Showing 141001 words to 144000 words out of 236327 words

Chapter 48 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45322

ta kalle ta kafin tace "Inaso zan fita waje...shan iska."

"But DEENAH..."

"Yanzu ma hana ni zakiyi right?, i know ba zaki barni ba, sabida kin daina yimin duk wani abu da nakeso yanzu."

"A'a DEENAH ba hana ki zanyi ba, ki bari ki jira ƙawayen naki kinga idan sunzo sai su kai ki koh?."

"No i don't want them, nikaɗai nakeson fita ba da kowa ba."

Shiru Umma tayi bata ce komai ba tana kallon DEENAH ɗin fuskar ta fal damuwa.

"Are you worried koh wani abu zai same ni right?, i will be fine and i will take care of myself."

Kai Umma ta jinjina mata nan tace "just kada ki daɗe please kinga dare ya kusa da zaran kinji an fara shirin kiran sallah ki dawo, sannan ki faɗamin inda zakije ɗin."

"Wurin da muka saba fita motsa ƙafa zani, wurin yafi daɗin zama da sha'ani."

"Alright, be careful, Okay?."

Bata ce da ita komai ba ta sauƙo daga kan bed ɗin tana maƙala mickey sleepers ɗinta a ƙafa kafin ta bar ɗakin inda Umma ta bita da kallo.

A hankali take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.

Sadeeq taga ya fito daga wani ɗaki, murmushi yayi da ganin ta da yayi nan yace "Patient, what are you doing out here?."

"I...inason fita shan iska ne."

"Wow how great, see you later then" ya faɗa yana ƙoƙarin wucewa.

"Listen?" ta faɗa.

Tsayawa yayi yana kallon ta yace "Yes?."

"Ɗazu YAZEED and his Grandma came to check on how i was doing, sun ce suna da patient anan suma, zaka iya nuna min ɗakin da suke?."

"Oh yeah sure, Cousin sis ɗinsu ce ba lafiya, anjima kaɗan ma za'a yi discharge nasu, idan kika bi straight haka zaki ga hanƴar da yayi left and right, take the left hand side, ɗaki na 78 anan suke, sorry ba zan iya raka ki ba i have alot to cover" ya ƙarashe cikin murmushi.

"It's Okay, Thank you" ta faɗa.

"You're welcome" ya faɗa yana wucewa.

Kamar yadda yayi mata kwatance hakan tabi nan kuwa ta tsinci kanta bakin ɗakin.

Ƙarasawa tayi kafin ta shiga knocking door ɗin, zuciyar ta na harbawa.

"Wa'alaikumusalam, ƙofar dai a buɗe take" cewar Grandma.

Hannu tasa tare da murɗa handle ɗin ƙofar tana tura ƙofar ta shige bakin ta ɗauke da sallama.

Ɗagowa Grandma tayi tana sauƙe idanun ta kan DEENAH da ta shigo tana ra6ewa jikin ƙofar kamar mai tsoro.

"DEENAH?" cewar Grandma tana kallon ta

Murmushin kan le6e DEENAH tayi tana kallon Grandma ɗin.

"Come on ƙaraso mana" cewar Grandma tana kallon ta cikin murmushi.

Ƙarasawa tayi tana zama kusada Grandma ɗin.

"Ya kike, and how is your health?."

"Alhamdulillah" ta faɗa.

"Masha Allah, Ummien taki bata dawo ba har yanzu?."

"Ta dawo, niɗin na fito shan iska ne, shine nace bari nazo na duba marar lafiya" ta faɗa kanta a ƙasa.

Murmushi Grandma tayi cike da farin ciki tace "Masha Allah how kind of you, ai sun fita tare da Boy wai suje ya saya mata kayan maƙulashe, kinsan abin ka da masoya yanzun nan zasu dawo."

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Kallon ta Grandma tayi kafin tace "DEENAH dear, tell me mai kikeji game da jika na YAZEED?."

Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon ta, kafin kuma tayi saurin sadda kai ƙasa zuciyar ta na racing.

"Ki kwantar da hankalin ki, i know kunƴa ta kikeji, but daga gani kema nasan kin kyasa da ɗan kyakkyawan jikan nawa" faɗin Grandma cikin murmushi.

Ita dai DEENAH kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalli Grandma balle ta maida hankalin ta kan abinda take faɗa, zuciyar ta babu abinda takeyi sai bugu kamar zata fito waje ganin Grandma na neman jawo mata ruwa.

