Showing 138001 words to 141000 words out of 236327 words
mata bala'in kyau kamar ka ɗauke ta ka gudu.
"Wowww" gaskiya ranki ya daɗe kinyi kyau sosai.
Murmushi Jalilah tayi dan kuwa ba ƙarya sukayi ba, ita kanta tasan ba ƙaramin kyau tayi ba.
Ƙarar jiniya da sauƙar motocin da suka fara jiyowa ne ya tabbatar musu da cewa prince ya dawo daga tafiyar da yayi.
Duk kallon ta suke kafin Kiki tace "Ina tabbatar miki da sai ya kasa ɗauke idanun sa akanki yau ranki ya daɗe."
Blushing tayi cike da farin ciki tana ficewa daga ɗakin.
Da wani irin mugun kallo Kiki ta bita kafin ta kalli ƴan matan tace "Kuna jina, duk wacce tayi kuskuren fidda abinda muke shiryawa ba sai nace komai ba, ta san yadda makomar ta zata kasance."
Duk kansu a ƙasa ba tare da sun iya ɗagowa sun kalleta ba.
"Lale lale, Marhaba bika ya Habiby" cewar Grandma tana buɗa masa hannayen ta.
Rungume ta yayi cike da farin cikin ganin ta yana murmushi yace "I miss you Grandma."
Ɗagoshi tayi tana bashi peck a kumatu tace "Ai baka kaini jin kewa ba Habiby, maza ƙaraso ciki" ta faɗa tana riƙo hannun sa zuwa cikin katafariyar falon ta zaunar dashi.
Da kallo yake bin yadda aka gyara part ɗin da irin decorating ɗin da akayi masa, nan yace "Grandma, wake yin birthday ne yau, i can see duk kun hau wanka like masu shirin zuwa wani taro."
Kallon sa Grandma tayi tace "Ba dole mu gyara gida mu tsaftace shi kuma mu hau wanka ba, yau Boy ɗina guda ya dawo, ai duk sabida kai akayi wannan abin."
Murmushi yayi yace "Me?" yana tashi tsaye ya kamo hannun ta.
"Kwarai kuwa Habiby, koh dai baiyi maka bane?."
Murmushi yayi yace "Yayi kyau sosai amma bai kai Grandma ɗita ba" ya faɗa yana ɗan jan kumatun ta.
Buge hannun sa tayi tace "Ni sa'ar wasar ka ce da zaka ja min kumatu koh?."
Riƙe kunnen sa ɗaya yayi yace "Sorry."
Murmushi tayi kafin tace "Jalilah, ina Yarinƴar nan ta shiga ne tunɗazu?, ke zo" ta faɗa tana yafito wata kuyanga da hannun ta.
Ƙarasowa tayi tace "Gani ranki ya daɗe."
"Jeki sama ki kirawo min Jalilah yanzun nan, kuma bance ki tsaya kalle-kalle da shige-shigen da ba'a saki ba, dan kunyi masters akan wannan, jeki."
"Grandma?" cewar ZEEYAD ɗin cikin murmushi.
"Barni ai ni nasan halin su ne shiyasa na faɗi hakan."
Jalilah dake la6e a sama tana kallon su ta kasa sauƙowa sabida kunƴa ne ta runtse idanun ta da ƙarfi tana sake ware su, "Yaa Rabb" ta furta tana fitowa daga inda ta la6e ɗin ta hau sauƙowa a hankali.
"Grandma mai..." maganar tasa ce ta ƙaƙare sakamakon idanun sa da sukayi arba da Jalilah dake sauƙowa kanta sunkuye sabida kunƴa.
Baki sake Grandma ke kallon sa kafin tace "Inajin ka, mai kake kallo ne..." itama kasa idda maganar tata tayi bayan ta juya dan ganin abinda yake kallo.
"Tabarakallah masha Allah, Masha Allah" kawai Grandma ke furtawa tana kallon Jalilah.
Idda sauƙowa tayi tana ƙarasowa wurin su, hannun ta Grandma ta kamo tace "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan kyakkywar halittar."
Kunƴa ce ta kama Jalilah dan haka blushing kawai take tayi ba tare da ta iya ɗagowa ta kalli idanun su ba, musamman ZEEYAD da yayi losting a kallon ta.
