Showing 111001 words to 114000 words out of 236327 words

Chapter 38 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45335

asibitin nan, i remember everything, ban ta6a tunanin zaki aikata hakan ba, how could you be so selfish, dan bakya son shi ba hakan ke nufin zaki kore shi daga cikin rayuwa ta ba, because i need him."

"You need him, ni kike wa magana cikin tsawa because of a random guy?."

Shiru DEENAH tayi bata ce komai ba, tanajin zuciyar ta na matuƙar suya kamar ta fito waje.

"You listen to me carefully, of course nice wacce na tilasta masa ficewa daga rayuwar ki, sabida banason alaƙar ki dashi, already zuwa yanzu nasan yayi moving on da life nasa you should also try and do so, and besides maiyasa bakya son rabuwa dashi tunda ba wai soyayya kuke ba, kodai kina son shi ne?."

Ɗagowa tayi tana kallon Umma ba tare da ta iya cewa komai ba.

"Answer me, son sa kike komiye?."

Maida duban ta tayi gun Jafar dake tsaye bakin ƙofa yana kallon su ba tare da ta bawa Umma amsa ba.

"Well i guess ba sonsa kike ba koh?, then ina buƙatar ki cire shi daga cikin rayuwar ki, koh da da wasa bana buƙatar jin sunan sa daga bakin ki, sabida ya riga da yayi miki nisa and am definitely sure idan shi mai zuciya ne ba zai ta6a dawowa ba, sabida na riga da na yanke alaƙar dake tsakanin ku, dan haka ki kwantar da hankalin ki sabida hakan ba zai sanƴa shi sake dawowa cikin rayuwar ki ba, haka ma hawayen da zaki zubar so i need you to give it a rest, no more tunanin da babu gaira babu dalili, yin hakan tamkar tsokano fushi na ne" tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta tankawa Jafar dake tsaye yana kallon su ba.

Duk da kallo suka bita kafin ya idda shigowa cikin ɗakin, rungume shi tayi tana sakin kuka sosai inda shi kuma ya hau rarrashin ta.

"Maiyasa Umma zatayi haka, maiyasa batason alaƙar mu dashi, maiyasa ba zata dubi halin da na shiga dama kuma wahalar da yayi akaina ba, Yaya yana sona koh ba haka ba?" ta faɗa tana ɗagowa ta kalle shi.

Kai ya jinjina mata alamun eh kafin yace "He was ready to sacrifice anything da ya mallaka akanki, actually balarabe yana matuƙar ƙaunar ki, he never rest tsawon watannin da kika ɗauka a asibiti, he just can't imagine life without you, yana sonki DEENAH hakan ya sanƴa shi karya dokar da Umma ta gindaya na kada wanda ya biyo ta a cikin mu har sai kin samu lafiya,but shi ya gaza yin hakan sabida kawai yanason ganin ki and ready to face and endure duk wani abu da Umma zata faɗa masa, but it turned out to be that Umma da kanta ta kore shi, not wondering irin halin da zaki shiga bayan hakan, ita dai burin ta shine taga ya bar cikin rayuwar mu ba tare da ma ta lura da cewar a ƙarƙashin sa nake aiki ba, and abin baƙin cikin shine ya saida company ɗinsa na nan Sokoto, that means kenan ba zai kuma dawowa ba DEENAH, i think he is out of our lives forever DEENAH."

Kuka sosai DEENAH ta fashe dashi tana komawa kan bed ta zauna "Maiyasa Umma zatayi haka, shikenan yayi laifi dan ya soni kenan, ina laifin wanda yaso naka?, maiyasa zata yimin haka?."

"Well DEENAH maybe she has a reason behind it..."

"Wane irin dalili ne hakan, koma menene dalilin ta baikamata tayi masa hakan ba, he doesn't deserved that, she humiliated him after all the love and care he had shown me, ba zan manta lokacin da ya durƙushe kan guiwowin ba sa pleading her akan kada ta raba shi da DEENAH but she turned a deaf ear ta wulaƙanta shi, sam bai cancanci hakan ba, menene laifin sa?."

