Showing 207001 words to 210000 words out of 236327 words

Chapter 70 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45307

my wife is about to be executed together with her maid, sakamakon mummunar laifin da suka aikata wacce ta sa6awa dokar Allah dama kuma ta MASARAUTA, wannan doka bata duban girman mutum koh level ɗinsa, muddin hukunci ya hau kanka toh tabbas dole ne ka fuskance shi koh kai waye, ta haka ne kaɗai zamu rage yawaitar aikata miyagun laifuka a doron ƙasa, Naseeba here has crossed the line dukda kuwa cewa ta san hukuncin duba da ita ɗin matata ce doesn't mean za'a yi mata sassauci ya zama dole ne a yanke mata hukunci kamar kowa, kowa ya san laifin da ta aikata dan haka she will be executed."

Shewa ne ya karaɗe wurin rabi da kwatan mutanen wurin duk suna bada goyon baya akan hukuncin yayin da wasu kuma ke ta Allah wadai da wannan sabuwar hukunci.

Bisa ga umarnin sarki aka kama Naseeba da Kiki aka ɗaura su kan wasu dogin abubuwa yayin da aka rataye kawunan su jikin igiya kafin a rufe musu fuska da baƙar abu kamar hula.

Sosai Kiki ke kuka babu abinda take sai tsinewa Naseeba, haka ma 6angaren Naseeba wata iriyar tarin kunƴa da nadama ce ta rufe ta.

DEENAH ji tayi ba zata iya jurar ganin hukuncin da za'ayi musu ɗin ba, gani take yayi tsauri tunda ba wai kashe mutum sukayi ba.

Kallon ZEEYAD tayi tare da faɗin "Abyad stop them."

"What, why?."

"Stop them please" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka.

"What are you saying DEENAH, they tried to get you killed."

"But am alive, just stop them please" ta faɗa hawaye na kawowa idanun ta.

Rungume ta yayi yace "Ba dole sai kin kallesu ba then" ya faɗa yana kare idanun ta daga kallon wurin.

Ita dai dukda haka bata yarda ba, dan kuwa bata tunanin zata iya bacci muddin akayi kisar nan a gaban ta.

Ɗagowa tayi ya sake maida ta, gently yake rubbing bayan ta tare da faɗin "Relax."

_"Pull_" shine abinda ta jiyo an faɗa da ƙarfi, kafin ta ankara kuwa tuni su Naseeba suka hau shure-shuren ƙafa har rai yayi halin sa, ƙara DEENAH ta saki tana sake ƙanƙame ZEEYAD ɗin.

Patting bayan ta yake a hankali yana sake rungume kanta a ƙirjin shi.

Wurin ne ya ɗau hayaniya bayan an kashe Naseeba da Kiki.

Kuka JALILAH dake kusa da YAZEED ta sanƴa inda ya juyo cike da mamaki yana kallon ta wondering koh menene ya sanƴa ta kuka kuma ita.

Ta6e baki Sairah tayi kafin tace "This is so interesting to watch, why is she crying?."

YAZEED bai kula ta ba, but hankalin sa na kan JALILAH ɗin dake ta sharar hawaye, tashi tayi ta bar wurin tana cigaba da goge hawayen ta.

Da kallon gefen ido ya bita yana karkaɗa ƙafafun sa dake yi masa zogi tare da umartar sa da akan ya bita, ɗan jim yayi kafin shima ya miƙe ya bar wurin.

Da kallo Sairah ta bisa kafin ta miƙe itama tana mara masa baya.


*********************

________Kwance take tayi lamo kan faffaɗar ƙirjin sa, har yanzun tunanin su Naseeba yaƙi barin mata kwakwalwa, da ta rufe idanun ta su kawai take gani.

Sake rungume ZEEYAD tayi tana 6oye kanta a ƙirjin shi, dan kuwa she feels so safe idan tayi hakan.

