Showing 63001 words to 66000 words out of 236327 words
kafin kuma ta shiga rero waƙa cikin zazzaƙar muryar ta
_I have been reading books of Old_
_The Legends and the Myths_
_Achilles and his gold_
_Hercules and his gifts_
_Spider-Man's Control_
_And Batman with his fists_
_And clearly i don't see myself upon that list_
_But she said, “where do you wanna go?”_
_How much you wanna risk?_
_Am not looking for somebody with some superhuman gifts,_
_Some superhero,_
_Some Fairy tale bliss_
_Just something i can turn to somebody i can kiss_
_I want something just like this_
_Tu-ru-ru, Tu-ru-ru_
"Woo bravo!" aka faɗa saitin kunnen ta.
Da sauri ta ɗago tana cire headphone ɗin kanta tare da binsa da kallo.
Zama yayi kusada ita, nan tayi saurin matsawa gefe.
Kallon ta yayi kafin kuma ya ɗan ta6e baki shima yana kauda kansa daga kallon ta yace "You're late today, why?."
Shiru tayi pretending tana duba takardar hannun ta.
Kallon ta yayi jin taƙi kulasa, hannu yasa ya kar6i takardar hannun nata ya shiga dubawa.
Ta6e baki yayi yace "Uhm this topic, sai yanzu kukeyin sa?, i have done it in my secondary school, but ku how comes sai yanzu kuke yin sa, strange" ya faɗa yana still idanun sa a cikin takardar.
Bata kula sa ba sai ma wayar ta da ta ciro ta hau daddanawa, ba tare da tabi ta kanshi ba.
Kallon ta yayi ta gefen ido bai ce komai ba sai ma maida duban sa da yayi cikin takardar yana kallo.
_"She is trying to show me attitude"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta ta gefen ido.
Rufe takardar yayi kawai ya zauna tare da crossing legs ɗinsa yana neman ta hanƴar da zai jata da hira.
"Ahm..oh yeah tell me, ke mawaƙiya ce?, you have a sweet voice."
Bata ɗago ta kallesa ba sai kai kawai da ta girgiza masa alamun "a'a."
_"She should atleast fake a smile on her face koh da bata so, i can't believe ta zage tana yiwa wancan tiny thing ɗin murmushi but taƙi sakar min fuska"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta.
Ɗagowa tayi ta kallesa nan yayi saurin sakar mata murmushi, kafin kuma ta sake sadda kai ƙasa tana cigaba da danne-dannen ta.
_"Oh GOD, did she just ignore my beautiful smile?"_
Takardar ta ta ɗauka ta shiga buɗewa tana bi a hankali.
Buɗe jakar ta tayi ta ciro farar glass tare da sanƴawa a idanun ta tana cigaba da duba takardar hannun nata.
Duk abin nan da take bata ɗago ta kallesa ba, sai shi da ya zama kamar soko yana ta bin ta da kallo.
A haka suke zaune babu wanda yace da wani uffan a cikin su har lokacin second period lecture ɗinta yayi.
Tattare komai tayi ta sanƴa a jaka kafin ta miƙe tana rataye jakar a kafaɗa.
Kafar uniform ɗinta da ta ɗanyi ƙura ta sunkuya to goge shi da handky ɗinta kafin ta jefa shi cikin jaka ta fara tafiya.
Sai da ta ɗanyi nisa kaɗan kafin ya ɗauke idanun sa da ya zuba akan coca-cola shape ɗinta yana mai mara mata baya.
Har cikin class ɗin ya biyo ta ta sami wuri ta zauna shima ya zauna, nan kuma hankalin ƴan class ɗin baki ɗaya ya dawo kansu.
Babu abinda kakeji sai maganar mutane ƙasa-ƙasa, da kaji kasan kowa tofa albarkacin bakin sa yake.
Shi kuwa koh kaɗan bai damu da kallon da ƴan mata da samarin class ɗin ke binsa dashi ba, sai ma sake tsuke fuska da yakeyi yana basarwa.
Ita kuwa DEENAH ba ƙaramin mamakin sa bane ya kama ta, ganin sai bin ta yake yawa jela koh bodyguard ɗin ta.
A hakan Lecturer ɗinsu ya shigo nan duk suka maida duban su tare da tattare dukkan nutsuwar su zuwa kansa.
Haka ma DEENAH hankalin ta ta maida kan lecturer ɗin bata sake kallon ZEEDAN dake zaune gefen ta ba.
