Showing 3001 words to 6000 words out of 236327 words

Chapter 2 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45378

aikata wannan aika-aikar.



"How dare you?, she is my mother, she is a queen, the greatest queen among all, ba zan ta6a kyale duk wanda yace zai zage ta ba, zan iya yafe komai amma ba zan ta6a yafewa wanda yaso cin mutuncin mahaifiya ta ba,babu abinda tayi maka, dukkanin ku kun kasance butulallu ne,babu irin kyautatawar da mahaifiya ta batayi muku ba sadda take raye,why then zaka zage ta bayan mutuwar ta?, ba zan ta6a kyaleka ba yau ɗinnan, sai na kashe ka, sai na kashe ka Mulahhh" yana faɗin hakan ne cikin azababbiyar 6acin rai yayin da hannun sa bai gushe daga kaiwa Mulah duka ba, yayin da ake ta kiciniyar ɗaga sa amma an kasa yin hakan.



Babu wanda yayi nasarar ɗaga ZEEYAD daga kan Mulah har sai da ya tabbatar da Mulah baya motsi tukun kafin ya barshi yana sauƙe wata iriyar azababbiyar huci, yayin da fuskar Mulah ba'a cewa komai wurin muni dama chan ba kyan gani ne dashi ba, balle yanzu da yasha uban bugu.



Hayaniya ce ta ƙecere a wurin inda kowa ke mamakin yadda akayi kamar ZEEYAD ya kai Mulah ƙasa yake bugu harda sumar dashi.



Hannayen sa ya shiga dubawa kafin ya kalli fuskar Mulah ganin abinda ya aikata ne yasa shi saurin sauƙa daga kansa, kafin kuma yayi hanƴar fita daga wurin cikin gudu.



Wurin haɗuwar su da Sadeeq yaje inda ya same sa zaune gindin wata ƙatuwar bishiya yana zaman jiran sa.



Hango sa da Sadeeq yayi ne yasa shi saurin miƙewa yana taro sa da faɗin "Har ka gama?, i know you can do it abinda yafi aikin nan ma zaka iya" ya faɗa cikin murmushi yana bubbuga kafaɗar shi.



"Zeeyaaaddd" sukaji an ƙira da ƙarfi, juyawar da sukayi suka hango tawagar abokan Mulah ne ke tunkaro su, ba tare da ya tsaya yin wata-wata ba yace da Sadeeq "Run" ya faɗa yana fita da gudu ganin haka yasa Sadeeq da bai fahimci komai ba mara masa baya shi ma cikin gudu...........