Gently yake patting bayan ta, lumshe idanu tayi tana sake cusa kanta cikin chest ɗinsa.

Ɗan murmusawa yayi kafin kuma yayi mata rumfa da hannayen sa yana kallon ta.

Buɗe idanun ta tayi kafin a hankali tace "What are you trying to do?."

"What i have been long waiting for" ya faɗa calmly yana goga hancin sa kan nata.

"I... i... i don't understand" ta faɗa cikin rawar harshe.

In a whisper yace da ita "It's just for an hour, i promise."

"What... bangane..." maganar tata ce ta carke sakamakon haɗe bakin su da yayi wuri guda.


_Toh ni dai har ga Allah naso tsayawa jiye muku gulma dama kuma kawo muku rahoton abinda zai wakana tsakanin su cikin wannan dare, sai dai iriyar muguwar kallon da oga ZEEYAD ya watso min ne ya sanƴa ni saurin fice musu daga ɗakin har biro ta na faɗi ƙasa, yanzu dai sai washe gari idan Allah ya kaimu na koma na ɗauko abina sannan na cigaba da suburbuɗo muku rahoto, yauwa_



*Yawan Comment, Yawan Posting*




07061979284
*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*



[9/4, 9:20 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```







*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*








*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*051...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




_________Buɗe idanun ta da sukayi mata nauyi sosai ta fara, koh ina na jikin ta ciwo yakeyi mata, abubuwan da ya aikata mata cikin dare ne suka shiga yi mata playing a kwakwalwa,lumshe idanu tayi wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo mata.

Da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe zaune tanajin yadda ƙasan ta keyi mata zugi sosai duk da kuwa irin ruwan zafin da ya taimaka ta shiga a jiyan cikin dare.

Yaye bargon dake rufe da ita tayi tana sauƙo da ƙafafun ta ƙasa, da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe ta nufi bathroom.

Wanka tayi sosai ta sake gasa jikin ta, sai a sannan ta ɗan ji dama-dama sakamakon ruwan zafin da ta sake shiga.

Fitowa tayi ɗaure da wata ƴar guntun towel tare da zuwa ta zauna bakin mirror.

Hand-dryer ta ɗauka ta shiga busar da jiƙaƙƙen gashin kanta da ta wanko, sai da ta tabbata ya bushe tass kafin ta gyara shi tana parking ɗinsa a baya sai sheƙi da ƙamshi na musamman yake tayarwa.

Lotions masu kyau da ƙamshi ta shiga mulke jikin ta dashi, tana cikin hakanne ZEEYAD ya buɗo ƙofar ɗakin ya shigo bakin sa ɗauke da sallamar wanda iya le6en bakin sa ne kawai sukayi motsi.

Sadda kai ƙasa DEENAH tayi cike da jin kunƴa har ya ƙaraso yana dafa kujerar da take kai.

Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta kai hannu ta ɗau deodorant ta shiga shafawa a jikin ta.

Ganin yayi shiru har wannan lokacin ne ya sanƴa ta ɗan ɗago da kanta tana kallon cikin mirror ɗin nan suka haɗa ido kafin kuma ta sake saurin maida kanta tana ɗan turo baki.

Hanci ya kai yana shinshinar daddaɗar ƙamshin gashin kanta, kafin kuma ya sumbace ta a wuya tare da yi mata raɗa a kunne yace "Good Morning Baby."

Cikin rawar murya take faɗin "Please ɗan miƙa min Hijabin chan."

Kallon ta yayi ta cikin mirror ɗin kafin yace "What Hijab?."

"Gashi chan."

"Ni ban gani ba" ya bata amsa.

Ɗan ɗagowa tayi ta kallesa kafin tace "Baka fah duba ba, idan ka juya bayan ka zaka ganshi."

Cikin kallon ta yake faɗin "Maybe sai dai idan zaki tashi ki nuna min inda yake sai na ɗauko."

Ɗan turo baki tayi cikin shagwa6e fuska tace "Please Abyaaad."