Lecturer hango Farin mutum mai suffar larabawa da yayi ba ƙaramin mamaki ne ya kama sa ba.
Takowa yayi zuwa kansu tare da tsayawa yana ƙare musu kallo ta ƙasan glass ɗin sa, babban mutum ne.
ZEEDAN kuwa wani irin basarwa yayi yana sake tsuke fuska tare da cin guna.
Buɗe baki lecturer yayi zaiyi magana nan DEENAH tayi saurin cewa "Am so sorry sir he is just my guard, baya ta6a samun sukuni indai ba ya aiwatar da abinda Mahaifi na ya sanƴa shi bane na lura dani kullum ba, he is just doing his job."
"Bodyguard kuma har cikin class?" cewar lecturer ɗin yana kallon ta.
"Kayi haƙuri sir, nasan an karya doka but nayi dashi to let me be, but he just don't wants to listen, zanyi ƙoƙarin naga na shawo kansa yanzu ya fita, am sorry."
Kai lecturer ya jinjina nan ta kalli ZEEDAN tace "Abyad, dan Allah ka tafi ni ba yarinƴa bace yanzu, zan iya kula da kaina and nasan kaima ba zaka rasa wasu abubuwan yi ba, just excuse us please" ta faɗa tana kallon shi.
Tunda DEENAH ta kira sa da bodyguard ɗinta ya kafe ƙaramin bakin ta dake motsi da idanun sa, he was lost a duniyar tunanin kallon ta, babu kuma abinda ya sake rikita masa lissafi sai sunan da ta kiraye sa dashi.
_Abyad_ ya maimata hakan a zuciyar sa.
"Yeah sure, i would be waiting for you outside" ya faɗa bayan ya miƙe tsaye tare da gyara zaman coat ɗin jikin shi.
Ficewa yayi daga class ɗin inda idanu dayawa suka bisa da kallo, especially ladies ɗin class ɗin.
Kan kace miye kuma class ɗin ya ɗau hayaniya, maganar lecturer ne ya sanƴa kowa saita nutsuwar sa.
Ajiyar zuciya DEENAH ta sauƙe tana maida duban ta kan board.
12pm suka fito dan haka Masallaci kawai ta nufa ta tare achan, sai da tayi sallar azahar kafin ta fito ta nufi Cafeteria dan sayan abinci.
Doughnut guda biyu ta saya sai ruwa da Malt kafin ta dawo inda ta saba zama ta zauna.
Bata iya cinƴe doughnut ɗin duka biyu ba dan haka maida sauran tayi cikin jakar ta kafin ta tashi ta koma class.
Suna cikin lectures ne taji marar ta ta fara murɗa mata sosai, kafin kuma tayi wani yunƙuri ta fara jin alamun damshi ta ƙasan ta, da alamu dai jinin ya riga ciwon marar zuwa.
_"Oh no, what's happening to me?"_ ta faɗa tana matse cinƴoƴin ta tana gyara zama.
Shal ta manta da cewa yau ne zata ga baƙon watan ta, sosai marar tata ta shiga murɗa mata gashi sam idan yazo baya yi mata da wasa, ba ƙaramin azaba take ci ba.
Sosai ta shiga tashin hankali dan kuwa already tasan farin kayan jikin ta ya 6aci, gashi kuma bata zo da after-dress ɗin da take ɗaurawa akai ba, tasan yau tata ta ƙare a cikin school ɗinnan.
Da kallo kawai take bin ƴan class ɗin da kallo tana runtse idanun ta.
Kifa kanta tayi akan bench ɗin da take, tana maida numfashin wahala.
A haka har aka gama musu lectures DEENAH bata cikin hayyacin ta, tsoro da rashin mafita ne suka haɗu mata da ciwon mara mai tsanani.
Da kallo ta fara bin ƴan class ɗin da suka fara fita babu wanda yabi ta kanta.
Riƙo rigar wata tayi ta baya tana kallon ta.
Juyowa yarinƴar tayi tana kallon fuskar DEENAH da ya gama zama do very pale kamar marar lafiya.
Sunkuyo da kai yarinƴar tayi DEENAH tayi mata magana.
Idanu yarinƴar ta zaro tana kallon DEENAH kafin ta kira sauran ƙawayen ta ta faɗa musu abin dake faruwa.
"Wayyo Allah, mu kuwa ba a hostel muke ba, gashi bamuda wani rigar karewa da sai mu bata" cewar ɗaya daga cikin su.
"Ƴan cikin hostel ɗinma duk sun tafi fah, dah sai mu bisu mu kar6a mata abin karewa" faɗin ɗaya.
