Showing 210001 words to 213000 words out of 236327 words

Chapter 71 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45375

sosai koh dan su saba da juna ma sannan DEENAH ma ta rage wasu daga cikin damuwar ta.




*THREE WEEKS LATER*


_______Sosai DEENAH ta warke taji sauƙin jikin ta, a yanzu har ta saba da zaman part ɗin nasu ita kaɗai, kasancewar ZEEYAD ya saya mata waya kullum tana cikin waya da ƴan gida hakan na rage maka kusan kaso 70 cikin damuwar da take ciki, ga kuma wata iriyar kulawa ta musamman da take samu daga 6angaren ZEEYAD da Grandma ɗinsa hatta mai Martaba ɗin ba'a barsa a baya ba wurin nuna mata ƙauna da kulawa.

Hakan ba ƙaramin baƙanta ran Sairah yake ba, ganin duk cikin surukan sa yafi ɗaukin DEENAH haka ma sauran mutane kowa ji da ita yake ita ɗin da ba komai ba.

Tsaye take gaban mirror tana rolling gyalen peach abayar dake jikin ta, dan kuwa so take ta kaiwa JALILAH da bata gajiya da zuwa duba ta ziyara ita ma yau.

Sosai tayi kyau cikin shigar tata, wayar ta kawai ta ɗauka tare da fitowa tana sanƴawa ɗakin nasu key kafin ta shiga sauƙowa ƙasa.

Bayin dake ta aikace-aikace ne tace dasu "Ku bar aikin haka nan, zan fita idan na dawo zan ƙarasar da kaina."

Cike da girmamawa suka tattari kayan aikin nasu suka fice.

Bin bayan su tayi tana rufo ƙofar falon, wasu bayi mata ne da aƙalla zasu kai biyar suka doso ta dawuri ganin kamar fita takeson yi.

Saurin ce musu tayi "Kuje ku huta bana buƙatar rakiya ba nisa zanyi ba."

Kasancewar part ɗinsu na kallon juna ya sanƴa kawai kwalta ta tsallaka tana shigewa ciki babu wanda yayi yunƙurin tsaida ta saima gaisuwa da tayi ta kwasa har ta isa ga falon ƙasa wanda yadda komai na part ɗinsu haka ma wannan ɗin yake.

Zama tayi cikin ɗaya daga couchs ɗin falon, wata kuyanga ce ta ƙaraso inda take tare da faɗin "Sannu da zuwa ranki ya daɗe gimbiya, da wa kikeson ayi miki sallama?."

"Da uwargidan" ta bata amsa a takaice.

Duƙar da kai tayi cikin girmamawa kafin ta shige wani lungu cikin falon.

Ba'a wani jima ba sai gata baiwar ta dawo tace "Tace na iyo miki iso zuwa ciki."

Miƙewa DEENAH tayi tana mara mata baya, JALILAH ta gani a kitchen da alama dai abincin rana take ƙoƙarin haɗawa.

Murmushi ta sakarwa DEENAH dake shigowa inda ta maida mata martani.

Kujera DEENAH taja daga cikin kujerun dining ɗin kitchen ɗin tana zama, kafin kuma wasu bayin su shiga serving ɗinta.

Wanko hannu JALILAH tayi kafin tazo taja kujera kusa da DEENAH tana zama tare da faɗin "Kece yau a gidan mu?."

Murmushi DEENAH tayi kafin tace "I thought yakamata nima yau na shigo, koh bakomai zan huta da gori."

"Gaskiya kam kin wanke kanki" ta faɗa cikin ɗan dariya kafin ta ɗaura da faɗin "Kin zo a daidai, favorite ɗin mijin ki nake ƙoƙarin haɗawa, mai zai hana ki koya ki dinga yi masa?."

Murmushi DEENAH tayi kafin tace "I will love to."

Miƙewa tsaye JALILAH tayi tace "Come and have a look then."

Miƙewa ita ma DEENAH tayi tana mara mata baya zuwa inda tukunƴar girkin take, sosai ta maida hankali gun abinda JALILAH ke koya mata ɗin har suka kammala.

Serving musu tayi bayan sun kammala girkin, suna cikin ci Sairah ta faɗo kitchen ɗin.

