Showing 54001 words to 57000 words out of 236327 words

Chapter 19 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45353

tayi suka nufi wurin har zuwa hawa na uku.



Sosai floor ɗin ya sha tsaruwa da haɗuwa, ɗaki na uku ya nufa tare da danna wasu codes ƙofar ta buɗe da kanta suka kutsa kai ciki.



Zaune ta ganta da wani ɗingilelen riga sai kuma matsetsen mini-skirt a jikin ta tana daddana waya.



Sosai ƙaton ɗakin ya ƙawatu da abubuwan motsa jiki kala daban-daban. (Nidai ba sanin sunan su nayi ba balle na lissafo muku su🥴).



Daga chan ƙarshen ɗakin yake zaune cikin gym wears ɗinsa baƙaƙe har takalmin ƙafar sa, yana motsa hannun sa da wata nannauyar ƙarfe.



Ganin ta yasa shi ajiye ƙarfen nan yana sake tsuke fuska a zuciyar sa yace _Am just sick of seeing her everyday_ tare da kauda kai kamar bai gansu ba.



Samun kujera tayi ta zauna akai tana kallon Surayya da kallo ɗaya kawai tayi musu tare da kauda kanta zuwa ga wayar ta.



"Excuse me ma'am, please ina sir yake?" faɗin Jafar ɗin yana tambayar Surayya dan kuwa bai ga ZEEYAD ɗin ba.



Kamar ba zata amsa masa ba tace "Yana chan ciki."



"Come on" ya faɗa yana kallon DEENAH, nan ta tashi tare da mara masa baya.



"Who is she?" DEENAH ta faɗa cikin hankali.



"Shushh" kawai ya faɗa suna ƙarasawa chan ciki.



Zaune suka same sa inda Jafar yace "Sir."



Ɗagowa yayi ya kalli Jafar nan ya tashi tsaye yana ajiye abinda yake motsa hannun nasa yace "I told you kada ka sake kawomin ita nan."



"Sir tanason yin magana ne da kai."



Wucewa kawai yayi yana ɗaukar ƙaramar toilet ya shiga goge fuskar sa.



Nan duk suka mara masa baya.



Ruwa Surayya ta miƙa masa nan ya amsa tare da furta "thank you" yana samun wuri ya zauna.



"Sir maybe i should get going" juyawa yayi ga DEENAH yace "Idan kin gama kizo ki same ni" ya faɗa yana shirin wucewa.



Riƙo sa tayi tace "Ka tsaya na bashi sai ka tafi" ta faɗa a hankali.



"DEENAH baki ga na bar mutane dayawa suna jira na ba?, idan kuma so kike muje mu dawo bayan na sallame su shikenan."



Sakin sa tayi tace "Okay."



Murmushi yayi ya wuce yana ficewa.


Tsaye tayi a kansu kamar wacce aka dasa tana bin su da kallo ta ƙasan ido.


Sosai take mamakin ganin sa tare da christian, bayan ya gama ci mata mutuncin tana bin maza amma yau ga shi tare da karuwa a wuri ɗaya.



Muryar Surayya ta tsinkayo tana faɗin "Babe, jibi birthday ɗina, what kind of gift are you buying me?."



Ɗan ɗagowa tayi ta kalli Surayya ɗin kafin kuma ta sake sunkuyar da kai.



Ɗan satar kallon DEENAH yayi yace "What do you want?."



Cike da zumuɗi Surayya tace "Really, kana nufin duk abinda nakeso?."



"Yeah" ya faɗa.



"Alright, tunda kace haka so nake ka turo gidan mu a sanƴa mana ranar aure" ta faɗa cikin murmushi.



Kallon ta yayi shima yayi murmushin yace "Done."


"Oh really?, Oh my GOD thank you, I love you" ta faɗa cike da jindaɗi tana tasowa daga inda take zaune ta rungume shi.



