Showing 168001 words to 171000 words out of 236327 words

Chapter 57 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45315

faɗa cike da jindaɗi tana rungume mahaifiyar tata.

Sosai Sarauniya Hafeezah tayi murnar da dawowan ƴaƴan nata, ɗago ta tayi tare da sumbatar ta a ƙunci tana sake rungume ta tace "Welcome home my beautiful princess."

Sun ɗan daɗe rungume da juna kafin su ɗago, nan Sarauniya Hafeezah tace "Rahila ku raka Rahinah izuwa masauƙin ta sannan ku samar mata da dukkanin wani abu da ta buƙata."

Duƙar da kai wacce aka kira da Rahila tayi tana faɗin "Angama ranki ya daɗe" ta faɗa tana riƙo Farha da niyyar janta su tafi.

Wani irin wawan mari ta ɗauke baiwar dashi in a rude manner tace "Yuck!, what the hell do you think you're doing, touching me with your fucking dirty hands?."

Rolling idanu kawai Sarauniya Hafeezah tayi kafin tace "Calm down princess, she will be careful next time."

Sosai ran Rahinah ɗin ya 6aci tana wiping inda baiwar ta ta6a ta kafin tace "I don't care, baki faɗa musu dukkanin rules ɗina bane, she must be punished for her misdeeds, i mean how could she touch me with this ugly, dirty and disgusting hands of her?."

"Apologised to her now" faɗin Sarauniya Hafeezah cikin tsawa.

Baiwar da ta sha rikitaccen mari duk ta rikice ne tayi saurin rissinawa tana faɗin "Ki gafarce ni ranki ya daɗe gimbiya, a bisa rashin sani na aikata miki hakan."

Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi tace "Listen princess, kiyi mata haƙuri kinji?."

Kamar ba zata yi magana ba tace "Dan kawai kince hakan ne, am tired of standing here a nunamin masauƙi na mana, are they going to keep staring at me like this?."

"Show her to her room, and make sure kunyi avoiding duk wani abu da zai sanƴa ta 6acin rai."

"Insha Allah ranki ya daɗe" suka amsa cikin girmamawa.

Biyu ne suka shiga gaba biyu kuma suna take mata baya inda suka sanƴa ta a tsakiya "ughh they stink" ta faɗa cikin doɗe hancin ta tana korewa da hannayen ta suka wuce.

Sarauniya Hafeezah maida duban ta tayi gun saurayin dake tsaye ya wani 6ata fuska haɗi da naɗo baki wanda daga gani ƙiris yake ya fashe tace "Ayaan my boy" ta faɗa tana ƙarasowa kusa dashi tana rungumar sa.

"I guess am not your favorite anymore how could you ignore me kamar baki ganni ba kinje kina kula wata Rahinah chan daban?" ya faɗa cikin ɗagowa yana aika mata da wani irin kallo ƙasa-ƙasa.

"Am sorry Sweetheart, kasan bama haka da kai koh, come on na sanƴa an girka maka favorite ɗinka am sure you will enjoy it."

Sai a sannan ya ɗan saki fuska yace "Really?."

"Kai dai kazo muje" ta faɗa tana riƙo sa suyi gaba.

Da kallo yabi wata baiwa da tazo wuce su tana gaida su cikin girmamawa yana wani irin cize baki.

"Control yourself Ayaan, wadannan matan are like your servants dan haka ka ɗauke idanun ka daga kansu."

"Sorry Ummie" ya faɗa suna cigaba da tafiya a haka har suka iso part nata.

Da wasu bayi ta haɗa shi inda shima akayi masa iso zuwa nashi part ɗin.


****************

_______Sosai taci kwalliya cikin baƙar doguwar gown ɗin ta, kasancewa shine Favorite color nata.

Sosai ta dami Anty Khadija dake yi mata ɗaurin head-tie akan tayi sauri.
"Anty Khadija yana ta jira fah, fisabilillah."

"Lallai ma DEENAH da ake kwalliya baki ce nayi sauri ba sai yanzu, toh wallahi ki zauna ki natsu kinsan dai banason abu da gaggawa, yanzu idan ban natsu na fidda ki mai kyau ba ai sai kije yace bakiyi kyau ba koh ma yaƙi yaba kwalliyar taki."

Ɗan turo baki tayi tana kallon fuskar ta cikin mirror ɗin.

Ameerah ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Miye nake ganin kamar duk kun shirya?."

Kallon ta Anty Khadija tayi tace "Toh da ɗin mai kikeso muyi idan ba shirin ba?."

