Showing 105001 words to 108000 words out of 236327 words
a hannu, kafin kuma yace "You need to rest Abhi, come on i will take you to your room" ya faɗa yana rungumo kafaɗar mai Martaba ɗin.
Kallon Grandma yayi yace "Grandma i will take him to his room."
Kai kawai ta jinjina masa tana murmushi.
_"Why is Grandma so excited to see me back together with this Man?"_ ya faɗa a zuciyar sa.
Har ɗaki ya kai mai Martaba tare da zaunar dashi kan bed ɗinsa.
Ɗakin ya shiga ƙarewa kallo kafin kuma ya ta6e baki yace yana niyyar juyawa.
"Listen son" yaji mai Martaba ya faɗa.
Tsayawa yayi akan shi yana kallon sa.
"I want to discuss something important with you."
"No time for that Old Man, i have alot to cover."
Shiru mai Martaba yayi kafin kuma yace "OK, zan jira zuwa lokacin da bakada wani abin a gaban ka."
Tsayawa ZEEYAD yayi kallon sa kafin kuma yayi saurin yatsina face yana juyawa.
Idanun sa ne suka sauƙa kan hoton Ummien sa dake manne a bango hakan ne ya sanƴa shi ja ya tsaya yana kallo.
Ya ɗauki almost 10mins yana kallon hoton nata yayin da zuciyar sa ke bala'in yi masa zafi kafin kuma ya fice a fusace daga cikin ɗakin.
Da kallo mai Martaba ya bishi yana mai jin tausayin sa tare da yin nadamar dukkanin abinda ya aikata masa a baya.
Sauƙowa yayi izuwa lokacin kowa ya watse except Sadeeq da Grandma da suka rage.
Sauƙowar sa yasa Sadeeq saurin ƙarasawa wurin sa tare da faɗin "Hey" yana murmushi.
Murmushi ZEEYAD ma yayi kafin kuma su rungume juna cike da murna da kewar da sukayi.
Sun ɗan jima kafin su ɗago kowanne da murmushi kan fuskar sa.
Sadeeq ne yace "I thought ka daɗe da mutuwa."
Ɗan bugun sa ZEEYAD yayi a kafaɗu kafin yace "Why don't you think of something good."
Murmushi yayi yace "I thought ba zaka ta6a dawowa ba."
"Why not, i have a family, remember?."
Kai ya jinjina kafin kuma ZEEYAD yace "Tell me how is Abhi?."
"He is good, should we go and see him?."
Shiru ya ɗan yi kafin kuma yace "Yeah sure."
Kallon Grandma yayi kafin yace "Grandma, i will be right back."
Rungume sa tayi tace "Take care, Allah yayi maka albarka."
Amsawa yayi da "Aameen" kafin kuma ya ɗaura hannayen sa kan kafaɗun Sadeeq suna ficewa daga fadar.
Fitowa sukayi tare da jerowa tafe.
"So tell me, how you made it."
"It's a long story" ya faɗa cikin murmushi.
"Really, but tell me what were you doing at the Hospital?."
"Hospital?" ya faɗa a ɗan mamakin ce, DEENAH ce ta faɗo masa a rai take kuma mood ɗinsa ya fara sauyawa.
"Yeah i saw you, i mean kana da wani alaƙa ne tsakanin ka da matar nan da ƴar ta?."
Shiru yayi kafin kuma yace "No."
"Really, but why were you begging her akan kada ta raba ka da yarinƴar."
"Wait, how did you know all this?" ya faɗa tare da tsayawa da tafiyar yana kallon Sadeeq.
"I was standing right there, i mean am the Doctor that you talked to."
Ƙanƙance idanu yayi tare da faɗin "Really, you mean you became a doctor?."
"Yeah" cewar Sadeeq cikin murmushi.
"Wow, that is wonderful, Congratulations Bro" ya faɗa yana bashi runguma.
"Thank you, and you tell me wane irin aiki kakeyi?."
Kallon sa yayi kafin yace "Aikin sayar da mutane nake."
"What?" ya faɗa cikin zaro idanu waje.
"Yep" cewar ZEEYAD suna cigaba da tafiya.
"What, you kidding me bro?."