*Share Fisabillah*




*MHIZZ JIDDHERR.........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E YA D*
```(The Abandoned Prince)```


*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*






*004...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





.............Kujera aka ja masa ya zauna kafin ya shiga ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.


Idanun sa ne suka sauƙa kan ZEEYAD da kansa ke sunkuye take yaji ransa ya 6aci,juyar da kansa yayi tare da buɗe tray ɗin breakfast ɗin dake gaban sa tare da ɗaukar fork da wuƙar da aka ajiye dan cin abincin,kafin yayi bismillah ya fara ci.



Ganin haka ya sanƴa kowacce buɗe nata abincin ta shiga ci,sa6anin ZEEYAD da bai buɗe nasa ba kuma har yanzu bai ɗago ba.



"ZEEYAD my dear,eat your food" faɗin Sarauniya Naseeba tana kallon sa.


Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi ta ƙasan ido kafin kuma ta kalli ZEEYAD ɗin shima a zuciyar ta tace _"What on earth is going on between them, she seems very nice to him, koma dai menene i must find it out very very soon"_ ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD.



Kai ya jinjina tare da ɗaga murfin da aka rufe tray ɗin dashi,ƙurawa abincin dake kan tray ɗinsa idanu yayi yana jin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciya.



Slice ɗin bread ne kwaya biyu sai kuma wata fale-falen soyayyiyar kwai da bata wuce yayi mata loma ɗaya koh rabi ba, kasa ɗagowa yayi ya kalle su dan kuwa yasan kowa shi yake kallo,dukda baya cin kwai haka nan ya daure ya sanƴa hannun sa tare da ɗaukar bread guda ɗaya ya haɗa da kwai ɗin tare da yin basmala ya kai bakin sa.



Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi dan ganin reaction ɗinsa,dan kuwa itace wacce tasa akayi masa serving ɗin wulaƙancin nan.


Idanun mai Martaba ne ya faɗa kan tray ɗinsa,magana zaiyi sai dai yaji bakin sa tayi nauyi ya kasa buɗe ta,hakan ya sanƴa sa maida hankalin sa kan abincin da yake ci.


_"Mai kuma wannan yaron ke son nunawa,kamata yayi ya tada husuma anan wurin ta yadda zai fusata mai Martaba a yi masa hukunci mai tsanani,sai dai ya fuske yana cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba,what is he actually up to?"_ cewar Sarauniya Hafeezah tana kallon sa har yanzun.


Bai iya cinƴe koh rabin wanda ya ɗauka ɗin ba sakamakon kwai ɗin da ya haɗa ta da ita yaji zuciyar sa na tashi,ga kuma jiri da ya fara ji duka a lokaci ɗaya.


Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki a cikin zuciyar ta tace _"Wow"_



Tashi yayi tsaye da kyar sakamakon kansa da yakejin tana juya masa,runtse idanun sa yayi yana sake ware ta tare da jijjiga kansa koh zai dawo saiti.



Ya san ba zai ta6a dawowa saiti yanzun ba indai har ba wai ya samu hutu da bacci bane,komawa yayi zaune kan kujerar tare da ɗaukar fork ɗin dake kan tray ɗin abincin sa yana damƙe ta a hannun sa inda yake trying so very hard ganin ya dawo nutsuwar sa,dan kuwa har dishi-dishi yake gani.



Miƙewa mai Martaba yayi bayan ya gama cin abincin sa tare da barin dining area ɗin ya haura sama.



Tashi Sarauniya Nazeerah tayi ba tare da ta tanka ba itama ta fice zuwa part ɗinta inda ya saura Sarauniya Hafeezah da kuma Naseeba.



Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi tare da miƙewa itama ta fice ta zuwa nata part ɗin.



Kallon sa Sarauniya Naseeba tayi kafin kuma ta hau duba arear wurin dan ganin babu hankalin wanda ke kansu, tasowa tayi ta ƙaraso wurin sa tana shirin kai hannu jikin sa ne yace "Don't you dare...don't you dare touch me" ya faɗa cikin muryar dake nuna alamun yana jin jiki.