Tsaye tayi tare da riƙe kunkumi tana aika musu da wani irin mugun kallo.

Murmushi JALILAH tayi tace "Sairah?, ki ƙaraso mana ki zauna."

Kallo ta ƙare mata sama da ƙasa kafin ta buɗi baki tace "Mai kike taƙama dashi ne?, i was waiting for my lunch tunɗazu only to find out kin ajiye wannan abar kuna cin abinci tare, ina nawa kason toh, kema dai kinsan ba girki na iya ba bale kice zan girka da kaina naci, idan ma kina tunanin akwai bayin da zasu girka su bani naci ne then miye amfanin ki, you know how to cook well that means kece zaki dinga yi mana girki muna ci baki ɗayan mu, wane irin salon rainin wayo kuma kika 6ullo dashi na hana ni abincin rana, a gidan miji na, i can't believe you JALILAH."

Shiru JALILAH tayi mata kamar wata mai tsoron ta, kallon ta DEENAH take ganin koh zata tanka mata amma batayi hakan ba, kenan ya tabbata tsoron ta takeji dagasken.

"You know what, dole ne Ummie taji wannan maganar."

"No please" cewar JALILAH ɗin tana miƙewa tsaye ta ƙaraso wurin ta tare da dafa kafaɗun ta tace "Ba sai maganar yaje gun Ummie ba, am sorry i thought we're sisters and..."

Yarfar da hannun JALILAH tayi tace "Sisters with who?, listen JALILAH ni fah kawai ina zama dake kuma ina ɗan kula ki coz i have no other choice, but that doesn't mean zaki dinga yimin dukkanin abinda ranki keso dan kawai an baki matsayin uwar gida ba shi ke nufin zaki yimin abinda ranki yaso bane..."

"But ban hana ki abinci ba, abincin ki a ajiye yake, why don't you try to make some peace koh da na kwana ɗaya ne a tsakanin mu, you always have a way of insulting me koh da abu bai kai ya kawo ba, sannan bakida aiki a kullum sai ɗaura min sharri a gun Ummie, babu abin dake a raina wanda ya wuce muyi zaman lafiya tsakani na dake but you always have a way of mocking and criticizing me a duk abinda nayi, and yarda da Ummie keyi dake a kullum shi ke ƙarfafa miki guiwar cigaba da halayen ki, why don't you understand cewa ni banason rigima atleast you should try to make some peace with me tunda har kika gane ni rigima ba abinda na kware a kai bane."

"Hmm, Peace?" ta faɗa tana kallon ta kafin ta ɗaura da faɗin "I never learnt what that was, bansan shi ba bale nayi zaman shi dake, ke kishiya ta ce which means am sharing a Husband with you, how do you expect me to make Peace with you then?, ban ɗau kishiya a matsayin abokiyar zaman lafiya ba, sai dai kuma kash you're so fucking calm sam banso halayen ki a haka ba..."

"Ba zan ta6a yin rigima dake ba, ina faɗamiki ne sabida kin fara kai ni bango, kiyi ƙoƙarin gyara halayyar ki towards me please."

Murmushin gefen baki ta saki kafin tace "Ai baki ma fara ganin komai ba tunda har dani kike kishi kaɗan kenan kika gani daga cikin abubuwan da zan iya aikatawa, sannan zan so ace na tunzura ki na kai ki bango ɗin sabida rigima cikin jinin jiki na take, bansan wani abu wai shi lumana koh makamancin sa ba, maganar da kikayi min yanzu ki tabbatar shine sanadiyyar buɗewar ƙofar duk wasu fitintinun da zasu cigaba da wakana tsakanin mu nan gaba, you just wait and see muddin ina cikin gidan nan then keda farin ciki kunyi hannun riga kenan, this is my promise to you" tana faɗin haka ta fice a fusace daga kitchen.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka sauƙowa JALILAH a ƙunci tana bin inda Sairah tabi da kallo.

Juyowa tayi ga DEENAH da ta zuba musu ido tunɗazu tana kallo, murmushi ta ɗan saki kafin tazo taja kujera ta zauna.

Koh kaɗan DEENAH batayi mata magana akan rigimar tasu ba, sai ma wani shafin hirar ta daban da ta buɗe har sai da taga Jalilah ɗin ta saki jikin ta sosai kafin ta tashi ta tafi.