"Malamai ban fah gane ba, wai kuna nufin kuce har tafiya zakuyi yanzu?."

"Tsaya anan."

Jafar ne ya leƙo cikin ɗakin shima cikin shigar sa mai kyau yana faɗin "He is here."

Kallon sa Amirah tayi baki sake tace "Bangane he is here ba, wallahi ba zaiyiwu ba, tayaya zakuyi ku tafi ku bar ni bayan nasa rai" ta faɗa idanun ta na tara hawaye.

"Toh kuma laifin waye, ina zuwa kikayi kika kafa TV a gaba kina kallo yawa baƙauyiyar da ta fito daga karkara, kuma da nayi ta kiran ki kizo ɗin ba manna min kikayi ba, kyaji dashi ai dan mu kam ba jiran ki zamuyi ba" cewar Anty Khadija.

Cikin kuka Amirah tace "Wallahi in ta yiwu na zama albasa, wallahi baku isa ba" ta faɗa tana ficewa tayi ɗakin Umma.

Kallon su Jafar yayi yace "Ya zakuyi mata haka?."

"Kyale ta nasan koh taje inbanda ƙauyanci babu abinda zata nuna, gara tayi zaman ta da akan ta kunƴatar damu."

"Anty Khadija, make it quick please."

"Ke ni dallah mai nakeyi ne yanzun, sai kisa na fasa na bar miki abin ki haka."

"Yi haƙuri" ta faɗa cikin sanƴi tare da tsuƙe bakin ta tayi shiru.

Ficewa Jafar yayi yana faɗin "We're waiting."

Ba'a daɗe ba Amirah ta dawo da Umma a bayan ta tana matsar kwalla lokacin har an gama ɗaurawa DEENAH ɗankwalin.

Daga bakin ƙofar Umma ta tsaya tana kallon su tace "Amirah tace kunje ba zaku tafi da ita ba, maiyasa?."

Anty Khadija ce tace "Anty tunɗazu fah nake ce mata tazo ta shirya amma taƙi kula ni taje ta ƙura TV a gaba wai ita nan tana kallon favorite series ɗinta."

"Wallahi ba haka bane, ni babu wacce ta kira ni a cikin su, kawai dai basa son zuwa ne dani kuma sai naje" ta faɗa cikin kuka.

"Toh ya isa haka nan jeki shirya da wuri, ku kuma ku jira ta."

"Amma Umma Abyad fah yana ta jira" cewar DEENAH ɗin cikin 6ata fuska.

"Kuyi mata haƙuri yanzun nan zata shirya ku tafi, abu na lokaci ɗaya kam menene dalilin ku na ware ta, wuce kije ki shirya."

Daɗi ne ya cika Amirah dan haka saurin wucewa tayi zuwa bathroom tana dariya ƙasa-ƙasa ganin yadda Anty Khadija da DEENAH suka 6ata fuska.

Ficewa Umma tayi daga ɗakin cikin ɗagun murya yadda Amirah ɗin zataji Anty Khadija tace "Kuma wallahi minti biyu ki idda wankan nan ki fito, minti uku ki shirya kinga dai 5mins kenan koh, idan kika wuce haka kuma kya same mu a chan."

Sanin halin Anty Khadija ya sanƴa Amirah saurin fitowa daga wankan tana tsuke baki.

Da sauri ta ɗau kayan ta mai kyau ita ma tasa kafin ta shiga shirin nata cikin sauri ganin yadda duk suke bin ta da harara yawa idanun su zai fito.

"Inbanda ma ƴar wahala iriyar ki kowa nan da kika gani da saurayin sa zashi ke koh da uwar wa zaki oho" cewar Anty Khadija tana aika mata da harara.

"Hmm Anty Khadija kenan nima fah saurayin nan ba rasa shi nayi ba..."

"Dallah ki rufewa mutane baki kiyi sauri, da wani ƙazamin saurayin naki a wurin hammata duk gumi idan yazo yawa wanda yayi gudun tsere kafin ya ƙaraso, ke har kina iya zama dashi a hakan ba tare da kinji komai ba mtssww."

"Oho dai, koma dai menene ba za dai ace banida saurayin ba."

"Da wannan abin ai gara babu, ke DEENAH kin ganshi kuwa, ni wallahi ina tantama ma idan ba irin samari ƴan ghetto masu yiwa ƴan mata ƙarƴar nan bane, who even knows koh baban bola mai ajakuta ne, dan kamar na ta6a ganin mai kama dashi yara na bin sa da gwangwan a baya."