Buɗo ƙofar akayi aka shigo inda Grandma ta maida duban ta gun mai shigowar.

Jalilah ce tafe tana murmushi tazo ta rungume Grandma ɗin tana cewa "Grandma."

Murmushi Grandma tayi tana ɗago ta nan tace "Wannan leda menene haka a ciki?" cewar Grandma cikin riƙe ha6a tana kallon Jalilah.

Jalilah kallon ledar hannun ta tayi kafin cikin murmushi tace "Duka fah Akhi ne ya sayamin, shi yace na ɗau duk abinda nakeso."

"Iyeee, kice kawai soyayyar ku kuka shawo, toh shi ɗin ina ya tsaya kuma?."

Zama tayi tace "Yana waje yana amsa kira" ta faɗa idanun ta akan DEENAH dake zaune kamar wacce aka dasa ba tare da ta ɗago ba.

"Toh masha Allah" cewar Grandma kafin tayi murmushi tace "DEENAH dear, wannan ita ce Jalilah marar lafiyar tamu amma yanzu alhamdulillah taji sauƙi anjima ma muna sa ran za'a bamu sallama, yakamata kusan juna tun yanzu dan kuɗin zaku zo ku zamto matar ya da ƙani ne, haka nake sa rai insha Allah" ta faɗa tana kallon su duka.

Murmushi Jalilah tayi tana kallon DEENAH da ta ɗago tana kallon ta kafin tace "Hi, ya kike ya jikin ki?."

"Hi, Alhamdulillah, ya naki jikin?."

"Alhamdulillah, naji sauƙi sosai but ke i don't think kin gama warkewa completely maiyasa kika fito?."

Ɗan murmusawa kawai DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa, Grandma ce tace "Iska ta fito sha, shine tace bari ta shigo taga ya jikin ki, kinga batada lafiya ma amma ta iya takowa ta duba ki."

"Wow Thank you so much, gaskiya kina da kirki sosai."

Jinsu kawai DEENAH keyi inda duk taji ta takuru, ɗagowa tayi ta kallesu tace "Grandma, i think ni zan wuce kada mahaifiya ta ta fara nema na."

"Haba ƴar nan, tafiya tun yanzu?, ki bari mana Boy ya shigo ku gaisa, kinji tace yana waya da zaran kun gaisa sai ki tafi koh?."

Kai kawai DEENAH ta jinjina tana jinta a matuƙar takure ga kuma wani irin feeling da ta kasa gane koh na menene, musamman yadda zuciyar ta ke harbawa yana tsinkewa tanajin duk tsikar jikin ta na tashi haɗi da wani irin sanƴi da taji yana ratsa dukkanin wani 6argo na jikin ta.

Sadda kai tayi ƙasa tana runtse ido da ƙarfi koh zata rage jin abinda takeji.

Shigowar sa ɗakin yayi daidai da wani irin bugawar zuciyar ta da taji, wanda yafi kowanne ga kuma wani irin gudu da yake yana beating so fast, runtse idanun ta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya sama-sama.

Da shigowar sa Grandma ta kallesa tace "Yauwa gara dai da ka shigo dawuri, ƴar nan nata son tafiya tunɗazu na hana ta nace ta bari kazo ku gaisa kafin ta wuce."

Har Grandma ta idda maganar tata bai kalli inda DEENAH ke zaune ba.

Jalilah ce tace "Yeah, i guess girlfriend ɗin YAZEED ce, she is so damn beautiful, right Grandma?."

"Ahaf ai zai ganewa idanun sa yanzu."

Maida duban sa kan DEENAH da kanta ke sadde da ƙasa yayi bayan sunce dashi girlfriend ɗin YAZEED ce.

A hankali ya buɗi baki yace "Hi."

Da sauri ta ware idanun ta da suka kasance a runtse jin muryar sa da ta ratsa dodon kunnuwan ta tana mai ɗago da manƴan idanun ta tana sauƙe su cikin nashi.

Zuciyar ZEEYAD ce tayi wani irin harbawa lokacin da idanun sa sukayi masa arba da fuskar ta.

DEENAH sake waro idanun ta tayi tana binsa da kallo inda ta shiga tashi a hankali daga zaunen da take still idanun ta cikin nasa.

Murmushi Grandma da bata wani fahimci komai ba tayi tana miƙewa tsaye kafin tace "DEENAH dear wannan shine Boy ɗina ZEEYAD shi ɗin yaya ne a gun YAZEED kokuma kawai ace dasu ƴan biyu ne tunda tazarar mintina goma ce kawai tsakanin su, sannan dukkanin su jikoki na ne."

