Showing 75001 words to 78000 words out of 236327 words

Chapter 26 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45342

ta mutu, amma shi sam babu alamun zai yarda da hakan nan kusa.

"Wait...don't tell me cewa kaima ka yarda cewa ta mutu?" ya faɗa yana kallon Jafar da yayi shiru yana saurarar sa.


Shiru Jafar yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, dan kuwa abinda yakeji a cikin zuciyar shi ba zai musaltu ba, dan kuwa DEENAH tamkar farin cikin sa haka take, ita ɗin ta kasance abar alfaharin sa ce, tabbas yayi rashin ƴar uwa, yarintar su kaɗai abar burgewa ce wanda idan ya tuna sai yaji wani irin kewar da yakejin har a abada ba zai daina ta ba, su kaɗai kawai iyayen su suka haifa, Mahaifin su tun DEENAH nada shekaru biyar ya rasu, inda ya saura daga shi sai Ummar su da DEENAH, su uku kaɗai, sun taso cikin so da ƙauna dama kuma kulawar juna, sai dai yau guda wannan ƙaunar ta yanke Saura shi da Umma kaɗai cikin family ɗinsu, bai san yaya rayuwar su zata kasance da rashin DEENAH ba, rayuwar su ba zata ta6a tafiya cikin farin ciki kamar ta dah ba, maiyasa DEENAH bata mutu tun a ƙaramar ta ba sai yanzu da ta zama budurwa wacce kowa ke so dama kuma ƙulla alaƙa da ita?.


Kuka Jafar yasa yana rufe fuskar sa da tafukan hannun sa, sosai zuciyar sa ke yi masa zafi, ganin gari ya waye kuma ya kusa rabuwa da ƴar uwar sa, rabuwa ta har abada, ba zai sake ganin ta ba, shi kaɗai yasan irin abinda yakeji a zuciyar sa, he can't believe it shima, sai dai babu yadda ya iya da lamarin Ubangiji, tunda dama duk Allah ne ya hallice mu sannan kuma wataran dole ne mu koma gareshi, koh ba jima koh ba daɗe, dan kuwa babu wanda zai dauwama a duniyar.

Sosai ya baiwa ZEEYAD tausayi inda shima har ya fara sanƴawa ransa cewa dagaske MADEENAH ɗin sa ta mutu ba, kafin kuma yayi saurin kawar da tunanin daga ransa yana girgiza kai.


A inda suke tsaye wata Nurse ta fito ta same su tare da sanar dasu cewar doctor na neman ganin su.


Mara mata baya sukayi zuwa office ɗin doctor ɗin, zuciyar su cike da zulumin abinda zai fito daga bakin sa.

Duk wuri suka samu suka zauna kowanne zuciyar sa cike da fargaba dama kuma tsoro musamman ZEEYAD da ya kasa zaune properly.


Kallon su likitan yayi yace "Menene matsayin ku a gare ta?."

Kallon juna sukayi kafin Jafar yace "Mu ɗin yayun ta ne."


Kallon ZEEYAD yayi alamun mamaki kafin kuma ya share yace "Well am sorry to said this, but...."


"Don't tell me please, please Doctor don't tell me that she is dead" cewar ZEEYAD kamar wanda zaiyi kuka.


Shiru doctor yayi yana kallon sa kafin kuma yace "Well am sorry..."


"Ta mutu right?, alright then zamu tafi da ita tun jiya da dare aka tabbatar mana da hakan a asibitin da muka fara zuwa, and gashi nan anan ma hakanne, I told you sir DEENAH is dead."


Sosai ZEEYAD ke jin wani irin abu mai ɗaci a maƙoshin shi, har yanzu bai yarda ba, babu ta yadda za'ayi ace DEENAH ɗinsa ta mutu ne, No it can't be.


Gyaran murya Doctor yayi yace "Well maybe ku tsaya ku saurari abinda zan faɗa tukun."


Duk maida duban su sukayi kansa dan jin abinda zai faɗa.

Nan yace "Your Sister is Half death, i mean she has fallen into a deep sleep which is, She is in a Coma, bata mutu ba, she is still alive."


Tunda ya fara magana duk suka saki baki da ido suna kallon sa, Jafar ne cikin rawar murya yace "Kana nufin, DEENAH bata mutu ba?."