**********************


_________Zaune yake gaban sa ɗauke da system ɗinsa yana dannawa, DEENAH dake kwance tayi matashi da laps ɗinsa ne ta kira sunan sa a hankali "Abyad?."

Rufe Laptop ɗin yayi kafin ta tashi zaune tana kallon sa, cikin kulawa yake kallon ta kafin yace "Seems like akwai magana a bakin ki, tell me."

"Abyad it's about JALILAH."

"What about her?" ya faɗa yana kallon ta.

Shiru tayi kafin tace "Baka fahimci tana cikin damuwa ba?."

Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Well ni kullum ke nake gani ba wata ba, how then zan san irin halin da take ciki."

Abinda ya faru tsakanin JALILAH da Sairah ta kwashe ta faɗa masa kafin ta ɗaura da faɗin "You should talk to you YAZEED he is their Husband and i know ba zai rasa hanƴar tackling ɗin issue ɗin ba, atleast JALILAH deserves to be loved, cemin fah tayi mahaifin ta da yayan ta koh taje gidan su sunyi ta ya6a mata baƙar magana suna sanƴa ta baƙin ciki in the other hand kuma YAZEED'S Mom tana yarda da dukkanin abinda Sairah ta faɗa mata akan JALILAH ita kuma ba zata so ji daga bakin ta ba sai ta hau ta da faɗa tana gaya mata baƙi, and YAZEED in the other hand sam shima baya nuna mata wani damuwa iyaka cin su gaisuwa ne kawai tsakanin su, talk to him please i know yana jin maganar ka sannan zai ɗau shawarar ka, kaji."

Huci ya fesar kan ya numfasa yace "Alright, i will talk to him tunda hakan kikeso, you happy?."

Kai ta jinjina masa nan ya rungumo ta jikin sa yana patting bayan ta a hankali yace "Your wish is always my command Queen."

Murmushi DEENAH tayi kafin kuma yace "Jibi zamu tafi Honeymoon ɗinmu, i know zaki so yin nesa da nan for sometime."

Cike da farin ciki ta rungume shi tightly tana murmushi tace "Allah ya kaimu."

Agogon dake manne jikin wall ɗin falon ya duba kafin kuma yace "It's getting late, mu kwanta haka nan."

Ɗagowa tayi tana tashi tsaye, shima ɗaukar system ɗinsa yayi tayi gaba yana biye da ita.

Canza kayan ta tayi izuwa silky doguwar rigar bacci, kafin ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito tare da nufar Bed ta kwanta bayan ta tofe jikin ta da addu'a.

Shima ZEEYAD canza kayan sa yayi izuwa brown Jallabiya ya ɗauro alwala kafin ya kashe musu hasken ɗakin, ƙarasowa yayi ya rage musu hasken side lamps ɗin kafin ya haye kan bed ɗin yana janƴo ta jikin sa.

Hannun ta ɗaura kan nasa dake manne a cikin ta a haka har bacci ya ɗauke ta.

Cikin bacci yaji kamar ana hura masa iska mai tsananin zafi koh wanda ake kwarawa dukkanin jikin sa ruwan zafi.

Tun yana iya daurewa har ya kasa ya shiga buɗe idanun sa da sukayi tsananin kaɗawa yayin da zuciyar sa keyi masa zafi da wani irin raɗaɗi haɗi da bugu tamkar zai faso ƙirjin sa ya fito.

Buɗe idanun sa ke da wuya yaga shigewar wani irin baƙin hayaƙi cikin jikin sa.

Runtse idanu yayi sakamakon wani irin zafi da zugi dake ta ƙara sukar zuciyar sa haɗi da fatar jikin sa.

Ƙame jikin sa da ya fara rawar sanƴi yayi yana jin kamar wanda ake yayyanka tsokokin jikin sa a haka har ya faɗi ƙasa dafe da saitin zuciyar sa, daga nan kuma duhu mai tsananin gaske ya mamaye masa idanu.