"Nasan fah duk dan naji haushi nace na fasa bin ku kike faɗamin haka, kuma wallahi ahir ɗinki kin dai san bana fushi da wuri."

"Toh dama mutum marar zuciya ina shi ina fushi komin ɗacin a da za'a faɗa masa, kina ganin wannan Amirah ɗin koh kaɗan batada zuciya wallahi, ka gama faɗa mata magana iya son ranka amma koh a jikin ta, dallah kiyi sauri da wani rigar ki yawa wacce zata wasan ƴan bori koh kyau."

Ita dai Amirah bata kula ta ba, haka Anty Khadija tayi ta gaggasa mata magana duk dan taji haushi amma ita koh a jikin ta sai ma waƙar ta da take tana dariya.

A haka Jafar ya sake dawo ya same su nan yace "It's already 8:30 fah."

Miƙewa DEENAH tayi tana gyara zaman rigar jikin ta tace "Muje Yaya, ku same mu a waje."

Miƙewa Anty Khadija ma tayi tace "Toh su Amirah sai a iske mu a waje koh."

Tsaye Amirah tayi da kwalliyar da take tace "Dan Allah Yaya Jafar ka jira ni, wallahi na kusa kammalawa dan Allah."

Kallon ta yayi yace "Amirah, kafin mu wuce yanzu zan biya na ɗau Ruqayyah da siblings nata, and kafin mu ƙarasa dare zai iya yi, kin dai san kuma bama son dare yayi sosai mu dawo koh?."

"Shikenan bakomai kuje" ta faɗa cikin sanƴi tana barin bakin mirror ɗin.

"Alright, 5mins ya isheki ki gama shiryawa?" ya faɗa.

Kai ta jinjina masa tace "Eh wallahi yanzu zan idda na fito."

"Alright, make it fast."

"Kashh wallahi na ɗauka kinyi zuciya ne, ashe dai duk burga ce" faɗin Anty Khadija.

Hararar ta Amirah tayi tana komawa ta cigaba da kwalliyar ta.

DEENAH marawa Jafar baya sukayi zuwa ɗakin Umma dan yi mata sallama.

"Jafar kada fah ku daɗe" cewar Umma.

"Insha Allah Umma."

Kallon Umma DEENAH tayi tace "Umma gift ɗina fah?."

"Ai dai kya je ki dawo tukun koh?."

Murmushi tayi tace "Toh shikenan" tana marawa Jafar baya.

Ficewa sukayi daga gidan, motar sa da ta hango ne yasa ta kallon Jafar tace "Tare dashi zamuje?."

"Yeah ke dasu Amirah ni zan wuce ɗauko Antyn ki da siblings nata."

"Cha6 wannan yarinƴar ce Anty na, na fah girme ta."

"Well she is your Aunt then tunda yayan ki na sonta."

"No case then" ta faɗa tana yin gaba.

Da kallo ya bita yana murmushi kafin shima ya wuce motar sa.

Knocking tayi jikin glasses ɗin window ɗin dake a zuge, ɗan buɗe murfin motar yayi kafin ta ƙarasa buɗewa tana kallon sa.

Sosai ya haɗe cikin shigar shadda baƙa mai ɗinkin armless wacce tayi matuƙar amsar farar fatar sa sai zuba ƙamshi yake.

Tsayawa tayi kallon sa ba tare da ta shiga cikin motar ba.

"Come in" kawai ya faɗa staring at her.

Shigewa tayi tana rufo ƙofar kanta a ƙasa tace "Sorry, i kept you waiting."

"It's alright babe, shall we?."

Kallon sa tayi kafin tace "Su Anty Khadija basu fito ba, yi haƙuri dan Allah ka sake jira."

"Okay" kawai ya faɗa idanun sa kan steering.

"Are you Okay?" ta faɗa tana kallon sa.

Kallon ta shima yayi yace "Mai kika gani?."

"You look somehow different, kodai kayi fushi ne mun 6ata maka lokaci?."

"Not at all, by the way you look so gorgeous" ya faɗa cikin murmushi yana kallon ta.

"Thank you, kaima kayi kyau, thats because you wore my favorite color."

Murmushi yayi yace "And you always look beautiful koh da baki sanƴa favorite color ɗinki or wore make-up ba."

Kallon sa tayi cikin murmushi tace "You mean banyi kyau da make-up ba?."

Kallon ta yake yace "Of course kinyi kyau, but not as beautiful as your natural look."

Murmushi tayi kawai tana kauda kai tace "Gasu nan sun fito."

"Alright" ya faɗa yana tada motar.

