Showing 165001 words to 168000 words out of 236327 words

Chapter 56 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45316

cakes ɗaya kuma cookies ne aciki.

Cup ta ɗauka ta tsiyaya masa lemun 5alive ɗin tana miƙa masa, amsa yayi still idanun sa a kanta.

"Ni ka daina kallo na haka kayi harkar gaban ka."

Ɗan murmusawa yayi yana kai hannu ya ɗauko cup-cake ɗaya "Ohh so soft" ya faɗa yana latsa cake ɗin.
Itadai bata ce dashi komai ba har ya kai cake ɗin bakin sa.

Tauna ɗaya yayi mata ya gimtse fuska yana saurin ɗagowa ya kalleta da idanun sa da suka fara canza launi.

"What, menene?" ta faɗa staring at him.

Runtse idanu yayi yana jin yadda kansa ta fara juyawa.
"Are you Okay?" ta sake faɗa tana kallon sa.

Idanun sa a runtse ya kasa buɗewa haka ma ya kasa taune sauran na bakin shi.
"Meke damunka ne wai?" ta faɗa cikin ɗan fara tsorata da yanayin shi.

Da hannu ya nuna mata cake ɗin ba tare da ya buɗe idanun sa ba "baiyi daɗi bane?" ta faɗa cikin kallon sa.

Da kyar ya iya girgiza mata kai "Yayi sugar dayawa?" ta sake tambayar sa, nanma kai ya girgiza mata, shiru tayi tana kame-kame cikin zuciyar ta dan kuwa ta rasa nayi, da sauri tace "Amai kakeji?" saurin jinjina mata kai yayi.
"Alright, come on let me help you" ta faɗa cikin tashi tsaye tana zuwa ta riƙo shi tsaye, dakyar ya iya miƙewa hannayen sa kan kafaɗun ta ta kai shi toilet ɗin cikin falon

"Alright, spit it out" ta faɗa cikin patting bayan shi gently, sunkuyar da kansa yayi yana tofar da na cikin bakin nasa, ruwa ta tara tana sanƴa masa ya kurkure bakin sa kafin ta wanke masa fuskar shi tana ɗago shi "Are you Okay now?" ta faɗa tana kallon sa

Kai ya jinjina mata still idanun sa a lumshe, taimaka masa tayi suka fito daga banɗakin tare da taimaka masa ya zauna gently, da gyalen jikin ta ta hau goge masa fuska, tana ɗan tatta6a goshin sa da ya ɗanyi zafi.

Sosai zuciyar ta ta cika da tsoro dama kuma mamakin abinda ya same sa daga sanƴa cake a baki.

Cikin ɗan galabaita yace "I...i...need a nap."

"You can sleep here" ta faɗa cikin damuwa tana kallon sa.

Da kyar ya iya buɗe idanun sa da suka ɗanyi jaa yana kallon ta, a hankali yace "Help me get to my car."

"Zaka iya kwanciya anan" ta faɗa, "No" ya bata amsa a hankali.

Tashi tayi tana riƙo hannun sa ya tashi, kafin su fara tafiya, ganin yana tangaɗi kamar mai jin hajijiya ne ya sanƴa ta saurin riƙe sa sosai suka fice daga falon ta ɗayar ƙofar.

Har motar sa dake waje ta kai sa ta buɗe seat ɗin baya tana taimaka masa ya shiga, kafin ta rufe tana komawa ta ɗayan gefen ta shige, kallon sa take with pity dan kuwa batasan menene ya haddasa masa losing control ɗin kansa suddenly haka nan ba, ganin kamar akwai zafi ne ya sanƴa ta kunna ac ɗin cikin motar tana riƙo hannun sa cikin nata.

Yadda take yi masa ɗinne ya sanƴa bacci ɗaukar sa nan take.

Kyakkyawar fuskarsa ta ƙurawa ido tana kallo, ɗan murmusawa tayi kafin ta rungumo hannayen sa tana ɗaura kanta a kafaɗun sa.

Ta san tabbas ƙaddara ce ta haɗa su idan ba haka ba babu ta yadda za'ayi ta haɗu da kamar sa, he is one in a million, ya tara komai, kama daga kyau, nasaba, arziki, addini, kwarjini da dai sauran su, sai dai with dukkanin abubuwan nan da ya tara hakan bai sanƴa shi looking so down akanta tare da ƙin ta ba, he loves her wholeheartedly and ready to sacrifice duk wani abu duk dan ya mallake ta, at first she thought koh ta rasa shi kenan har abada but a yanzu ta fahimci cewa ita ɗin ƙaddarar sa ce tunda ƙaddarar ce ta haɗa su, dah ba dan ƙaddara ba there is no way da zata haɗa koh da inuwa ɗaya ne dashi.

