Showing 78001 words to 81000 words out of 236327 words

Chapter 27 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45380

ƙuna da sunan Miskiniya da Khairat ta kira MADEENAN sa dashi.


"ZEEYAD, kayi haƙuri haƙika nayi maka mummunar fahimta akan halayen ka, kayi haƙuri kaji?" cewar Momy.

Sai a sannan ya ɗago yace "Bakomai Mom, ni ne yakamata na baku haƙurin watsa muku ƙasa da nayi a ido, sannan kuma na baku kunƴa a gaban baƙin da kuka gayyato bayan kuma kunyi ta tsanmanin zan dawo a ranar but i didn't show up, am sorry."


"Bakomai ZEEYAD, kada ka damu kaji?."


Idanu kawai su Umma ke bin su dashi dan kuwa basusan meke faruwa ba.


"Daddy tunda yanzu an ganshi, kuyi Engaging ɗin mu gudun kada a sake samun wata matsalar."


"Khairat ai koma dai menene kya jira mu fita daga nan wurin tukun koh?" cewar Momy cike da mugun takaicin hali irin na Khairat ɗin.


Baki ta turo tana harɗe hannaye a ƙirji, tare da cika tana batsewa.


"Koh da an fita daga nan ɗin ZEEYAD ba zai auri Khairat ba" cewar Daddy.





*Yawan Comment, Yawan Typing*





*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*025...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





_*BANYI EDITING BA*_




""""""""""""""Shiru ɗakin ya ɗauka inda kuma kowa ya zubawa Daddy idanu yana kallo.

Ficewa Daddy yayi daga cikin ɗakin inda duk suka bisa da kallo musamman ma Khairat da bata yarda da abinda kunnuwan ta suka jiye mata ba, yayin da ZEEYAD ma da ya cika da mamaki yayi saurin mara masa baya.

"W..w...what the hell is he saying?" faɗin Khairat cike da ɗumbin mamaki.

Wuri Momy ta samu ta zauna not minding Khairat dake tsaye.

"Momy kinajin abinda Daddy yake faɗa, he must be kidding right?."
Ajiyar ta Momy ta bata bata kula ta ba, dan kuwa itama ta fara gajiya da hali dama kuma ɗabi'u irin na Khairat ɗin.
"Momy am talking to you" ta faɗa da ɗan ƙarfi tana kallon Mom ɗin.

"Maybe you should lower your voice" cewar Jafar yana kallon ta.

Wani irin mugun harara ta wulla masa haɗi da jan dogon tsaki kafin cikin tsiwa tace "A wane dalilin zan sassauta murya ta?, zanyi magana ne yadda raina ke so a duk inda naga dama, who do you think you're ma da zaka buɗi baki kace min nayi lowering voice ɗina, a wane dalilin?."


"A dalilin marasa lafiyar dake kwance anan, koh kin manta a asibiti kike ne?."

Maida duban ta tayi kan DEENAH da ta kafe wuri ɗaya da ido bata motsi nan tace "Ohh wai wannan miskiniya mai shanyayyen jikin?, mttssww, who even cares about her, akanta dai ba zan fasa yin magana da ƙarfi yadda naso ba."

Hannu Jafar ya ɗaga da niyyar bata mari Umma tayi saurin dakatar dashi da faɗin "A'a Jafar, kyale ta."

"Umma baki..."

"Ka kyale ta nace."

Sauƙe hannayen sa yayi zuciyar sa na mugun ƙuna yana kallon Khairat ɗin dake bin sa da kallon Up&down.

"Wai kana nufin dah ɗin hannu zaka ɗauka ka mare ni dan bakada hankali, ƙarya nayi ne ba miskiniyar bace?, i just do hope that ba akanta ZEEDAN ke wulaƙanta ni ba" ta ƙarashe tana kallon cikin idanun DEENAH dake saitin ta.

Momy ce ta tashi tare da fizgo hannun Khairat sukayi waje.

Duk da kallo su Umma suka bisu, zuciyar su cike da ɗumbin mamaki akan Khairat ɗin.