DEENAH ji tayi wani irin abu ya tokare mata zuci nan tace "I want to talk to you."



Murmushin gefen baki ZEEDAN yayi yace "Talk."



"Not here" ta faɗa kamar zatayi kuka.



"Not here, a'ina kenan?."



"Maybe somewhere else."



"What do you want from me, i told you that i despised seeing your face, didn't i?."



Shiru tayi tana kallon sa da Surayya da har yanzu bata bar jikin sa ba tace "Fine then, am leaving" ta faɗa tare da juyawa da niyyar barin ɗakin.



Da sauri ya ture Surayya dake jikin sa yana aika mata da wani irin mugun kallo kafin ya maida duban sa gun DEENAH dake kiciniyar buɗe ƙofar amma ta kasa.



"Kin manta ne sai kin sanƴa code kafin ƙofar ta buɗe?."



Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba zuciyar ta nayi mata zafi.



"Come let's talk then" ya faɗa yana juyawa yayi inda ya fito.



Juyowa tayi tare da mara masa baya tana satar kallon Surayya dake bin su da kallo.



Tsayawa yayi tare da zuba hannaye cikin aljihu yace "Tell me."


Ɗago da watery eyes ɗin ta tayi ta zuba masa, taune le6e yayi tare da kawar da kai gefe.



Goge hawayen nata tayi tace "Inaso na baka wani abu mai muhimmanci but you aren't ready to listen to me."



Ta ƙasan idanu ya kalle ta nan yace "Something important?" he then chukles and said "You have nothing important to give me, wait" ya faɗa yana kallon ta kafin ya ɗaura da faɗin "Something important kina nufin kin jawo ni nan ne dan ki danne ni kiyimin abinda kika saba?, i see nothing important left in you..."



"Stop this, stop it, i have had enough of this, maiyasa kake danganta ni da irin mummunar abin nan ne?."



"Because that's what you're."



"Kana yi min abubuwan nan ne duka dan kawai kanajin haushin 6atar sarƙar ka da nayi sanadiyya right?" ta faɗa cikin sanƴin murya.



Magana zaiyi nan ta ciro sarƙar tana nuna masa.



Da sauri ya kai hannu zai ɗauka tayi saurin damƙe shi a hannun ta tana kawar dashi.


"My..m..my...that's my Necklace" ya faɗa cikin rarrabewar harshe idanun sa akan hannun nata yana ƙoƙarin kar6a.



Sake damƙewa tayi a cikin hannun ta tace "Sabida shi ne ka tsane ni kuma baka son gani na isn't it?, ka faɗamin baƙaƙen maganganun da sukayi matuƙar ƙona min zuci duk dan abinda ya faru shekaru goma da suka wuce."



"Give it" ya faɗa.



"Zan baka sabida mallakin ka ne, but you've to admit your mistake for insulting me first, and you've to apologise."



Wani irin kallo ya zuba mata jin abinda ta faɗa, wato ya bata haƙuri.



"Apologise now" ta faɗa tana kallon sa.



Iska ya furzar yana sake kallon ta from down to top.



"Kana targeting yadda za'ayi ka kwace ne, toh ba zaka iya hakan ba, sabida ba zan bari ba nima har sai ka bani haƙuri."



Resting bed ɗin dake wurin ya samu ya kwanta yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da lumshe idanun sa.



Mamaki ne ya kama DEENAH nan tace "Do you think am joking, ba zan baka ba har sai ka..."



"Toh ki bushe tsaye anan mana" ya faɗa kafin ya sake lumshe idanun sa.



"What!?" ta faɗa.



"Alright then, am leaving" ta faɗa tana juyawa ta bar wurin tare da nufar ƙofar direct da niyyar buɗewa ta fita.



Ji tayi wani irin kunƴa ya zubo mata, dan kuwa batasan pin ɗin buɗe ƙofar ba.