Shiru Jafar yayi yana mai jin tausayin ƙanwar tasa ganin yadda take ta kuka, baisan wane irin kuka zata yi ba bayan ta gano cewar ba zata kuma haɗuwa da shi ba maybe yace har abada, he is very sad da abinda Umma tayi gashi kwata-kwata yanzu he can't get through ZEEYAD, hakan na nufin yayi nesa dasu sannan ba zai sake dawowa Nigeria ba, da wannan tunanin ya bar cikin ɗakin tare da ficewa daga gidan ma baki ɗaya.

DEENAH kuwa wuni tayi a ɗaki ranar koh abinci bata fito taci ba, sosai takejin haushi da zafin abinda Umma tayi, dah Umma tasan irin son da take yiwa ZEEYAD dah bata fara yi masa hakan ba, tasan yanzu ita da farin ciki kuma wataƙil sai a lahira, sabida Umma zata sake jefa ta halin da yafi na baya da tayi, sosai take kuma jin haushin kanta na kasa tuna ZEEYAD da tayi a wannan lokacin, after irin wahalar da ya sha a kanta, what if dagaske ta rasa shi har abada kenan, toh tabbas itama zasu rasa ta ne.



************************


__________Tsaye take ta a gaban wani ƙaton tekun, wurin shiru yake bakajin ƙarar komai sai na iskar dake kaɗawa dama kuma ruwan tekun ɗin dake kai komo yawa zai haɗiyo mutum, tana sanƴe da farar gown ɗin da ya kai mata har ƙasa kanta ɗaure da farar ɗankwali, ta juya baya.

A hankali yake takowa wurin ta staring at her back.

Juyowa tayi suna haɗa idanu kafin kuma ta sakar masa wani irin murmushi tana cigaba da kallon sa.

"DEENAH?" ya furta.

Hannu ta miƙa masa alamun yazo gare ta, babu musu yayi saurin ƙarasawa yana shirin kama hannun nata.

Wata budurwa ce wacce baiga fuskar ta ba tayi saurin shigewa tsakiyar su, kafin ta juya ga DEENAH tana tunkuɗa ta cikin ƙaton tekun ɗin.
"DEENAH!" ya furta da ƙarfi, a daidai lokacin ne kuma ya farka daga mafarkin da yake yi ɗin.
Dafe kansa yayi da hannayen sa yana jin yadda zuciyar sa ke mugun gudu, idan da wannan sau huɗu kenan yana yin thesame mafarki da DEENAH, wanda ya rasa gane mai hakan ke nufi, addu'a yayi sosai yana mai ɗago da kansa.
Idanun sa ne suka sauƙa kan wata Baƙar kuliya mai wani irin manƴan Hazel eyes staring at him in the dark.

Koh kaɗan bai wani ji koh da ɗar bane a cikin zuciyar shi sai ma idanun kuliyar da yake kallo shima.
"So it's you again, it's been long since i saw you" ya faɗa.

Wani irin kuka mai ban tsoro kuliyar tayi kafin kuma tayi saurin sauƙa daga kan gadon tana ficewa da gudu ta window ɗin ɗakin.

Da kallo yabi inda tabi kafin kuma ya miƙe tare da zuwa ya tsaya ta window ɗin.
"I know you're evil, but whatsoever you may be i would make sure i get you one day."





*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[7/31, 12:45 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```



*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*033...*




*A NEW LIFE*




____________Kwance take kan bed ɗinta da duƙunƙune kanta cikin pillow.

Buɗe ƙofar ɗakin Umma tayi ta shigo, ganin har yanzu DEENAH ɗin na yadda ta barta yasa ta fara magana cikin takaici da baƙin cikin halin da ta 6ullo dashi ƴan kwanakin nan "MADEENAH watau dai ba zaki bar wannan kukan na dalilin banza da wofin da kika tsirowa kanki ba koh, shikenan ke kullum bakida aiki sai rufe kanki a ɗaki kiyi ta kuka, ai yaci ace koh ciki ɗaya aka haifo ki da yaron nan kin manta dashi yanzu, toh ki sani ba zan kuma lamintar hakan daga gareki ba, zaki tashi ne tukun ki wuce kizo kici abinci koh sai ranki yayi mugun 6aci yanzun?."

