Showing 18001 words to 21000 words out of 236327 words
bata ƙarewa.
Sarauniya Hafeezah kuwa idanun ta yayi zuru-zuru,inda kuma take tunanin komawa wurin bokan ta dan kuwa taga kamar asirin ta na shirin tonuwa.
Sarauniya Naseeba kuwa ba ƙaramin tashin hankali da baƙin cikin 6acewar ZEEYAD ɗin take ba, dan kuwa bata samu ta aiwatar da burin ta akansa ba, sai dai fah bata cire rai ba komin daren daɗewa sai ta aiwatar da abinda tayi niya akansa.
Duka sauran miƙewa sukayi suna ficewa da Family ɗinsu ɗaya bayan ɗaya, kafin Abdulhakeem ma ya tashi suka fice da nasa iyalan.
Kallon Sarauniya Hafeezah Nazeerah tayi tace "Uhm, idanu sun raina fata yau Hafeezah, da alamu kamar muguwar ƙullin ki na shirin warware wa koh?."
Tsaki taja tana miƙewa tsaye ta fice kamar zata tashi sama.
Da kallo ta bita tana murmushi kafin kuma ta dawo da idanun ta kan Naseeba, murmushi ta sakar mata tace "Ke kuma fah, kina kewar masoyin naki ne?, sai ki bada himma wurin gano inda ya shige."
Kamar zatayi kuka haka nan ta tashi itama tana ficewa ba tare da ta tanka Nazeerah ba.
"Wow! Wow!! Wow!!!, inajin daɗin wannan drama sosai da sosai, dukkanin su sun ɗaurawa kansu babban aiki, basu san da cewa dukkanin abinda suke aikatawa mai Martaba na sane ba kawai kyale su yake yaga iya gudun ruwan su, mahaukatan banza da wofi, yanzu kuma da suka kai sa maƙura bari muga mai zai aiwatar akai dan kuwa da alamun yanzu aka fara wasan, yayin da nikuma zan zama ƴar kallo" ta ƙarashe cikin murmushi mai cike da jindaɗi.............
**********
.........."Tsaye yake gaban tafkeken hoton ta yana kallo inda kuma hawaye suka shiga yi masa zarya a kan fuska.
"Lateefat, Haƙiƙa naci amanar ki, ban kula da amanar da kika barmin ba, na gaza kula da ɗa kwaya ɗayan da kika bari,na ruguza masa rayuwar sa dama kuma mafarkin sa, bana ta6a tunanin zai iya yafemin, Hafeezah tayi nasarar raba ni dashi, Haƙiƙa ina matuƙar ƙaunar ZEEYAD fiye da kowa, sai dai nazo na wayi gari babu shi babu labarin sa, sai a sannan ne kuma hankali na ya dawo, bayan ɗa mafi soyuwa a gareni yayi nisa dani, bayan sunyi nasarar cusa masa tsana ta a zuciyar sa, bana tunanin zan yafewa ɗaya daga cikin su akan abinda suka aikata.".............
*Idan kin karanta kiyi sharing sabida ƙaunar Allah da Manzon sa👏🏽*
*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*008...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
..........Haka nan yayi ta zama a wannan wuri shi kaɗai inda kuma yake bin kowanne mahaluƙi da yazo wucewa da idanu.
Sosai ya jigata da ƴunwa wannan karon dan kuwa ga abinci nan na saidawa yana gani amma babu damar ci, dan kuwa ya lura ma da cewa mutanen wannan tasha kamar ɗabi'ar su ce masifa da faɗa, dan kuwa a ɗan zaman san nan anyi faɗa a gaban shi ya kai sau shida, ga kuma ƴan shaye-shaye da bushe-bushe nan birjik abin ba'a cewa komai.
Tashi yayi da jakar sa a hannu ya fice daga tashar.
Tafiya mai nisan gaske yayi kafin ya samu gindin wata ƙatuwar bishiya ya zauna.
Jakarsa ya ajiye anan tare da ɗaura kansa akai kan kace miye kuma baccin wahala ta kwashe shi.
Sosai ya sha bacci kafin ya farka, dube-dube ya hau yi ganin babu jakar sa babu alamun ta.