Murmushi tayi tare da ɗago fuskar sa tana kallo tace "I can see that you are so allergic to Egg, come on zo muje part ɗina nikuma zan kula da kai yadda yakamata, irin kulawar da koh a wurin Mahaifiyar ka baka same sa ba."



Hannun ta ya buge yana miƙewa tsaye ya fara tafiya cikin tangaɗi.



Fizgo sa tayi ta baya tare da riƙe sa gamm idanun ta na yin jaa tace "Babu inda zaka ZEEYAD, dan kana ganin ina nuna maka kulawa a gaban sauran mutane ba hakan na nufin na baka umarni kuma kaƙi bi bane ba, ya zama dole ne ka biya min buƙata ta idan kuwa ba haka ba sai na tabbatar da na ya6a maka baƙin fentin da har ka mutu ba zaka ta6a zama fari a idanun jama'a ba."



"You are such a Monster" ya faɗa yana fuzge hannun sa daga riƙon da tayi masa.



Murmushi mai ciwo tayi tace "Ka dube ni da kyau ZEEYAD, har yanzu ni sabuwar jini ce wannan tsohon uban naka babu abinda zai iya yimin,wanda kafin na gansa ma wataran na kan shafe watanni, a haka kake tunanin zan zauna ba tare da namiji ba a matsayi na ta lafiyayyar mace?".



Kai ya girgiza kafin kuma ya shiga tafiya inda tabi sa da kallo a zuciyar ta tana faɗin

_"You could avoid me as hard as you can, but i will make sure that i get what i have been craving for from you."_



A hanƴar sa ta fita yaci karo da sarkin Dakaru,ganin halin da ZEEYAD ɗin yake ciki ne yasa shi saurin riƙo sa tare da faɗin "Yau ɗinma kwai aka sake baka kaci?, what a cruel world."



Dakarun dake jeka ka dawo daga wurin ya sanƴa su kama ZEEYAD ɗin su kai sa ɗakin sa,ba tare da musu ba suka zo suka kama sa dan aiwatar da abinda ya umarce su.



Har ɗakin sa suka kaisa suka kwantar kan motsatsiyar katifar sa, kafin su fito suna mai ja masa ƙofar.



"She just wants to see me dead" ya faɗa chan ƙasan muryar sa yana sauƙe nannauyar numfashi.



Ya sha fama kafin ya samu wani irin wahalallen bacci ya ɗauke shi........



****************



.............A hankali ya shiga buɗe idanun sa da sukayi masa nauyi yana ware su kan 6antararriyar ceiling ɗin ɗakin nasa da idan akayi ruwa mai ƙarfi da iska zata iya faɗowa kafin kuma ya miƙe zaune yana jinsa dama-dama.



Tashi yayi ya fito waje tare da ɗaukar wata motsatsiyar bokitin ƙarfe ya nufi wurin tuƙa-tuƙar da aka ware wurin wankin bayi mata ya ɗebi ruwa inda duk ta 6u66ule ruwan na tsiyayewa.



Haka nan ya kawo ta zuwa banɗakin da yake wanka,Wankan yayi da kyau kafin ya fito ya koma ɗakin sa.



Koɗaɗɗiyar Ghana-Must go ɗinsa da duk ta yayyage kamar wanda aka kwato daga bakin kura ya janƴo kafin ya shiga bincika kayan da zai sanƴa a ciki.



wata jallabiya mai hula a baya brown colour wacce itace mai ɗan kyau a cikin kayan nasa ya ciro duk da itama wasu wuraren sun 6ule kwari sun cinƴe amma haka nan ya sanƴa abarsa.



Wata ƴar ƙaramar drawer ya buɗe ya ciro wata sarƙa,sai sheƙi take da ɗaukar ido, jujjuya ta yayi a hannun sa tare da buɗe abin dake jikin sarƙar inda hoton wata Kyakkyawar mace ta bayyana fuskar ta ɗauke da murmushi, murmushin shima yayi kafin yace "You are the only treasure i have left."



maida abin yayi ya rufe kafin kuma ya sanƴa sarƙar a wuyar sa yana cusa ta cikin rigar sa.



Baƙar sumar kansa dake ta taruwa kullum bata samun isasshen aski da gyara ya taje inda ta bazu masa har kan kafaɗa,kafin ya shafa mai da jikin sa ya fito.



Hanƴar barin fadar ya kama har ya fice bai tanka wa kowa ba dukda kuwa kallon da bayi da dakaru dayawa ke binsa dashi suna gulmar sa hakan sam bai sanƴa sa yaji haushi ya tanka musu ba, dan kuwa koh kaɗan hakan baya basa haushi face ma gani yake wata daraja ce da Allah ya bashi tunda har ana iya nuna sa idan yana tafiya koh ayi maganar sa a bayan idanun sa.



