Showing 159001 words to 162000 words out of 236327 words

Chapter 54 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45355

nan kuma taga babu carpet ɗin ɗakin sa, kafin kuma taje ɗakin Umma, nan ta same ta zaune.

Shigowa tayi tana zama kusada Umma ɗin tace "Umma ina kwana?."

"Kin tashi lafiya, ya gajiyan ki?."

"Alhamdulillah" ta amsa kafin tace "Wa ya fidda kujeru da carpets ɗin?."

"Yayan ki ne ya kai wurin wankewa bai dawo ba tukun."

"Allah yasa dai bai manta da nawa ba."

"A'a duka ya kai."

"Yauwa, Umma zan gyara ɗakin naki."

Kallon ta Umma tayi tace "Baki gaji bane, kya bari dai anjima ki ƙarasa koh?."

"A'a Umma indai nace zan bari yanzu anjima ba zan iya ba gara kawai na haɗa nayi su kai ɗaya yanzu na huta."

"Toh shikenan, bari yayan naki ya dawo tukun muyi breakfast."

Da "Toh" kawai ta amsa tana kwanciya, runtse idanu tayi jin bayan ta ya wani riƙe yaushe rabon ta da tayi irin aikin nan ta manta tun kafin ta faɗa rashin lafiya.


Da sauri kuma ta miƙe tana zuwa ta janƴo kwalin da Grandma ta bata ta buɗe dan ganin menene a ciki.

Blue ɗin doguwar rigar gown ce mai kyau iriyar wacce taga JALILAH na sawa da takalmi mai kyau sai kuma bangles a ciki.

"Wow, Umma kinga" ta faɗa tana ƙarasowa kusa da Umma.

Kallon kayan Umma ma take tace "Masha Allah sunyi matuƙar kyau sosai."

Murmushi tayi tace "Aikuwa dai sosai."

Ƙarar motar da taji ne ya tabbatar mata da Jafar ɗin ya dawo dan haka tashi tayi ta fice cikin gudu, dan kuwa ba wai sun samu sun gaisa mai kyau jiya bayan dawowar su bane ba kuma ƙaramin kewar sa taji ba.

Cikin farfajiyar gidan nasu ta fita tana nufar inda yayi parking motar.

Buɗe motar yayi fuskar sa washe da murmushi.

"Oyoyo yayana" ta faɗa tana rungume shi.

Farin ciki ne cike fal a zuciyar Jafar ganin ƙanwar tasa ta dawo ainihin ita babu kuma wata damuwa tattare da ita.

"I miss you lil sis" ya faɗa cikin murmushi yana patting bayan ta.

Ɗagowa tayi cikin murmushi tana kallon sa tace "Yaya mai ka samu ne haka sai wani kyau kake ƙarawa kana sake yin fresh" ta faɗa tana shafa fuskar sa cikin murmushi.

Ɗan sosa kai yayi kafin yace "You wanna know, it's a secret but ke kaɗai zan faɗawa and kada ki sanar da Umma, Promise?."

Kallon sa take cikin murmushi kafin kuma tace "Promise" tana tafa hannayen ta da nashi.

Kumatun ta yaja tare da ɗaura hannayen sa kan kafaɗun ta suka fara tafiya, wayar sa ya ciro ya ɗanyi danne-danne kafin ya miƙa mata.

Amsa tayi fuskar ta ɗauke da murmushi yace "Is she beautiful, do you like her?."

Shiru tayi tana kallon hoton tana sake zooming ɗinsa kafin tace "Uhmm....kamata yayi ace ka nemo matar da tafi ƙanwar ka kyau."

Tsayawa yayi yana kallon ta kafin kuma ya kar6e wayar sa yana faɗin "You mean kin fita kyau?."

Kai ta jinjina masa kafin tace "She is just fair in complexion, but look at her nose" ta faɗa tana ta6a hancin ta.

Sake ƙure hoton yayi da idanu kafin kuma yace "Lies there is no way zaki fita kyau, ."

Nan fah suka hau musu tsakanin su kamar wasu yara, inda yake cewa budurwar sa ta fi DEENAH kyau, ita kuma take cewa tafi budurwar tasa kyau.

"Ok, ok, ok, naji let's bait, indai har dagaske girlfriend naka ta fini kyau zan haɗa cake mai kyau ka kai mata, and indai it turns out that na fita kyau zaka saimin sabuwar waya, agree?."

"Yeah, bait" ya faɗa yana tafa hannun ta da ta miƙa masa.