Ɗagowa tayi tana sake kallon fuskar sa kafin kuma ta sake maida kanta tana lumshe idanu.


********************


_______"Yes, and what about this?" ya faɗa yana kallon ta.

Cikin rawar murya take kallon sa da idanun ta da suka tara hawaye tace "It...it was a picture of them together."

"A'ina kika samo shi?."

"Kawomin akayi."

"Who?" ya faɗa yana kallon ta.

"I don't know, kawai dai an bawa maids ne su kawomin suma sunce basu ga fuskar wacce ta kawo musu ba."

Sake duba hotunan hannun nasa yake kafin ya sami wuri ya zauna yana faɗin "I don't think wannan is something to worry about JALILAH."

"You don't think, she is your girlfriend isn't she, and he..." shiru tayi ta kasa iddawa.

"And he is what, look JALILAH i guess is time da yakamata ki fahimci cewa ZEEYAD has no taste akanki, yana kula ki ne kawai for his Grandma's sake."

"What?, ya zaka ce haka, he loves me" ta faɗa idanun ta na tara kwalla.

Kallon ta yayi yace "No he doesn't."

"Ofcourse he do, and DEENAH is she not your girlfriend?."

"No she was my girlfriend."

"Mai kake nufi da she was?."

"Listen JALILAH, I know you may find this strange, but maganar gaskiya is that ZEEYAD and DEENAH have known each other for a very long time now, ita ce first love nashi."

"What do you mean, that can't be possible."

"Nothing is Impossible JALILAH."

"But how did you know that, ya akayi kasan hakan?."

Shiru yayi yana sake kallon photon hannun sa yace "Ranar da aka ɗau hoton nan, i accidently bumped into them and over-heard their conversation, they know each other for a very long time, bansan menene sanadiyyar rabuwar su ba, i can't believe ZEEYAD yayi ƙoƙarin sadaukar da farin cikin sa just because of me, i can't believe how stupid he was na ganin yayi sacrificing love nasa just to see me happy, DEENAH belongs to him and he chose ya barmin ita and decided ya 6oye komai daga gareni, but i can't endure ganin hakan ta faru, that is why na yanke decision ɗin haƙura da DEENAH not just because akan kalaman Ummie na but because of my brothers happiness."

Sosai jikin JALILAH yayi sanƴi tanajin zuciyar ta na karyewa, cikin rawar murya tace "I can't believe you did this to me, i love him and you decided to re-unite him with his Ex."

"She isn't his Ex JALILAH, they are inlove, he loves her so very much more than anything you can imagine JALILAH, how then kike tunanin na shiga tsakanin su tare da datse farin cikin su after inada mafita, wanda bai wuci na basu space suyi rayuwar su yadda yakamata ba, they love each other JALILAH and they are happy together, so there is nothing i can do da ya wuce na sake uniting ɗinsu."

Kuka JALILAH ta fashe dashi inda ya ɗago yana kallon ta, ajiyar zuciya ya sauƙe nan yace "You have to take heart JALILAH, i know it's not easy ace kanason mutum kuma shi ba hakan bane a ransa."

"But he is all my hope, a wurin sa da Grandma kaɗai ne nake samun farin ciki, i just can't do without him."

"Well then dole ki koyawa kanki cewar bakomai ne kake so kuma ka same shi, sometimes wasu abubuwan ba alkhairi bane a gare mu, so dole sai munyi haƙuri mun rungumi yadda Allah ya tsara mana rayuwa no matter how worst it is."

Cikin gudu ta fice daga falon tana cigaba da rera kuka, da kallo ya bita kafin kuma ya ɗan ta6e baki.

Part ɗin Grandma ta nufa tana cigaba da kuka, Grandma dake zaune tana duba wasu sabbin kaya da aka kawo mata ta saya ɗagowa tayi da sauri tana kallon JALILAH dake kuka.

"Subhanallah, Allah kasa dai kukan alkhairi kike, zo nan mai ya sameki?."

Ɗagowa tayi da idanun ta da sukayi sha6e-sha6e da hawaye tace "Akhi ne..."

"Wane Akhi ɗin, ba sai Sooraj ba koh?" cewar Grandma cikin waro idanu.

Kai ta girgiza tana cigaba da kuka.

Kallon mutanen da suka kawo mata kayan tayi tace "Ku ɗan sallame mu."

Cike da girmamawa suka tashi tare da ficewa daga falon.

Kallon ta Grandma take tana cikin share mata hawaye tace "Faɗamin ina jinki, meke damunki?."

"Akhi, dama ba sona yake ba?."

"Ban fahimce ki ba, Boy kike nufi kowa?."

Kai ta jinjina tana kallon Grandma.

Murmushi Grandma tayi tace "Ka jiki dai da wani magana, yana sonki mana, maiyasa kike wannan tunanin, wa zai ƙi kyakkyawar ƴa kamar ki."