DEENAH da ta ƙara volume ɗin kukan ta, ɗagowa tayi tana wurgi da pillow ɗin kafin kuma ta tashi tana faɗawa cikin bathroom ta rufo ƙofar da ƙarfi.

Da kallo Umma ta bi ta kafin kuma ta ƙarasa bakin ƙofar bathroom ɗin tace "Idan kin gama kukan naki marar dalili ki fito yanzun nan ina jiran ki, idan kuma kika kuskura kika sa raina ya 6aci baki fito dawuri ba ni dake ne a gidan nan" tana faɗin haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.

Kuka mai ƙarfi DEENAH dake cikin banɗaki ta sanƴa, sai da tayi mai isarta kafin ta wanke fuskar ta da duk ya kumbura tsabar kuka ta fito.

Cikin falon ta fito ta zauna ba tare da ta tankawa Umma dake binta da kallon takaici ba.

"Zaki zo ki ɗau abincin kici ne kokuwa?."

Tashi tayi daga inda take zaune ta sauƙo inda Umma take tare da ɗaukar plate ɗin abincin tana niyar barin wurin.

"Ina zaki?, dawo nan ki zauna kici."

Dawowa tayi ta zauna tana ƙoƙarin haɗiye kukan dake son ku6uce mata tare da buɗe plate ɗin ta hau cin abincin.

Tusawa kawai takeyi ba wai dan tanajin daɗin sa ba, yayin da hawaye ke gangaro mata kan ƙunci.

Bai fi cokali huɗu tayi ba taji amai na ƙoƙarin zuwan mata, dan haka ajiye cokalin tayi tana kya6e fuska inda dakyar ta iya haɗiye na cikin bakin ta.

"Ba dai ki cemin har kin ƙoshi ba."

"Umma dan Allah kiyi haƙuri wallahi bana jin cin abincin" ta faɗa cikin kuka.

"Aa ba dai a gidan nan ba kam, banga dalilin da zai sa kice bakya jin ƴunwa ba bayan lafiyar ki ƙalau, maza ki buɗe baki kici abincin nan yanzu."

Hannu ta kai ta ɗau cokalin tana sake ɗebo abincin ta kai bakin ta.

Bata kai ga haɗiye wa ba, taji amai na zuwa mata ba tare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta shiga kwararo shi anan yawa ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago duka.

A ruɗe Umma ta iyo kanta tana kama ta, tare da jero mata sannu yawa zata ari baki, kafin kuma ta kama ta suyi cikin ɗaki, bathroom ta kaita ta wanke mata bakin ta kafin kuma ta fito dan barin ta tayi wanka.

DEENAH idanu ta ƙurawa cikin mirror ɗin banɗakin tana kallo da idanun ta da sukayi luhu-luhu tsabar kuka wanda gani ɗaya zakayi mata kasan ba isasshiyar lafiya gare ta ba.

Wanka tayi ta fito kafin ta shirya cikin wasu irin Baggy ɗin riga da wando tana komawa kan bed ta kwanta tare da rufo bargo har izuwa kanta.

Sosai ta shiga halin tunani da ƙuncin rashin sa, a dah tasha ƙaryata kanta cewar bata sonshi but a yanzu ta gane gaskiya, tanason ZEEYAD sannan kuma tun ba yau ba ta kamu da son nasa, and now Umma tazo ta ruguza komai, tana neman kai rayuwar ta ga halaka, a yanzu babu abinda takeji a cikin zuciyar ta sai zafi da ƙunci, sosai zuciyar ta keyi mata raɗaɗi, musamman idan Umma tayi maganar ta mance dashi dan kuwa ya riga da yayi mata nisa, ita kanta tasan indai ZEEYAD ya cika mai zuciya toh kuwa koh da waiwayar ta ba zai sake ba.
Duƙunƙunewa tayi tana cigaba da rera kukan nata da ya zame mata jiki a hankali.


*********************


_________Da dare ganin jikin DEENAH ya rikice ya sanƴa Umma kiran likita yazo ya duba ta har gida, inda akayi mata ƙarin ruwa dama kuma allurai.