Nan tace "Yauwa muje wurin Tijjani mai gadi ya tantance mana."

Nan fah duk suka ɗeba sukayi wurin sa suna cigaba da musun su.

Tijjani mai gadi dake ta washe haƙora yana kallon su tun daga nesa ne yace "Hajiya DEENAH, lafiya ta samu, Allah Ubangiji yaqara miki lafiya mai ɗaurewa."

"Aameen Tijjani, yauwa Tijjani musu zaka raba mana dan Allah kar6i hoton nan ka gani, Yaya ka bashi wayar" ta faɗa tana kallon Jafar dake ta faman hura hanci.

Miƙawa Tijjani wayar Jafar yayi kafin tace "Wannan budurwar Yaya ce, dan Allah musu zaka raba mana wai cewa yayi ta fini kyau haka ne?."

Kallon cikin wayar yake yana kallon DEENAH haƙora washe yace "Toh kai yallabai Jafar ai Madam ɗin taka jar fata kawai zata nuna wa Hajiya DEENAH amma ba dai kyau ba kam."

Ihu DEENAH tasa haɗi da yin tsalle tana faɗin "Mai na faɗamaka Yaya" ta faɗi hakan cikin dariya tana riƙo shi.

Sosai Jafar ya cika yayi fam sai hura hanci yake yace "Ba wani nan kinyi bribing ɗinsa ne, haɗa baki kawai kukayi."

Dariya duk sukayi kafin yace "Toh yallabai Jafar inbanda abin ka tayaya zamu haɗa baki ita da ma bata ƙasar."

"Koma dai menene, ban waya ta" ya faɗa yana kar6ar wayar sa.

"Mungode Tijjani" cewar DEENAH tana marawa Jafar baya tana cigaba da yi masa dariyar shaƙiyan ci.

Ja sukayi suka tsaya a falon nan ya juyo ya kalle ta yace "Da nayi niyyar taya ki aikin but yanzu na fasa."

Dariya tayi tace "Nidai ba wannan ba, yaushe zaka kawomin waya ta?."

Ɗan ta6e baki yayi yace "Wani waya?."

Tsaya kallon sa tayi kafin tace "You promised to buy me a new Phone, koh ka manta bait ɗin da mukayi ne?."

"Ohh, ai banyi alƙawari ba, i just said _"Bait"_ ba wani abu ba kuma."

6ata rai tayi ta tsaya tana kallon sa, murmushi yayi yace "Don't worry, i promised to buy it for you on your 20th birthday."

Murmushi tayi tace "Really?."

"Yeah" ya faɗa.

"Toh amma fah saura 2weeks kenan jira zanyi har lokacin?."

"Yeah, indai kinason na saya miki mai kyau ba."

"Alright then, amma zaka dinga bani naka ina amfani dashi koh?."

Ɗan waro idanu yayi kafin yace "Amfanin mai?, ina wanda ke hannun ki?."

"What are you saying?, na dawo na tarar ya ɗauke gabaɗaya baya kawowa."

"Alright ba case."

Murmushi tayi cike da jindaɗi kafin tace "Toh yanzu ka tayani mu gyara gidan, gashi ma ƴunwa nakeji" ta faɗa cikin yamutsa fuska tana shafa cikin ta.

"Ohh, kinga kinsa har na manta akwai food-stuffs na kawo suna booth, muje mu kwaso" ya faɗa yana ficewa kafin tabi bayan shi.

Kwaso kayan abincin da ya sayo sukayi suna shigar wa ciki har suka kammala, Umma ce ta shiga kitchen dafa musu breakfast inda kuma ita da Jafar suka ƙarasar da gyaran gidan baki ɗaya.

Bayan sun gama ne suka yi breakfast, Jafar shiryawa yayi ya fice ita kuma ɗaki ta koma, wanka tayi ta shirya cikin armless doguwar riga marar nauyi kafin ta tada sallahr Azahar tayi, bayan ta idar ne kuma ta haura kan bed, dan kuwa ba ƙaramin gajiya tayi ba.

Idanun ta ta lumshe kafin kuma murmushi yayi forming kan fuskar ta, babu abinda take tunawa sai moment nasu na shekaran-jiya dashi, sai dai har yanzu ta rasa dalilin da ya sanƴa bai kira ta ba.

Mirginawa tayi tana gyara kwanciyar ta, kafin bacci mai daɗi yazo ya kwashe ta.