Tashi yayi tsaye yana duddubawa har bayan bishiyar ya zaga babu an sace.
"It was Stolen" ya faɗa kamar zaiyi kuka.
Da sauri kuma ya kai Hannu kan wuyar sa nan dai yaji sarƙar tasa na nan, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furta "Alhamdulillah" yana maida ta cikin rigar sa, kafin kuma ya hau tafiya yana barin wurin...........
*THREE WEEKS LATER*
........Rayuwa a haka tayi ta tafiyar wa ZEEYAD cike da wahala da ƙunci.
Dakyar yake samun na ci da sha balle kuma na wankan tsaftace jikin shi.
Duk inda ya shiga kowa tsangwamar sa da hantarar sa yake, musamman yarbawa da inƴamuran nan masu shegen masifa kamar saci kai.
Da kyar da ikon Allah ya samu wani local Restaurant inda wata mata ke saida abinci yana yi mata wanke-wanke inda ita kuma take biyan sa da abinci, a takaice dai ya zama ɗan aiken ta dan kuwa shi ke serving customers abinci ma yana kai musu idan sun zo saya koh ci.
Yau ma zaune yake yana wanke plates ɗinda akaci abinci dashi sabida sunyi ƙaranci sai an wanke kafin a samu na sanƴawa wasu abinci.
Bayan ya wanke ne ya ɗauka ya kai yana miƙa mata cike da girmamawa.
Amsa tayi cike da masifar baya sauri sai ya kora mata customers ta fara zuba abincin kan ta miƙa masa ya kai.
Cikin ɗan ɗakin da aka ware na zaman customers ya shiga tare da nufar teburin wanda akace ya kaiwa abincin.
Samun mutumin yayi zaune yana waya inda kuma yake ta kyakyata dariya da alamun dai wani abin ake faɗa masa a wayar.
Ajiye masa abincin ZEEYAD yayi sannan yaje ya ɗauko masa ruwan pure water guda ɗaya ya ajiye masa yana shirin ficewa ne wannan mutumin ya yafito shi da hannun sa kan ya tsaya.
Tsayuwa yayi jiran sa inda shi kuma ya cigaba da wayar sa yana kyakyata dariya ga kuma abinci da ya sanƴa a gaba yana ci.
Da kallo kawai ZEEYAD ke binsa ganin ya barsa tsaye shi bai ce masa komai ba, sannan kuma bai barsa ya tafi ba.
Har saida ya kusa idda cin abincin kafin uwargijiyar ZEEYAD ta shigo ciki kafin kuma ta hau balbale sa da masifar ya shanƴa ta a waje bai zo ya baiwa sauran customers abinci ba "So kake ka kora min customers su daina zuwa wuri na kalan ma suce ba'a kar6ar su yadda yakamata, ni banma san uwar miye da tsautsayin da ya kai ni ɗaukar ka aiki ba dallah wuce kaje ka wanke min plates mutane na jira" ta ƙarashe tana aika masa da muguwar kallo.
Wannan mutumin kuwa da kallo kawai yake bin su bai ce komai ba yana cigaba da wayar sa da cin abincin sa.
"But he asked me to wait" ya faɗa.
"Zaka wuce ne kokuwa sai raina ya 6aci?."
Wucewa yayi yana mamakin wai a hakan ma ranta bai 6aci ba kenan da wannan uban masifar da ta rufe shi.
Fitowa tayi kamar zata tashi sama dan masifa ta hau aikace-aikacen ta.
Da kallo yabi mutumin da ya fito yana biyan matar kuɗin ta kamar baya so sannan yayi gaba yana jin kamar ya bishi ya rufe shi da duka dan haushi.
A haka har dare kafin ta sallame sa da naira ɗari biyu tace "Yau ka 6ata min rai shiyasa ba zan baka ɗari uku ba, ina mai tabbatar maka idan ka sake ka kuma 6ata min rai zan daina ma baka abincin baki ɗaya da tukwuicin aikin" ta faɗa tana wani yayyatsina fuska.
Amsa yayi ba tare da ya raina ba yayi godiya yana sanƴawa cikin aljihun sa kafin yayi mata sai da safe ya wuce.
Tsinkayo muryar ta yayi tana faɗin "Ka tabbatar fah gobe ka fito dawuri sabida kasan akwai share-share da gyare-gyaren da zakayi koh?."