Zaune Umma take kusa da ita tana jin yadda take ta rera kukan nata da yaƙi ci yaƙi cinƴewa tunɗazun.

Jafar ne ya kalli Umma yace "Umma inason magana dake?."

Kallon sa Umma tayi tace "Inajin ka."

"Maybe in private" ya faɗa.

Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe kafin ta tashi tana ficewa daga ɗakin inda Jafar ma ya mara mata baya.

Kallon ta yayi yace "Umma nasan ni ban isa na ja dake kokuma naga rashin kyautatawar ki akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke a matsayin ki ta uwa a gareni ba, sannan kiyi haƙuri ki gafarce ni da maganar da zan faɗa miki yanzu, maganar gaskiya Umma shine sam baki kyautawa ZEEYAD ba haka ma DEENAH, duk da bansan dalilin ki na ganin kin raba alaƙar mu dashi ba amma inason nasan menene dalilin da yasa bakya ƙaunar sa kokuma ya ra6e mu har ma wata alaƙa ta dauru tsakanin sa da DEENAH?."

Kallon sa Umma keyi kafin tace "Ba wai ƙaunar sa bane bana yi, sai dai kamar yadda ka faɗa sam banason wata alaƙa ta ƙullu tsakanin sa da DEENAH."

"Amma Umma maiyasa, Umma he loves DEENAH so very much, sam baiyi deserving abinda kikayi masa ba, Umma ke kanki kinsan yadda yake matuƙar nuna kulawar sa akan DEENAH wanda koh wannan so called saurayin nata Abdul bai nuna mata koh da kwatan hakan bane, Umma ZEEYAD bai guji DEENAH ba bayan rashin lafiyar da ta faɗa a baya, that means he has a good heart sannan a shirye yake da yayi accepting ɗinta duk yadda take, bai ta6a nuna gajiyawar sa na nuna kulawar sa a gareta ba, he was always worried about her na rashin samun lafiyar ta, Umma ZEEYAD has a good heart sannan tsakanin sa da Allah yakeson DEENAH ke kanki kinsan da hakan but maiyasa zaki saka masa da breaking heart nasa wurin raba shi da DEENAH, after all what he did."

"So kana son na ɗauki auren ƴata na baiwa total stranger wanda bansan menene tushen sa da asalin sa ba, bance bashida kirki ba, ofcourse he is kind hearted sai dai barin sa cikin rayuwar mu shine yafi alkhairi a gareshi dan kuwa koh da yana nan ɗin, babu abinda zai sanƴa na ɗau auren DEENAH na basa, bayan ban ta6a sanin kowa nasa ba, hasali ma ba sanin ingantaccen inda ya fito koh wanene shi mukayi ba, bansan ta wace hanƴa ya samu ɗumbin arzikin da yake juyawa ba, bayan daga gani bashida kowa koh wata alaƙa da wannan ƙasar, how comes yaron da na sani yake yawo tamkar almajiri a dah chan turns to be yayi wannan uban kuɗin alhalin bayida wani gata koh mai tsaya masa a ƙasar, and you expect me na ɗau auren DEENAH na basa, daga nan kuma na shiga bakin duniya cewar arziki da kuɗi sun rufemin ido na ɗau ƴata na aura wa wanda bansan asalin sa da tushen sa ba, he had done enough for us, tayaya kake tunanin zan barsa ya cigaba da yiwa DEENAH hidima bayan nasan ba bashi auren ta zanyi ba, yaje shi Allah zai haɗa kowa da rabon sa."

Baki kawai Jafar ya saki yana kallon Umma har ta idda zancen ta nan yace "But...but Umma Allah ya kan sauya rayuwar mutum cikin abinda bai fi daƙiƙa ɗaya ba, dama duk sabida bakisan asalin sa da tushen sa dama kuma yadda akayi yayi arziki bane ya sanƴa ki yanke wannan hukuncin?."

"Kwarai kuwa, koh kai kasan asalin sa da tushen nasa ne, kana aiki ne kawai a ƙarƙashin sa sannan a iya zaman ka dashi ya ta6a buɗar baki ya baka cikakken labarin koh shi wanene?."

Shiru yayi yana nazari kafin kuma ya girgiza kai alamun Aa, sannan yace "Ya dai ta6a cemin shi ɗan ƙasar Egypt ne."

