Showing 195001 words to 198000 words out of 236327 words

Chapter 66 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45331

ita "Haa."

Ita dai shiru tayi tana kallon sa kafin a hankali ta girgiza masa kai tana faɗin "Bana ma jin ƴunwan fah."

"Look DEENAH, this food can't go to waste, you've to eat it coz Grandma ba zata ji daɗi ba."

"Don't force me please" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka.

"Am not forcing you DEENAH, you've to eat it, and besides yana ƙara lafiya da ƙuzarin jiki."

"Really?."

"Really" ya faɗa.

Ɗan murmusawa tayi kafin tace "I will eat it sabida Grandma, ba dan kai ba."

"Whatever, all that matters is for you to eat it" ya faɗa cikin kallon ta.

Spoon ɗin hannun sa ta amsa kafin ta kai ta ɗebo abin tana kallon sa, murmushin gefen baki ya saki kafin ta kai abin baki tana ɗan runtse idanu.

Idanu ya zuba mata yana kallo har ta haɗiye abincin, spoon ɗin ta ajiye dan kuwa koh kaɗan baiyi mata daɗi ba.

Ganin irin kallon da yake binta dashi ne ya sanƴa ta faɗin "Why are you staring at me like that?."

"Coz i can't really believe how fool you're and easy to fall into a trap our future queen" ya faɗa cikin murmushi suffar sa na komawa na Sarauniya Naseeba.

A wani irin mugun razane DEENAH ta waro manƴan idanun ta cike da kiɗima take bin Naseeba da ta miƙe tsaye da kallo.

Murmushi Naseeba ta saki kafin tace "Oh my Darling future Queen, i can't believe wane irin tsautsayi ne ya ɗebo ki zuwa wannan MASARAUTAR a matsayin matar ZEEYAD, the boy that i have been craving to taste how good and sexy he is in bed will finally be in my custody today" murmushi ta ƙara saki tana gimtse fuska cikin wullawa DEENAH mugun kallo take cigaba da faɗin "ZEEYAD is mine, and only i can get intimate with him, i will make sure that i keep you far away from him wanda koh ƙamshin sa ba zaki sake ji ba balle muryar sa, you've made a very big mistake na kawo kanki cikin wannan fadar, this food that you just ate now, it's poisoned" ta faɗa cikin murmushi still idanun ta akan DEENAH da ta kasa motsi daga inda take bale tayi moving eyes ɗinta daga kan Naseeba.

"But... luckily for you ba irin poison ɗin da zai kashe ki bane, it's that kind of poison that will knock you down to sleep forever."

Tsugunnawa tayi daf da DEENAH da jikin ta ya gama yin lagwai bata iya motsa koh da ƴar yatsar ta tana shafo gefen fuskar ta haɗi da hura mata iska a hankali take faɗin "Sleep, sleep tight beauty, am sure zakiji daɗin sabuwar duniyar da zaki tsinci kanki ciki yanzun."

A hankali DEENAH take lumshe idanun ta da take ganin dishi-dishi sakamakon maganin da ya fara tasiri cikin jinin ta.

"Sleep so that i can take your position, sleep so that i can have ZEEYAD for all myself, sleep so that i will be the next Queen of this Kingdom."

Ture DEENAH da jikin ta ya gama sakewa tayi tana faɗi kwance kafin idanun ta da suke tsiyayar da wasu irin siraran hawaye su gama rufewa ruff.

Da kallo Naseeba ke bin ta, kafin ta miƙe tsaye tana kyakyata dariyar mugunta, sai da ta shafe almost 1min tana yi kafin ta tsagaita tana gimtse fuska "Finally, i told you ZEEYAD didn't i?, nothing will ever stop me from having you as mine, am sending your dear wife inda ba zaka ta6a ganin ta ba, you will live with me a matsayin ita, and we will live a life full of love and care" ta faɗa cikin yin hajijiya tana dariya.

Tsagaitawa tayi kafin ta kuma takowa inda DEENAH ke kwance, hannu ta sanƴa a jikin ta tare da karanto wasu irin makaran tsafi take kuma komai nata ya koma irin na DEENAH, kai kace DEENAH ɗin aka raba biyu.

