doing such a terrible thing..."
"Enough Son, ka bar su su ƙarasar da abin da suke faɗi."
"I can't believe you also, kana biye musu that means ka yarda da sharrin da suka ɗaura mata kenan" ya faɗa cike da 6acin rai yana kallon mahaifin nasa.
Shiru mai Martaba yayi yana maida duban sa kan bayin kafin yace "Proceed."
Shiru sukayi na ƴan seconds kafin ɗaya tace "A daren da aka kawo ta wato daren jiya kenan, bayan mun zo wucewa ta ƙofar ɗakin da aka sauƙe ta ne muka ji kamar alamun wasu sumbatu cikin yaren da bamu san koh menene ba, koh da muka ji hakan, sai muka yanke shawarar leƙawa ta taga dan ganin abin dake faruwa cikin ɗakin..." shiru tayi ta kasa iddawa.
Ɗayar ce ta ɗaura da faɗin "Koh da muka leƙa ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba da abinda idanuwan mu suka gane mana, durƙushe muka ganta idanun ta a rufe yayin da bakin ta ke ambatar abinda bamu da masaniya akan koh menene, ba'a jima ba wani jan haske ya fito daga cikin tafin hannun ta, nan mukaji tana kiran sunan Yarima Z..."
"Hold it right there lady, jiya da misalin ƙarfe nawa ne kika faruwar abin" faɗin Grandma cikin katse ta.
Shiru duk sukayi kafin tayi saurin faɗin "Da misalin ƙarfe sha ɗayan dare ne."
Dariya Grandma tayi tace "Silly souls, ai jiya har ƙarfe ɗayan dare muna tare da DEENAH, babu abinda muka kwana munayi tare da ita wanda ya wuce sallah da roƙon Allah akan sharrin makiya, mahassada dama kuma annamimai irin ku, ranka ya daɗe mai Martaba ina da shaidar da zai tabbatar maka da cewa ina tare da ƴar jika ta jiya har misalin ƙarfe ɗayan dare, idan ma shaida kake so ga nan manƴan hadimai na kusa dani ka tambaye su."
Kallon matan dake bayan Grandma mai Martaba yayi yace "Menene gaskiyar wannan lamari?."
Ɗaya daga ciki ce tace "Kwarai kuwa ranka ya daɗe jiya ai a ɗakin Hajiya Babba ma ta kwana sabida gudun kada ta kasance ita kaɗai wani mummunan abin ya same ta, tunda ba wai masoya shi mijin nata ke dashi cikin fadar nan ba."
Kallon su yayi yace "Mai zakuce akan wannan batu, Hajiya babba ta shaida cewa tana tare da amaryar Yarima haka ma hadiman ta, ku kuma mai zaku iya cewa game da wacce kuka gani ƙarfe sha ɗayan?."
Shiru duk sukayi suna wuwwula idanu cike da rashin gaskiya, kafin ɗaya tayi caraff tace "Nayi maka rantsuwa ranka ya daɗe mun ganta, har ma abinda ta sanƴa ƙarƙashin gado dan asirce wani daga cikin ku."
"They are lying i...i...i didn't do anything" faɗin DEENAH cikin kuka ganin yadda suke ta ya6a mata sharri.
"Naji dukkanin bayanan ku, muje a duba ƙarƙashin gado inda kuka ce ta sanƴa abin, muddin aka samu wani abu toh tabbas hukunci zai hau kan matar Yarima, muddin kuwa na gano sharri kukayi mata toh tabbas sai kun fuskanci hukunci mai tsanani tare da nadamar hakan."
"Mun amince ranka ya daɗe" suka haɗa baki wurin faɗa.
Murmushi Hafeezah tayi tana juyawa ta kalli DEENAH tace "Wannan karon haƙar ki ba zata cimma ruwa ba Young lady, let's go and find out what she is hiding under that bed."
Hawaye kawai DEENAH keyi haɗi da nadamar kasancewar ta cikin wannan family masu nuna wa junan su tsantsar ƙiyayya, riƙo ZEEYAD tayi ƙam a hankali take faɗin "They are lying babu abinda na aikata muku, please believe me."
Rungumo ta yayi kawai dan kuwa baya tunanin zai iya magana jin yadda wani abu mai ɗaci ya tokare masa maƙoshi.