Satar kallon Surayya dake bin ta da kallo tayi kafin kuma ta sake jan ƙafafu ta koma inda yake tare da yin tsaye akan sa.



Fuskar sa ta ƙurawa idanu tana kallo babu koh kyaftawa tana jin wani abu na taso mata daga ƙasan zuciya tare da bin surar jikin sa da kallo.



Saurin kauda idanun ta tayi nan ta tsinkayo muryar sa yana faɗin "Da alamu zaki iya yi min fyaɗe da wannan kallon da kike yimin ɗin" ya faɗa yana tashi zaune.




"Give me the Necklace" ya faɗa yana kallon ta daga zaunen da yake.



"Apologise first" ta faɗa.



Kai ya jinjina yana miƙewa tsaye kamar mai shirin make ta hakan yasa ta jan baya da sauri.



"What?" ya faɗa yana kallon ta.


Tsuke fuska tayi tace "Ka buɗemin ƙofa."



Murmushi yayi jin yadda tayi maganar nan yace "Na buɗe miki ƙofa while kuma kina riƙe da farin ciki na, do you think kwakwalwa ta irin naki ne?."


Matsowa yayi kusa da ita yace "give me the Necklace."



6oye hannun sarƙar tayi a bayan ta tana sake tsuke fuska.



"Give it" ya sake faɗa.



Sake matsowa yayi daf da wanda har yana jin sauƙar numfashin ta akan fuskar sa yace "Give me the Necklace or else i will kiss you."



Da sauri ta ɗago ta kallesa, nan take kuma hawaye ya taru a idanun ta, kwafa tayi tare da ciro hannun daga bayan ta ta buɗe masa.



Tsaya kallon Necklace ɗin nasa yayi yana murmushi kafin ya sanƴa hannu ya ɗauka tare da sumbatar sa.



"Finally, you're now back to me, 6arawo kuma yaji jiki" ya faɗa yana damƙe sarƙar a hannun sa.



Magana zatayi nan yace "Don't you dare say anything, so kike ki musa kice ba sata kikayi ba right?, i know abinda kike shirin faɗa kenan, can you remember ten years back lokacin da kike kallon sarƙar since from that day na fara zargin yayi miki kyau kuma kike son satar sa, but you know what a kullum bana gajiya da sallahn dare akan Allah ya bayyanar min da 6arawon sarƙa ta, then boom finally ashe kece."



"I didn't steal it."



"Ohh really, kuka zakiyi?, koh dayake dama marasa gaskiya idan aka carke su a lungu sun iya ƙirƙiro kuka dan aji tausayin su, but that won't work on me."



Wucewa zatayi nan yayi saurin dafa bangon yana tare ta yace "Where do you think you're going?, am not done with you yet."



"Mai kuma kake so?."



Shiru yayi yana kallon ta yadda hawaye suka taru a idanun ta, kafin kuma cikin calm voice nasa yace "Thank you."



Da sauri ta ɗago da idanun ta tana kallon sa, nan ya sake faɗin "You returned my Happiness to me, so ya zama dole na gode miki, and i can't believe yadda kika iya ajiyan shi har tsawon wannan lokacin, you're unbelievable and amazing."



Batasan sadda murmushi ya su6uce mata ba, nan ta share hawayen ta zuciyar ta fal da farin ciki.



"I guess i should gift you something."



Ɗago da idanun ta kawai tayi tana kallon sa nan yace "Tell me, tell me dukkanin abinda kikeso and i promise to give it to you no matter how expensive it is, koh da kuwa ba anan ƙasan yake ba i promise to get it for you komin nisan inda yake" ya ƙarashe yana kallon cikin idanun ta.



Sunkuyar da kai tayi tana murmushi ba tare da ta iya cewa komai ba.



"Hey look, don't be shy Okay, just tell me dukkanin abinda kikeso, please" ya faɗa pleadingly.




"Kayi alƙawarin dukkanin abinda nakeso zakayi min shi."