"Bu... but YAZEED ne yace min ba sona yake ba, yana da wacce yake so."

"Ki jiki kuma du, indai akan wannan maganar ne ki share hawayen ki ki daina kuka, insha Allah Boy mijin ki ne, kuma na tabbata yana sonki har cikin zuciyar sa, ki bar damun kanki kinji?."

Kai kawai ta ɗagawa Grandma ba wai dan hankalin ta ya kwanta ɗin ba.

Rungumo ta Grandma tayi tana cigaba da kwantar mata da hankali.

*******************

"Seems like you've lost your stupid mind YAZEED, a matsayi na ta mahaifiyar ka nake umartar ka da kaje kaga yarinƴar nan, ƴa ce ga tsohuwar aminiya ta,am sure you will like the girl sabida tafi wancan abar da ka kawo a farko komai, amma kazo kana cemin ba zakaje ba, how dare you?."

"Please Ummie i guess kin nuna batayi miki ba kuma nace na haƙura da ita koh, toh dan Allah na roƙe ki kada ki sake maganar ta ya isa haka nan."

"Whatever, miye ma zan ƙaru dashi idan nayi maganar asararriyar?, you just do what i asked of you muddin ba so kake ka fuskanci fushi na ba."

Cike da ƙosawa yace "Fine, fine then i will do whatever you asked of me, ba so kike ki haɗa ni aure da ƴar aminiyar ki ba, then bakida case da wannan, you can do whatever you think is right, but mind you... duk wani abu da ya biyo bayan hakan don't blame me for it."

Murmushi tayi kafin tace "That sounds good, ka shirya gobe kaje kaga yarinƴar na riga da na sanar da mahaifiyar ta and they are ready to welcome you anytime, just don't messed things off idan kaje ka, behave like a real good boy mai bin umarnin mahaifiyar sa, and yes... ka tabbata kaje musu da kayan alatu dan sake tabbatar da cewa ba gidan ƙananun mutane zasu bada ɗiyar su ba, koh dayake ka bar komai a hannu na i will take care of that, kai dai ka zamto a shirye kake zuwa gobe, clear?."

Shiru yayi zuciyar sa na ƙuna kamar ba zai amsa ba kuma ya buɗi baki dakyar yace "Yeah."

Murmushi tayi tace "Good" juyawa tayi ta fara tafiya, sai da ta kawo bakin ƙofar fita ta tsaya ba tare da ta juyo ba tace "Ƙannen ka zasu dawo sati mai zuwa, so be ready to welcome them" tana faɗin haka ta fice. _(Idan baku manta ba a first page munyi mention ƴaƴa shida mai Martaba ke dashi, soon sauran zasu bayyana)_

Huci ya fesar yana naushin table ɗin gaban sa yace "Fuck your friend and her damn family."

********************

________Idanun sa da suka ɗanyi masa nauyi ya shiga warewa a hankali, numfashi ya sauƙe yana bin hannun ta dake sarƙe da nashi da kallo.

Motsa hannun sa yayi yana squizing ɗin hannun ta, hakan ya sanƴa ta fara buɗe ido a hankali, kafin kuma ta ɗago da sauri tana sauƙe idanun ta cikin nasa.

"You're... alright?" ta tambaya cikin tatta6a goshin sa.

"Yeah am fine actually, am fine" ya faɗa.

Lumshe idanun ta tayi tana sake ware su tace "You scared me... i have never seen you like this."

"Not as much as you scared me lokacin da baki da lafiya."

Kallon sa take kafin kuma ta ɗan saki murmushi tace "But tell me, what happened to you, da akwai wani abu a cikin cake ɗinne da baiyi maka ba?."

"Who made the cake?" ya tambaye ta.

Shiru tayi na ƴan seconds kafin kuma tace "Actually siyowa mukayi a wani gida daga ƙasan street ɗinnan, it's just that naga babu daɗi ne na barka babu abin da zaka ta6a, so Anty Khadija tayi mana ordern shi daga gidan su ƙawar tata."

"What, you went out dressed like this?" ya faɗa cikin haɗe fuska yana kallon ta.

Kallon kanta tayi kafin kuma ta kallesa tace "No i can't go out dressed like this."

Lumshe idanun sa yayi kafin yace "Actually nayi perceiving kwai a ciki ne, thats why kika rasa gane kaina, i don't like egg."

"Oh God, you're allergic to egg na tuna hakan, you once told me cewa baka cin kwai."

"Not allergic though tunda baya fito min da sign a jiki."

"I guess duk ɗaya ne, coz yana cutar da kai, but the egg is disolved how comes kuma ka iya ganewa akwai kwai a ciki?."

"I can smell it no matter how tiny kika sanƴa shi cikin girki, it's smell makes me go a little wild crazy."

"Am so sorry" ta faɗa kamar zatayi kuka.

