Showing 42001 words to 45000 words out of 236327 words
a great outing" ta faɗa tana rungume shi, da sauri ya janƴe ta daga jikin shi kafin ya wuce ya haura sama.
Da kallo ta bishi kafin tayi blowing masa kiss tana murmushi...........
**********
...........Zaune yake a katafariyar offishin nasa yana rubuce-rubuce a jikin wasu papers.
Turo ƙofar akayi kawai aka shigo kafin ya sami wuri ya zauna fuskar sa ɗauke da murmushi yana kallon ZEEDAN.
"Good Morning Sir" ya faɗa.
"Morning Mansoor, ka tashi lafiya?."
"Alhamdulillah Sir."
Sai a sannan ya ɗago ya kalle shi yace "Naji labarin ance zakayi aure, Congratulations."
Cike da farin ciki ya amsa da "Thank you sir, ai yanzu ma Invitation Card ɗina na kawo maka, nan da 2weeks ne auren, shine nakeso dan Allah kayi attending sir" ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa masa Card ɗin.
Amsa yayi ya shiga karantawa nan ya ɗago yace "You're my MANAGER, so ba sai ka roƙe ni zuwa auren ka ba, i will surely attend it, although last week na dawo daga Sokoto, but don't mind Okay?."
"Nagode sosai sir, Allah ya ƙara buɗi."
"Aameen" ya amsa.
"And sir idan ba zaka damu ba ranar ɗaurin auren akwai Dinner party da dare, i hope ba zaka ƙi amsa gayyatar zuwa ba."
Murmushi yayi kafin yace "Kaima kasan ban cika attending Party ba, but i will surely attend tunda ka buƙaci hakan."
"Thank you so much sir, Nagode sosai da amsa gayyata."
"You're welcome, Saura one month mu fara ɗaukar sabbin workers, hope you're working on that?."
"Yes sir, ai mun rigada mun kusa kammala komai ma."
"Alright, idan ka fita ka turomin Secretary."
"Yes sir, thank you sir" ya faɗa yana ficewa daga office ɗin.
Ba'a jima ba Secretary ya shigo tare da gaida shi cike da girmamawa, nan ya buƙaci a kawo masa breakfast kafin ya amsa da toh yana ficewa.
10mins mai kyau bai ɗauka ba ya dawo hannun sa ɗauke da ɗan madaidaicin tray da breakfast akai.
Wuraren couch ɗin da aka ware a gefe kamar falo a cikin office ɗin ya nufa ya ajiye akan Table kafin ya fice.
Kammala abubuwan da yake yi yayi kafin ya taso yazo ya zauna tare da haɗa Black tea ya sha, sannan ya buɗe plate ɗin abincin tare da yin basmala ya hau ci.
Tunanin ta ne ya faɗo masa kwakwalwa lokacin da take kawo masa lunch box ɗinta a matsayin breakfast ɗinsa yaƙi ci, kafin kuma yayi saurin kauda wannan tunanin yana tuno da sharrin da tayi masa.
Rufe plate ɗin yayi ya koma kan chair ɗinsa tare da danna wani abu kamar Alarm.
Ba'a jima ba Secretary ya shigo nan ya umurce sa da ya kwashe breakfast ɗin, ba tare da musu ba yaje ya ɗau tray ɗin ya fice yana mamakin mai ya 6atawa Uban gidan nasa rai da sassafen nan ganin 6acin rai ɗauke a fuskar sa............
***************
..........."2Weeks to bikin Ruqayyah kuma har yanzu bamuyi anko ba Wayyo ni Khadija" ta faɗa kamar wacce zata yi kuka.
"Kema Anty Khadija in banda abinki fisabillah ga Abba nan kije mana ki kar6a a wurin sa kin zo kina ta tada hankalin ki kawai."
"Hmm ba zaki gane bane Amirah, kin manta last 2Weeks akayi bikin wata ƙawar mu kuma na kar6i kuɗin fitar biki almost 70k, yanzu kuma ki sake cewa na koma na kar6o wani kuɗin a wurin sa dan kawai banida tausayi?."