Kai likitan ya jinjina masa kafin yace "Yes, but tana buƙatar aiki da gaggawa, da akwai internal injuries tattare da ita so ya zama dole ne muyi mata aiki in less than an hour..."


"Just tell me, nawa ne kuɗin aikin i will pay any amount indai zata samu lafiya, i know she is not dead,i know it, just tell me how much you need for the surgery" faɗin ZEEYAD da ya rasa farin ciki zaiyi koh baƙin cikin faɗawar ta Coma.


"Yeah sure she will definitely be fine muddin mukayi aikin, the amount is 3million."


"Just start preparing for the surgery and make sure that she is fine, i will bring the money as soon as i can, now."


"Yes sure, but don't forget the money is for her Internal surgery, not for the Coma."


"What do you mean?."


"I mean, ba lallai ne ta tashi daga Coma ɗin ba koh da kuwa munyi mata aikin, sabida da akwai raunikan da taji su zamuyi aiki a kai,but for the Coma sai dai kuyi ta yi mata addu'a Allah yasa ta farfaɗo nan kusa kawai."


"What?."

"Yes."


"But like how many days zata ɗauka a hakan?" cewar Jafar yana kallon likitan.


"It depends, i can't decide it gaskiya, but zaiyiwu maybe a week or couple of WEEKS, a month, a year or even decades."


"What, a DECADE!?" ya faɗa cikin zaro idanu yana kallon likitan.


ZEEYAD ne yace "I will go get the money just make sure that she is alright please."


"Sure" cewar Doctor.

Miƙewa ZEEYAD yayi ya fice daga cikin office ɗin ba tare da yabi ta kan su Jafar da doctor ɗin ba kuma.


Motar sa ya nufa ya buɗe ta ya shiga, Cheque ya ciro tare da rubuta amount ɗin kuɗin yayi signing sannan ya fito ya koma ciki.


Amsa likitan yayi ganin harda ƙarin 2million akai dukda kuwa basa kar6ar cheque.


Wani takarda ya basu Jafar ya sanƴa hannu akai kafin kuma a shiga tiyatar.


Kallon Jafar ZEEYAD yayi yace "She would be fine."


Rungume sa Jafar yayi hawaye na kawo masa yace "Ban yarda da kai ba tun farko da kacemin DEENAH bata mutu ba, but yanzu i can clearly see that you're saying the truth, how did you know cewa bata mutu ba?" ya faɗa yana ɗagowa.


Murmushin kan le6e ZEEYAD yayi kafin kuma ya sanƴa hannu ga dafe saitin zuciyar sa.

Kallon sa Jafar yayi na ƴan seconds kafin yayi murmushi yace "Kanason DEENAH, don't you?."

Ɗagowa yayi ya kalli Jafar kafin ya saki murmushi mai ciwo yace "But she doesn't like me, she hate me."

Shiru Jafar yayi bai iya cewa komai ba.


Kallon sa ZEEYAD yayi yace "Your Mom, you should go to her, and tell the good story of DEENAH being alive."


Kai Jafar ya jinjina yace "Yeah sure, zanje na faɗamata yanzun nan, i know she must be so worried musamman idan ta farka bata ganmu ba."


Kai ZEEYAD ya jinjina kafin yace "See you."

Tafiya Jafar yayi ya bar ZEEYAD, wuri ya samu ya zauna minutes after minutes yana ɗagowa ya kalli ƙofar ɗakin tiyatar.


*************************


*2 DAYS AFTER*

Sosai suka yi matuƙar damuwar rashin ganin ZEEYAD yau tsawon kwana biyu kenan.

Sun buga kiran wayar tasa tun tana shiga ba'a ɗauka har yazo ya zamto switched off.


Khairat kuwa kuka har tayi shi ta gaji dan kuwa ta sadaukar ZEEYAD guduwa yayi dan kawai kada ya aure ta.

"Daddy i told you bayasona, Daddy ka duba afterall wahalar da kasha akan shi ka maida shi mutum,m yau ya butulce maka, bayan yau ne ranar Engagement namu, amma ya gudu, he left ba tare da ya sanar da kowa inda yaje ba" ta ƙarashe cikin kuka.


Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe kafin yace "ZEEYAD ba zai ta6a guduwa ba, wani abin ne dai ya faru dashi, nasa anje chan gidan shi an bincika min but they found his cell-phone scattered on the floor, sannan guards ɗinsa sun ce ya fita ne cike da tashin hankali sannan tundaga nan kuma basu sake sanin inda yaje ba, sannan kuma har yau da muke maganar nan bai dawo ba, something must be very wrong Khairat."