Murmushi tayi tare da miƙewa tsaye tana kallon DEENAH ɗin kafin kuma ta shiga karanto wasu irin makaran tsafi cike da yaren da ba zaka san koh na menene ba, take wata tsohuwa gijib ta bayyana, kallon Naseeba tayi tare da faɗin "Burin ki ya cika, and now the girl is mine, kin cika alƙawari bani ita akan lokaci kamar yadda kika faɗa" ta faɗa cikin jinjina kai tana kallon DEENAH.

Murmushi Naseeba tayi kafin tace "Take her, take her far awayyy from here, take her to inda babu wani mahaluƙi da zai iya gano ta, yadda zanji daɗin rayuwa da wanda na ɗau shekaru ina begen sa."

Dariya tsohuwar tayi tace "Ofcourse tunda kikayi min abinda nakeso dole nayi abinda kema kika ce, zan ɗauke ta na kaita inda babu wani ɗan adam da ya ta6a taka ƙafafun sa zuwa wurin, ita ɗin sadaukar wa ce garemu dan haka zan ɗauke ta nayi nisa da ita inda duk neman da za'a yi mata cikin duniyar ba za'a gano inda take ba, sai dai kema ki kiyaye sharuɗan da na gindaya miki indai kikayi hakan toh tabbas komai zai tafi dai-dai yadda kowannen mu yaso."

Alamu tayi mata da hannu tana faɗin "Take her tun kafin ya dawo cikin gidan nan."

Murmushi tsohuwar tayi tare da jinjina kai tana kallon DEENAH, wasu surutan ta tayi tana nuna DEENAH da sandar hannun ta take kuma dukkanin su suka 6ace ya saura sabuwar DEENAH wato Naseeba.

Wata iriyar ajiyar zuciya ta sauƙe cike da relief zuciyar ta fal farin cikin burin ta ya cika.

Zubewa tayi kan couch ɗin ɗakin tana sake bin jikin ta da ya zama DEENAH sak da kallo, murmushi tayi tare da faɗin "I can't believe this."

Miƙewa tayi ta koma cikin ɗaki, tare da tsayawa a gaban mirror tana ƙarewa kanta kallo, sake gyara ɗaurin kanta tayi kafin ta sake yiwa fuskar ta kwalliya ɗan kaɗan inda ta fito tare da yin kyau sosai da sosai.

"Uhm what a great day for me" ta faɗa cikin murmushi tana faɗawa kan bed ɗin ɗakin.


*********************

__________ZEEYAD bai tashi dawowa part ɗin nasa ba sai da akayi sallahr la'asar kai tsaye ya wuce cikin part ɗin nasa.

Haurawa sama yayi tare da tura ƙofar falon bakin sa ɗauke da sallama.

Lumshe idanu yayi sakamakon ƙamshin turaren da ya bugo sa, idda shigewa yayi yana rufo ƙofar falon.

Ganin baiji motsin DEENAH bane ya sanƴa shi nufar ɗaki, sai dai wayam yaga bata nan.

Shiru ya zauna dan koh a tunanin sa tana toilet ne, sai dai jin shiru ya sanƴa shi miƙewa yana yin bakin toilet ɗin tare da kwankwasawa a hankali yace "DEENAH?."

Jin shiru ya sanƴa shi sake faɗin "Are you in there?."

Tura ƙofar toilet ɗin yayi ya shige inda ya duba kowane lungu da saƙon ciki yaga bata nan, fitowa yayi wondering koh ina ta shige.

Muryar ta yaji daga cikin ɗakin closet tana faɗin "Abyad kazo ka taimaka min na anan."

"Ohh" ya faɗa a hankali yana ƙarasawa bakin ƙofar kafin yaja ya tsaya yana faɗin "Should i come in?."

"Yes come in" ta faɗa.

Tura ƙofar yayi ya shiga inda ya ganta tsaye ɗaure da towel ɗin da kaɗan ya wuce mazaunan ta.

Juyowa tayi tana kallon sa cikin murmushi, murmushin shima ya saki cike da mamakin ta ba tare da ya iya ɗauke idanun sa daga kanta ba.

Ƙarasowa tayi inda yake tsaye hannun ta ɗauke da doguwar rigar kanti take faɗin "Zip ɗin ya cize, will you please help me ka gyara min shi."

"Sure" ya faɗa yana amsar rigar daga hannun ta, nan yace "By the way, when did you loose your hair" ya faɗa yana kallon gashin kanta dake a tsafe.