"No, why should i, na ta6a 6oye maka wani abu ne?."
"Serious bro?" ya faɗa tare da tsayawa yana ƙare masa kallo.
Murmushi ZEEYAD yayi yace "Just kidding you."
Murmushi shima yayi kafin su cigaba da tafiya, duk inda sukayi kuwa da kallo ake bin ZEEYAD da ya zame sabon halitta a gare su.
"But ZEEYAD honestly speaking mai Martaba yayi nadamar abinda ya faru da kai a kullum bashida magana wacce ta wuce taka, i was Surprised da yadda ya canza bayan tafiyar ka, do you know what he did?, yasa an garƙame dukkanin wadanda suka ta6a muzguna maka tare da yi musu horo mai tsanani har na tsawon shekaru uku, hatta Abdulhakeem da ya kasance ɗan uwansa sai da ya kore sa daga fada sannan ya kwace duk wata dukiya da kadara tasa dake hannun sa, sabida yana sane da abinda Sooraj yayi maka amma yayi shiru, babu wanda ya tsira a cikin mutanen da suka muzguna maka har sai da sarki ya sanƴa su ɗanɗana guɗar su, sai dai fah akwai aiki a gaban ka."
Kallon sa ZEEYAD dake saurarar sa tunɗazu yayi kafin ya jinjina masa kai yace "Yeah, Sooraj a kullum bayida wani buri wanda ya wuce ka dawo ya ɗauki fansar abinda akayi masa ta dalilin ka, sabida ya gaji da zama cikin talauci wanda yake ganin hakan ya faru ne duk ta dalilin 6acewar ka hakan yasa akayi musu wannan hukunci."
"Sooraj my foot" ya faɗa cikin tsukewar fuska ba tare da ya ɗauki maganar Sadeeq ɗin serious ba.
A haka suka ƙarasa gidan su Sadeeq,inda Abhi ba ƙaramin murna yayi da dawowar ZEEYAD ba, inda shima ya sake jaddada masa da irin halin da mai Martaba ya shiga bayan tafiyar sa, sai dai dukkanin abin nan da suke faɗa koh kaɗan babu wanda ya ta6a zuciyar ZEEYAD.
***********************
*1 MONTH AFTER*
________Sati uku kenan da dawowar Yarima ZEEYAD fada, duk da ba wani kula mai Martaba yake sosai ba sai dai hakan bai damu mai Martaba ba sabida yana samu yana ganin shi hakan ke sanƴa hankalin sa kwanciya.
ZEEYAD kullum a part ɗin Grandma ɗinsa yake wuni, sosai take nuna masa wata iriyar kulawa ta musamman wanda bai ta6a samun irin ta ba tunda yake.
Shiyasa a kullum baya rabuwa da maƙale mata sabida wurin ta kaɗai yake samun farin ciki da kwanciyar hankali, duk da kuwa babu abinda ya nema ya rasa a nashi part ɗin.
Sosai kuma ya maida hankalin sa karankatakaf kan business ɗinta, wanda shi kanshi yasan ba ƙaramin profit ya samu a ƴan kwanakin nan da ya maida hankalin sa ba.
YAZEED ma ya kan zuwa part ɗin Grandma time to time dan kawai su zauna yayi hira da ɗan uwan nasa.
YAZEED da ZEEYAD tamkar ƴan biyu haka suke dan kuwa koh da ganin su kayi sun jera suna tafiya ba zaka iya banbance wanne ne ZEEYAD koh YAZEED ba muddin ba wai ka kalli fuskar su bane ba.
Sosai MASARAUTAR ta koma ainihin ita sakamakon dawowar ZEEYAD, kasancewar mai Martaba baya rabuwa da fitowa cikin fada kullum suna tattaunawa akan matsalolin yau da kullum yasa komai ke tafiya smoothly a cikin MASARAUTAR.
ZEEYAD baya kula kowa haka kuma baya shiga harkar kowa, daga shi sai Grandma ɗinsa da YAZEED ne kaɗai suke zama suyi hira.
Sarauniya Hafeezah kullum neman hanƴar raba ZEEYAD da YAZEED take sai dai hakan yaci tura, hakan ne kuma ya sanƴa ta canza wani sabon boka dan a cewar ta wancan babu abinda ya iya.