"Haba Alhaji, ba'a yiwa ɗan yau shaida fah, ni dama sai da aka gargaɗe ni akan yaron nan wataran zai iya butulce mana, gashi nan ai yau daga cewa zaka haɗa shi aure da ƴar ka ya gudu, amma kai nan sam bakaga laifin sa ba, sai ma cewa da kakeyi wani abin ne ya faru dashi bayan an zagaye kaf garin nan ba'a ganshi ba, hatta abokan kasuwancin sa basu san inda yake ba, gaskiya dai wannan yaron ya bani mamaki ban ta6a zaton abinda zai saka mana dashi ba kenan" ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata.

"A'a Hajiya, baikamata muyi saurin yanke hukunci ba, ZEEYAD must be somewhere in this country, tayaya zai gudu bayan rabin business nasa a wannan ƙasar yake running ɗinta?, mu sake bashi lokaci su kuma baƙin da aka gayyata zan fita na basu haƙuri akan cewa an ɗaga saka ranar" yana faɗin haka ya fice daga cikin ɗakin.


Da kallo suka bishi kafin Khairat ta sanƴa kuka, nan kuma Momy ta shiga rarrashin ta.

"Kada ki damu kinji, kisa a ranki indai ZEEYAD mijin ki ne toh fah babu abinda zai hanaki mallakar sa da izinin Allah, maganar mahaifin ki na kan gaskiya, maybe wani abin ne ya faru da ZEEYAD, ki kwantar da hankalin ki."

"How Momy how, tayaya zan kwantar da hankali na, kinsan irin burirrikan da naci ne akan wannan engagement ɗin, wane irin kallo kike tunanin friends ɗina zasuyi min, maiyasa komai kuke goyon bayan sa ne, amma nikuma duk abinda nayi banyi dai-dai ba, hakan na nufin kun fi sonsa a kan ƴar da kuka haifa komiye?."


"Haba Khairat ya zakice haka, muna sonki mana, ki daina irin wannan maganar please."


"Zan daina ne ranar da kuka aura min shi ya zama mijina mallaki na ni kaɗai" tana faɗin haka ta tattari wedding gown ɗin ta irin ta turawa sak da ta sanƴa tayi waje.


************************


Zaune yake kusada ita, tana kwance helplessly kamar gawa, hancin ta manne da oxygen dama kuma wasu life saving machines ɗin da aka jona mata.


It hurts ZEEYAD sosai fiye da yadda yaji lokacin da akace dashi ta mutu ganin ta cikin wannan hali, bata motsi, bata jin wadanda ke kusa da ita, haka take kwance kawai ba tare da ta san meke wakana around ita ba.


Hannu yasa cikin aljihun sa ya ciro wata ƴar ƙaramar box ɗin zobe.

Ciro zoben yayi yana jujjuya ta a hannun shi, kafin kuma ya kalli fuskar ta tare da kamo hannun ta yace "Am supposed to get ENGAGED to someone else today, but ƙaddarar mu ta yanke yiwuwar hakan, MADEENAH you're my source of happiness, i can't be happy with someone else idan ba ke ba, So i guess we should get ENGAGED instead" ya ƙarashe yana kallon fuskar ta.

Yatsar ta ya kama tare da sanƴa mata zoben, nan ya zauna cif yayi mata kyau sosai.


Murmushi yayi yanajin zuciyar sa na yin zafi ganin yadda take kwance motionless bata motsi.


Allah ne kaɗai yasan yaushe ne zata farka, abinda yafi tsorata shi shine maganar da Doctor ɗin ya faɗa musu na cewar da akwai posibilities ɗin zata iya samun stroke or maybe memory loss.


"No, that won't happen insha Allah" ya faɗa cikin girgiza kai yana sarƙe yatsun su wuri ɗaya.


Jafar ne ya shigo cikin ɗakin tare da ajiye ledar take-away ɗin abincin da ya iyo musu, kafin yaja kujera ya zauna shi ma yana kallon DEENAH.


"Yau ne Engagement naka and you haven't called them ka faɗa musu abin dake faruwa ba, wane irin tunani kake ganin zasuyi akan ka?."