"Alright then Hafeezah tunda kin ƙeƙashe cewar DEENAH ta aikata asiri then muje a duba cikin ɗakin nata, muddin aka samu wani abu toh ina goyon bayan hukunta ta bisa ga karya dokar MASARAUTA da tayi, muddin kuwa ba'a sami Wani abu kamar yadda suka faɗa ba then ya zama dole DEENAH itace wacce zata za6i irin hukuncin da za'ayi musu bisa ga sharri da suka ɗaura mata."
Kallon juna sukayi kafin suce "Mun amince, ayi mana dukkanin hukuncin da aka tanadar muddin ya kasance sharri mukayi mata."
Kallon Grandma ZEEYAD yayi nan ta jinjina masa kai akan ya kwantar da hankalin sa.
YAZEED tashi yayi ya bar musu fadar dan kuwa abin na mahaifiyar sa ya fara yin yawa, da kallon tausayi ZEEYAD ya bisa kafin kuma ya tsinkayo muryar mai Martaba na bada umarnin aje a duba ɗakin da aka sauƙe DEENAH ɗin.
Kallon su Hafeezah tayi tace "Am trying to save my children daga faɗawa halaka ta sanadiyyar wannan abar da ka auro, dan haka let's wait and see koh ita ɗin mai gaskiya ce kamar yadda kai da kakar ka ke faɗi."
Jan hannun DEENAH yayi da niyyar barin fadar ya tsinkayo muryar mai Martaba.
"You know that you're not allowed to leave here until an aiwatar da dukkanin bincike."
Juyowa yayi a fusace yace "This is humiliating and i can't stand someone accusing my wife of doing something bad, kamar yadda i won't allowed anyone to touch her da sunan kama ta da aiwatar da wani laifi."
"Boy lower your voice, sannan ka jira sakamakon abinda zasu taho dashi bayan sunje sun bincika ɗin."
"Grandma you're supporting them, kema kin yarda DEENAH zata aikata abinda suke zargin ta dashi, we all know this selfish woman here only cares about her happiness and she would stop at nothing har sai taga farin cikin wasu ya ruguje, i can't believe all of you here da yarda da zancen ta dama kuma na wadannan bayin da ta saya against DEENAH."
"Listen Boy, daga ni har mahaifin ka babu wanda ya yarda da abinda Hafeezah ta faɗa but in order to prove her wrong ya zama dole a gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanadar."
"But Grandma i did nothing, why will she accuse me of using a spell against you?" cewar DEENAH da zuciyar ta ke mugun burning.
Share mata hawaye tayi kafin tace "Listen DEENAH, i know baki aikata abinda ake zargin ki dashi ba, this doesn't make sense at all, i mean jiya shigowar ki cikin gidan nan, koh da kuwa da sharri kika shigo ba zaki fara aiwatar da ƙudirin ki tun wuri haka nan ba, i know you're innocent and gaskiya zatayi halin ta yau ɗinnan."
Ita dai DEENAH kanta sadde a ƙasa tana cigaba da shessheƙa.
Mai Martaba ne ya sanƴa aka kira masa guards wadanda aikin su ne bincike aduk sadda aka kama wani da laifin aikata wani abin, kafin ya umurce su da suje su dubo masa ɗakin.
Kallon DEENAH amaryar YAZEED tayi tanajin wani irin farin ciki a ranta, dan kuwa ba ƙaramin burge ta Hafeezah tayi ba.
JALILAH kuwa jikin ta ne yayi matuƙar sanƴi duk sai tausayin DEENAH ɗin ya kama ta.
Naseeba dake tsaye da munafukar jakadiyar ta Kiki ce tace "I wonder mai ya gani jikin yarinƴar nan da har zata ɗauke masa hankali ya auro ta a matsayin mata."
Murmushin gefen baki Kiki tayi tace "Ranki ya daɗe ai kishi ma kaɗai ba zai hana ki ganin abinda ya gani jikin yarinƴar nan ba, but zan iya yin rantsuwa duk matan dake cikin nan babu wacce zata nuna mata kyau sai dai hasken fata, uwa uba gata da diri mai kyau dan dama naji ƴan chan ƙasar tasu ba dai iya kula da namiji ba tare da basa dukkanin wasu haƙƙin auren sa ba, kinga kuwa Yarima abubuwa dayawa ya gani game da yarinƴar nan wanda shi kaɗai ya barwa kansa sani, ni duk sai naji ta burge ni ma..."