Sarauniya Naseeba kuwa kullum zuciyar ta soyayyar ZEEYAD ce ke ƙaruwa mata a ciki, ji take zata iya rasa rayuwar ta muddin bata mallake shi ta gusar da ƙishin ruwan da takeji akan sa ba, dan kuwa gayen yayi mugun haɗuwa.
Sarauniya Nazeerah kuwa ita dama ƴar a bi Yarima asha kiɗa ce, babban burin ta bai wuce kullum taga ana hayaniya da cece kuce ba, wannan shi ne tata damuwar.
Abdulhakeem da iyalan sa kuwa tuni sarki ya maido dasu cikin fada bayan Abdulhakeem yayi rantsuwar ba zai sake aikata abinda yayi ba.
Mugunta dama kuma baƙin halin Sooraj bai ragu ba sai ma abinda yayi gaba, sabida kullum burin sa shine rigima ta shiga tsakanin sa da ZEEYAD, ya tsani ZEEYAD fiye da komai, musamman yadda yaga how wealthy and successful he become, hakan na mugun ƙona masa rai bama shi kaɗai ba hatta Sarauniya Hafeezah dama kuma sauran dangi. *(Duk zasu bayyano nan gaba)*
Grandma kullum cikin farin cikin ganin ɗan jikan nata take, batason yin nesa dashi koh kaɗan.
6angaren su Jafar kuwa ba ƙaramin baƙin cikin raba ZEEYAD da DEENAH da Umma tayi yaji ba.
Yasan DEENAH ba zata ta6a samun masoyin gaske kamar ZEEYAD ba, he loves her wholeheartedly sai dai Umma ta watsa masa ƙasa a idanu, and now yasan ZEEYAD yayi wa DEENAH nisan gaske dan kuwa koh shi yanzu ba sosai suke magana a waya ba, sosai yakejin baƙin ciki da haushin abinda Umma ta aikata.
Yau ma kamar kullum, zaune suke a ƙatuwar falon Grandma, gaban su kuwa kayan fruits ne kala daban-daban jibge akan tray suna sha.
Kallon su Grandma tayi tace "Kuna ji na ku gama ku tashi dawuri haka nan, mai Martaba na jiran ku a fada kun dai san yau zaiyi manƴan baƙi sannan yakamata ace dukkanin ku biyu kuna wurin."
Yatsina face ZEEYAD yayi yana tsuke fuska yace "Am not going YAZEED yaje shi."
Kallon sa YAZEED yayi shima yace "Am also not going, duk wadannan baƙin ba zuwan Allah da annabi suke ba, they just wants to find a suitor for their daughters."
"Toh miye a ciki ai wannan abin farin ciki ne ma..."
"Grandma, menene abin farin ciki anan ɗin?, haka kurum aje ayi ta tallata mu yawa wadanda sukayi kwantai, nidai nafi ƙarfin a haɗa ni aure da wata wallahi" cewar YAZEED.
Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "You're right bro, kafi ƙarfin a tallata ka, i mean look at you what if aka haɗa ka da wacce batayi maka ba fah."
"Toh uban zigi, idan ka gama sai ka tashi kuje koh."
"Grandma please..."
"Ba wani zancen please, ya zama dole ne ku tafi idan ba haka ba kuma ku haɗu da 6acin raina yanzun nan."
"Alright, alright zamuje."
"Da yafi muku kam."
Nan dai suka cigaba da hirar su inda sai da Grandma ta sake yin dagaske kafin su tashi su wuce fada.
***********************
_______Yau ma kamar kullum da sassafe ya fice jogging da motsa jiki.
Sosai ya haɗe cikin gym wears ɗin nasa wadanda suka yi matuƙar amsar sa haɗi da bayyanar da murɗaɗɗiyar jikin sa da muscles ɗinsa kasancewar kullum baya rabuwa da yin Exercise ɗin da zasu ƙara masa ƙarfi da ƙarfin jiki.
Kwance yake akan ƴar ƙaramar carpet ɗin sa da ya saba fita da ita yayi matashi da hannayen sa inda yayi crossing legs nasa idanun sa a lumshe.