Tsaye suke la6e daga saman benin suna kallon su kafin Kiki tace "Nan da Awa ɗaya maganin zai fara aiki a jikin ta, ku sani indai wannan aikin yayi kyau ba ƙaramar kyauta da karramawa zamu samu daga wurin Uwargijiya ta Sarauniya Naseeba ba."
Kiss Grandma ta manna mata a goshi tana kamo ta ta zaunar da ita.
"Lallai ba ƙaramin kyau kikayi ba ƴar nan, wannan duk wankan tar6ar Boy ne haka?."
Murmushi kawai Jalilah tayi ba tare da tace komai ba.
ZEEYAD ɗauke idanun sa yayi akanta yace "Grandma, i will be right back" yana faɗin haka ya sanƴa kai ya fice ba tare da ya jira cewar Grandma ba
Da kallo duk suka bisa kafin Grandma tace "Barshi kinga yana basarwa ba ƙaramin kyasawa yayi ba."
Murmushi mai sauti Jalilah tayi tana sadda kai ƙasa.
***********************
______ZEEYAD bai dawo ba sai da yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya wanda ba ƙaramin kar6ar sa sukayi ba.
A dining ya hango Grandma da Jalilah tsaye suna jere plates.
Zama zaiyi nan Grandma tace "Maza ƙaraso nan wurin."
Tashi yayi inda taja masa kujera ya zauna.
Ba'a daɗe ba YAZEED da Sadeeq suka shigo inda suma sukayi joining nasu a dining ɗin.
Jalilah ce ta shiga serving ɗin kowa, kafin ita ma ta sami wuri ta zauna.
A nutse kowannen su ya shiga cin abincin gaban shi, inda ZEEYAD dake ta iya ƙoƙarin sa na ganin kada ya sake kallon ta ya ɗago tare da yi mata slight kallo yana kauda kai.
"What's wrong, ai yaci ace yanzu, poison ɗin ya fara reacting a jikin ta" cewar Kiki da har yanzu suke la6e ta sama suna kallon su.
"Mu ɗan bada kamar minti goma haka" cewar ɗaya daga ciki.
Gyara tsayuwa sukayi duk suna zuba idanun ganin abinda zai faru da Jalilah.
"Jalilah dear, yi haƙuri kije kitchen ki ɗauko min Inibi cikin fridge, wannan abinci yayi yaji dayawa."
"Toh Grandma" ta faɗa tana tashi tayi kitchen ɗin inda ZEEYAD yabi bayan ta da kallo.
Haɗa ido Sadeeq da YAZEED sukayi kafin Sadeeq yace "Looks like someone is inlove."
Kallon Sadeeq wanda kamar ba shi yayi maganar ba ZEEYAD yayi kafin yace "Grandma, kinajin shi koh?."
"Boy kenan, toh ai ni na daɗe da fahimtar hakan idan baka sani ba."
Tsuke fuska yayi yana kai cup ɗin juice baki yayi sipping.
"Oh Grandma, i forgot ban faɗamiki ba, remember the girl i told you about?."
Kallon YAZEED dake magana tayi tace "Yeah, nace dai ka samu shiga?."
Ɗan sosa kai yayi yace "Tukun nan dai, actually the girl is sick again."
"Subhanallah, meke damunta, har yanzu jikin nata ne bai dai-dai ta ba."
"Yeah Grandma."
"Allah Ubangiji ya bata lafiya mai ɗorewa."
"Aameen Granny will you mind idan mukaje gobe kika duba ta?."
"Masha Allah, zanso hakan" ta faɗa cikin murmushi tana kallon sa.
Ɗan ta6e baki ZEEYAD yayi yana tsakurar abincin gaban shi a hankali.
Ihun Jalilah da suka jiyo ne yasa su duk sake kasa kunnuwa dan jin koh gaske ne.
_"Grandma?"_ suka jiyo da ƙarfi cikin kuka.
Duk miƙewa tsaye sukayi muryar ta da suka sake jiyowa a karo na uku ne ya sanƴa su dugunzuma zuwa hanƴar kitchen ɗin.
ZEEYAD dake gaba ne ya fara shigowa, inda ya same ta durƙushe rungume da jikin ta tana susa.
"Jalilah?" ya faɗa yana cupping fuskar ta.