**************************



________Kallon sa Sadeeq yake kafin kuma yayi gyaran murya yace "Ya zakayi da JALILAH kuma?."

Buɗe idanun sa dake lumshe yayi yana zuba su kan Sadeeq ɗin kafin ya gyara zama yace "Na baka ita."

Da wani irin kallo Sadeeq ya bisa yace "An gaya maka cewa nayi kwantai ne komiye?, you know tun farko kai ka kwafsa abin nan why hiding your feelings you should have told her cewar kana da wacce kake so, it isn't a big deal maybe ta fahimce ka sannan ta haƙura tunda tana da sauƙin kai, but yanzu babu ta yadda za'a yi ka fara confronting ɗinta akan wannan zancen ne sabida she thinks koh kaima you have feelings for her, ta kwallafa rai a kanka sosai and telling her cewa kanada wacce kakeso won't make a sense to her, it may broke her heart."

Shiru ZEEYAD yayi yana sauraren Sadeeq ɗin har ya kai aya a zancen nasa, "What about YAZEED then?."

"Bakaji abinda Ummien sa ta faɗa masa bane, it's like ta haramta masa dukkanin wata alaƙa da DEENAH, so i don't think zai sake confronting ɗinta kuma."

"But he loves her and he may think that koh nayi masa kwace ne."

"No, he would never think that way, bale ma ba kwacen kayi masa ba."

Shiru yayi ya rasa ta cewa nan Sadeeq ya sake faɗin "Ka bar damun kanka haka nan, idan kana tunanin zaka iya hurting JALILAH why not kawai ka haɗa su biyun ka aura?."

"What?" ya faɗa yana kallon sa.

Kafaɗu ya ɗaga masa yace "Yeah kaga babu wacce zata ce ka yaudare ta a cikin su."

"Two wives, at same time?, listen i don't have that niyyar yin mata biyu" ya faɗa cikin 6ata rai.

"Alright then choose between the two of them, DEENAH or... JALILAH" Cewar Sadeeq ɗin cikin murmushi.

"You think this is funny?, zanje wurin Grandma, i will tell her everything idan yaso then ta warware ƙulin da ta haɗa."

"You mean bakason JALILAH?, poor her i feel so bad for her."

Tashi tsaye ZEEYAD yayi yana faɗin "Am going home now, idan Abhi ya dawo ka gaida shi."

Tashi shima Sadeeq yayi yace "Insha Allah."

Jerawa sukayi suka fito tare, inda yayi wa Ummien Sadeeq sallama kafin ya wuce.

*************

A hanƴar zuwa part ɗin Grandma yaci karo da YAZEED dake fitowa daga nan.

Murmushi yayi masa inda YAZEED ɗin ya kallesa yace "I have been looking for you" ya faɗa fuskar sa babu yabo babu fallasa.

"Are you Okay?" cewar ZEEYAD yana kallon sa.

Shiru ya ɗanyi damuwa fal akan fuskar sa yace "It's about DEENAH... I want you to call her and apologised to her on my behalf please, am worried tun ranar da abin ya faru, i know kai kaɗai ne zaka iya conviencing ɗinta ka kwantar mata da hankali."

Kallon sa kawai ZEEYAD yake cike da tausayawa yace masa "No i guess kai yakamata ka bata haƙuri da kanka, you should call her on phone, i guess kana da numbern Ummien ta, right?."

"Yeah ina dashi, but... I can't do that Ummie duk ta 6ata komai, she doesn't like DEENAH for the first time and ka santa i know ba zata ta6a son nata ba koh ya kuwa nayi da ita, so i don't think i can go any further with our relationship... I guess am living her for good."

ZEEYAD was shocked for a moment jin kalaman da suka fito daga bakin YAZEED, he knows that YAZEED is deeply inlove with DEENAH but baisan dalilin da ya sanƴa shi saurin haƙura da ita haka nan ba, he think ba zaiyi minding kalaman mahaifiyar sa ba zai cigaba da kula DEENAH sai dai kuma ba hakan bace ta kasance, he feels so bad wa ɗan uwan nasa sam baiyi dacen mahaifiya ba.

Muryar YAZEED ne ya katse masa tunani da faɗin "You know koh da na tilastawa kaina auren DEENAH then ba zata ta6a jindaɗin rayuwa dani ba, coz seems like she loves someone else, there is someone else in her mind, and above all kuma halin Ummie kaɗai ya isa ya dawwamar da ita cikin ƙunci na har abada, so what's the point of marrying her indai ba zan ta6a bata farin ciki ba?" ya ƙarashe yana kallon ZEEYAD.