"A'a tsaya, ta zauna, ke Rahila ki zauna tare da ita, mu kuma zamuje Hostel mu taho mata da wani sabon kayan ta canza."
Hakan kuwa akayi wacce aka kira da Rahila ce ta zauna tare da DEENAH kafin kuma sauran biyun su fice daga cikin class ɗin........
*******************
.........Tsaye yake yaga fitowar ta daga cikin class ɗin, sai dai har ƴan ciki duka suka fito bai ba fitowar DEENAH ba.
_"Why isn't she out yet?"_ ya faɗa a ransa yana kallon ƙofar class ɗin.
Tsayuwar 10mins ya ƙara sai dai har yanzu bai ga ta fito ba, hakan yasa shi yanke shawarar duba cikin class ɗin.
A hankali ya fara takowa gaban class ɗin yana kaɗa key ɗin motar hannun sa.
Hango ƴan mata biyu yayi a ciki ɗaya a zaune ɗaya kuma kanta kwance akan desk.
Ƙarasowa bakin class ɗin yayi tare da yin knocking ɗin door ɗin.
Ɗayar ce ta ɗago ta kallesa kafin tayi saurin kallon DEENAH tace "Ga nan Bodyguard ɗin ki ya biyo sawun ki."
Da sauri DEENAH ta ɗago da kanta suna haɗa ido.
"MADEENAH?" ya furta a hankali yana ƙarasowa cikin class ɗin.
Ɗagowa tayi tana gyara zaman ta tare da sunkuyar da kanta ƙasa.
"Hey, i have been waiting for you since, what are you still doing here?."
Goge gumin fuskar ta tayi tace "Nothing."
"Alright, shall we?."
Kallon yarinƴar kusa da ita tayi tana maida kanta kan benchin tare da runtse idanu.
"MADEENAH, is she Okay?."
"No, bata jin daɗi ne, but i think you should get going, zata samo ka a gida."
"What?" ya faɗa yana durƙusawa kusada ita.
"What's wrong with her?" ya faɗa.
Ɗagowa tayi tace "Am fine, ka tafi kawai, i would be alright."
"Have you lost your mind, bakida lafiya and you expect me to leave you here alone."
"Am not alone, bakaga akwai friends ɗina bane, they would be back soon" ta faɗa tana runtse idanu tare da riƙe ciki lokacin da ya sake murɗa mata.
"MADEENAH?" ya faɗa cikin tashin hankali.
Ƙawayen yarinƴar ne suka dawo da jaka a hannun su, nan duk suka tsaya kallon ZEEDAN suna ƙarasowa.
"Gashi mun kawo mata kaya ta canza" cewar ɗaya.
Ɗagowa DEENAH tayi ta kallesu kafin kuma ta kalli ZEEDAN tace "Ka fita waje please, zan fito yanzu."
Kallon ta yake kafin yace "No, am not going anywhere, ki faɗamin meke damunki."
"Just get out please" ta faɗa cikin ƙosawa.
Cikin idanun ta yake kallo nan kuma tayi saurin kauda idon ta.
"Are you on your period?" ta jiyo ya faɗi hakan.
Da sauri duk ƙawayen suka kallesa kafin su kalli juna suna ware idanu, DEENAH kuwa wani irin kunƴa ne taji yayi mata rumfa, she can't believe maiyasa Balaraben nan bashi da kunƴa koh kaɗan.
Rasa ya zata yi tayi kai kawai ta juya masa idanun ta a runtse.
Miƙewa yayi daga durƙushen da yakeyi yace "I understand, get up i will take you home."
Bata juyo ta iya kallon sa ba, sai ma kunƴar shi da takejin yake sake lullu6e ta.
"MADEENAH?" ya furta yana kai bakin shi saitin kunnen ta.
"I can't stand up, ba zan iya tashi nayi tafiya ba, ƙafa na ya riƙe, so just go please i don't need your help, just let me be, please" ta faɗi hakan ba tare da ta juyo ta kallesa ba.
Baki ya cize kawai kafin kuma yaja ƙafafun sa ya bar cikin class ɗin.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon ƴan matan "Thank you so much" ta faɗa.
Zuwa sukayi tare da taimaka mata ta tashi tsaye, sosai bayan ta yayi staining dan haka taimaka mata sukayi ta canza kayan jikin ta tare da bata sabon Pant da Pad ta saka.
Taimakawa sukayi tare da gyara inda ta zauna ɗin, kafin su sanƴa wanda ta cire a ƙaton baƙin leda suka ƙulle.