Hannu ta kai ta ta6a gashin tare da faɗin "My hair?, ɗazun nan ne bayan ka fita."

Gyara mata Zip ɗin rigar da ya cize yayi yana miƙa mata, amsa tayi cikin murmushi tana kallon sa haɗi da furta "Thank you."

Folding hannu yayi a ƙirji yana kallon ta, nan kuwa ta fara shirin warware towel ɗin jikin ta ba tare da ta kore sa ba, ɗan waro idanu yayi kafin yace "Are you being real?."

"What?" ta faɗa.

Murmushi yayi tare da jawo ta jikin sa yace "I thought zaki kore ni ne."

Murmusawa tayi kafin tace "No why zan kore ka, you're my Husband aren't you, and dukkanin wani abu dangane dani is all yours" ta faɗa cikin shafo lallausar gashin gefen fuskar sa.

Haɗe hancin su yayi guri ɗaya yace "I thought you will wait har sai Grandma ta kawomin ke da kanta, but i can see you're so eager to get this done."

Murmushi tayi tana sake shigewa jikin sa tace "Let's do it now" ta faɗa cikin riko gaban rigar sa.

Shi dai ZEEYAD sosai ya cika da mamakin DEENAH ɗin ganin canzawar ta lokaci guda haka, riƙe hannun ta yayi daga 6alla buttons ɗin rigar sa da take kafin ya kalleta yace "This will be more interesting at night" ya faɗa yana maida su ya rufe, kafin ya ɗan ja hancin ta yace "I will see you tonight, i know Grandma zata iya aikowa any moment from yanzu azo a tafi dake, and nima inason zuwa ganin YAZEED, so make sure you're well prepared tonight" ya faɗa cikin bata peck a gefen kumatu kafin kuma ya fice daga cikin ɗakin ma gabaɗaya.

Da wani irin kallon mugun haushi ta bishi, nan kuma tace "Anyways then, i will wait for you tonight Darling, koh da nan da zuwa gobe kace i will wait, muddin i can have you then banida wata matsala" ta faɗa tana sanƴa kayan jikin ta tare da fitowa cikin ɗakin.


*********************


__________Grandma da kanta ta kawowa ZEEYAD amaryar sa har kan bed ɗinsa.

Sosai ta sanƴawa DEENAH albarka kafin kuma tace "Ni zan barki haka nan, duk wani abinda yayi miki wanda bakiji daɗin sa ba ki kawomin ƙarar shi nikuma zanyi maganin sa kinji koh?."

Kai ta jinjina wa Grandma ɗin kafin kuma tace "Ni na barki cikin farin ciki ƴar nan, Allah ya dauwamar da farin ciki cikin rayuwar auren ku" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin tana rufo ƙofa.

Fitar ta keda wuya fake DEENAH ta buɗe fuskar ta dake cikin mayafi tana bin ƙofar da kallo tare da sakin wani irin shu'umin murmushi.

Maida duban ta tayi ga agogon dake manne a ɗakin taga ƙarfe goma saura.

Miƙewa tayi daga kan bed ɗin tana sauƙa ƙasa kafin ta nufi closet room, bata jima ba ta fito cikin wasu irin tsinannun night wears wanda marabar su da babu kucil ne.

Feshe jiki tayi da turaruka masu daɗin ƙamshi kafin ta koma kan bed tana jawo bargo ta rufe a jikin ta tare da faking baccin ƙarya.

Like after 20mins aka buɗo ƙofar ɗakin, sosai ya haɗe cikin shigar sa ta manƴan kaya sai zuba ƙamshi na musamman yake.

Jinginuwa yayi da bakin ƙofar yana kallon ta cike da mamaki ganin kamar har tayi bacci.

A hankali ya shiga takowa bakin bed ɗin yana durƙushewa kan guiwowin sa tare da ƙure kyakkyawar fuskar ta da kallo.

Sai da ya gama kallon ta tsaf kafin ya miƙe yana shigewa ɗakin closet, bai wani jima ba ya fito cikin ƙananun kaya da 3quater wando tare da yin hanƴar toilet, alwala ya ɗauro ya fito kafin ya tako inda take, a hankali ya shiga buga pillow ɗin da kanta yake kai.