Alarm ɗin ƙarfe ukun da ta saita a wayar ta ne ya shiga ringing, idanu ta buɗe tana janƴo wayar daga kan bedside drawer tare da kashe alarm ɗin, zaune ta miƙe ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci kafin ta kunna bedside lamp tana maida duban ta gefen da yake kwanciya, wayam ta gani dan haka maida duban ta tayi ga inda suke sallah nan ma dai bata gansa zaune ba.

Miƙewa tayi ta sauƙo daga kan bed ɗin ta shiga takawa zuwa bakin ƙofa, jin ƙofar tayi a rufe alamun dai ba'a fita daga ɗakin ba.

Wutar ɗakin ta kunna take ɗakin ya gaurayu da haske, bathroom da nufa tare da buɗewa ta shige sai dai tayi dube-duben ta bata ga kowa a ciki ba, tsoro ne ya fara kama ta, toh ina yayi?, shine tambayar da ta yiwa kanta.

Takowa tayi da niyyar zuwa ta duba closet room taji tayi tuntu6e da abu take ta faɗi ƙasa dan sam bata lura dashi ba, ƙara ta ɗan saki sakamakon goshin ta da ya ɗan bugu kafin tayi saurin maida duban ta kan abinda tayi tuntu6e dashi ɗin.

ZEEYAD ta gani kwance, ba tare da ta kawo komai ranta ba ta rarrafa zuwa inda yake hannayen ta ta ɗaura kan ƙirjin sa ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa akan ya tashi suyi sallar Nafila.

Gani tayi koh motsawa baiyi ba "Abyad?" ta sake kira a hankali.

"Abyad ka tashi mana" ta faɗa tana sake jijjiga shi.

Ji tayi kodai wasa yakeyi mata ne tashi tayi ta ɗauko ruwan gora kafin ta shiga yayyafa masa, nanma gani tayi koh gezau baiyi ba.

Dropping ruwar gorar tayi yana faɗi ƙasa kafin ta durƙusa da sauri tana manna kanta da ƙirjin sa tare da saurarar bugun zuciyar sa.

A razane ta ɗago zuciyar ta na dukan tara-tara, sake maida kanta tayi dan koh tana tunanin bataji bane mai kyau, nan ɗinma dai thesame thing ta sake ji.

Ɗagowa tayi da sauri idanun ta na tara hawaye ta shiga lalumar jikin sa, hannun sa ta ɗaga tana saurarar pulse ɗinsa, sakin hannun tayi da sauri tana ja da baya kafin kuma ta shiga girgiza kanta cikin kukan dake zuwan mata ta shiga faɗin "No... no... this... this can't be... you can't be dea.." bata ƙarasar ba ta sake rarrafawa da sauri tana komawa wurin nasa tare da ɗago da kansa tana rungume shi a ƙirjin ta, fuskar sa ta shiga kallo kafin tace "I know you're kidding me, i know you're not dead, maybe... maybe you're sick... yes i know you must be sick that is why you're unconcious" ta faɗa cikin tatta6a fuskar sa zuwa wuyar sa da yake sanƴi babu alamun zazza6i.

Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri tana zuwa ta lalumo wayar sa kafin kuma cikin rawar hannu ta shiga neman numbern Grandma.

Kafa wayar tayi a kunnen ta lokacin da ya shiga ringing, har ya katse bata ɗaga ba, dan haka ta sake dialing sai a karo na uku kafin ta ɗaga kiran, ba tare da DEENAH ta jira cewar ta ba ta shiga faɗin "Grandma... Grandma kizo dan Allah Abyad ba shida lafiya... dan Allah kizo da wuri" tana faɗin haka ta katse wayar da sauri tana komawa wurin sa tare da tallafo kansa tana sake kiran sunan sa "Abyad dan Allah ka tashi, kada kayimin haka you can't be dead now, baikamata ka tafi ka bar ni ba i will be doomed without you Abyad dan Allah ka buɗe idanun ka and talk to me i beg you Abyad please" ta ƙarashe cikin kuka sosai tana shafa fuskar sa.

Bai fi da 5mins ba Grandma ta ƙaraso kafin ta shiga kwankwasa ƙofar tana kiran sunan "DEENAH."