Baya su Anty Khadija suka buɗe suka shiga tare da gaida shi ya amsa musu cikin sakin fuska.

Kallon DEENAH yayi yace "Shall we Ma'am?."

Kai ta jinjina masa cikin murmushi kafin yaja motar sukayi gaba.

Amirah dake ta rarraba idanu ne tace "Uhm kaga soyayya wai motar ma da zai ja sai ya tambaya ta, lallai DEENAH kin more."

Gwa6e bakin ta Anty Khadija tayi tana aika mata da harara.

Murmushi ZEEYAD yayi tare da kallon DEENAH yace "What's is she saying?."

"Don't mind her, ta ɗan zauce ne."

Murmushi yayi yana maida hankalin sa kan tuƙin da yake.

Satar kallon Anty Khadija Amirah tayi kafin tace "DEENAH kice yasa mana ɗan kiɗa mana, mota shiru haka biya."

"Wai ke miye haka ne?" faɗin Anty Khadija ƙasa-ƙasa kamar ta make ta, kafin kuma tayi kwafa tana kauda kanta.

Ta6e baki Amirah tayi haɗi da yin shiru sai rarraba idanu take har suka isa inda zasu.

Babban Event center ne mai kyau da tsaruwa, koh ina gauraye yake da hasken wutar lantarki kasancewar dare ne.

Wuri ya samu yayi parking motar, nan duk suka buɗe suka fito.

Amirah ce tace "Uhm lallai rabon da nazo wuri irin wannan ai tun auren Anty Salma."

Tsaki Anty Khadija taja dan kuwa ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba.

"Shall we?" ya faɗa nan duk suka juyo suna kallon sa, nuni yayi musu da hanƴar da zasu bi kafin ya shige gaba suna take masa baya.

Amirah ce tazo kusa da DEENAH tace "Ke DEENAH anƴa ba asirce wannan bawan Allahn kikayi ba kuwa?, wallahi ya haɗu Kafci."

Harara DEENAH ta zuba mata dan kuwa itama ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba, ta 6ata musu lokaci gata bakin ta baya iya yin shiru indai taga abu.

"Allah ya huci zuciyar ki, ni da ba dan nazo bama wallahi da sai na koma tunda naga sai wani gani-gani kuke yimin dake da Anty masifatu ɗin chan."

DEENAH dai bata kula ta ba har suka iso entrance ɗin hall ɗin da aka kama musu ɗin, yadda aka ƙawata wurin ba ƙaramin kyau yayi ba, style akayi wa wurin da balloons baƙaƙe ga kuma dim lights da suka sake ƙawata cikin wurin abin sai wanda ya gani.

Wow duk sukayi exclaiming bale ma Amirah da ta saki baki tana sake bin wurin da kallo.

Juyowa yayi ya kalli DEENAH yace "You have a seat, i will be back in a moment."

Kai ta jinjina masa tare da zama cikin kujerun da aka zuba a wurin tana sake bin ɗan daidaikun mutanen dake jeka ka dawo a wurin da kallo.

Fitar sa keda wuya Anty Khadija ta hau Amirah da faɗa "Ke wace iriyar banza ce Amirah, ke shikenan kwata-kwata ba zaki ta6a hankali ba, miye amfanin abinda kikayi yanzu ke koh kunƴa bakiji ba, shikenan ke baki baya iya yin shiru a komai, ai dama abinda yasa nace ba zaki bimu ba kenan sabida kwata-kwata bakida hankali ne amma sai ake ganin kamar banason ki ra6e mu ne, ke shikenan ba zaki ta6a wayewa ba kenan a rayuwa, kina komai kamar baƙauyiya, haba yaci ace kin gyara yanzun babu abinda kika nema kika rasa a gidan ku amma duk inda kikaje sai kin nuna ƙauyanci har inda mutanen ba zasu nuna miki komai bama, toh wallahi koh ki gyara koh mu yi ta samun matsala dake, wannan ai daƙiƙanci ne."

Shiru Amirah tayi kamar ba ita ce mai bakin surutu ɗazun nan ba.

Wuri Anty Khadija ta samu ta zauna ranta fal a 6ace.

Basu fi 5mins da zama sai ga Jafar ne tafe da wata kyakkyawar yarinƴa da ba zata wuci 17-18yrs ba, bayan su kuma wasu yara ne da ba zasu wuci 10yrs ba mace da namiji, da alama dai ƴan biyu ne yaran sabida yadda suke ɗan kama da juna.