Shiru yayi yana saurarar Jafar kafin kuma yace "That doesn't matter, all what matters here is naga MADEENAH taji sauƙi, i want to see her talk and smile again, i want her to yell at me it cheers me up akan ganin ta kwance haka.


Knocking akayi a ƙofar shigowa, nan Jafar ya tashi yaje ya buɗe.


Amirah ce dama kuma Anty Khadija, hanƴa ya basu suka shigo kafin su sami bakin bed ɗin su zauna.


"Ya jikin nata yanzu?" cewar Anty Khadija.


Jafar ne yace "Alhamdulillah."

"Allah ya tashi kafaɗun ta" suka faɗa.


"Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum."


Sun ɗan zauna kaɗan kafin tace "Bari muje wurin su Anty itama mu duba jikin ta."


Kai kawai Jafar ya jinjina mata kafin kuma su fice.


*********************

Umma ce zaune cikin tagumi ta sanƴa DEENAH a gaba tana kallo, kallo ɗaya zakayi mata ka san ita ɗinma ba isasshen lafiyar gare ta ba.


Yau 5days kenan, amma haka nan take kwance kamar gawa koh wata mai bacci bata motsa ba.

Jafar ne yace "Umma ki kwantar da hankalin ki, insha Allah zata samu sauƙi, Umma yakamata ki dinga shan magungunan ki, da wanne kukeson naji ne, dukkanin ku bakuda lafiya and ke kuma kin ƙi kisha maganin ki kin sanƴa damuwa a ranki" ya ƙarashe kamar wanda zaiyi kuka.

Ɗagowa Umma tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace "kawomin maganin na sha."


"A'a Umma, mu koma ɗakin da akayi admitting ɗinki kici abinci sannan ki sha maganin naki ki samu hutu, idan yaso sai kizo ki duba ta anjima."


Babu musu Umma ta miƙe kafin ya taimaka ya riƙe ta suka fice daga ɗakin.


Da kallon tausayi ya bisu kafin kuma ya maido duban sa kanta.


Zuwa yayi ya zauna dan kuwa koh kaɗan bayason yin nisa da ita.


Fuskarta ya ƙurawa idanu yana kallo tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" kamar wani mai son tada ta daga bacci.


Idanun sa ya ɗan waro yana sake kallon fuskarta da kyau ganin kamar ta motsa idanun ta.

Matso da fuskar sa yayi yana cigaba da kallon ta tare da sake kiran sunan ta.


Idanun ta ta fara motsawa alamun tanason buɗe su, murmushin farin ciki ne ya fara forming akan fuskar ZEEYAD nan ya tsaya kallon ta yadda take ƙoƙarin buɗe idanun nata a hankali har ta gama buɗe su tana ware su cikin nasa da ya kafe ta dasu.


Murmushin farin ciki ya sake yace "MA...MADEENAH, you're awake, Alhamdulillah" ya faɗa cike da farin cikin yana faɗawa Sujudu Shukur, kafin ya sake tasowa yace "Wait..i will call the doctor i will be right back" ya faɗa yana ficewa daga ɗakin cikin gudu.


Da idanun ta da su kaɗai take iya motsawa ta bisa.


Ba'a jima ba ya dawo tare da Doctor ɗin yace "Look ta buɗe idanun ta, she is awake" ya faɗa cike da tsananin farin ciki.


Duba ta Doctor ɗin ya shiga yi, sai dai ya tabbatar komai is normal kafin ya ɗago yana kallon ZEEYAD.


Maida duban sa ZEEYAD yayi kanta yana kallon idanun ta da ta kafe su wuri ɗaya bata motsa ƙifta su bale ta motsa su.

Farin cikin da yake ciki ne ya fara gushewa nan yace "Why..why is she not moving her eyes, i just saw her blinking kafin na fita kiran ka, why then yanzu..."


"Her health is improving, thank GOD ta fito daga Coma, but i told you that there is posibility ɗin zata iya samun stroke or brain loss, and now that is exactly what is happening to her."


"W...w..what?" ya faɗa cikin rarrabewar harshe.

"Yes, amma ka kwantar da hankalin ka sannan ku cigaba da addu'a zata ji sauƙi very soon insha Allah" yana faɗin haka ya fice tare da barin ZEEYAD da sakakken idanu yana bin DEENAH da kallo.


Juyawa yayi ya fice daga ɗakin trying so hard ganin yayi controlling kukan dake cin zuciyar sa.