"For what?."

"For being so stupid na manta da cewar baka cin kwai, it's because of me that you're in this state."

"Oh come on baby, why the cry?" ya faɗa hugging her lightly."

"Am sorry" ta sake faɗa.

"It's alright babe you did nothing wrong" ya faɗa giving her a light peck a forehead.

Ɗagowa tayi tana kallon sa, nan ya shiga goge mata hawayen fuskar tata, kumatun ta duka biyu ya kama yaja tare da faɗin "Cry cry baby."

Murmushi tayi tana 6oye kanta kan faffaɗar kirjin shi.

"Thank you so much baby, for taking a good care of me" ya faɗa calmly cikin murmushi.

Shiru tayi ta lafe kawai tana sauraron bugun zuciyar sa haɗi da shaƙar daddaɗar ƙamshin dake tasowa a jikin sa, bata ƙi ace sun dawwama a haka ba, dan kuwa har wani irin bacci mai daɗi taji yana zuwan mata.

Jin tayi shiru kuma taƙi ɗagowa ne ya sanƴa shi faɗin "Babe, bacci?."

DEENAH buɗe lumsassun idanun ta tayi tana ɗagowa tare da zuba masa idanun ta da sukayi kama da na mai jin bacci.

"Bacci kikeji?."

Kai ta jinjina masa kawai, nan yace "Alright, you should go back inside, i will be back anjima."

Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "Are you sure ka warware, can you drive?."

"Yeah, am fine yanzu" duba agogon hannun sa dake nuna 12:23 pm yayi kafin kuma ya kalleta yace "I will be back at night."

"Alright" kawai ta faɗa tana murza idanun ta.

Buɗe murfin motar duk sukayi suna fitowa, inda ya shige gidan gaba, waving tayi masa da hannu tare da yi masa addu'ar Allah ya tsare, kafin ta juya ta shige cikin gida.

Sai da yaga shigar ta gidan kafin ya tada motar sa ya bar wurin.





_*Ayi haƙuri da wannan, zazza6i ke son kama ni, kuyi addu'ar Allah ya kawar dashi daga kaina zuwa kan LATEEFAT dan kuwa sati ɗaya kenan bata comment tsabar samun wuri irin nata🙄🤧*_





*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[8/19, 10:37 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*044...*



_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




_*NOT EDITED*_




__________Motoci ne kusan huɗu a jere suka shigo cikin MASARAUTAR kowanne na samun gurbin parking.

Bai wuci da ƴan sakonni da tsayuwar su ba driver ɗin dake jan motar da ta kasan ce ta biyu a jerin huɗun ya fito da hanzarin sa yana zuwa ya buɗe murfin motar kamar zai kife ƙasa tsabar hanzari da yadda jikin sa ke rawa.

Tunkuɗe driver ɗin yayi da ƙafar sa yana mai fitowa daga cikin motar, kyakkyawan saurayi ne sosai wanda ba zai wuci 25yrs ba ya fito fuskar nan tasa a wani irin mugun tsuke, yana sanƴe cikin shigar ƙananun kaya irin ta ƴan gayun zama ni wanda sukayi matuƙar kar6ar sa tare da amsar fatar jikin sa, hannu ya sanƴa tare da cire baƙar shade ɗin idon sa yana mai sake bin farfajiyar MASARAUTAR da kallo, chan ƙasan maƙoshi ya "Wow" yana barin jikin ƙofar kafin driver ɗin ya maida ta ya rufe.

"OMG!, this place is so fucking hot" cewar wata ƴar matashiyar budurwa dake ƙarasowa kusa dashi cikin rangwaɗa tana fifita da hannun tana wani irin yatsine fuska, sosai na ƙare mata kallo, tundaga kan curly dyed gashin kanta har izuwa kan doguwar takalmin da take sanƴe dashi, kyakkyawa ce sosai ba laifi, inda itama ke sanƴe cikin shigar ƙananun kaya, doguwar riga irin ta turawa wacce bata wuce mata guiwa ba, ƴar matashiyar budurwa ce da ba zata gaza shekaru ashirin ba.

Kallon ta saurayin yayi kafin yace "Seems like mutanen nan basu wani damu da dawowar mu ba, nobody even cares da zuwa tar6ar mu."

Yatsine fuska tayi kafin tace "Damn them, let's find our way inside."

Kallo yake ƙarewa farfajiyar inda suke tsaye yana kallon yadda bayi maza da mata kowanne ke fice da shige.

Daga nesa macen ta hango mahaifiyar su tafe kuyangun ta na take mata baya, nan tace dashi "Seems like she is happy da ganin dawowar mu."

"She looks a bit kind of Old."

Ɗan dariya tayi tana ƙarasawa wurin mahaifiyar tata.

"What kind of beautiful Mom i have got" ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login