Cikin sanƴi ZEEYAD yace "Am sorry, it's really painful indeed."

"No everything will be alright insha Allah, i guess Allah baya ɗaurawa bawan sa abinda ba zai iya ba right?, so i will be patient na ganin na sami kalar matar da takeso na aura."

Rungume ɗan uwan nasa yayi yanajin babu daɗi sosai a ransa.

Patting bayan sa YAZEED ya shiga yi suna ɗagowa nan yace dashi "So are you calling her for me?."

"Yeah" ya bashi amsa.

Murmushi yayi yace "Thank you" yana sake rungume shi.

Ɗagowa duk sukayi suna murmushi nan YAZEED yace "Muje so that na baka numbern ka kira" jerawa sukayi suka shige part ɗin Grandma ɗin.

A falo suka yaɗa Zango kafin YAZEED ya kira masa numbern Umma ɗin yana sawa a wayar sa.

Wayar ya miƙawa YAZEED bayan yayi dialing number ɗin.

*******

______DEENAH da ta kar6i wayar Umma tana game ne taga kirar sabuwar layi ta shigo wayar, gashi kuma ba na ƴan Nigeria bane.

Murmushi tayi dan kuwa koh ba'a faɗa mata ba, ta san shine, sai da taga ya kusa yankewa tukun ta ɗaga tana mai yin sallama.

Kallon ZEEYAD YAZEED yayi jin ba Umma bace ta ɗau wayar, dan haka saurin miƙa masa wayar yayi a hankali yake faɗin "I guess it's DEENAH."

Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yana kai wayar kunnen sa tare da furta "DEENAH?."

Murmushi DEENAH tayi tace "I know it must be you, so are you missing me already?."

Cize baki yayi kafin kuma yace "Actually YAZEED is here with me, he asked me to call you."

Expression na fuskar ta ne ya canza nan tace "Ohh."

"He wants to apologise to you about what happened the other day, he is very sorry DEENAH, please forgive him and his Mom too."

Cikin sanƴi tace "It's alright, actually komai ya wuce, kace masa kada ya wani samu damuwa, and ya kwantar da hankalin sa, ni nama manta ma da anyi hakan."

Murmushi ZEEYAD yayi nan yace "Thank you, he really appreciate that."

"He is welcome" ta faɗa.

Kallon YAZEED yayi tare da yi masa alamun komai ya wuce, murmushi yayi yanajin daɗin hakan a ransa.

"So Bye DEENAH."

"Bye" ta faɗa a hankali tana datse kiran, turo baki tayi tana 6ata fuska ganin ba kiran shi bane na musamman.

"So how do i tell her that our relationship is over?."

"Maybe you should text her."

"This is her Mom's phone, what if she saw it instead of her?."

"Maybe then you should go visit her."

"Really?, what if kai kaje maimakon ni fah, you know it i can't talk to her right?."

"You really want me to go?."

"Yeah, i know kasan abinda zaka faɗa dan ganin bataji haushin hakan ba."

Murmushin gefen baki kawai ZEEYAD yayi ba tare da yace komai ba.

"Yakamata kaje a cikin week ɗinnan please."

"This week?, i mean why not mu bari sai next upper week?."

"Alright then, duk yadda kace."

"So you want me to find a new girl for you?" ya faɗa cikin murmushi yana kallon YAZEED.

"No, let her find one for me, what if wacce na kawo ma tace batayi mata ba fah?."

"What if wacce ta kawo maka kuma batayi maka ba fah?."

"Then i will manage her, na rungumi haƙuri har mu rabu lafiya."

"Wow" cewar ZEEYAD ɗin cikin jinjina hali irin na ɗan uwan nasa.


*******************


_________Zaune take tsakiyar bed ɗinta tana gyara faratan hannun ta.

Sallamar Jafar taji bakin ƙofar dan haka izinin shigowa ta bashi.

Bai ce da ita ba kawai ya miƙa mata wayar sa cikin murmushi yana ficewa.

Da kallon mamaki ta bisa tana juyo fuskar wayar.

Ƙanƙance idanu tayi tana ƙara ƙure screen ɗin da kallo ganin kamar shi take gani cikin wayar.

"Why are you looking so ugly Babe?" taji ya faɗi hakan.

Saurin matsar da wayar tayi daga kusada fuskar ta tana wani irin tsuke fuska jin ya kira ta da mummuna.

Ɗan murguɗa masa baki tayi tace "A mummunar ne kuma a maƙale min ba."