"Toh ai yana dashi dah kamar bashida shi ne zakiyi shakkar zuwa ki tambaye sa, amma dama dan su waye yake neman kuɗin ba dan mu bane, sabida kar muga wani abin a wani wuri muji muna so kuma ace ya kasa yi mana shi, balle kuma shi da bakin sa yace duk wacce take da buƙata ta faɗa masa zai biya mata indai bai fi ƙarfin sa ba, toh miye a ciki dan kinje kin tambaye sa kuɗin anko?."
"Toh please kije min dan Allah kice ankon ƙawarki ne ki samo min kuɗin,kinji ƴar ƙanwata?."
"Cha6 Allah ba zani ba, ba kece kike da buƙata ba dan haka kije ki wallahi."
"Haba Masoyiya ta..."
"Nikam wallahi ba zakiyi min daɗi baki ba, dan babu inda zani."
Sai a sannan ta ɗago ta kallesu daga karatun da takeyi, sabida sun cika ta da surutu.
Tashi tayi kawai ta fice daga ɗakin inda suka bita da kallo kafin Khadija tace "Nikam ina mamakin halin DEENAH."
"Nima dai haka, koh meke damunta, na tambayi Yaya Jafar yace wai haka nature ɗinta yake."
"But she looks disturbed from the inside."
"Maybe she was heartbroken."
"Heartbroken?, no it can't be that, ban fah ta6a ganin ta da Saurayi ba, maybe gaskiya Jafar ya faɗa haka take Naturally."
"Kinsan maiyasa na faɗi haka, coz i caught her crying last night na tambaye ta tace min babu komai and she left, bakya tunanin maybe saurayi ne ya yaudare ta."
"Really?, but wane asararre ne zaiyi dumping DEENAH?, she is beautiful and gorgeous , and so calm also ta haɗu ne ta koh ina, she is classy and total definition of a wife material, she doesn't deserved it."
"And she is kind also, ita dai matsalar ta shine she is always moody and sannan batason yawan shiga mutane da surutu, she feels safe and comfortable when she is alone, i guess."
"Inaso muje bikin Ruqayyah da ita, kina tunanin zata yarda ta bi ni muje?."
"Cha6, bikin friends nata ma yaushe taje, bale kuma azo ga na wata Ruƙayyah, but maybe you should try asking her koh zata yarda."
"Idan ma bata yarda ba, zan sa Mami koh Anty suyi forcing nata."
"Why zakiyi forcing nata?, inaga dai idan tace ba zata je ba, you shouldn't have to force her."
"Allah ya kaimu kawai, bari dai naje wurin Abba haka nan, ace bikin best friend ɗinka bakayi komai ba ai da matuƙar kunƴa ban isa ba" ta faɗa tare da ɗaukar Hijab ɗinta ta fice daga ɗakin..........
******************
.........Kwance take tayi matashi cinƴar wata mata mai kama da Umma sak sai dai Umma ta fita farin fata.
DEENAH ce tace "Mami maiyasa har yanzu zuciya ta ta kasa samun sukuni tun ranar da abin nan ya faru?, ina tsoron kada na mutu ba tare da na nemi yafiyar sa ba, Mami yace ba zai ta6a yafemin ba kuma ya tsane ni, shekara goma fah kenan amma har yau ban sake ganin sa ba, what if yayi nisa dani ba zan sake ganin sa ba har abada" ta faɗa tana tashi zaune hawaye na biyo mata fuska.
Cike da tausayin ta Mami ta shiga share mata hawayen tace "MADEENAH a lokacin da abin nan ya faru kina ƴar ƙaramar ki ne, baikamata ace har yanzu abin nan na damunki kin kasa mantawa dashi ba, you have to let go of all your sorrows and move on with your life, you have to live happy koh da na rana ɗaya ne, stop disturbing your Peace kina ɗaurawa kanki damuwar da bakisan ranar yankewar ta ba, am definitely sure shi ya ma mance da abinda ya faru kuma ya manta dake, but i can't believe ke har yanzu abin nan na ranki."
"Mami ya manta ni fah kika ce?."