Yadda tayi maganar cikin langwa6ar da kai ne yayi bala'in tafiya da imanin sa, hakan ya sanƴa shi sakin baki yana kallon ta.

Sadda kanta tayi tana wasa da ƴan yatsun hannayen ta.

Murmushi ZEEYAD yayi kafin ya bar wurin zuwa closet room ɗinsu, ganin ya tafi ne ya sanƴa ta saurin miƙewa tana zuwa inda Hijab ɗinta yake ta sanƴa shi kafin ta sake dawowa gaban mirror ɗin ta cigaba da kwalliyar ta.

Shi kuwa fito mata yayi da kayan da zata sanƴa a hannun sa, murmushi kawai yayi ganin sai wani 6o66oye jikin ta take, shi kuwa babu abinda bai ƙarewa kallo ba a daren jiya.

Ajiye mata kayan yayi kan bed kafin yace "Idan kin shirya YAZEED is waiting for you downstairs kizo a canza miki sabon bandage."

Kai ta jinjina masa kawai, tana ganin ya fita ta miƙe tsaye ta taka zuwa bakin bed ta ɗau kayan da ya fito mata dashi ɗin.

Ba tare da ta cire Hijabin ba ta shiga shiryawa dan kuwa bata yarda koh yana la6e yana leƙen ta ba.

Cire Hijabin tayi tana nannaɗe shi, nan kuwa ta jiyo muryar shi a bayan ta yana faɗin "Seriously?."

Juyowa tayi nan ta ganshi ya haɗe girar sama da ta ƙasa yayi folding hannaye a ƙirji yana kallon ta.

Dama ta sani yana nan la6e yana leƙen ta, murmushi tayi kawai tana zuwa ta rataye Hijabin inda shi kuma ya ƙaraso cikin ɗakin yana riƙo waist ɗinta ta baya tare da saƙala kansa ta wuyan ta, cikin cool voice ɗinsa yace "Are you sure ban ji miki ciwo ba?."

Shiru DEENAH tayi tana rarraba idanu nan tace "What?."

Sake holding ɗinta yayi tightly bakin sa saitin kunnen ta yace "Well last night was full of..., i really don't know how to describe it, but you are so very very special babe."

Kunƴa ne ya kama DEENAH idanu ta runtse tana jin yadda palms ɗinsa ke yawo a cikin ta, hannun ta ta kai kan nasa tana riƙewa kafin ta shiga zame jikin ta.

Sake riƙo ta yayi yace "Am sorry i made you cry yesterday, i mean na ƙara miki ciwo akan wanda kikeji..."

Katse shi tayi da faɗin "It's alright, am fine" dan kuwa ta lura ma kamar bayida isasshiyar kunƴa kwata-kwata.

Murmushi ZEEYAD yayi yana juyo da ita tana fuskantar sa, kallon cikin idanun ta yayi kafin ya saki murmushi yace "Idan kin warke gabaɗaya, we're going on a honeymoon daga nan kuma zamu wuce Nigeria ki gaida ƴan gida" ya ƙarashe cikin ɗan jan ha6ar ta.

DEENAH bata san sadda ta saki wani irin murmushin farin ciki ba, nan tace "Really?" cike da farin ciki da zumuɗin da ya darsar mata lokaci guda.

Kai ya jinjina mata cikin murmushi, rungume shi tayi ƙam cike da farin ciki tace "Wow am so happy" kafin kuma ta ɗago tana duban sa tace "Yaushe zamuje."

"Idan kin warke gabaɗaya" ya faɗa.

"Nidai gaskiya na warke yanzu" ta faɗa cikin muryar shagwa6a.

Ɗan waro idanu yayi kafin yayi murmushi yace "Sabida kinji nace zan kai ki kiga ƴan gida, i can't take you there like this coz babu tantama idan na kai ki a haka then ba zasu bar ki ki dawo ba" ya faɗa cikin rashin jindaɗin abubuwan da ya faru da ita ɗin kafin ya ɗaura da faɗin "And it's all my fault, the blame is all on me, tun ba'a je koh ina ba na kasa baki kyakkyawar kulawa and i hate myself for that."