"Yauwa you look better now" ya faɗa.

"Wait a minute" ta faɗa tana ajiye wayar kafin ta sauƙa daga kan bed ɗin ta sako doguwar Hijabin ta ta dawo ta zauna tana saita wayar da kyau.

"Uhm, kin ɗanyi kyau yanzu."

Murmushi tayi tana tallafe kumatun ta tace "When are you coming to see me, and tun ranar chan baka kira kaji ya nake ba sai yanzu?" ta ƙarashe cikin shagwa6e fuskar ta.

"Come on tell me, i will come duk ranar da kikeson gani na."

"Seriously, koh da yanzu nakeson ganin ka zaka zo?."

"Only if idan Aljani ne ni kenan" ya faɗa.

Ɗan dariya tayi kawai ba tare da tace komai ba.

"Babe?" ya kira ta.

Kallon sa tayi kamar wacce ke gaban sa a zahiri nan yace "I miss you."

Murmushi tayi tana rufe fuskar ta tace "You really do?."

"Yes Babe."

"If you really do then, kazo cikin kwanakin nan, let's spend more time together."

"You really want that?."

"Uhum" ta faɗa cikin jinjina masa kai nan yace "Alright then, your wish is my command."

Murmushi tayi kawai tace "I Know ba zuwa ma zakayi ba."

Murmushin shima yayi yace "Don't worry, i will surprise you."

"Alright then, dare yayi nikuma bacci nakeji."

Ɗan 6ata fuska yayi dan kuwa sam bai gaji da kallon ta ba yace "So soon?."

"Yeah, inada school gobe, Bye" ta faɗa tana yi masa waving da hannu kafin tayi saurin yanke kiran.

Ita ɗinma sam ba wai ta gaji da kallon sa bane, but dole sai tana ja masa class yadda zai cika da kewar ta sosai har ya taso daga inda yake zuwa ganin ta, ba wai tayi ta sakar masa sosai haka ba.

6angaren ZEEYAD kuwa ji yayi duk wata farin cikin sa ta yanke, dan haka rufe Laptop ɗin tasa yayi yana wani irin tsuke fuska kai kace wani gagarumin laifi akayi masa.




*FIVE DAYS LATER*



_____Zaune take ita da su Anty Khadija kasancewar suma kwana biyu da ya wuce suka dawo daga tafiyar da sukayi, hakan ya sanƴa ta kawo musu ziyara.

"Wai ke dan Allah dagaske kike ni fah ban yarda ba" cewar Amirah tana kallon DEENAH dake basu labarin Abyad ɗinta.

Tsaki Anty Khadija taja tace "Ke nikam dallah ki rabu da wannan ki cigaba da bamu labari, yanzu dai kina nufin kice wata sabuwar soyayyar ce ta ƙullu tsakanin ku, kai gaskiya am very happy for you, after all the struggles da kikayi fama dashi a rayuwa kukan ya kusa zuwa ƙarshe yanzu."

Murmushi kawai DEENAH tayi tana sauraren ta, Amirah ce tace "Yanzu fah kenan balarabe zaki aura, kinji daɗi kice zaki sha tarairaya da soyayya."

"Aikuwa dai larabawa ba ƙaramin iya soyayya da tarairayar matan su suke ba, dukda dai bansan ya salon nasu soyayyar yake ba" faɗin Anty Khadija.

Ƙarar wayar Anty Khadija ne ya katsewa Amirah maganar da take shirin yi.

Ɗagawa Anty Khadija tayi tare da karawa a kunne tana amsa sallamar mai maganar.

"DEENAH?, gata nan" ta faɗa tana miƙawa DEENAH wayar.

Amsa DEENAH tayi tana karawa a kunne ganin Yayan ta ne "Ki fita ƙofar gida kinyi baƙo" shine abinda yace mata, waro idanu tayi tace "Wane ƙofar gidan, ina gidan Mamy fah."

"Yeah i know, nan ɗin he is waiting for you" daga haka ya katse kiran ba tare da yaji ta cewar ta ba.

Da kallo tabi wayar kafin ta kalli Amirah tace "Amirah dan Allah leƙa min ƙofar gida kiga waye ne?."

"Baƙo kikayi ne?" cewar Amirah ɗin tana ɗaukar Hijabin ta.

Kafaɗa ta ɗaga tace "Haka Yaya Jafar yace min, dubo min kiga waye ne please."

Ba tare da Amirah ta amsa ba ta fice dan dubo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login