"MADEENAH, zai iya yiwuwa mana, shekaru goma fah ba wasa bane, abubuwa dayawa su kan iya faruwa cikin shekaru goma wanda Allah ne kaɗai yasan dasu, but inaso ki sa a ranki cewar koh ba daɗe koh ba jima indai har Allah yace kina da rabon sake ganin sa toh tabbas zaki ganshi, sai dai fah zakiyi haƙuri ne kawai da wannan jarabawa, gashi kuma koh sunan sa fah baki sani ba, amma kin sa shi a ranki har yau kin kasa cire shi, you've to move on MADEENAH."
"Mami i can't, i can't move on happily indai har ban sake ganin sa ba, how do you expect me to be happy bayan akwai haƙƙin wani a kaina, indai har bai yafemin ba then i would never be happy har ƙarshen rayuwa ta."
Share mata hawaye Mami tayi tana rungumo ta jikin ta tana rarrashi...............
*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*015...*
............Khadija ce zaune a gaban mirror sai tsarawa kanta kwalliya take, kasancewar ta make-up artist, sosai tayi kyau kasancewar dama kyakkyawar ce ita.
Kallon DEENAH da ta fito daga wanka tayi tace "Sai yanzu kike fitowa daga wankan?, zaki sani latti wallahi."
Zama DEENAH tayi kafin tace "Anty Khadija ni nace miki ba zanje ba kije abin ki dan Allah."
"Haba rabin zuciya ta, ya zakiyi min haka fisabilillah?, ni shigar da kikayi wanka ma i thought koh zakije ne, na tsaya zaman jirar ki."
Shiru DEENAH tayi bata kula ta ba sai ma lotion ɗin da ta ɗauka gaban mirror ta shiga shafawa, nan Khadija ta sake faɗin "Naji yau ba zakije kamu ba, amma ai gobe zamuje ɗaurin auren koh?."
Kallon ta tayi kafin tace "Dan Allah Anty Khadija ki bar ni" ta faɗa kamar zatayi kuka.
Shiru Khadija tayi ta cigaba da ɗaurawa kanta ɗan kwali, nan ya zauna tayi kyau sosai sannan tace "Wallahi Aliyu ba zai kalli kwalliyar nan a banza ba tunda ba shi ya bani kuɗin sayen kaya da kayan kwalliya ba har sai ya biya."
Murmushi DEENAH tayi kawai, kafin ta nufi wardrobe ta ɗauko kayan sawar ta ta rufe.
Tashi Anty Khadija tayi tare da ɗaukar gyalen ta ta yafa da jakar ta tace "Toh ni na tafi, sai na dawo."
"A dawo lafiya" DEENAH ta faɗa.
Sanƴa kayan ta tayi wanda yayi mata kyau sosai kasancewar straight gown ne English wear yasa shi ɗan kama jikin ta inda ya fito mata da shape ɗin hips ɗinta wanda yayi daidai da yanayin jikin ta, dan kuwa batada ƙiba kuma ba siririya bace har chan.
Wani drawer ta buɗe ta ciro English novel, kafin ta haura kan bed ta zauna tare da buɗe sa.
Sarƙar ta gani a cikin Book ɗin sai sheƙi yakeyi.
Ɗauka tayi tana ƙare masa kallo, kafin ta buɗe abin dake jikin sarƙar hoton kyakkyawar matar ya bayyana.
_"She must be his Mom, i have ruined his entire Happiness, nayi masa sharri sannan kuma na raba sa da abu mafi muhimmanci a gareshi, i know he would never forgive me for hurting him, he trusted me but i fucked off"_ ta faɗa a zuciyar ta tana manna sarƙar a ƙirjin ta.
"Hey, what's that?" cewar Amirah tana hawowa kan bed ɗin kusada DEENAH.
Hawaye fuskar ta ta lakuto tace "You're crying again, what on earth is wrong with you?" ta faɗa cike da damuwa.
DEENAH goge hawayen da batasan sun zubo mata ba tayi kafin tace "I..i bansan sadda hawayen suka zubomin ba, am not crying."
"Uhm i can see that, please sis tell me, meke damunki you always looked disturbed."
Rufe takardar tayi tace "Nothing, am fine."
"What is that Necklace?" ta faɗa tana kallon sarƙar dake hannun DEENAH.
"It's nothing" ta faɗa tana damƙewa a hannun ta kafin ta tashi ta nufi wardrobe ta buɗe tare da ɗaukar wata ƴar ƙaramar jaka ta sanƴa shi a ciki.