Tafiya mai nisa yayi kafin ya iso gidan su abokin sa Sadeeq, kasancewar gidan ba baƙon sa bane ya sanƴa sa shiga har ciki bakin sa ɗauke da sallama


Sadeeq ɗin ya tadda da iyayen sa da ƙannen sa zaune suna cin abinci, hakan ya sanƴa shi saurin komawa.



"Abhi...ZEEYAD ne" cewar Sadeeq ɗin da ya miƙe tsaye dan kiran ZEEYAD ɗin, sakamakon kallon da mahaifin sa ke binsa dashi ne yasa shi dakatawa.



"Daga yau nayi maka iyaka tsakanin ka da yaron nan, kai ba ɗan kowa bane dan haka ka tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ka na ɗan talaka mai ƙoƙarin neman na kansa tun kafin a kwace wannan matsayin daga gare ni, kana sane da irin kashedin da mahaifin sa Sarki Abbas yayimin akanka da ɗansa, ba zan iya ja da Adalin sarki mai nagarta irinsa ba koh da kuwa ina da ikon yin hakan balle kuma da banida shi, kai kanka kasan Sarki Abbas baya magana sau biyu, dan haka rabuwar ka da yaron sa shine alkhairi a tsakanin mu baki ɗaya sannan kuma shine zaman lafiyar mu."



"Amma Abhi indai har sarki Abbas adali ne kamar yadda ka faɗa maiyasa yake muzgunawa ZEEYAD kamar wanda ba ɗan cikin sa ba?, koh da ƴan waje baya yi musu abinda yakeyi masa."



"Wannan ba damuwar ka bace Sadeeq, wannan tsakanin su ne, bakasan komai ba dan haka ka bar komai a yadda yake kai dai naka idanu ne, sannan koh da da wasa kada ka kuskura makamancin wannan maganar ta fito daga bakin ka a wani wurin, zaka iya zuwa ka sallame sa ya tafi idan kuma ba zaka iya ba ni zan fita da kaina na faɗa masa."



Shiru Sadeeq yayi yana kallon mahaifin nasa kafin kuma daga bisani yayi hanƴar waje dan aiwatar da abinda mahaifin nasa ya umarcesa, tsinkayo muryar sa yayi yana faɗin "Sannan kuma kada ka manta da faɗa masa cewar ya fita daga hanƴar ka, koh da a hanƴa kukayi kici6us dashi ku nuna bakusan juna ba."



Juyowa yayi ya kalli mahaifin nasa kafin kuma ya jinjina masa kai ya fice.



A bakin dakalin gidan su ya sami ZEEYAD ɗin zaune yana jiran shi.



Cikin sanƴi ya ƙaraso wurin sa, ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa tare da yin murmushi yace "Ka gama?."



Kai Sadeeq ɗin ya jinjina masa zuciyar sa a cunkushe dan baisan mai zai cewa ZEEYAD ɗin ba.



"Alright, shall we?" ya faɗa yana miƙewa tsaye.



"ZEEYAD" Sadeeq ɗin ya kiraye shi.



Kallon sa ZEEYAD yayi nan yaga damuwa fal fuskar Sadeeq ɗin ba kamar yadda ya saba ganin sa kullum cikin walwala da nishaɗi ba idan suna tare.



"ZEEYAD, inason faɗamaka wani abu amma fah ka sani babu yadda na iya ne, Umarnin mahaifi na kawai zan bi, inaso daga yau...." shiru yayi yana kallon ZEEYAD ɗin da ya zuba masa idanu yana kallo dan son jin abinda zai faɗa.



"Ba zaka iya faɗa masa bane?" ya tsinkayo muryar Mahaifin nasa ta bayan sa.



Ƙarasowa yayi wurin su kafin ya kalli ZEEYAD yace "Kayi haƙuri ɗa na ZEEYAD, amma abinda zan faɗamaka a yanzu ƙila kaji babu daɗi, inason daga yau ka rabu da Sadeeq sannan kuma kada ka sake nunawa ka sanshi a wani wurin koh da kuwa haɗuwa kukayi a hanƴa, ZEEYAD ka tsaya a matsayin ka na ɗa ga shugaban wannan ƙasa, shima Sadeeq zai tsaya a matsayin sa na ɗa ga sarkin manoman wannan gari, ina tsoron faɗamaka cewa alaƙar ka da Sadeeq ɗana daga yau babu ita..."