Ƙara ta saki tace "Jiki na, my body is burning" ta faɗa tana sosa hannun ta da takejin kamar ana zuba mata ruwan zafi a jiki dama kuma dukkanin jikin ta.
Duk kwalalo idanu sukayi waje ganin yadda lokaci guda jikin ta yayi wani irin manƴan jajayen tabo a duk inda ta sosa, abarka da jar fata.
"What...what is this?" cewar ZEEYAD dake riƙe da ita cikin rawar murya.
"Grandma help me, my body is burning bansan meke faruwa ba, the pain is unbearable" ta faɗa cikin kuka, tana ƙoƙarin unzipping rigar, ZEEYAD yayi saurin riƙe hannun nata yace "Ki bar sosawa haka nan, you guys should do something."
Ɗage doguwar gown ɗin tayi cike da muguwar azabar da takeji a ƙafafun ta da cinƴoyin ta, saurin maida gown ɗin ZEEYAD yayi yana rufe mata cinƴoƴin ta dake waje free ana kallo, kafin ya juyo ga Sadeeq da YAZEED da suka tsaya kamar poster suna kallon su, a tsawace yace "What are you all staring at?, do something."
"Sai dai muje hospital" cewar YAZEED.
Cicci6ar Jalilah dake cikin azaba bata ma san abinda take yi ba yayi, nan duk suka mara masa baya, Grandma hankalin ta a mugun tashe.
*Yawan Comment, Yawan Posting*
*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[8/8, 11:47 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*038...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
_________Umma ce zaune kusa da DEENAH da taƙi ta kalle ta tun wayewar garin yau, haka ma taƙi ta amshi wani abu daga gare ta.
"DEENAH, kici wani abu mana, kodai ba zaki ci abin hannu na bane?."
Juyowa tayi ta kalli Umma jin abinda ta faɗa, tashi tayi zaune daga kwancen da take kafin ta amshi plate ɗin soyayyen chips da kwai ɗin dake hannun Umma ta fara ci.
Shayi mai zafi Umma ta tsiyaya mata cikin mug tana miƙa mata.
Amsa tayi tana sipping a hankali, bata wani sha sosai ba ta ajiye.
"Kin ƙoshi ne?" cewar Umma.
Kai kawai ta jinjina mata tana komawa ta kwanta.
"Bara naje na sayo wadannan magungunan na dawo yanzu, you will be fine koh?" cewar Umma tana kallon ta.
Kai kawai ta jinjina mata kafin ta tashi ta fice.
Da kallon DEENAH ta bita kafin kuma ta miƙe tana sauƙowa daga kan bed ɗin tana sanƴa takalmi.
Zuwa tayi tana yaye labulen window ɗin ɗakin tana kallon waje.
Sosai tayi nisa a tunani, inda batasan da shigowar Sadeeq ba sai muryar sa da taji yana yi mata magana.
Juyowa tayi tana kallon shi kafin kuma ta bar bakin window ɗin tana komawa bakin bed ta zauna.
Murmushi yayi mata yace "Good Morning?."
"Morning" ta maida masa martani.
"So zan iya yin aiki na?" ya faɗa.
Kai ta jinjina masa nan yace "Alright, let's start from duba level na blood pressure ɗinki."
Kai ta jinjina masa tana gyara zama, nan ya shiga aiwatar da aikin shi cikin kwarewa.
"Where is your Mom?" ya tambaye ta.
Shiru tayi kamar ba zatayi magana ba kafin kuma tace "Tace zata je ta dawo."
"Okay" kawai ya faɗa, nan ya gama aikin sa ya fice.
Shiru tayi zaune ita kaɗai, ganin zaman ba zaiyi mata bane ya sanƴa ta miƙewa ta fice daga cikin ɗakin.
Fitar ta keda wuya ta hango YAZEED da Grandma tafe.
Daga inda YAZEED da ya hango DEENAH ta fito yace "Yo Grandma, there she is" ya faɗa yana ɗaura hannayen sa kan kafaɗun Grandma yana murmushi.
Murmushi Grandma tayi suna ƙarasowa gun DEENAH da ta tsaya kallon su har suka ƙaraso.
Murmushi Grandma tayi cikin muryar larabci ta kalli YAZEED tace "Tabarakallah Masha Allah, lallai Allah yayi halitta anan, i just hope yadda take kyakkyawa ɗinnan haka halayen ta suke kyawawa" cewar Grandma ɗin tana maida duban ta kan DEENAH dake kallon su da gajiyayyun idanun ta.