"You're hiding something from me."
"Amirah babu abinda nake 6oye miki, i have nothing to hide OK, so just let me be please" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.
Kitchen tayi ta sha Kuka sosai kamar ranta zai fita kafin kuma ta fito ta koma ɗakin.
Akwatin ta ta sauƙar ta fara shirin haɗa kayayyakin ta a ciki.
"Wait, what are you doing?."
"Am leaving, dama ai sati biyu Umma tace nayi na dawo."
"What, are you kidding me?, you can't go anywhere, wallahi zan kira miki Mami."
Tsayawa tayi da haɗa kayayyakin nata kafin kuma ta fashe da kuka tana zama bakin bed ɗin.
Sosai hankalin Amirah ya tashi nan ta nufe ta tare da tambayar ta abinda ya same ta.
Ganin taƙi kulata ne yasa ta fita taje ta kirawo Mami.
Rarrashin duniyar nan Mami tayi wa DEENAH amma kamar sake zugata take ta cigaba da kukan.
"Mami i hate myself, dan Allah Mami ku nemo min shi duk inda ya shiga, mutuwa zanyi idan ban sake ganin sa na bashi haƙuri ba, dan Allah Mami ku taimaka min kada na mutu Allah ya hukunta ni" ta faɗa cikin shesheƙa kamar zata shiɗe.
Haƙuri kawai Mami ke bata cike da tausayin ta.
"Mami rayuwa ta baya yimin daɗi, banajin daɗin rayuwa a haka Mami, dan Allah ku bar ni naje na nemo shi idan ku ba zakuje ba, am so bored Mami komai ya daina yimin daɗi, na gaji da zama cikin damuwa da ƙunci kullum, nayi dukkanin ƙoƙari na ganin na kasance cikin farin ciki koh da na awa ɗaya ne amma na kasa, dan Allah Mami ki faɗamin maiyasa hakan ya faru dani?" ta faɗa tana kamo hannun Mami ɗin.
Rarrashin ta Mami tayi sosai tare da yi mata wa'azi kafin ta samu DEENAH tayi shiru.
Amirah kuwa duk hankalin ta ya tashi kuma kanta ya ɗaure dan batasan abinda ke faruwa ba.
A haka ta raya wunin wannan ranar cikin ƙunci da rashin walwala kamar kullum............
***********************
...........Agogon hannun sa yake dubawa time to time yana kaɗa ƙafafu.
Ba'a jima ba ta shigo ɗauke da wata ƴar ƙaramar akwati tana jan shi.
Ƙarasowa tayi tana murmushi sakamakon kallon da yake binta dashi nan tace "Am so sorry babe, i kept you waiting bayan nasan tafiya zakayi" ta faɗa tana zama cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin falon.
"Are you travelling somewhere?" ya tambaya cike da mamaki yana kallon akwatin nata.
Kallon akwatin tayi tace "Oh Yeah, ba tare zamu ba?, i can keep you accompany all day long sabida kaɗaici."
"Are you kidding me?."
"What do you mean?" ta faɗa cikin ɗan dariya.
"Do you think this is funny?, am not going anywhere with you."
"Oh come on calm down, ba bin ka zanyi ba, nima biki zani Sokoto shiyasa na biyo ta wurin ka muje tare since kai ma nan zaka."
"No ba zaki bini ba, i don't hang around with indecent girls like you" ya faɗa cikin ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kana tsuke fuska.
"What, what do you mean, are you trying to insult me?."
"Look Surayya, sai dai ki bi wani ku tafi amma ba ni ba, a hakan kike tunanin zan aure ki?, you're not decent at all, just take a look at yourself and the way you dress...."
"Enough of this ZEEDAN" ta faɗa a ƙufule tana miƙewa tsaye kafin kuma ta ɗaura da faɗin "Ai ba sai ka ci min mutunci ba, ai dama na daɗe da gano sam ba so na kake ba..."
"Then kuma sabida kwakwalwar kifi ne dake kika kasa rabuwa dani tuntuni bayan kin daɗe da sanin hakan?, don't you dare raise your voice at me, i respect you sabida ke macece, i guess lokaci yayi da zakije kiyi aure ki daina 6atawa kanki lokaci a kaina, ni dake sam bamu dace ba, hali na da naki sun sha bambam infact koh kaɗan bakida tsarin irin macen da nake burin rayuwa da ita, your life is totally disgusting."