"Wannan wace iriyar yarinƴa ce haka, anƴa kuwa kwakwalwar ta ɗaya?" faɗin Mami.

Shiru kawai Umma tayi tana kallon DEENAH idanun ta na kawo ruwa.

"Su waye su ɗin, maiyasa suke son ƙarawa ƴata damuwa?" ta faɗa tana tashi tayi wurin DEENAH tana rungumo ta jikin ta.

"Umma am definitely sure yarinƴar nan bata da hankali, ki daina wani damuwa akan abinda tayi, bakya tunanin idan DEENAH taji kina kuka hakan ne zai sanƴa ta cikin damuwa?" cewar Jafar.

"Kai kuwa Jafar tayaya zata ji mutumin da babu abinda ke motsi a jikin shi" cewar Mami cike da mamaki.

"Mami tanajin dukkanin abin dake faruwa, sai dai kawai ba zata iya reacting bane sakamakon motsin da bata iya yi, amma dukkanin abinda akeyi tana ji."

Kallon ta kawai Mami keyi cike da tausayin ta, ace ƙaramar yarinƴa kamar DEENAH da cutar stroke "Allah ya baki lafiya, ya tashi kafaɗun ki" ta faɗa.

Da Amin Jafar ya amsa kafin yace "Umma nikam na tambaye ki mana, tunda deen ta samu hatsari Abdul yazo duba ta kuwa?."

Kai kawai Umma ta girgiza masa alamun a'a kafin kuma tace "DEENAH tace min yayi tafiya kafin ta samu hatsarin nan, maybe har yanzu bai dawo ba dan kuwa nasan babu abinda zai hana shi zuwa."

Yatsina fuska Jafar yayi dan kuwa shi dama Abdul ɗinnan ba wani burge shi yake ba duba da yadda yabi yayi ta takurar sa har ya samu ya shawo masa kan DEENAH, ba dan yaso hakan ba sai dan kawai shi ɗin ya kasance ɗa ne ga Ƙawar Umma.
"Amma Umma mahaifiyar sa fah?, ai ita yaci ace ta sani koh tunda ƙawar ki ce."

"Hajiya Dija ai bata ma ƙasar ita, amma na sanar mata bansan koh ta faɗawa Abdul ɗin koh bata faɗa masa ba."

Shiru kawai Jafar yayi ba tare da ya sake cewa komai ba.



*********************


"Dad maiyasa kace ka..."

"ZEEYAD sabida idan nayi hakan toh haƙika na cuce ka, sabida na daɗe da gano cewa zuciyar ka ba Khairat takeso ba sai dai dan kawai kada ka sa6awa umarnin mu yasa ka amince da hakan, bayan nan kuma ɗabi'u da halayyar Khairat sam basu dace da mutum kamar ka ba, haƙiƙa idan na aura maka Khairat na cuci rayuwar ka ne, duk da kuwa bansan komai akanka ba, amma nayi tunanin idan na baka auren Khairat ban kyauta maka ba, dah ace kanason Khairat dah ka bar dukkanin abinda kasan kakeyi kazo anyi muku Engagement, sai dai kuma ka kasance wurin wacce zuciyar ka ke so wato wannan yarinƴar, na san ba ƙaramin so kakeyi mata ba tunda har ka iya kasancewa da ita tsawon wadannan kwanaki, ZEEYAD ba zanyi maka dole koh tilasta maka cewa sai ka auri Khairat ba bayan da akwai wacce kakeso, ni nan zan tsaya maka indai kanason yarinƴar chan da aure nikuma zan nema maka auren ta, sannan kuma na tabbatar da cewa ba'a sami wata matsala game da gano koh ainihin wanene kai ba, ni nan zan zame maka uba."