Dukkanin su babu wani wanda ya maida hankali kan maganar da Grandma keyi, sosai sukayi losting a kallon juna, inda kowane ya kasa ɗauke idanun shi kan ɗan uwan shi.

"DEE...DEENAH?" cewar ZEEYAD a hankali cikin rarrabewar harshe yana binta da kallo.

DEENAH batasan wane irin feeling takeji game da ganin sa ba, ta rasa daɗi takeji koh baƙin ciki, ji tayi zuciyar ta na murnar ganin sa ta wani 6angaren, ta wani gefen kuma akasin hakan ne, lumshe idanun ta tayi hawayen da suka taru mata suna samun damar sauƙowa kafin ta sake ware su akan sa tana cigaba da kallon shi.

Grandma da Jalilah kawai ƴan kallo suka koma suna bin kowanne da ido tunda sukaji ZEEYAD ya ambaci sunan DEENAH.

ZEEYAD kauda idanun sa yayi daga kallon DEENAH, yana kallon Grandma da ta saki baki tana kallon su.

"Boy...ka santa ne?."

Shiru yayi ya ɗan kalli DEENAH da har yanzu bata bar kallon sa ba, cikin tattaro dukkanin nutsuwar sa yace "I...no...i don't know her" ya faɗa kamar wanda aka matse masa baki.

"Toh ya akayi kasan sunan ta?."

Ba tare da ya kalli DEENAH ɗin ba yace "I know she is DEENAH, right?, YAZEED's girlfriend."

Murmushi Grandma ta saki kafin tace "Haka ne, ita ce DEENAH."

Murmushi Jalilah tayi tace "She came to check on me, even though she is also sick."

Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yace, kafin yace "That's so kind of her."

"Yeah dole ka faɗi haka ai tunda tazo duba rabin ranka koh?" cewar Grandma.

Tsuke fuska ZEEYAD yayi kawai yana sadda kansa ƙasa hannayen sa zube cikin aljihu.

Murmushi Grandma tayi kafin tace "Dama ni nace ta jira kazo idan kun gaisa sai ta tafi."

"Uhm" kawai ya faɗa cikin jinjina kai.

DEENAH ji tayi zuciyar ta na breaking into tiny pieces da jin abinda ZEEYAD ya faɗa, she feel completely shattered and useless daga yadda yake avoiding kallon ta and pretend like everything is all okay with him, har yake iya forming murmushi kan fuskar sa a gaban ta, how he told his Grandma cewar bai santa ba and how he called her budurwar YAZEED make her feel so stupid.

How she spend half of her life dashi maƙale a zuciyar ta and how take ganin babu wani wanda ya saura mai ƙaunar ta except him, and how take ta tunanin cewar shima yana chan yana tunanin ta kamar yadda takeyi, and how take tunanin baiyi moving on ba sabida irin ƙaunar da yakeyi mata make her feel like a fool.


"DEENAH de..."

Grandma bata ƙarasar da abinda take shirin faɗi ba DEENAH ta wuce a fusace fuuu tana bangaje ZEEYAD dake tsaye yawa an kafa shi ta fice daga cikin ɗakin.

Duk da kallo suka bita kafin Grandma tace "What's wrong with her?."

"Seems like wani abin na damunta ne" cewar Jalilah.

"We should check on her" faɗin Grandma tana mara mata baya inda Jalilah ma ta bita.

Shiru ZEEYAD yayi yana shafa inda ta bangaje shi ɗin kafin a hankali ya furta "Am sorry DEENAH."

DEENAH da fitar ta gudu ta kama bata tsaya koh ina ba sai ɗakin da akayi admitting nata, tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga tare da rufowa tana sakin wani irin marayan kuka mai tsuma zuciya.

Ɗagowa Umma tayi a razane tana kallon ta, ganin ta faɗo ɗakin tare da sakin kuka ba ƙaramin ɗaga hankalin Umma yayi ba.

"DEENAH?" ta faɗa tana tashi daga inda take zaune tayi kan DEENAH.

Da gudu DEENAH tazo tana faɗawa jikin ta tare da rungume ta ƙam tana cigaba da kuka kamar wacce za'a zarewa rai.

Rungume ta Umma ma tayi tana ɗan bubbuga bayan ta a hankali, jin yadda DEENAH ke kuka yasa itama taji hawayen sun zo mata.