"Hey bro" ya faɗa yana zama gefen shi.
Buɗe idanun sa yayi yana kallon YAZEED kafin kuma ya tashi zaune yana kallon sa.
"What?" cewar YAZEED.
"Nothing kawai ina mamaki ne wai kaine ka fito motsa jiki yau."
Ɗan dariya yayi kafin yace "Who told you cewa da ɗin bana yi it's just that ba kullum nakeyi kamar kai ba."
Ɗan murmusawa yayi kawai ba tare da yace komai ba.
Kallon sa YAZEED yayi yace "You know what?."
"No" ya faɗa.
"Am Inlove."
Juyowa yayi ya kallesa kafin kuma ya ɗanyi murmushi mai sauti yace "You what?."
"You heard me right, don't you?."
Ɗan ta6e baki yayi yace "Love is just a waste of time" ya faɗa cikin karyewar zuciya.
Dariya YAZEED yayi yace "Waste of time, you really take love as a time waste, well actually ni ba haka na ɗauke shi ba, besides tell me ka ta6a yin soyayya ne da kake cewa haka?."
Ɗan murmusawa yayi tare da yin shiru bai ce komai ba.
"Well actually i guess love is a beautiful thing, don't you think so?."
Shiru ZEEYAD yayi kafin kuma yace "Well i don't know, i have never been inlove."
"Really?, lallai ka bar daɗi."
"Kana nufin kai ka ta6a soyayya ne?."
Dariya yayi yace "Yeah, with wata yarinƴa a chan cyprus, but i dumped her."
"What, you did?" cewar ZEEYAD cikin mamaki yana kallon sa.
"Yeah actually, the girl is non-muslim and you know a MASARAUTA ba zasu ta6a yarda da auren non muslim ba, thats why i dumped her don't get me wrong, i didn't broke her heart."
"Kana nufin kace bataji ciwon rabuwa da kai ba?."
"She understands me bro."
Kallon sa yayi kafin kuma ya ɗan murmusa yana yin shiru.
"So, zaka raka ni hira anjima?."
"No, am not going."
"Oh come on please."
"I said no" ya faɗa yana tashi tsaye.
"Alright then, i won't force you, where are u heading to now?."
"Grandma."
"OK see you then."
Kai ya jinjina masa kafin ya tattari carpet ɗinsa yayi gaba...............
*Yawan Comment, Yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[7/29, 8:08 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*032...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Alhamdulillah, Allah yayi mun dawo, Nagode sosai
*ZEEYAD FANS CLUB* haƙiƙa da bazar ku nake taka rawa, Nagode Sosai masu kira, masu message dukkanin ku ina godiya har ma da ƴan likimo duka, da addu'ar da kukayi tayi min kuna sake nuna kulawar ku akan ƙanina, Alhamdulillah ya samu lafiya kuma mun dawo gida zamu cigaba daga inda muka tsaya, Haƙiƙa ina matuƙar Ƙaunar ku fisabilillah❤️🥰
*_NOT EDITED_*
_________Tafe yake riƙe da ƴar ƙaramar rug ɗinsa a hannu, tun daga nesa ya hango Sooraj tafe hakan yasa shi sake tamƙe fuskar sa sosai kasancewar bayason raini koh wani abin da zai shiga tsakanin sa da Sooraj ɗin.
Sooraj ma tundaga nesa ya hango ZEEYAD tafe dan haka murmushin gefen baki ya sake yana shafa gemun fuskar sa.
Zuwa sukayi zasu wuce juna kafin kuma Sooraj yayi saurin sanƴa hannu yana dafe ƙirjin ZEEYAD cikin tsayar dashi.
Da kallo ZEEYAD yabi hannun sa dashi izuwa kan fuskar sa, koh kaɗan baiyi mamaki ba sabida kaɗan daga cikin halin Sooraj kenan, tun yana ƙaramin sa he is a bully bale kuma da ya taso da halin babu mai iya kwa6ar sa.
"Seems like you're avoiding me, loser" cewar Sooraj ɗin cike da muguwar baƙin hali irin nasa.
Cize baki ZEEYAD yayi tare da karkaɗa kai ba tare da yace dashi komai ba.