Lamo tayi kamar bata ji ba, har sai da yayi ya gaji ya daina.

Zuwa yayi ya kashe wutar ɗakin inda ya rage saura hasken side lamps, suma rage hasken su yayi.

Hawowa kan bed ɗin yayi yana cuddling ɗinta ta baya tare da manna mata sumbata a neck.

Kame jikin ta tayi wani irin farin ciki na nuƙurƙusar zuciyar ta finally yau burin ta zai cika.

Kwanciya ta gyara tana juyowa facing ɗinsa still idanun ta a lumshe kamar mai baccin gaske.

Hannu ta kai kan faffaɗar ƙirjin sa tana rubbing gently, riƙe hannun nata yayi sabida haka kawai yakejin duk wani ta6a sa da tayi ya kanji wani iri a zuciyar sa.

A hankali cikin muryar bacci ta kira sunan sa "Abyad."

Kallon fuskar ta yayi tare da amsa mata da "Um."

Shiru tayi kamar wata iriyar mai magagin baccin nan tana sake shigewa jikin sa.

Rungume ta shi ɗinma yayi yana mai manna mata kiss a goshi tare da rufa musu bargo.



*********************


_________A razane ya tashi daga mafarkin da yayi ɗin, yana dafe kansa da hannuwa bibbiyu, same mafarkin da yake yi kwanaki akan ana tura DEENAH cikin ruwa ya sake yi wannan karon ma.

Addu'a ya karanto sosai cikin zuciyar sa kafin kuma ya ankara da rigar jikin sa dake a tu6e.

Kallon DEENAH dake shar6ar baccin ta cikin kwanciyar hankali yayi wondering koh itace wacce ta cire masa rigar.

Miƙewa yayi daga kan bed ɗin yana faɗawa toilet, fuskar sa ya wanke kafin kuma ya ɗauro alwala ya fito.

Darduma ya shimfiɗa kan chinese carpet ɗin dake ɗakin kafin ya tada sallah.

Sosai yayi sallahr haɗi da karanto addu'oin neman tsari da sauran su, bai idda ba har sai da yaji ana kiraye-kirayen sallahr Asuba.

Miƙewa yayi ya koma toilet ɗin tare da sake ɗauro wani alwalan yana zuwa inda DEENAH ke kwance tare da buga pillow ɗin da take kai.

A hankali ta ware idanun ta akansa, alamu yayi mata da anyi sallah kafin kuma ya juya ya fice daga ɗakin zuwa masallaci.

Da kallo tabi sa kafin kuma ta wani turo baki tana komawa ta kwanta ta cigaba da baccin ta.

ZEEYAD bai dawo ba har sai ƙarfe bakwai bayan rana ta fito, dawowa ɗakin yayi yadda ya barta haka nan ya same ta still tana bacci.

Zuwa yayi ya sake tada ta akan ta tashi tayi sallah, zaune ta miƙe tana wage baki ba tare da ta koh rufe sa ba, gashin kanta duk ya wani barbaje yawa sabuwar mahaukaciya.

Da mamaki fal ransa ya fice daga ɗakin.

Miƙewa tayi tare da faɗawa Toilet, wanka tayi ta fito kawai kafin ta shirya cikin English wears ɗin doguwar riga iya cinƴa mai hannun vest.

Bata damu da ta gyara kan gadon ba ta fito zuwa falon ƙasa, bayin dake ta gyare-gyare t umurci ɗaya da ta kawo mata breakfast yanzun nan kafin kuma ta koma sama.

Buɗe sauran ɗakunan tayi taga baya ciki hakan ya sanƴa ta nufar gym room ɗinsa anan ta tadda sa yana motsa jiki.

Murmushi tayi tana ƙarasawa gun sa tare da faɗin "Good Morning."

Dakatawa yayi da abinda yakeyi tambayar da ya wullo mata shine "Have you prayed?."

"Yeah of course, sorry kana ta tashi na ban farka dawuri ba, na gaji ne sosai shiyasa."

Shiru yayi bai tanka mata ba, sabida sam bai zaci haka halayen ta suke ba, rashin yin sallah akan lokacin sa.

Ganin kamar ransa a ɗan 6ace ne ya sanƴa ta ƙarasawa inda yake tana rungumo sa ta baya.