"Am so sorry Umma na dan Allah ki yafemin, for getting you all wrong akan dukkanin abinda kuka cemin."

Bayan ta Umma ta cigaba da bubbugawa a hankali ba tare da ta iya cewa komai ba sai hawaye kawai da Itama keyi.

Ɗagowa DEENAH tayi tana cupping fuskar Umma ɗin a hannun ta tace "Dan Allah Umma kiyi haƙuri ki yafemin da dukkanin abubuwan da nayi miki, nayi miki alƙawarin ba zan sake ba, sannan zanyi duk wani abu da kika sanƴa ni ba tare da nayi miki gardama ba, kice kin yafemin dan Allah" ta faɗa cikin kuka.

Share mata hawaye Umma tayi tace "Bakiyi min komai ba DEENAH, nice nayi miki laifin raba ki da..."

Yatsa ta sanƴa tana rufe bakin Umma kafin ta girgiza mata kai tana sake rungume ta tace "Baki raba ni da kowa ba, as long as ina tare dake da yaya Jafar then i will be happy forever, am so sorry for everything, am sorry da nuna muku cewar baku isa ba, and am sorry for proving you all wrong akan duk wani abinda kuka so fahimtar dani, am sorry for everything Umma na."

"It's alright dear, ki bar kukan nan haka kinji?, komai zai daidaita insha Allah."

Kai kawai ta jinjina tana lumshe idanun ta dake cike taf da kwalla.

Ɗagowa tayi tana kama hannun Umma tace "Umma am all fine now, mu tafi mu bar nan wurin, sannan kada mu sake dawowa i feel so useless here."

"DEENAH, meke damunki ne, mai ya faru?."

Girgiza kai tayi tace "It's nothing, just mu bar nan wurin naji sauƙin komai i promise."

"No DEENAH you doesn't seem alright, ki faɗamin meke damunki, lafiya ƙalau kika fita daga nan, tell me meke damun ki?."

Cikin kuka tace "Kwarai lafiya ƙalau na fita daga nan, amma da naji maganar ki na cewar kada na fita da babu abinda zan gani koh shaida wanda zai zamto sanadiyyar tashin hankali na na har abada, but daga yanzu nayi miki alƙawarin zama ƴar ki wacce kika sani a dah, ba zan sake bijirewa umarnin ki ba."

Kallon ta kawai Umma keyi har ta idda maganar tata.

"Naji dukkanin abinda kika faɗa amma baki sanar dani abinda ya sanƴa ki cikin tashin hankali haka ba, tell me DEENAH meke damunki?."

Shiru kawai tayi tana kallon Umma idanun ta na tsiyayar da hawaye ba tare da ta iya buɗar baki tace mata komai ba.

"Tell me DEENAH, talk to me" Umma ɗin ta sake faɗa tana kallon ta.

Idanun ta dake yaji ta lumshe kafin a hankali tace "Na...i..."

Ƙarar buɗewar ƙofar da akayi aka shigo ne ya sanƴa ta kasa idda maganar ta.

"DEENAH dear" cewar Grandma tana ƙarasowa wurin ta Jalilah na biye da ita.

Da kallo Umma kawai Umma ke binsu dan kuwa batasan su ba.

Grandma ce tace "Afuwan, daga gani kece mahaifiyar DEENAH koh?."

Kai kawai Umma ta jinjina tana kallon Grandma.

"Masha Allah ni ɗin kakar YAZEED ce ina kyautata zaton kin sanshi."

Murmushi Umma tayi tace "Kwarai."

"Masha Allah, bansan mai ya sami DEENAH ba, muna tsaye and she suddenly left, shiyasa muka biyo ta dan jin abinda ke damun ta."

Kallon DEENAH Umma tayi kafin tace "DEENAH ki faɗa mana meke damun ki?."

Goge hawayen fuskar ta tayi ta juyo tana kallon Grandma tace "Am completely fine, kawai nazo ne dama nace miki mahaifiya ta zata neme ni shiyasa na dawo."

Kallon ta Grandma keyi kafin tace "Kin tabbata gaskiya kike faɗamin DEENAH, ba wani abin bane?."

Kai kawai DEENAH ta jinjina mata tana kallon Jalilah dake tsaye bayan Grandma, kafin tayi sauran kauda idon ta.

Dama tasan tunda ya sami kamar wannan babu ta yadda zai sake bin ta kanta ne, and seems like wadannan ɗin dagaske family ɗinsa ne, sai kuma yanzu take hango kamannin jinin ZEEYAD a fuskar YAZEED, ashe dai they are related ne.