Riƙo hannun ta Grandma tayi cikin murmushi tace "Ƴar nan ya kike, ya kuma ƙarfin jikin naki?."
Ɗan murmusawa DEENAH tayi tace "Alhamdulillah" tana kallon Grandma ɗin.
YAZEED ne yace "Grandma ɗita ce ita ɗin, she came to see you."
Kai DEENAH ta jinjina kafin Grandma tace "Ina Mahaifiyar tata fah, sannan ina zataje ita da batada lafiya?."
Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Ina Ummien ki?."
"Ta...ta fita sayo magani, yanzu zata dawo."
"Toh ke kuma ina zakije haka, keda bakida lafiya?" cewar Grandma tana kallon ta.
Ɗan murmusawa kawai tayi ba tare da tace komai ba.
"Daga gani kinsha dogon jinƴa, muje daga ciki kada mu tsaya anan" cewar Grandma ɗin tana kamo hannun ta zuwa cikin ɗakin.
Zaunar da ita tayi kan bed itama tana samun wuri ta zauna, kafin tace "Ai YAZEED yana yawan bani labarin ki, babu ranar da zata zo ta wuce ba tare da yayi min zancen ki ba, ashe dai duk ba a banza bane, kyakkywar haliita iriyar ki ai dole ta sace zuciyar maza dayawa bama YAZEED ba, menene kake yimin ido ɗin koh ba gaskiya na faɗa ba" cewar Grandma dake kallon YAZEED dake tayi mata alamu da hannu da ido kan tayi shiru.
DEENAH da bata wani fahimci inda zancen ta ya dosa bane tace "Ban..bangane ba."
"Listen DEENAH, Actually Grandma ta ɗauka ke ɗin masoyiya ta ce" ya faɗa yana sosa kai.
"Kamar ya na ɗauka, kai da bakin ka fah kacemin kullum da tunanin ta kake kwana kuma kake tashi, toh mecece ita ɗin idan ba masoyiyar ka ba?."
YAZEED ji yayi kamar ya nutse anan wurin jin yadda Grandma ke ta sakin zance barkatai haka, duk sai yayi nadamar kawo ta duba DEENAH ɗin.
Fara'ar dake kan fuskar DEENAH ne ya ɗauke diff kamar an ɗauke wutar nepa.
"Grandma we should get going idan Ummien ta ta dawo anjima sai mu dawo koh?."
"Kinga ƴar nan, muma nan marar lafiya ce damu, yarinƴar da ɗan uwansa zata aura ce babu lafiya, mu nan zamu wuce idan mahaifiyar ki ta dawo ki gaida ta sannan kice zamu dawo zuwa anjima."
Haka kawai DEENAH taji gaban ta yayi mummunan faɗuwa, murmushin gefen baki kawai tayi tana kallon Grandma ɗin.
YAZEED kuwa sakin baki yayi yana kallon Grandma jin abinda take cewa "Grandma?" ya faɗa.
Miƙewa tayi daga zaunen da take tana faɗin "Toh ƴar albarka mu mun wuce koh, Allah ya tashi kafaɗun ki ya baki lafiya mai ɗorewa, muje" ta faɗa tana kallon YAZEED.
Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Bye DEENAH."
Kai kawai ta jinjina suna ficewa daga ɗakin.
"Grandma what do you think you're doing?" cewar YAZEED bayan fitar su.
"Kamar ya?, bangane ba dama mai kace min?."
"Grandma ce miki fah nayi inason ta but har yanzun batasan da hakan ba, but..."
"Toh ai dai-dai kenan, miye kuma wani abin damuwa, kai bakasan sauƙi ma na kawo maka ba?, yanzu tunda tasan abinda kake ji game da ita indai itama ta kyasa da kai tuni za'a wuce wurin, da kai da Boy fah ku ɗin na musamman ne duk wacce tayo dacen auren ku ai ta more."
Kallon Grandma kawai yake ba tare da yace komai ba har ta idda zancen ta, nan yace "But Grandma naji kince Jalilah yarinƴar da ZEEYAD zai aura shi yace miki yana sonta?."