Sosai yakejin wani iri idan ta ta6a shi, dan haka zame hannayen ta yayi daga jikin sa yace "I need a Morning coffee to warm me up, can you prepared it right away?."

"What, a coffee?" ta faɗa tana kallon sa.

"But i'm the future Queen, how do you expect me to make some coffee for you after all akwai masu aiki dayawa cikin MASARAUTAR nan, am sure they can make a nice one."

"Don't worry then, i will make it da kaina."

"No you don't have to do that, sabida na sanƴa a haɗo mana breakfast."

Da mamaki yake kallon ta kafin kuma ya fice daga ɗakin zuwa ɗayan ɗakin.

Tarar da bed ɗin yayi scattered kamar yadda ya barsa, juyowa yayi ya kalleta kafin yace "Are you that tired that gado ma ba zaki iya gyarawa ba?."

Rolling idanu tayi kafin tace "I guess we should talk about dalilin da ya sanƴa baka bani haƙƙi na jiya da dare ba, bayan munyi da kai cewa we will have alot of fun."

"I need you to answer my question first, why isn't this room tidy DEENAH?."

Shiru tayi tana kallon sa kafin kuma tace "Sabida ban saba ba, sannan kuma dukkanin abinda nakeso yi min shi akeyi."

Mamaki ne ya cika ZEEYAD ganin yadda take maida magana garangatsai haka, shiru yayi mata yana shigewa closet room, nan ma wasu kayayyakin ya tadda a wawwatse an ciro su ba'a maida su gurbin zaman su ba, koh shi nan wasu bayi basu ta6a tsaftace masa ɗaki ba bale kuma DEENAH.

Sosai ya kai maƙura a 6acin rai sabida ya tsani ƙazanta kwata-kwata a rayuwa.

Tarar sa tayi da faɗin "Don't be mad please, the maids are here zasu tsaftace komai."

Kallon ta yayi yace "Bana buƙatar wasu bayi cikin ɗaki na, don't you ever make the mistake of asking them in" yana faɗin haka ya fice a fusace.

Da kallon mamaki ta bisa, she thought yana mugun son DEENAH and ba zai ta6a yin fushi da ita dawuri haka ba, sai dai koh kaɗan hasashen ta bai zamto gaskiya ba, tun jiya ya kasa ta6a ta, duk kuwa iya ƙoƙarin ta na ganin ta kusance shi cikin dare sai dai bai bari hakan ta faru ba, ta rasa mecece matsalan kodai dama bayason DEENAH ɗin ne?, shine tambayar da tayi wa kanta.

Cike da mugun haushi ta hau gyara ɗakin duk bata ma wani iya ba ta dai kwa6a shi ne kawai.


*BAYAN SATI BIYU*


_________Sosai suke samun rashin jituwa tsakanin su, Grandma har mamaki abin yake bata, ZEEYAD kuwa koh kaɗan baisan haka halin DEENAH yake ba, though yayi mamakin canzawar ta but baisan abinda ya faru ta canza all of a sudden ba.

Mai Martaba ne ya gayyace su fada yin Dinner tare dashi da dukkan su family ɗin, zaune ZEEYAD yake DEENAH kusa dashi inda dining ɗin ya ɗau shiru sosai.

Hafeezah ce tace "You should contact Naseeba ta dawo daga tafiyar da tayi haka nan, naga dai bata saba daɗewa idan taje gaida iyayen ta ba, tsananin ta tayi kwana uku but yau har sati biyu kenan."

Tari DEENAH ta saki nan ta kai hannu da sauri tana ɗaukar glass ɗin ruwan gaban ta, hannu na rawa ta kafa akai ta fara sha.

Koh gefen da take ZEEYAD bai kalla ba, Hafeezah ce ta kallesa ganin halin koh in kula ɗin da ya nunawa DEENAH, ta6e baki tayi tana kauda kanta daga garesu.

Amaryar YAZEED ce tace "DEENAH, what's wrong shin kun samu wani matsala ne da mai gidan ki, i thought zai nuna damuwar sa ne ganin rabin zuciyar sa na tari."

JALILAH ƙarasowa tayi tana jan kujera ta zauna da alamu dai fitowar ta kenan, kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "What took you so long?."

Kanta a ƙasa take faɗin "Am sorry Ummie, na tsaya gyara ne."

"Gyaran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login