Kai ya jinjina mata yana wucewar sa.
Gidan wani wanka ya biya ya biya kuɗi yayi wanka da wasu ƴan buƙatun sa kafin ya wuce inda yake kwana.
Rumfar wani mai shayi ne yake zuwa ya kwana inda yake biyan sa naira ɗari kullum kuɗin kwana.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a garin na Lagos wanda babu laifi ya ɗan tara kuɗaɗen sa, sannan kuma duk wani aiki idan ya samu na ƙarfi Wanda za'a biya sa yin abinsa yake, a haka har ya fara ganewa da yanayin rayuwar Lagos ɗin ya rage shan wahala kamar dah.
Cikin kuɗaɗen da ya ɗan tara ne yaje kasuwa ya ɗan sayi kayan sawa da ɗan abubuwan da ba'a rasa ba na amfanin shi.
Wata rana yana zaune Shi kaɗai kasance matar da yake mata aiki ta daɗe da korar sa hakan yasa yake shan wahalar samun wani aikin kuɗin.
Aljihun sa ya duba ya ciro ƴan kuɗaɗen sa dake ciki tare da ƙirga su, dubu ɗaya ce da ɗari uku da hamsin ta rage masa a hannu.
Tunani yake tayi dan kuwa indai bai sami wani aikin ba, babu inda zai dinga samun kuɗin biyar wurin kwana indai wadannan na hannun sa suka ƙare.
Miƙewa yayi dan kuwa yau yayi alƙawarin sai ya samu wani aikin yi ɗin.
Sosai yayi yawo sai dai babu abinda ya samu, wuri ya samu ya zauna yana hutawa.
Wata Mota ce ƙirar Golf tayi parking kusada wani gida da yake zaune, inda wani mutum ya fito daga ciki jikin sa sanƴe da manƴan kaya irin ta Hausawa.
Da kallo yabi ZEEYAD kafin ya shige cikin gidan nan.
Ya daɗe sosai kafin ya fito nan yaga har yanzu yana nan ya haɗa kai da guiwa, zuwa wurin sa wannan mutumin yayi tare da dafa sa.
Da sauri ya ɗago yana kallon sa buɗar baki mutumin yayi yace "Mai kakeyi anan?" cikin muryar turanci.
"Babu komai ina hutawa ne sabida gajiya da nayi" ya basa amsa.
"Da alamu kai ba ɗan ƙasar nan bane koh, daga wace ƙasar kake?."
Shiru ZEEYAD yayi bai basa amsa ba hakan yasa mutumin cewa "Na gane bakason faɗamin, amma koma dai menene da alamun kana buƙatar taimako koh?."
Da sauri ZEEYAD ya girgiza masa kai yace "Duk aikin da ka bani zan iya shi kuma nayi maka alƙawarin ba zan 6ata maka rai a aikin ka ba, zanyi maka aiki ne tsakani da Allah."
"Kai musulmi ne?" mutumin ya tambaye shi.
Kai ya jinjina masa nan yace "Masha Allah, zan baka aiki idan kanaso amma fah ni ba anan nake zaune ba kuma ba anan nake aiki ba, sai dan nakan zuwa kowane ƙarshen sati biyu ina duba iyali na, nan ne gida na sannan kuma ni mutumin Kano ne kuma bahaushe."
"Kaima musulmi ne?" cewar ZEEYAD ɗin.
"Kwarai kuwa."
Murmushi yayi yace "Sai yau na haɗu da musulmi tunda nazo wannan ƙasar, kuma kai ne mutum na farko da ka tausaya min har kake ƙoƙarin bani aiki bayan ban sanka ba, Nagode."
Murmushi mutumin yayi yace "Badamuwa, duk yiwa kai ne, yanzu haka Kano zani, shin zaka iya bina yanzu kokuwa zaka jira sai nazo wani hutun kuma?."
Da sauri ya jinjina masa kai yace "Zan bika indai har hakan zai sa na sami na kaina."
"Insha Allah, kada ka damu taso muje."
Nan ya tashi yabi wannan mutumin da baisan koh wanene shi ba suka kama hanƴa.......