Sosai ZEEYAD yaji farin ciki a ransa game da maganganun da Daddy yayi, tsugunnawa yayi ya hau korawa Daddy godiya "Nagode, Nagode maka Daddy da Allah yasa ka fahimce ni, kayi haƙuri da ƙin amintar da zuciya ta tayi wa ƴar ka, tun ban kai haka ba na fara son MADEENAH, she is my first love, ita ɗin ta daban ce a cikin mata, tana da kirki kuma tana da hankali, she was 10 and i was 20 back then, zuciya ta ta fara sonta ne tun lokacin da na ɗaura idanu na akanta, sai dai ban gane hakan ba har sai bayan rabuwar mu da shekaru goma, ta kyautata min sannan kuma bata kyamace ni ba a lokacin da nake yawo tamkar almajiri, bata guje ni ba a lokacin da kowa yake gudu na sannan kuma yake nisan ta kansa da kaina a lokacin ne kuma ita take sake kusanto ni, ta yi min abinda koh Family na basuyi min ba a rayuwa, why then ba zan sota fiye da haka ba ma, she is a girl with a golden heart, I Love Her Dad."


Dafa kafaɗun sa Daddy yayi yana miƙar dashi tsaye yace "Alright ZEEYAD, just consider auren ka da ita kamar ya ɗauru ne, i will make sure it happens."


"Thank you so much Dad, kayimin abinda koh wanda ya haife ni baiyi min ba."

"Stop saying that ZEEYAD, koh ka manta tun kana ƙarami iyayen ka suka mutu ne?, haka Allah ya tsara taka rayuwar ba tare da zakaci moriyar mahaifin ka ba."

Shiru ZEEYAD yayi yana kallon Daddy kafin kuma yace "Actually Dad, na daɗe inason na faɗamaka gaskiya, am sorry but nayimaka ƙaryar koh ni wanene."

"What, what are you saying ZEEYAD."

"I know ranka zai 6aci sabida nayimaka ƙarya tun farko that i have been fooling you all this while, the truth is that...." shiru yayi bai iya ƙarasawa ba yana kallon Daddy ɗin.


"Come on tell me, menene baka faɗamin ba game da rayuwar ka?."

"Actually Dad, my Father is alive, sannan kuma ina da family, ban rasa family na a hatsari kamar yadda na faɗamaka a farko ba, sabida gudun kada kace na koma garesu."

"What, you have a Family?."

Kai ya jinjina masa nan yace "Come on let's sit and discuss this" ya faɗa yana samun wuri ya zauna.

Zama ZEEYAD ma yayi kafin Daddy yace "Tell me everything about your life ZEEYAD."


Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina kansa a ƙasa yace "The truth is that, i wasn't a begger but...but an Abandoned Prince" ya faɗa kansa a ƙasa zuciyar sa na zafi.

Shiru Daddy yayi yana duban sa cike da mamaki, dan kuwa sam bai fahimci inda zancen ZEEYAD ɗin ya dosa ba "An Abandoned Prince?, bangane ba, can you explain further?."

Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa kafin yace "I mean am a Prince, but my Dad abandoned me when i was 10."

"Kana nufin kace min kai ɗan Sarki ne?" cewar Daddy cike da mamaki yana kallon sa.

Kai ZEEYAD ya jinjina masa, nan Daddy ya sake cewa "But..how could you be a Prince i mean bakayi kama da ɗan sarki ba."

"That is because i was Abandoned after my Mom's death, my own Father Abandoned me, he treated me like an outsider."

"ZEEYAD tell me more about yourself."

Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina dan kuwa sam bayason tuno irin rayuwar wahalar da yayi a baya, bayason tuno da kowa daga cikin family ɗinsa hakan na matuƙar ƙona masa zuciya tare da ƙara tsanar su a cikin zuciyar sa, babu abinda zai sanƴa shi komawa ƙasar sa a yanzu face saboda Family ɗinsa dake chan wato Family ɗin abokin sa Sadeeq, dan kuwa Family ɗinsa maƙiyan sa ya ɗauke su ba ƴan uwa ba, sai dai dukda haka ba yanzu yakeson komawa ba tukun har sai yayi gagarumar shirin da koh kallon banza mutum bai isa yayi masa a bayan sa ba, so yake yayi proving ɗinsu wrong kan cewar ba zai ta6a samun cigaba a rayuwar sa ba, sai dai yanzu baya cikin nutsuwar da zai tinkare su har sai MADEENAHn sa ta samu lafiya ta hakan ne kaɗai zai sami kwanciyar hankalin aiwatar da abinda yayi niyya.

Ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya miƙe tsaye tare da zuba hannayen sa cikin aljihu, juyawa Daddy baya yayi kafin kuma yace "20 Years Ago, A Heir was born to the King of Egypt(Cairo), bayan jiran da yayi shekaru goma Allah bai basa haihuwa ba, One fateful day, my Mom got pregnant to me, and after nine good months....i was Born."


*20 YEARS BACK*


"""""""""Cike da matuƙar girmamawa suka zube gaban mai Martaba "Your Highness, an turo mana cewar mu faɗa maka cewa naƙuda ya kama Sarauniya LATEEFAT dama kuma Sarauniya Hafeezah, zaka iya zuwa dan ganin wacce zata riga haifa maka magaji a cikin su kamar yadda al'adar wannan MASARAUTA ta tanadar."

Cike da kiɗima mai Martaba ya fice daga ƙatuwar faffaɗar Fadar tasa izuwa babban asibitin Masarautar dan shaida wa idanun sa wacce zata riga haihuwa tsakanin matan nasa biyu wato Hafeezah dama kuma Lateefat.

Isar sa asibitin bai zarce koh ina ba sai ɗakin haihuwar, inda mata biyu ke kwance koh wacce akan gado daban, inda kuma wasu dattijai mata uku ke kan kowacce daga cikin su dan kar6ar haihuwar ta.

Duban sa ya maida gun ta gefen dama wacce da alamu tafi ɗayar shan wahala sosai sakamakon irin nishin da take.

Da sauri ya tako wurin ta yana kama hannayen ta cikin muryar tausayi ya furta "Lateefat?."

"Your Highness...mu...tuwa zanyi" ta faɗa cike da azabar da take ciki inda kuma gumi duk ya gama wanke mata fuska da jiki.

"Ki bar faɗin haka Lateefat ba zaki mutu ba, zaki haifa mana ɗan mu sannan kuma mu rayu cikin aminci da ƙaunar juna, ba zaki mutu ba" ya faɗa yana sumbatar ta a goshi.

"Your Highness, muna buƙatar ruwan maganin gargajiyar nan dan baiwa Sarauniya Hafeezah dan kuwa da alamu har yanzu haihuwar tata da ɗan saura, gashi kuma ba ƙaramin wahala take sha ba, wannan ruwan maganin shi zai rage mata zafin naƙuda."

"Wanne irin maganin gargajiya kuma, Ina ruwan addu'ar da Liman ya aiko?" cewar mai Martaba da ya ruɗe ganin halin da Lateefat ke ciki.

"Allah ya huci zuciyar ka ranka ya daɗe, amma wannan ruwan Sarauniya Hafeezah ta zubar dashi bayan munyi-munyi akan ta sha amma taƙi."


Cike da zafin zuciya mai Martaba yace "Ku kyale ta, ku cigaba da kula da ita har lokacin haihuwar tata tayi" ya faɗa yana juyawa ga Sarauniya Lateefat.

Bayan doguwar naƙuda dama kuma gwagwarmaya da Sarauniya Lateefat ta sha ne, ta haiho santalelen ɗanta kyakkyawa sosai son kowa ƙin wanda ya rasa, wata iriyar doguwar ajiyar zuciya taja tare da furta "Alhamdulillah."


Murna a wurin mai Martaba ba'a cewa komai, dan haka saurin goge yaron akayi bayan an yanke masa cibi akayi wrapping ɗinsa da towel sannan aka miƙa shi ga mai Martaba dake ta miƙo hannu tunɗazu dan kar6ar ɗan nasa.

Kallon fuskar yaron da yake kama dashi yakeyi ba tare da murmushi ta gushe daga kan fuskar sa ba.

Sumbatar yaron yayi tare da rungume sa yanajin soyayya dama kuma ƙaunar yaron na baibaye duk wani 6argo dama kuma cikin jini haɗi da jijiyoyin jikin shi.

Bakin sa ya kai kunnen yaron tare da yi masa huɗuba da sunan *ZEEYAD* yana sake rungume sa a jikin shi.