"Alright" ya katse shi cikin rawar murya kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Duk dan nine abinnan yake faruwa, kowa bayason alaƙa ta tsakanin sa da ɗansa, kowa gudu na yakeyi, ba sabon abu bane a wuri na, am already used to it, so why should i feel bad dan Mahaifina ya yanke alaƙa ta da Sadeeq?, koh bakomai yanada wasu abokan ai, dama ni kaɗai akeson muzgunawa kuma kullum suna samun nasarar hakan, i won't put the blame on anyone of you coz i guess i was born to suffer, ƙaddara ta ce hakan dan haka kada ku wani damu kanku, kuma zanyi duk abinda kakeso sabida ai kaima ka ɗauke ni ne tamkar ɗanka...Unlike my Father, so why should i said No to what you ask?, nima ba zan so wani abu ya sami kyakkyawar Family ɗinku ba, koh bakomai kunyi min gata a rayuwa, and now....ba zanyi musu da duk abinda kace ba, zanyi yadda duk kace dani kuma zan rabu da Sadeeq" ya ƙarashe cikin jinjina kai.



"ZEEYAD..."



"Sadeeq, in dai har ni zanji maganar mahaifin ka, maiyasa kai ba zaka ɗau abinda zai faɗamaka ba, you know what?, na daɗe ina fatan wannan ranar tazo ta, ranar da za'a raba ni da kai, ba dan komai ba sai dan kawai rayuwar ka ta inganta, dan kuwa rayuwa tare dani dai-dai take da rugujewar duk wani farin ciki naka kaima, am Glad Sadeeq, so very Glad" yana faɗin haka ya juya yayi tafiyar sa trying so very hard to control his tears.



Da kallo Sadeeq da mahaifin sa suka bi ZEEYAD dashi dukkanin su zuciyoyin su cike da tausayin sa har ya 6acewa ganin su.



Dafa kafaɗun Sadeeq yayi yace "Kayi haƙuri Sadeeq, nasan kanajin zafin rabuwa da aminin ka a zuciyar ka."



Saurin goge hawayen da suka kawo masa yayi kafin yace "No...inaga hakan shine dai-dai" kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Abhi kace yau zamuje Gona, zamu iya tafiya yanzu?."



Kai mahaifin nasa ya jinjina masa kafin kuma ya dafa kafaɗun sa,suka koma cikin gidan...............





_Yauwa nace ƴan ZEEYAD fans group kodai kurame na tara ne ni bansaniba🤔, kun iya karanta littafi mai read more biyu zuwa uku amma sharhi ya gagare ku?, toh gaskiya bana kar6an ƴan la6e a cikin group ɗina, almost 300+ participants amma bai wuce mutane biyar bane masu comment, lallai daɗi ne yayi muku yawa toh tsaf yau ɗinnan zanyi aiki a kanku insha Allah😑da ba zan kar6i hakan ba yauwa_




*Share Fisabillah*






*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```(The Abandoned Prince)```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*(MHIZZ JIDDHERR)*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





_Bismillahi_Rahmanin_Rahim_




*003...*




......"ZEEYAD, mai ka aikata ne haka, maiyasa suke bin ka, mai kayi musu?" cewar Sadeeq da har yanzu basu bar gudun ba cikin huci.



Tuntu6e yaci ya faɗi a ƙasa, Juyowa ZEEYAD yayi nan yaga ƙafar Sadeeq ɗin na fitar da jini, alamun ciwon da yaji ba kaɗan bane.




Kallon tawagar su Mulah da suka kusan isko su yayi kafin kuma yaje da sauri ya kamo Sadeeq ɗin tsaye suka cigaba da gudu.



"ZEEYAD, just go ba zamuyi sauri ba, zasu iya taddo mu" faɗin Sadeeq dake ɗingisa ƙafar sa.



"You just shut up now, idan ba so kake suyi maka dukan mutuwa ba" faɗin ZEEYAD ɗin.



Wani ƙaton ƙarfe suka wullo nan ya same shi a kai, take kuma duk suka zube a wurin,nan kuwa akayi nasarar cafke su.



"Kai ɗan iska ƙasƙantacce, har kai ka isa ka aikata wannan mummunar laifin kuma kace zaka gudu?, ba dai a cikin wannan masarautar ba" cewar wani dogari yana ɗago sa tsaye.



ZEEYAD kansa ne ke mugun juya masa dan kuwa bibbiyu ma yake ganin su sakamakon abinda suka buga masa a kai, nan aka tusa su gaba daga shi har Sadeeq ɗin zuwa fadar sarki..........



************



............Durƙushe suke a gaban mai Martaba da kallo ɗaya zakayi masa ka gano 6acin rai ɗauke akan fuskar sa.



Duban sa ya maida kan ZEEYAD da har yanzu baijin kansa dai-dai kafin kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login