Murmushi DEENAH da ta hango su tayi tana miƙewa ta nufe su zuciyar ta fal farin ciki tace "Yaya itace?."

"Yeah" ya amsa mata cikin murmushi.

"Wow tafi kyau a zahiri akan a cikin hoto" ta faɗa tana kallon yarinƴar.

Murmushi itama yarinƴar tayi tace "Ina wuni?."

Kallon Jafar DEENAH tayi kafin ta amsa mata gaisuwar cikin ɗan dariya, kafin kuma ta riƙo hannun ta tana nuna mata seat ta zauna da ita da ƙannen nata.

Kallon su Anty Khadija yarinƴar tayi ta gaida su cike da girmamawa suka amsa mata.

Kallon DEENAH Jafar yayi yace "Where is he?."

"Ahm, yace min zai dawo yanzu."

Kai ya jinjina yace "Okay, you wait here i will be right back, Okay?."

"Okay" ta amsa masa kafin shima ya bar wurin.

Jafar bai daɗe da barin wurin ba ZEEYAD ya dawo, duk zuba masa ido sukayi suna kallo har ya wuce wurin DEENAH ɗin, ɗan duƙawa yayi yana yi mata magana a kunne kafin ya ɗago yana kallon fuskar ta.

Kai ta jinjina masa tana miƙewa tsaye, kallon Anty Khadija tayi tace "Dan Allah Anty Khadija zamuje mu dawo yanzu, ki kular min da baƙin nawa."

"Okay toh, bakomai" ta faɗa.

Kallon sa tayi tace "Muje."

Mara mata baya yayi suka wuce, yayin da duk suka bisu da kallo, Amirah magana ne fal a bakin ta sai dai ganin kada Anty Khadija ta sake dizga ta a gaban budurwar Jafar ne ya sanƴa ta tsuke bakin ta tayi shiru.

Waje suka fito nan ya kalle ta yace "Actually, i have nothing to said."

"What?" ta faɗa tana kallon sa.

Shafo lallausar sumar kansa yayi cikin murmushi yace "I just wanna spend some time with you alone."

"You're unbelievable" ta faɗa.

"Am i?."

"Without a doubt."

"Alright, muje chan na saya miki sweet-cotton" ya faɗa yana nuna mata wurin wani mai saida sweet-cotton a farfajiyar wurin.

"It's my birthday, we should be celebrating, dare yana yi fah."

"Yeah we will celebrate, but atleast we should have a little date here."

Folding hannaye tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba.

"Shall we?" ya faɗa yana kallon ta.

"Yeah, but muyi sauri kar mu 6ata musu lokaci."

"Alright" ya faɗa yana miƙa mata hannun sa, da kallo tabi hannun nasa kafin kuma ta miƙa masa nata hannun yana riƙewa cikin nasa suka fara tafiya.

Isowa wurin sukayi nan ya kalleta yace "Tsinke nawa kike so?."

"Kasan ni ba wani shan sa nake sosai ba, koh da muna yara ma idan baban-bola yazo ni ban cika amsar sweet-cotton ba, tsinke ɗaya ya ishe ni."

"Really?, ba shida auki fah" ya faɗa yana kallon ta.

"Yeah ni ba dayawa nakeso ba."

"Alright" ya faɗa yana ciro wallet ɗinsa, wayar sa da tayi ƙarar shigowar message ya ciro yana miƙa mata wallet ɗin yace "Pay him" yana yin gaba.

"Nawa ne kuɗin?" ta tambayi mai saida abin.

"Ɗari biyar ne Hajiya" ya amsa mata.

Baki sake take kallon sa tana sake maida duban ta kan tsinken sweet-cotton ɗin.

Shiru tayi kawai tana ciro 1k ta miƙa masa tace "Toh ka kawo biyu."

Tsinke biyu ya ɗauko yana miƙa mata ta amsa kafin tace "Nagode" tana juyawa ta tayi inda yake tsaye.

Wallet ɗinsa ta miƙa masa ya amsa tana bashi tsinke ɗaya.

"No bana shan zaƙi" ya faɗa.

"What, why?."

"I just don't like ire-iren abubuwan nan, it's for kids like you."

Kallon sa take kafin tace "Kids, you mean am a kid?."

"Yeah, i can't believe sai yau kike cika 20yrs."

"Kids are children's below 10, and am 20."

"Well then that doesn't make any difference, believe it or not you're still a Kid."

"No am not."

"What are you then, a teenager?."

Something similar to that" ta basa amsa.

Murmushi yayi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba har suka iso inda suka bar su Anty Khadija zaune.

"Where

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login