**********
.....Kamar yadda wannan mutumin ya faɗa sai gasu a garin Kanawan dabo.
Da kallo kawai ZEEYAD ke bin koh ina da kallo dan kuwa daga ganin wannan garin yafi garin da ya baro fasali dama kuma daɗin zama.
Hotel ne mai kyau da tsada suka nufa inda wannan mutumin ya biya kuɗin ɗakin mutum biyu, sannan yayi ordern abinci.
Ɗakin ZEEYAD ya nuna masa kafin ya umarce sa da yin wanka ya huta kafin a kawo masa abinci.
Haka kuwa akayi bayan yayi wanka ya sauya kayan sa zuwa wata ne aka kawo masa abinci da abin sha mai rai da lafiya yaci ya sha ya ƙoshi.
Mutumin ne ya dawo yace dashi Nasan mun ɗebo gajiya ka kwanta ka huta kafin zuwa gobe da safe dan kuwa akwai baƙon da zamuyi shine zai baka aikin nan.
Kai ya jinjina yace "Nagode."
Nan mutumin ya fice kafin shi kuma yabi lafiyar gado ya kwanta.
Bacci yayi cike da jindaɗi da kwanciyar hankali, cikin dare ya farka yayi Nafilolin sa kafin zuwa washe gari yayi sallahr Asuba.
Da safe aka kawo masa breakfast mai rai da lafiya yaci, kafin wannan mutumin ya shigo ya basa wasu kaya sannan yace dashi yayi wanka ya gyara jikin sa baƙon ya kusa zuwa.
ZEEYAD da bai kawo komai cikin ransa ba yayi kamar yadda wannan mutumin yace dashi,wanka yayi ya sanƴa kayan nan, shadda ce janfa da tayi matuƙar kar6ar sa yayi kyau dukda kuwa ba iya sanƴa ta yayi ba amma ta kar6e sa matuƙa inda mutumin nan kuwa yayi ta yaba kyawu da haɗuwa irin ta ZEEYAD ɗin kamar wani mace, shi kuwa sam bai kawo komai a ransa ba dan kuwa ya ɗauka wannan mutumin na Allah ne.
Bayan wani lokaci wannan mutumin ya shigo da wani Alhaji ya sha manƴan kaya cikin nan nasa kamar tulu sai zuba ƙamshi yake.
Ganin ZEEYAD kuwa ya sa shi rikicewa nan yace da wannan ɗinnan cikin muryar hausa da bai fahimci mai
suke cewa ba yace "Lallai aikin ka na kyau Lawal, a ina ka samo wannan santalelen hallitar haka, tunda nake ban ta6a ganin kyakkyawa kamar yaron nan ba, lallai kyautar ka ta musamman ce wannan karon da fatan dai kayi masa bayanin komai?."
Cike da girmamawa yace "Godiya nake ya Alaj, ai banyi masa bayani ba tukun dan kuwa baya ma jin hausa sannan kuma ba ɗan ƙasar nan bace da alama neman kuɗi ce ta kawo sa nan, wannan ne dalilin da yasa nayi amfani da wannan dama na kawo maka shi kaji daɗin ka, dan kuwa tundaga Lagos na ɗauko shi sannan bashida kowa anan."
"Madallah aikin ka na mugun kyau Lawal, bani jakar kuɗin nan."
Nan ya miƙa masa Briefcase ɗin hannun sa kafin ya nufi ZEEYAD cikin muryar turanci yace "Yaro ya sunan ka?."
"ZEEYAD" ya bashi amsa.
Murmushi yayi yace "masha Allah, Allah yayi halitta anan wurin" nan ya buɗe jakar inda rafa-rafa ɗin American dollars suka bayyana.
Idanu ZEEYAD ya waro kafin ya kalli mutumin.
Dariya mutumin yayi yace "Na san da ganin kuɗin nan ba zai sa kaƙi amincewa da buƙata ta ba, indai ka amince wadannan kuɗaɗen gabaɗaya sun zama naka har ma da ƙari idan kana buƙata, zakayi dukiyar da har ka mutu ba zaka gama cinƴe ta ba."