"Yeah i promise."



"I...i...i..."



"Come on tell me" ya sake faɗa.



"I...i want..."



"You want what, get away from her" ta faɗa tana janƴe ZEEDAN ɗin, tare da ɗaukar hannu tana shirin kwaɗawa DEENAH mari taji cak hannun nata a sama.




ZEEDAN tabi da kallo tace "You're mine, you have to understand that, who the hell is she?" ta faɗa kamar zata shaƙo DEENAH da tayi tsuru-tsuru da idanu.




Sakin hannun nata yayi yace "Are you trying to raise your hand on her, infront of me?" ya faɗa cikin 6acin rai.



Kallon DEENAH tayi tace "Ke, who the hell do you think you're?, why are you so closed to him, he is my Man, no one else can have him, understand?" ta faɗa tana nuna DEENAH da tayi tsuru-tsuru da idanu tsoro fal a cikin idanun ta da yatsa.



"Do you wanna know who she is?" ya faɗa calmly cike da kwanciyar hankali yana samun wuri ya zauna.




Murmushi yayi yana kallon DEENAH yace "She is that little cutie."



"Look ZEEDAN, ya kake behaving as if nothing big is wrong here?."



Kallo ya ƙare mata tsaf yace "Babu wani babban lamari dake faruwa anan, if you want something big to happen then just try raising your hand on her."



"ZEEDAN you're mine..."



"Am not yours, and i will never be yours Surayya" ya faɗa cike da mugun jin haushin ta.



Zuwa tayi ta zauna kusa da shi tana kamo fuskar sa tace "Look ZEEDAN, ka ƙaremin kallo da kyau babu abinda yarinƴar nan zata nunamin, she is not that beautiful, na fita komai why don't you just concentrate on me?."



Tashi tsaye yayi ya ƙarasa gaban DEENAH da duk hawaye ya gama wanke mata fuska yace "Who told you that?, only i can see how beautiful she is, her wide captivating innocent eyes and how her cute her face is, only i can see that, i don't care whether kin fita kyau or ta fiki all i know is that babu wacce nakeso a cikin ku, so why all the misunderstanding, she is not my girlfriend i told you to stop stressing yourself like this, you're just wasting your time on me" ya ƙarashe yana juyowa ga Surayya ɗin.



"Lies, you're lying to me" cewar Surayya.



"Alright then, continue wasting your time pursuing me" ya faɗa yana yin gaba.



Da sauri ta mara masa baya.



DEENAH kuwa ta rasa mai takeji a zuciyar ta, ta rasa daɗi zata ji koh haushi.



Zubewa tayi zaune anan wurin tana sakin silent kuka.



Sai da ta ɗanyi mai isar ta kafin ta goge hawayen ta ta miƙe ta bar wurin.



Tsaye ta gansu shi da Surayya da ta ƙanƙame sa ta baya tana kuka fuskar nan tasa a matuƙar murtuƙe.



Wucewa tayi zuwa bakin ƙofa ta tsaya ba tare da tasan abinda zatayi ba, dan kuwa batasan code ɗin buɗewa ba.



Juyowa tayi ta kallesa nan taga shima ita yake kallo, saurin kauda face nata tayi tana sake jin zuciyar ta na zafi, haushin sa da na yarinƴar da taji ya ƙira da Surayya wacce sam batayi kama da musulmai ba duk ya gama cika mata zuci.



So kawai take ta tafi ta daina kallon su koh zata ji sassauci a ranta.



_Ashe haka Balarabe yake bashi da kunƴa koh kaɗan, i thought he is a good guy_ ta faɗa a zuciyar ta tana sake juyowa ta kalle su.



Saurin sake kawar da kanta tayi tanajin wani irin abu da batasan koh miye bane na taso mata daga chan ƙasar zuciya.



"Dan Allah don't do this to me i beg you" ta jiyo muryar Surayya.