"You got something to say?" ya sake faɗa.
"Why don't you just mind your own fucking business with me Sooraj?."
Cikin hura hanci Sooraj yace "Mind my business hahaha, ai yanzu na fara shiga gonar ka ƙasƙan..."
Kallon da ZEEYAD ya ɗago yana yi masa ne ya sanƴa shi haɗiye saurar maganar kafin kuma cikin borin kunƴa yace "Miye kake yimin irin kallon nan, koh kana tunanin zanji tsoron ka ne iyeh?."
Cikin clicking tongue ZEEYAD ya yatsine fuska yana kan yace "Idan kaji tsoro na ma wannan damuwar ka, just know one thing for sure that ba wannan old ZEEYAD ɗin da ka sani bane a gaban ka yanzu, just don't try to mess up with me, uhm?" ya faɗa yana kallon Sooraj ɗin da kamar ya tashi sama sabida haushi.
"Har kai wanene da zaka ce zaka tsare ni da maganganu...?."
"Oh come on, i told you not to try to messed up with me didn't i?."
"Mai zaka iya yi?" ya faɗa cikin aika masa da mugun kallo.
Kallon sa ZEEYAD keyi kafin kuma cikin ɗagun murya yace "Guards!."
Duk fitowa sukayi daga spot ɗin da kowanne ke tsaye suna iyowa wurin da ZEEYAD da Sooraj ke tsaya, cikin girmamawa da duƙar da kai suka ce "Yes the great Prince."
Ba tare da ya kalle su ba yace "Lock him up in the dark room for 3hours."
"Yes Prince" suka amsa cikin girmamawa suna iyowa kan Sooraj da niyyar kama shi, tsawar da ya daka musu ne ya sanƴa su dakatawa duk suna kallon sa kafin ya kalli ZEEYAD cikin hura hanci da huci yace "Ni zaka wulaƙanta, how dare you?."
Ɗan ta6e baki ZEEYAD yayi yace "I warned you, didn't i?."
"I will make sure kayi nadamar abinnan da kayi" ya faɗa yana nuna ZEEYAD ɗin da yatsa.
"Take him away" ya faɗa.
Duk iyowa kansa sukayi tare da kama shi sukayi gaba dashi kamar yadda ZEEYAD yace musu.
Muguwar kallo mai cike da ma'anoni iri-iri kawai yake aikawa ZEEYAD yanajin zuciyar sa kamar ta tarwatse tsabar ƙunar da takeyi masa.
Barin wurin ZEEYAD yana kimtsa iriyar rayuwar da zai bi kowanne daga cikin fadar tasu dashi, ba zai ta6a samun salama ba har sai yaga kowannen su ya ɗanɗana ƙuɗar sa fiye da yadda sukayi masa, one after the other zaiyi maganin su.
Da wannan tunanin ya isa ga part ɗinshi da tafi na kowane ɗa a cikin masarautar girma da haɗuwa.
Da kallo yabi bayi matan dake ta aikace suna kai komo dashi, kafin kuma cikin 6acin rai yace "I want to be alone."
Sum-sum kowacce ta fice da kayan aikacen ta yana sake tsuke fuska ya haura sama, sam baiga dalilin da zai sanƴa ana barin masa bayi mata sukayi masa aiki ba, hatta ruwan wanka da kanshi wankan ma wai masu yi masa daban aka ware tsabar ance musu shi ɗin shege ne, sai da ya yiwa abin tufkar hanci kafin su daina shigo masa ɗaki, iyakan su cikin falo da sauran ɗakunan dake cikin part ɗin ba dai su taka zuwa ɗakin kwanan shi ba.
Ɗakin motsa jikin sa ya nufa wanda ke ƙawace da ababen Exercise kala daban-daban na bada ƙarfi.
Ƴar ƙaramar rug ɗin hannun sa ya ajiye kan couch, kafin ya nufi ɗaya daga cikin *DECLINE BENCH PRESS* ɗin dake jere cikin instrument ɗin motsa jikin ya kwanta, kafin kuma ya ɗaga ƙarfen ya fara aiki da ita cikin kwarewa.
Ya kai almost 30mins yana yi inda Knocking ɗin da