Ta ɗan ji ta comfortable yanzu, dukda kuwa a matuƙar takure take, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a cikin ɗakin ta.
Ɗingisawa tayi ta zauna tana jin kanta na sara mata, ciwon ciki da na ƙafa duka sun haɗe mata wuri ɗaya.
"Sannu" sukayi ta jera mata kamar su ari baki.
Da kyar dai suka taimaka mata ta tashi tare da riƙo ta sukayo waje.
Hango su yayi daga inda yake tsaye duk ya rasa sukuni, nan ya iyo kansu yana kiran sunan ta.
A galabaice ta ɗago ta kallesa tace "mai kakeyi har yanzu baka tafi ba, dan Allah ka tafi nace koh?."
Kallon ta yake, sosai yakejin kamar ciwon a jikin sa yake, ganin yau kaɗai har ta ɗan faɗa ba ƙaramin tausayi ta bashi ba.
Kallon ƙawayen yayi yace "I will take care of her, you should get going."
"How can you take care of me, how?, dan Allah ka tafi haka nan mana" ta faɗa cikin ɗan ɗagun murya dan kuwa ya fara bata haushi.
"MADEENAH...."
"Suna na ya fita a bakin ka haka nan, stay away from me please, Okay?."
"Let's go" ta faɗawa ƙawayen nata.
"Motar zamu kai ki?."
Kai ta girgiza musu alamun a'a.
Wucewa sukayi inda ya bisu da kallo yana jin ba daɗin yadda tayi masa maganar a zuciyar sa.
Komawa yayi ya jinginu da motar sa tare da folding arms ɗinsa yana kallon su.
Adaidaita suka tara tare da sanƴa ta a ciki, suna ƙara yi mata sannu kafin yaja suka fara tafiya.
Motar sa ya shiga tare da mara musu baya.
Sun ɗanyi tafiya mai nisa, kafin kuma ya ƙara gudun motar tasa yana shan gaban su.
Burki mai Napep ɗin yaja da ƙarfi ya tsaya yana fitowa daga cikin napep ɗin, dan ganin wane marar hankalin ne wannan.
Fitowa ZEEDAN yayi daga cikin motar sa ya tunkaro su, kai tsaye wurin DEENAH dake ta aikin kallon sa cike da mamaki yayi yace "Come out."
Kawar da kai tayi alamun ba zata fito ba ɗin ba.
"MADEENAH?" ya kira sunan ta.
"Nace maka ka rabu dani haka nan, ba zan iya takawa ba, ka barni mana nik..."
Bata iya ƙarasar da maganar ba sakamakon jinta da tayi cak akan hannun sa.
"Idan ba zaki iya takawa ba, then nikuma miye amfani na a matsayi na na guard ɗinki?" ya faɗa yana kallon cikin idanun ta da ta waro su cike da mamaki ta saki baki tana kallon sa.
"Pu..pu..put me down" ta faɗa cikin rawar baki tana niyyar sauƙa.
Sake ƙanƙame ta yayi yace "I won't put you down, ba'a ja da abinda na faɗa, when i said i want to take you home then i mean it and nothing can change that, so now stay still" ya faɗa cikin harɗe fuska yana kallon ta.
Motar ya nufa ya sanƴa ta a ciki yana kwantar mata da seat ɗin.
Dubu ɗaya ya ciro ya baiwa mai Napep ɗin da ya saki baki kawai yana kallon su kafin ya wuce ya shige cikin motar.
Lumshe idanu tayi sosai take jin matuƙar haushin shi, how dare him da zai dinga ta6a ta yadda yaso, koh ya ɗauka ita ɗin irin Karuwar sa Surayya ce? Ta faɗi hakan a zuciyar ta idanun ta a lumshe.
Ƙamshin turaren sa da ya mannu mata a kaya ne ya cika mata hanci, hakan yasa take sake 6ata rai cike da jin haushin sa.
Sun ɗanyi tafiya kafin taji motar ta tsaya, daga nan kuma ya buɗe ta ya fita.
Idanu ta buɗe tare da bin sa da kallo kafin taja ɗan ƙaramin tsaki tana hararar sa.
Sosai ya jido mata fruits kala-kala a cikin leda ya dawo motar kafin ya jata suka cigaba da tafiya.
Shiru motar ta ɗauka kafin kuma wayar sa ta hau ringing.
Dubawa yayi yaga sunan Mom ke yawo a jikin screen ɗin.