"It's alright Stop crying" ya faɗa cikin rarrashin ta yana share mata hawaye, yau cike yake da farin ciki but this Surayya na neman 6ata masa mood.



DEENAH ganin yana share mata hawaye ba ƙaramin sake ƙulewa tayi ba, but ta dake dan ganin gudun ruwan su da ƙarshen iskancin su.



Bata ankara ba taji yana ƙoƙarin sanƴa pin ɗin buɗe ƙofar.



Buɗuwa ƙofar tayi, ɗagowa tayi ta kallesa nan yace "You should get going."



Sosai taji zafi, nan kawai tasa kai ta fice da gudu trying so hard ganin ta riƙe kukan dake son zuwan mata.



Da kallo ya bita, haka kuma kurum yakejin rashin daɗin hakan a ransa, ta6e baki yayi tare da wurgawa Surayya mugun kallo yana wani jin tsanar ta da haushin ta na ƙaruwa masa a zuci.



Ficewa yayi shima tare da mara mata baya................





*Yawan Comment, yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*019...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





...............Da sauri yabi bayan DEENAH da har ta fice zuwa flour ɗin ƙasa.



Tsayawa yayi ta sama tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" ya faɗa.



Cak DEENAH taja ta tsaya tana jin zuciyar ta nayi mata zafi sosai, nan tayi saurin goge hawayen fuskar ta.



Sauƙowa yayi ya tako zuwa inda take tsaye yana kallon ta, kafin a hankali ya sake cewa "MADEENAH."



Kallon sa tayi suka haɗa ido nan tayi saurin kawar da nata idanun.



"Am Sorry" ya faɗa cikin sanƴi.



Kallon sa tayi tace "Sorry...for what?."



"I said alot of bad things about you, and i know you..."



"It's alright, If you think am bad that won't hurt me, my family knows who i really are and they have trust and believe in me, dah suna suka faɗamin abubuwan da ka faɗamin then i would be sad forever, but kai a matsayin ka na wanda bansaniba bansan komai akan sa ba, haka kuma baisan komai a kaina ba maiyasa zanyi fushi dan ka kiraye ni da sunayen banza?."



Shiru yayi yana kallon ta cikim cize baki.



"Ohh kana tunanin ina takurawa rayuwar ka koh?, all this while abu biyu ne kawai ya sanƴa ni faɗawa halin neman ka, kuma kake tunanin kamar ina shisshige maka ne, na farko dan na nemi yafiyar ka, na biyu kuma dan na baka sarƙar ka dake tare dani nothing else, look MADEENAH ba kamar cheap ladies ɗinnan da kake hanging around dasu kullum bane, i have my own way of living, kana tunanin dah ba dan dalilai biyun nan ba zaka sake gani na ne kuma anan?" Kai ta girgiza sannan ta cigaba da cewa "Koh da inuwa ta ba zaka gani ba, and now Alhamdulillah finally babu komai tsakanin mu kuma, a yanzu zanyi bacci cike da kwanciyar hankali sannan zanyi farin ciki, dariya dama kuma walwala kamar kowa" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon sa.



Sosai ya sha jinin jikin shi, hannaye kawai ya zuba a aljihu yana kallon ta.



Juyawa tayi ta cigaba da tafiya kafin kuma ta tsaya ta juyo tace "And yes, kada ka wani sanƴa damuwa a ranka saboda ni, coz a yanzu na dawo maka da farin cikin ka, yakamata ka saki fuska kayi dariya cike da farin ciki, koh da murmushi ma kayi sabida koh bakomai zai ɗan ƙara maka lafiyar zuciya" tana faɗin haka ta sanƴa kai ta fice.



Da kallo ZEEDAN da ya rasa ta cewa ya bita yanajin jikin sa yayi sanƴi, shikenan kuma yanzu ya rasa ta yadda zai kuma sanƴa DEENAH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login