Saurin cupping fuskar sa tayi tana kallon sa tace "What are you saying Abyad, ka bar faɗin haka komai da kaga ya faru damu then a rubuce yake haka Allah ya ƙaddara rayuwar auren mu zata kasance, ba laifin kowa bane but jarabawar mu ce haka, i know we've gone through alot in life but that doesn't mean zamu baiwa kanmu koh wasu laifi akan dukkanin abinda suka faru, those that did wrong to us Allah ne ya ƙaddara hakan a garesu but sun kasa controlling ƙiyayyar su a garemu tare da rungumar yadda Allah ya ƙaddara musu rayuwar su shiyasa ƙarshen su batayi kyau ba, i know you and i know how much you love me koh da da wasa ne ba zaka ta6a attempting yin wasa da rayuwa ta ba, na shaidi hakan tun ba yau ba, i just can't imagine what my life will turn without you Abyad, so stop blaming yourself i know kana dukkanin ƙoƙarin ka na ganin ka kula dani but 6ata garin dake biye da rayuwar ka suna neman hana yiwuwar hakan, ba kai kaɗai ne yakamata ace ka kula dani ba, nima lokaci yayi da zan kula da kaina dama kai kanka, we will now both look after each other and make sure that no harm ever visit our ways again, just promise me that you will always be there for me though nasan kullum you always stood for me a duk lokacin da wani yaso cin zarafi na, nima i guess lokaci yayi da yakamata na kula da kaina and make sure ban kar6i duk wani cin mutunci koh zarafi daga wurin wani koh wata ba, na daina nuna tsoron su a fili, domin kuwa maƙiyi na samun hanƴar cutar da kai ne a duk lokacin da yaga wani gazawa tattare da kai musamman idan ya hango tsoron sa a cikin idanun ka then ya dinga farautar ka kenan har sai ya cimma burin sa, banason ka sake baiwa kanka laifi akan dukkanin wani abu da maƙiya zasu yi mana nan gaba ba fatan hakan nake ba, and i know insha Allah ba zasu sake samun damar ƙuntata mana koh cin galaba akanmu ba" ta ƙarashe tana shafa gefen fuskar sa.

Kallon ta kawai yake har ta kai aya a zancen nata, murmusawa yana rungume ta tsam a jikin shi yace "Insha Allah, we're ready to fight our enemies, and ke kanki yanzu kin ƙarfafa min guiwa fiye da tsanmanin ki, i love you so much DEENAH, you really mean the world to me" ya ƙarashe cikin raunanniyar murya yana rubbing bayan ta.

Murmushi DEENAH tayi, ji take wani irin farin ciki na fizgar ta, though ta san bai wuci alƙawarin zuwa Naija da yayi mata ba.

Ɗagowa yayi yana cupping fuskarta, murmushi tayi ganin yadda yake kallon ta, kissing lips nata ya shiga yi har sai da yayi mai isar sa kafin ya ɗago yana sake bata peck a goshi.

Gyalen kayan jikin ta ya ɗauko daga kan bed ɗin yana yafa mata a kafaɗu kafin ya riƙo hannun ta su fito.

Tun daga kan stairs ɗin take hango JALILAH da YAZEED dake zaune babu mai yiwa juna magana a cikin su, duk sai taji babu daɗin hakan sam baikamata ba atleast JALILAH ta cancanci kulawa daga gun YAZEED koh dan kyawawan halayen ta ma.

Taimaka mata yayi ta sauƙo daga stairs ɗin kafin ya zaunar da ita daga cikin couchs ɗin dake zube a kyakkyawan falon.

Murmushi JALILAH tayi mata tana tasowa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗun ta tace "How are you doing DEENAH, ya lafiyar jikin ki?."