"Sir?" Jafar ya kira shi.

Saurin tsarewa yayi cikin dauriya ya juyo yace "Jafar, ka bawa Ummar taku maganin ta?."


Kai ya jinjina masa nan yace "Mu koma ciki."


Duk ciki suka koma Jafar ne yaga idanun DEENAH a buɗe, da sauri ya ƙarasa farin ciki na cin shi yace "DEENAH?, look she is awake, DEENAH ta tashi."


Kallon sa kawai ZEEYAD keyi cike da tausayin sa.


Jafar ne ya lura da bata motsa idanun ta nan yace "But...maiyasa bata motsa idanun ta, i guess she is fully awake, right?" ya faɗa yana juyowa ya kalli ZEEYAD.


"No" ya faɗa a taƙaice.


Ɗagowa Jafar yayi kawai cikin sanƴi ya samu wuri ya zauna yana dafe kansa da hannayen sa.


*******************


*A WEEK LATER*

Sosai Umma taji sauƙi dan haka hutu ta ɗauka a wurin aikin ta har sai DEENAH ta gama warkewa, wanda kullum take cikin addu'ar hakan.


ZEEYAD kuwa kullum yana kan DEENAH daga safe har zuwa dare da zai koma masauƙin sa, kasancewar yanzu Umma ce ke kula da ita.


Umma tayi da ZEEYAD akan ya maida hankali kan business ɗinsa amma yaƙi dan kuwa indai ba gani yayi DEENAH ta warke gabaɗaya ba, ba zai iya ta6uka komai ba, haka take tayi masa kullum har ta gaji ta kyale shi.


Zaune suke dukkanin su inda Umma da Mami ke hira ƙasa-ƙasa.


DEENAH kuwa pillow aka jingina mata aka ɗan zaunar da ita akan bed ɗin.


Inda kuma ZEEYAD da Jafar ke zaune kan Couch kowa da abinda ya dame sa, Jafar maganar business ɗinsu yakeyi masa discussing sai dai koh kaɗan shi hankalin sa baya kai, idanun sa na kan DEENAH yana kallon ta kamar kullum baya gajiya, hakan yasa Jafar jan bakin sa yayi shiru.


Banko ƙofar ɗakin akayi aka shigo hakan yasa su saurin ɗagowa dan ganin koh wanene.


Tsaye tayi tana ta faman huci kamar wata zakanƴa, fuskar nan tata manne da ƙatuwar shade kamar kullum ta sha make-up.


Miƙewa yayi tsaye yana kallon ta, kafin kuma idanun sa su sauƙa kan Momy da Dady dake shigowa.


Sosai ZEEYAD yaji wani irin kunƴa ta kama shi hakan yasa shi sadda kai ƙasa, yana lumshe idanu.


"Toh macuci, butulu wanda baisan alkhairi ba, Allah ya toni asirin ka, ashe dama nan wurin kazo ka maƙale a wurin wata banza nan, miskiniya..."


Tsawar da Daddy ya daka mata ne yasa ta yin shiru da bakin ta tana kumbure-kumbure tare da hararan ƴan cikin ɗakin.


Kallon DEENAH dake kan bed Momy da Daddy sukayi, kafin kuma Daddy ya haɗa hannayen sa alamun neman yafiya yace "Dan Allah ina baku haƙuri akan halayyar ƴata Khairat."


Duk shiru sukayi suna kallon su kafin Momy tace "Dan Allah muna baku haƙuri, kuyi haƙuri kwata-kwata Khairat batada hankali, kuyi haƙuri dan Allah, mun faɗo muku ɗaki haka babu koh sallama."


"Bakomai" inji Mami cikin ɗan murmushi.


Murmushi suma sukayi kafin kuma su shiga gaisuwa tare da kuma bada haƙuri akan halin Khairat, idanun su akan DEENAH cike da tausayin halin da take ciki.


Daddy ne ya kalli ZEEYAD yace "ZEEYAD, ka kwantar da hankalin ka, ni dama nasan dole da akwai wani abin dake faruwa, dan kuwa haka kurum ba zaka 6ace mana mu kasa samun inda kake ba, amma tunda ka kira ka shaida min komai naga yakamata ace mun taho dan ganin abin dake faruwa."


Sunkuyar da kai ZEEYAD yayi yanajin zuciyar shi na mugun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login