Ɗan tallafowa yayi yace "Lateefat, ba na faɗamiki ba, zaki haihu lafiya sannan kuma mu rayu da ɗan mu cikin ƙaunar juna."

Murmushi tayi tana miƙa masa hannu alamun ya bata yaron.

Yaron ya bata kafin ta rungume sa tanajin soyayyar sa sosai a cikin zuciyar ta, Allah ya amsa addu'ar su yau bayan shekaru goma da sukayi basu samu haihuwa ba, babu abinda zasu ce sai dai su ƙara miƙa godiya marar iyaka ga Ubangijin sammai da ƙassai.

Yaron aka amsa kafin mai Martaba ya fice dan zuwa ya sa a sanar da haihuwar mata mafi soyuwa a gareshi cikin matan nasa.

Fitar sa bai wuci da mintina goma ba Sarauniya Hafeezah ta sambaɗo nata kyakkyawan yaron shima.

Inda kuma zuciyar ta ke cike da ɗumbin baƙin cikin riga ta haihuwa da Lateefat tayi.

A haka aka sallami kowacce bayan sun huta.


****************


Duk wani lungu da saƙon wannan MASARAUTA cike take da dumbin jama'a kowane na kai da komowa, kallo ɗaya zakayi musu kaga irin tsantsar farin cikin da suke ciki, sakamakon sadakar kayan abinci haɗi da na sawa da ake tayi musu.

Yayin da kuma kiɗan Drums ke ta tashi ta koh ina, fadar ta cika da ɗumbin jama'a dan taya sarki murnar samun ƴaƴa maza a lokaci guda.


Zaune suke kusa da sarki Inda shi kuma yake tsakiya kan doguwar throne ɗinsa fuskar cike fal da farin ciki.

Gefen sa Queen's ɗinne kowacce da nata jaririn a hannu, hankalin su na kan wasannin da ake gabatar wa dan taya su murna.

Sai dai kallo ɗaya zaka yi wa Sarauniya Hafeezah ka gano tsantsar baƙin ciki akan fuskar ta, babu abin dake ƙara mata hakan sai ganin Sarauniya Lateefat dake farin ciki tana murmushi.

_"Kiyi murmushin ki yadda kika so, muddin ina raye wannan murmushin ya kusa zama baƙin ciki a gare ki, i will make sure that i ruin your happy life"_ ta faɗa a zuciyar ta cike da mugun nufi.

Sarauniya Nazeerah kuwa da ta kasance Uwar gida kuma bata samu haihuwa ba, koh a fuska bata nuna alamun baƙin ciki da haihuwar kishiyoyin nata ba, sabida ta san da akwai wata babbar gwarama da ta kusa afkuwa tsakanin wadannan kishiyoyi biyu da suka haifu rana ɗaya, nata dai bai wuci kallo ba, dan kuwa bata ga abinda zai sa tayi baƙin ciki dasu ba, dan koh bakomai ita ya fara sani kafin su, sannan kuma babu abinda ta nema ta rasa a cikin gidan, kama daga kan dukiya, abinci sutura da sauran su, haka kuma baya ƙunsa mata baƙin ciki koh yi mata gori akan rashin haihuwa, dan haka bata ga wani abin tada hankali ba, ita dai nata bai wuci taji daɗin husuma ba.

A gaban ɗumbin mutane aka naɗa Sarauniya Lateefat a matsayin *QUEEN MOTHER* kasancewar ta uwa ga babban yarima kuma ɗan da zai gaji sarki.

Sarki da kansa ya ɗaura mata Diamond Crown a kanta tare da yi mata Tsadaddun kyaututtuka, haka ma kuma ƴan uwa da abokan arziki kowa yaba ta yake da ɗan da ta haifa tare da yi mata kyaututtuka masu kyau da tsada.

Ganin anfi koɗa Sarauniya Lateefat akanta hakan ya sake hura mata wutar tsanar ta dama kuma tsanar jaririn da ta haifa ɗin a cikin zuciyar ta.

Haka aka gama taro mutane suka watse daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login