ZEEYAD da zuciyar sa ta fara raya masa ba alkhairi tattare dasu ne yace, "Mai...mai Kake nufi, wadannan kuɗaɗen dollars ne, aikin mai zanyi muku da har zaku biya ni da wannan uban kuɗaɗen?."
Dariya yayi yana shafo gashin kan ZEEYAD tare da lashe baki yace "Kai dai kawai ka bada haɗin kai wannan aikin sirri ce, ba kowa ne ya santa ba sai mai sa'a da rabon yin dukiya."
Ja da baya yayi ransa na 6aci yace "You are a Gay."
Murm mutumin yayi yace "Ya'akayi ka gano dawuri haka, shikenan ma tunda ka fahimce ni, ka bani haɗin kai muyi abin nan ka amshi wadannan ɗumbin kuɗaɗen."
"Never" ya faɗa tare da Ɗaurawa da faɗin "Ba abinda ya kawo ni ba kenan neman kuɗi ta hanƴar haram, i will never engage myself into that shit, koh da kuwa zan mutu ne da talauci, zuciya ta ba matacciya bace kuma ba gur6atacciya bace, duk halin da na tsinci kaina jarabawar Ubangiji ce, dan haka ba zan ta6a yarda na faɗi ba akan wadannan kuɗaɗen da basuda albarka kuma suke saurin cinƴewa kamar wuta na ƙona takarda, sai dai ku nemi wani mai kwaɗayin irin halin ku amma ba ZEEYAD ba, kai kuma na ɗauka na haɗu da mutumin kirki ne kamar yadda ka nuna min a farko ashe dai ba haka bane, all of you are a disgrace to our religion, kunyi asara duniya da lahira muddin baku tuba ba" yana faɗin haka ya ɗau ledar kayan sa tare da bangaje su yayi ficewar sa zuciyar sa na mugun ƙuna.
Ya rasa dalilin da ya sanƴa yake ta haɗuwa da gur6atattun mutane marasa tsoron Allah a rayuwar sa hakan na nufin ba zai ta6a haɗuwa da na kirki koh ɗaya ba kenan komiye?.
Sosai yaga garin na Kano ya sha bambam da inda ya baro, garari ya sha sosai kafin ya samu wani wuri ya fake yana maida ajiyar zuciya.
Lalumar aljihun sa yayi koh nan yaji wayam babu kuɗin sa, nan kuma ya tuna fah ashe ba kayan bane a jikin shi.
Wani lungu ya samu ya shiga ya canza kayan jikin nasa yana zubar da wanda suka basa "They are so disgusting" ya faɗa yana barin su a wurin, dan kuwa da da hali ma abincin da suka basa amayar da banza zaiyi dan ba zai iya cin haram ba.
Hamsin ya ɗauka daga cikin kuɗin wurin sa ya sayi ruwan sha da biscuit yaci kafin kuma ya sake kama hanƴa duk inda yabi kuwa sai dai ayi ta kallon sa.
A haka har ya samu ya shigo wani ungwa dukda baisan koh ungwa bace amma dai yaga gidajen mutane dama kuma yara na ta wasan su.
Gefe da wani Islamiyya ya samu ya zauna yana ta6a wuyar sa yaji har yanzu sarƙar sa na nan.
Anan yakeyin sallahr sa har yamma tayi aka tashi daga wannan islamiyya.
Yara ne suke ta fitowa suna wucewa gidajen su, wasu na tsalle-tsalle wasu kuwa da guje-guje haka suke tayi.
Ɗago kai yayi ya hango ta ta ƙura masa idanu tana kallo, kamar wacce taga wani sabon halittar da aka jefo daga sama.
Maida kansa yayi sakamakon zuciyar sa da yaji tayi wani irin bugu lokacin da ya haɗa idanu da yarinƴar.
Sake ɗagowa yayi nan yaga dai shi take kallo har yanzun, 6ata fuska yayi yana kallon cikin manƴan idanun ta da ta kafe sa dashi.
_"Is she a witch?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa.
_"I know she must be one, dan naji labarin mayu sunyi yawa a chan garin, Maybe nan ma hakan ne"_ ya sake faɗa.
Kauda nasa idanun yayi yana faɗin "Her eyes are so damn wide."
"Ke dallah banza wuce mu tafi kin wani kafawa mutane da idanu kamar wata mayya