Amsawa yayi yana sanƴa wa a hands-free tare da tattara dukkanin nutsuwar sa zuwa kan tuƙin da yake.
"Assalamu Alaikum" ya faɗa.
"Wa'alaika Assalam, ɗan albarka ina ka shiga ne kwana biyu ban ganka ba?."
"Am sorry Mom, tafiya ce ta taso min urgently shiyasa ban faɗa miki ba, kuma i thought koh zan iya dawowa a ranar."
"Toh ai shikenan, Khairat ta dawo kun haɗu kuwa tunda ta dawo?."
Shiru yayi yana tare da haɗiye wani abu mai ɗaci yace "Yes Mom."
"Masha Allah, nima goben nan zanyi tafiya zuwa London dan samo muku engagement ring mai kyau da tsada, domin ƴaƴan nawa na musamman ne" ta faɗi hakan cikin dariya.
Shiru yayi yana cize baki zuciyar sa na mugun ƙuna, yace "Hakan yayi kyau Mom, maybe we should talk later ina driving ne yanzu."
"Alright, idan ka sauƙa ka kira ni, we have alot to discuss, kaji?."
"Yeah" ya faɗa.
Katse ƙiran yayi yana cigaba da kallon gaban sa.
Har suka iso gidan babu wanda ya yiwa wani magana a cikin su.
Parking motar yayi a parking space, kafin ya ɗaga seat ɗin da take ɗin, fuskar nan tata a matuƙar tsuke.
Fitowa yayi ya zagayo tare da buɗe mata ƙofar yana miƙa mata hannu.
Da kallo tabi hannun nasa zuciyar ta na daɗa yin zafi sosai, kafin ta yunƙura ta tashi da kyar tana dafa murfin motar.
"Careful" ya faɗa cikin muryar sa da tayi rauni.
"Zan wuce" kawai ta faɗa, hakan yasa shi matsa mata.
Ledar kayan ta da jakar ta ta ɗauka, kafin dai ta daure ta fara takawa a hankali.
Abubuwan da ya saya mata ya ciro tare da bin bayan ta dashi.
A falo ta sami Umma zaune da waya a hannun ta.
Jin sallamar DEENAH yasa ta ɗagowa tace "Yanzun nan nake shirin ƙirar ki, naga kin daɗe."
Zuwa tayi ta faɗa jikin Umma tana sakin kuka sosai.
"Subhanallah, lafiyan ki, daga dawowa kuma sai kuka auta, mai akayi miki?."
"Umma ciki na ne ke ciwo, period ɗina ne yazo min a makaranta ya 6ata min kaya sai da wasu ƴan ajin mu ne suka kawomin wani kayan nasa."
"Toh alhamdulillah, gaskiya sun kyauta Allah yayi musu albarka, toh kuma miye abin kukan toh?, gashi nan ma har jikin ki yayi zafi" cewar Umma tana tatta6a wuyan ta.
Shesheƙa kawai DEENAH keyi kafin Umma ta taimaka mata ta tashi ta kaita ɗakin ta.
Ruwan zafi ta haɗa mata na yin wanka tace "Ki shiga kiyi wankan, ki fito kici abinci ki sha magani sannan ki kwanta koh?."
Kai ta jinjina mata kafin Umma ta fice, ita kuma ta tashi tare da yin shirin wankan, har yanzun bata bar kukan ba.
Sosai taji daɗin wankan da tayi shiryawa tayi ta fito falo wurin Umma.
"Yauwa ƴar albarka, zo ki zauna na kawo miki abincin" cewar Umma tana zaunar da ita kafin kuma ta tashi tayi cikin kitchen.
Dawowa tayi da plate ɗin abincin a hannun ta, kafin ta ɗauko ruwa marar sanƴi ta shiga bata abincin a baki.
"Toh su kuma wadannan hawayen na menene haka da suka kasa tsayuwa?."
Goge hawayen tayi tana cigaba da amsar abincin da Umma ke bata.
Ta ɗan ci sosai kafin ta 6alli magani ta bata ta sha tace "Tijjani ya kawo min ledar fruits wai inji wani a waje yace a baki, yana kitchen idan kin tashi sha, yanzu dai kije ki kwanta koh kyaji sauƙin ciwon."
Kai kawai ta jinjina mata tana tashi ta koma ɗaki.
Bed ɗinta ta hau tana jawo bargo ta rufawa kanta tare da jinjina tsantsar yaudara dama kuma kwashe-kwashe irin ta Balarabe.
Babu maganar dake tayi mata yawo a