Maida mata martanin murmushin DEENAH tayi tace "Alhamdulillah."

"Good Morning DEENAH, how is your health?" cewar YAZEED dake facing ɗinta.

Amsa masa tayi da da sauƙi kafin kuma ya ɗau first aid box ɗin gaban sa yana ƙarasowa inda take zaune.

Bandage ɗin ƙafar ta ya shiga warware mata kafin ya sake yi mata dressing wurin yana ɗaura mata sabo, inda haka yayi wa hannun ma.

Kallon ZEEYAD dake tsaye akansu yayi kafin yace "Ka 6ata min lokaci bayan you know Hospital zani."

Idanu ZEEYAD ya ɗan waro yace "Actually ba nine na 6ata maka lokaci ba, it was DEENAH" ya faɗa yana nuna DEENAH dake zaune.

Waro idanu itama tayi tace "No it wasn't me" ta faɗa tana hararar ZEEYAD ɗin.

"Ofcourse i know it wasn't you, coz nasan ba zaki 6atamin lokaci ba."

Murmushi tayi tana ɗan yiwa ZEEYAD dake tsaye gwalo.

YAZEED ne yace "Alright, i will take my leave, see you later."

Rakiya ZEEYAD yayi masa kafin su fice DEENAH tayi saurin faɗin "Baka yiwa matar ka sallama ba."

Duk juyowa sukayi inda Jalilah kuma ta sadda kanta ƙasa, ɗan murmusawa YAZEED yayi yana kallon ZEEYAD da ya zuba masa ido shima yana jiran abinda zai ce.

Hararar ZEEYAD yayi in a whisper yace "How do i said it?."

Murmushi ZEEYAD yayi shima cikin raɗa ya shiga faɗin "You walk gently to her, bind your kneels down, lean her hands gently and look straight into her eyes then you say Bye Wifey am gonna miss you so badly."

Kunkumi kawai ya riƙe yana kallon ZEEYAD ɗin, kallon sa ZEEYAD yayi nan yace "Come on do it."

"You think this is a joke, i just want to do it yadda ba zataji wani iri ba."

"Then you must do as i told you, it's the only way da ba zataji wani iri ba."

"Are you guys planning something?" ya faɗa yana kallon DEENAH da ta tsare su da ido tana kallo.

Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yace "Go on with it bro" ya faɗa yana nuna masa hanƴa.

Kai kawai YAZEED yayi nodding yana takawa zuwa inda JALILAH ke zaune, ɗan duƙawa yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ɗanyi gyaran murya yace "Am leaving for work, da akwai abinda kike buƙata na taho miki dashi?."

Kai kawai ta girgiza masa alamun a'a tace "No nothing."

"Are you sure?" ya sake faɗa yana kallon ta.

Kai ta jinjina masa nan yace "Alright, bye then."

Ɗan murmusawa tayi kawai tana jinjina kai, kallon DEENAH dake kallon su yayi kafin ya ɗan saki murmushi yana sauƙe 6oyayyiyar ajiyar zuciya, juyawa yayi yana takawa zuwa wurin da ZEEYAD ke tsaye yana ɗan 6oye dariyar dake son zuwa masa.

"Best friends never make fun of each other talkless of best brothers" cewar YAZEED yana ficewa daga falon nan ZEEYAD ma yayi saurin mara masa baya.

Kallon DEENAH JALILAH tayi kafin tayi murmushi tace "Zan iya taya ki zama?."

Kai DEENAH ta jinjina mata tace "Sure."

Murmushi JALILAH tayi dan kuwa koh ta koma part ɗin YAZEED ba daɗin zama takeji ba koh dan rigima da tsokanar da Sairah ke damun ta dashi ma.

Ba'a jima ba ZEEYAD ya dawo, kallo ɗaya yayi musu yana haurawa sama coz atleast yakamata ya ɗan basu space koh sa samu suyi hira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login