"What, you can't do this to me ."
"And why shouldn't i?, kece kika kawo kanki da kanki gareni ba ni na shigo dake cikin rayuwa ta ba, you proposed to me and i couldn't deny or disappoint you infront of your friends, da farko i thought you would be good for me but then i realized that i made a great mistake for allowing you into my life."
"Kana nufin ka daina sona kenan?" ta faɗa kamar zatayi kuka tana matsowa kusada shi.
"I never loved you, banta6a sonki ba sannan kuma ba zan ta6a son naki ba" ya ƙarashe cikin ɗaure fuska yana kallon ta.
"And you keep Playing me all this while?."
"That is because ke kika takura min, koh kin manta ne kece kika ce kina sona ba ni ba?."
"Amma maiyasa kaƙi sanar dani hakan tuntuni sai yanzu, idan halaye na ne baka so, i promise to change for good just please don't leave me i beg you."
"Yanzu na faɗa miki, it's not late though we've been together for 5months and banga amfanin ki cikin rayuwa ta ba, i only keep valuable things in my life not people like you."
Kuka ta fashe dashi, nan ya fice ya bar ta nan tsaye, sai da tayi mai isar ta kafin ta tsagaita tace "Why is he ignoring me all of a sudden, kodai yayi wata sabuwar budurwar ne?, he can't do this to me."
"Ma'am yallabai yace idan kin gama ki fice zamu rufe ƙofar" cewar wani bodyguard ta bayan ta fuskar nan tasa a murtuƙe.
Jan akwatin ta tayi cike da haushi ta fice tana faɗin "Sai muga ta yadda zai fitar dani daga rayuwar tasa ai."..........
***********************
...........Yau Saturday sannan kuma yau ne ɗaurin auren ƙawar Anty Khadija, sai shirye-shirye suke ita da ƙawayen ta da suka zo dan tayi musu kwalliya.
Ɗaya ce tace "Please Khadija ki gwangwaje ni a party ɗinnan nafi kowa kyau, i can't believe wai that Famous rich and Handsome artist will be there."
"Ke kam dai Aisha kinji kunƴa da shegen son samari wallahi mtssww" cewar ɗaya daga cikin ƙawayen.
Ɗaya ce tace "Ke kinga laifin ta ne, kika san wani ikon Allah idan ya ganta yace yana so, ai koh nima wallahi gwangwaje ni za'a yi shiyasa ma musamman naje aka sake yimin wani ɗinkin kece raini ɗin."
"Toh gaskiya dai kunji jiki wallahi, wannan guy ɗin ma mai zaiyi daku?, wallahi koh kaɗan ku ba ajin sa bane kuna tafiya kamar iska ya ɗebe ku ɗin, musamman ma da naji shegen girman kan tsiya garesa."
"Wallahi dai kema kya faɗa musu, naji ance balarabe ne fah koh?" cewar Anty Khadija.
"Aa nikuma kamar ji nayi ance ɗan Nigeria ne, sai dai koh half-cast ne shi."
"Kai anƴa?, toh dai ba zanyi musu ba tunda ba ganin sa mukayi zahiri ba, but the guy is damn hot and Handsome wallahi, i can't wait to set my eyes on him, messages ɗina sun fi dubu a dm ɗinsa na Instagram but he isn't replying koh buɗewa baya yi" cewar ta farkon cike da damuwa.
Dariya duk sauran suka kwashe dashi nan ɗaya tace "Wallahi Aisha kinji jiki, yoh angayamiki ma shine tukun, yanzu idan kika bibiya kawai Boys ɗinsa ne masu using da account ɗin ba shi ba, amma kenan tsabar aiki bai ishe ki ba kullum bakya gajiya da commenting akan posts ɗinsa kamar wata mayya."
"Wallahi kuwa shi ina ma yaga time ɗin tsayawa su posting da chatting, ke nan kinzo kina ta hauka, Allah ya shirye ki" cewar Anty Khadija cikin dariya.
"Allah sarki matar sa kam ta more