Da sauri DEENAH dake rungume da ZEEYAD ta tashi tana ƙarasawa bakin ƙofar ta buɗe, tare da riƙo Grandma cikin kuka take faɗin "Thank GOD you're here, ina ta tashin shi tunɗazu baya motsi bansan mai ya faru dashi ba."

Hankali tashe Grandma ta ƙarasa inda yake kwance da sauri tana kallon sa a hankali kuma ta shiga kiran sunan sa "Boy" tana shafo fuskar sa.

Cikin kuka DEENAH tace "He isn't waking up tunɗazu nake tashin sa amma baya motsi, am scared kada wani abin ne ya same shi."

"He will be fine insha Allah, i know he will be fine, ɗaukomin waya na kira YAZEED."

Da sauri ta miƙe tana zuwa ta ɗau wayar sa tare da miƙawa Grandma, amsa tayi kafin ta lalumo wayar YAZEED ta shiga buga masa.

Firgigit Sairah da wayar ke riƙe a hannun ta tayi lokacin da ya ɗau vibration, ganin mai kiran ne ya tabbatar mata da cewa aikin su ya tafi according to plan, ta san DEENAH ce mai kiran, murmushin gefen baki ta saki har kiran ya katse bata ɗaga ba.

Wani kiran taga ya sake shigowa shima har ya tsinke bata ɗaga ba, kira na uku taga ya sake shigowa dan haka tayi rejecting call ɗin, har sau uku ana sake kira tana rejecting kafin ta rubuta text message da faɗin _"Stop disturbing Bro"_ murmushi tayi kafin kuma ta danna send button take text ɗin ya tafi.

Goge duk wani call log da text ɗin tayi yadda dai ba za'a gane ta ɗau wayar ba, kafin kuma ta shiga settings tayi disabling ɗin fingerprint ɗinta da ta sanƴa, wayar ta ta ɗauko kafin ta yiwa Sarauniya Hafeezah text da _We did it, everything went according to planned"_ tare da danna send button ya tafi.

Lalla6awa tayi izuwa ɗakin YAZEED dake bacci kamar ma wanda baisan inda kansa yake ba, ta ajiye masa wayar sa tare da ficewa cikin sauri.

Wurin Hafeezah kuwa murmushi ta saki bayan tayi receiving text ɗin Sairah "So now let's see how you become the king, muddin ina raye only YAZEED can be the King no one else, you were my biggest problem but now that i have get ridden of you i feel like the world is my hands" ta ƙarashe cikin dariya ranta fari sol sabida ta gama da ZEEYAD sai dai wanin sa kuma ba shi ba, tunda taji nan da jibi za'a naɗa shi Sarki kamar yadda Abdulhakeem ya sanar da ita hakan ya sanƴa batayi ƙasa a guiwa ba ta aiwatar da shirin ta bayan ta sami wani babban boka da ya kware wurin aikin sa.

Dariya tayi kafin tace "Let's see who you Surprised then your Highness, idan bakayi surprising ɗinsa wurin naɗa sa sarki ba, ni nan nayi surprising ɗinka da gawan ɗanka gobe da safe, so prepared to cry the tears of true remorse your Highness, your dearest son is no more, let's see who you give your throne to then" ta faɗa cikin gimtsewar fuska.



6angaren Grandma kuwa mamaki ne ya cika su ganin abinda YAZEED yayi musu.

DEENAH ce tace "Grandma, ki kira Sadeeq i know he will be here soon."

Kallon ta Grandma tayi kafin tace "Kafin Sadeeq ya iso nan yanzu gari zai iya wayewa, sabida tsakanin gidan su da nan akwai nisa sosai."

"But what do we do Grandma, we've to save him kafin wani abin ya same shi" ta faɗa cikin kuka.

Kallon ZEEYAD da baya motsi Grandma tayi, sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi dan kuwa bata tunanin inda akwai rai tattare dashi, ta san maƙiya sunyi nasara akan shi.

Sunkuyar da kai tayi wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo mata, a hankali itama ta fara sakin shessheƙar kuka ganin angama mata da ɗan jikan nata wanda shi kaɗai ne yanzu gatan ta a duniya.

Cikin rawar murya DEENAH dake kallon ta tace "Grandma, maiyasa kike Kuka, bai fah mutu ba, bashida lafiya ne kawai."

Shiru Grandma tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login