"Kai kaji ka da wani magana, ai koh bai ce yanason ta ba ni naga hakan tattare dashi, kai bakaga duk yadda yabi ya nuna damuwar sa akanta ba yanzu, koh wurin ta ya kasa bari."
Numfashi YAZEED ya sauƙe cike da gajiyawa da halin Grandma ɗin nan yace "Alright Grandma, muje" ya faɗa yana nuna mata hanƴa.
Gaba tayi yana binta a baya inda take ta sake jaddada masa yadda ta hango soyayyar Jalilah a idanun ZEEYAD, shi dai bai tanka mata ba har suka isa ɗakin da akayi admitting ɗinta.
Zaune suka samu ZEEYAD yana danne-danne a wayar sa, kan bed kuma Jalilah ce kwance jikin ta shafe da wani farin abu da alamu dai magani ne, inda kuma akayi mata ƙarin ruwa.
"Ha'a mai nake gani haka, kai da zaka ɗebe ta da hira ne kuma ka sanƴa wayar ka a gaba kana daddanawa, toh miye amfanin zaman ka anan ɗin dama?."
Ɗagowa yayi ya kalli Grandma, bai ce da ita komai ba sai ma sake sadda kansa da yayi yana cigaba da abinda yakeyi.
"Toh ai shikenan, tunda banza tayi magana ba."
Ɗagowa yayi yana kallon ta, kafin kuma ya kashe wayar yana tashi yayi inda take zaune yace "Sorry Grandma, ina ɗan wani aiki ne shiyasa."
"Toh koma dai menene dai kaji dashi, YAZEED ka sake kiran Marwa a waya mana kodai ba zata zo ta duba ya ƴar tata take bane?."
"She is not coming?" cewar Jalilah.
Kallon ta duk sukayi kafin Grandma tace "Toh maiyasa, a wane dalilin?."
"Sabida Abhi ba zai bar ta ba, a cewar sa yanzu babu ruwan sa dani tunda nice nayi sanadiyyar rufe Sooraj da akayi, bana tunanin zai bar ta tazo."
Duk kallon juna suka shiga yi, kafin YAZEED yace "Zan iya kiran mai Martaba na sanar dashi, maybe yayi masa magana ya bar ta tazo."
"A'a kyale su kawai tunda zuwa anjima ma zamu koma gidan" cewar Grandma.
Kallon YAZEED ZEEYAD yayi yace "Ya jikin budurwar taka?."
Ɗan hararar sa YAZEED yayi yace "Ba kaƙi zuwa ka duba ta ba, she is pretty fine....maybe" ya faɗa.
"Maybe?" cewar ZEEYAD ɗin.
"Yeah, you know she has a brain tumor or is it problem ne, so she have to fight for full recovery, and i can sense something huge na damunta deep down."
"Really, and ka tambaye ta koh menene shi?."
Shiru yayi yana kallon ZEEYAD kafin ya girgiza masa kai alamun a'a sannan yace "The girl is kinda cool, she is an introvert batason magana da kowa or maybe tayi sharing feeling ɗinta wa wasu, and i guess tun dah chan ma haka yanayin rayuwar ta yake."
Shiru kawai ZEEYAD yayi bai iya cewa komai ba, kafin yaji muryar YAZEED ɗin na sake faɗin "Anjima da kai zamuje mu duba ta, coz Grandma tayi mention ɗinka a wurin ta and yanzu idan bakaje ba, ba zata ji daɗi ba, right Grandma?."
"Ofcourse right, ai dolen sa ma yaje tunda bama wani nisa ne ke tsakanin nan da ɗakin nasu ba."
"Nima zanje, i want to see her too" cewar Jalilah da tayi shiru tunɗazu.
"Keda baki da lafiya, idan kika je musu haka ai sai yarinƴar ta ɗauka koh mutuwa ce tazo mata yadda kika sha farar abu a jiki haka" cewar Grandma.
Duk dariya sukayi harda Jalilah dake kwance babu lafiya ɗin, except ZEEYAD da yakejin zuciyar sa ta kasa yin resting tun jiya da ya tako ƙafar sa cikin asibitin, musamman yanzu da ya tsinci wasu bayanai game da abinda YAZEED ya faɗa masa akan yarinƴar da yakeso ɗin.
************************
__________Kallon Umma dake zaune tayi tace "Umma?."
Ɗagowa Umma tayi