Mugun kallon da Naseeba ta watsa mata ne ya sanƴa ta saurin sadda kai ƙasa tana jan mayafin kanta tare da faɗin "Afuwan ranki ya daɗe, ni banyi dan na 6ata miki rai ba, kawai dai na faɗi ra'ayi na ne tunda ba wai nasan koh kin tsane ta koh baki tsane ta bane ba."
"Wannan wace iriyar maganar banza kike?, ke kanki kinsani duk wacce ta ra6i ZEEYAD a shirye nake da dealing da kowace sakarya ce ita, it's a pity da ya kasance ba ni kaɗai ce maƙiyar ta ba, but that won't Stop me daga aiwatar da abinda na ƙudurta a raina, ya zama dole nayi gaggawar aiwatar da wani abin tun kafin ya kusance ta, ta nan ne kaɗai zan iya samu burin dake cikin raina ya cika, ki koma wurin kakar ki ki kar6o min dukkanin wasu abubuwan da zan buƙata wurin aiwatar da aiki na kafin dare yayi a kaita ɗakin sa, dan kuwa i won't stop at nothing har sai haƙa ta ta cimma ruwa jeki yanzun nan."
"An gama ranki ya daɗe" ta faɗa cikin sadda kai tana wucewa da sauri dan zuwa aiwatar da abinda Uwargijiyar tata ta sanƴa ta.
Ajiyar zuciya Sarauniya Nazeerah ta sauƙe tana ƙarasowa inda Hafeezah ke tsaye cikin raɗa yadda babu wanda zai ji mai take cewa bale ta san da ita take magana tace "Listen Hafeezah, don't you dare try to do something silly to this innocent girl here, bata tauye miki komai ba, da mijin ta kaɗai kike ƙiyayyar ki, everyone knows bana shiga abinda bai shafe ni ba, but, you just be careful ki rage wannan ƙiyayyar taki da bata da ranar yankewa coz da dukkanin alamu wannan yarinƴar ce zata zamto sanadiyyar tonuwar asirin ki, the girl da kika raina tabbas will be your downfall Hafeezah" tana faɗin haka ta ɗan ja da baya tana kallon reaction ɗin Hafeezah wacce daga gani ranta ya kai maƙura wurin 6aci.
Suna nan tsaye wadannan Guards ɗin suka dawo kai tsaye gaban mai Martaba suka zube kansu duƙe.
Kallon su mai Martaba yayi yace "Inajin ku."
Babban su ne ya fara faɗin "Duk wani wanda yayi wa sarki ƙarya toh kuwa babu shakka ya aikata babban laifi sannan hukuncin hakan zai hau kansa kamar yadda dokar MASARAUTA ta tanada, musamman ma ace ga wanda akayi wa ƙazafin ya kasance ɗan cikin MASARAUTA ne, mun je mun duba koh ina na cikin ɗakin sannan..."
"Wannan wace iriyar maganar banza kake faɗi, ka tafi kai tsaye ga abinda aka tura ka nema mana, miye kuma na wani jan zance, ka faɗa kowa yaga gaskiyar ainihin wannan annobar da ya ɗauko..."
Maganar ta ce ta katse sakamakon jin abinda ya faɗa, manƴan idanun ta ta waro tamkar zasu zubo daga cikin socket ɗinsu.
"Maganar banza kake faɗi, na yarda da baiwa ta sannan nasan ba za..."
"Hafeezah" mai Martaba ya katse ta a tsawace kafin ya ɗaura da faɗin "Tabbas kin raina mana hankali sannan kin maida ni ƙaramin mutum a idanun jama'a musamman a gaban innocent girl da kika ɗaurawa sharrin aikata abinda batayi ba."
"M...mai..mai kake faɗa ne haka ranka ya daɗe?, tayaya zanyi mata sharri ba fah ni na ganta da idanu na ba, ga nan wadanda suka kawomin labarin abinda ya faru, dama ba shaidu uku ake nema ba kafin aje ga aiwatar da wani abin, su suka shaida min da..."
"Ke wace iriyar sakarya ce da zaki ɗau maganar bayi ki yarda dashi har ma ki kai ga tozarta yarinƴa a gaban jama'a?, hukunci zai hau kan kowannen ku daga ke har su bayin naki."
Idanu ta waro cike da tashin hankali tana kallon sa tace