"Egypt?" Umma ta faɗa tana kallon sa.

Kai Jafar ya jinjina nan tace "Who knows if faɗamaka hakan kawai yayi, but koh kaɗan baiyi kama da Balaraben Egypt ba, he must be from Asian countries, koh ma dai menene i have already made up my mind, and i won't go back on my words."

"Amma Umma, think about DEENAH..."

Hannun ta ɗaga masa tace "DEENAH will be fine, am sure kawai tausayin sa dama kuma kyautatawar da yayi mata lokacin da batada lafiya ke damun ta, idan ta ɗanyi kwana biyu yanzu ita ma mantawa zatayi dashi."

"Umma yakamata ace kin fahimci DEENAH, she is inlove with him."

"No she is not, she is still a child, ƙuruciya ce kawai ke damunta, dah zaka yi bincike mai zurfi yanzu zaka gane ba wata soyayya da takeyi masa, just let me deal with her issue."

"Umma you misunderstood DEENAH's feeling, she is actually inlove with him, if not then maiyasa tun bayan dawowar ta hayyacin ta bata kuma sake samun nutsuwa ba, batada wani magana kullum da ya wuce nasa, sannan batada wani aikin yi sai kuka and you called it tausayin sa take, of course akwai tausayin nasa haka kuma akwai soyayyar sa tattare da DEENAH, think about it Umma kina neman jefa rayuwar DEENAH ga halaka ne tun ba'a je koh ina ba ta fara zazza6i imagine kuma mai zai faru nan gaba."

"Enough of this Jafar, babu abinda zai faru, am sure DEENAH will be fine, kayi mata addu'ar samun lafiya kawai."

"Umma ai it's a must nayi mata addu'a, but Umma kinyi kuskuren raba DEENAH da ZEEYAD coz am sure ba zata kuma samun mai sonta kamar sa ba."

"Have you lost your mind koh menene Jafar?, addu'a zakayi mata Allah ya musanƴa mata shi da wanda yafi alkhairi ba wai ka dinga irin maganganun nan ba, it doesn't make sense, and mind you banason sake jin maganar wani ZEEYAD or something similar to that a cikin gidan nan, kayi ƙoƙarin ganin kayi calming ƙanwar ka na ganin ta mance dashi sannan kuma she have to move on,DEENAH ba zata rasa masoyin gaske ba da izinin Allah, banason ka kuma sake yimin wannan maganar, kaji?."

Kai kawai ya jinjina yace "Am sorry, ki gafarce ni idan na 6ata miki rai."

"It's alright, muje mun barta ita kaɗai a ɗaki."

Juyawa sukayi tare da komawa cikin ɗakin.

Kallon DEENAH da har yanzu bata bar kukan nata ba yayi cike da tausayin ta kafin yace "DEENAH, it's okay haka nan kinji, stop crying kada ki jawa kanki wani ciwon."

"Umma...Umma bata sona yanzu."

Kallon juna Jafar da Umma sukayi kafin yace "No DEENAH ki bar faɗin haka, kema kinfi kowa shaida yadda Umma ke ƙaunar mu, take kuma iya ƙoƙarin ta na ganin ta faranta mana da dukkanin wani abu da ta mallaka, Umma ba zata ta6a aikata wani abu da zai zamto cutarwa a gareki ba."

"Mai kake nufi, kana nufin Abyad shi ɗin cutar dani zaiyi ne, maiyasa Umma ta kasa ganewa ne, yanada kirki sosai maiyasa zatayi masa abinda ta aikata, bai cancanci hakan ba."

"No DEENAH ki bar faɗin haka, bance ZEEYAD cutarwa ne shi ɗin a gareki ba, but am definitely sure indai har keda shi a destined to be together then babu abinda ya isa ya hana yiwuwar hakan,.just kawai ki kwantar da hankalin ki kici gaba da addu'a kinji?."

Kai ta jinjina masa cikin kuka tana lumshe idanu ba tare da ta kalli Umma dake zaune gefen ta ba.



*************************


__________Tsaye yake gaban mai Martaba dake zaune kan Throne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login