"DEENAH, are you sure babu abinda ke damun ki?."

Kai ta jinjina mata kawai.

Nan Grandma tace "Toh shikenan dai dukda dai ban yarda ba akwai abinda kike 6oyemin, amma tunda kince babu komai shikenan."

"Thank you" cewar Umma.
Murmushi Grandma tayi tace "Babu komai, your daughter is so sweet and lovely, kallo ɗaya nayi mata naji ta kwanta min a rai, just do hope that zaki yarda ki aurawa YAZEED ita."

Kallon DEENAH Umma tayi kafin ta ƙirƙiro murmushi kawai ba tare da tace komai ba itama.

"Mu zamu wuce koh, zuwa anjima muma za'a sallame mu, wannan ita ce Jalilah sannan itama matsayin jika ta take, ƴa ce ga ƙanin mahaifin YAZEED."

"Masha Allah" faɗin Umma cikin murmushi.

Murmushi Jalilah tayi itama, kafin ta kalli DEENAH tace "Bye DEENAH, Allah ya baki lafiya."

Kallon ta kawai DEENAH keyi ba tare da ta bata amsa ba.

Sallama Grandma ma tayi musu kafin su fice daga ɗakin.

Da kallo DEENAH ta bisu kafin taje tana zama bakin bed.

Da kallo Umma tabi ta kafin tazo tana dafa ta.

Rungumo Umma ɗin ta sakeyi tana runtse idanun ta trying so hard na ganin tayi controlling feeling ɗinta dama kuma hawayen ta.

Kanta kawai Umma ke shafawa cikin kwantar mata da hankali.


***********************


________ZEEYAD tun bayan ficewar su shima ya fice, babu inda ya nufa sai gida.

Sosai yake ta jeka ka dawo cikin tsakiyar ɗakin nasa, zuciyar sa fal nadamar abinda ya aikatawa DEENAH.

Yasan yayi hurting ɗinta so deeply, how could he do such a thing bayan yaga yanayin ta, seems like har yanzu bata gama samun sauƙi ba duba da yadda ya ganta da uniform ɗin patients a jikin ta, and in the other hand DEENAH itace yarinƴar da YAZEED ɗan uwan sa keyi masa maganar ta kullum, wanda ba ƙaramin so yakeyi mata ba.

He thought DEENAH ta riga da ta zama past nasa ne, sai dai kuma ganin ta a yanzu babu abinda ya tayar masa, sai tsohon feeling ɗin da yakeji tattare da ita.

Zubewa yayi bakin bed ɗinsa yana sanƴa hannayen sa duka biyu cikin gashin kansa, sosai yakejin nadama haɗi da tausayin ta cikin zuciyar sa.

He knows koh kaɗan batayi deserving abinda yayi mata ba coz she is completely innocent, he thought koh zuciyar sa ta fara tafiya ga Jalilah ne but ganin DEENAH a yanzu ya tabbatar masa da cewa itace abinda zuciyar sa ke so da bege a kullum, kasancewar Grandma ɗinsa kusa dashi ne yasa shi jin like ya mallaki komai da komai na farin ciki, but now ya gane that da akwai abinda ya rasa tattare dashi wanda kullum yakejin sa incomplete, and now tozali da yayi da abar nan yau ya tabbatar masa da cewar he still needs her and loves her dearly, he may be sad da abinda mahaifiyar ta tayi masa but hakan ba zai ta6a goge soyayyar ƴar ta daga zuciyar sa ba, and yau ya tabbatar da hakan.

Sosai idanun sa sukayi jazir yanajin sunayi masa wani irin zugi but ya kasa yin kukan koh yaji sassaucin abinda yakeji cikin zuciyar sa, babu abinda yafi tada masa hankali wanda ya wuce son DEENAH da YAZEED ɗan uwan sa keyi.

Ya san YAZEED ba zai ta6a jindaɗi ba idan ya gano cewar yanason DEENAH, shi kuma ba zai ta6a bari wani abu ya sami relationship nashi da ɗan uwan sa ba, so the best abinda yakamata yayi shine yayi pretending like baisan DEENAH ba, yasan ba ƙaramin hurting feeling nata yayi da hakan ba, but babu yadda ya iya, wannan shine kaɗai abinda zaiyi na ganin komai na tafiya smoothly tsakanin sa da ɗan uwan sa wanda shine yayi sacrificing love nasa wa YAZEED

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login