Showing 99001 words to 102000 words out of 236327 words
ya sake maida su ya rufe yanajin haushin farkawar sa daga baccin, baiƙi ya dawwama cikin barci ba har abada muddin hakan zai mantar dashi damuwar da yake ciki.
Ya ɗau almost ten mins a haka kafin kuma ya buɗe idanun sa yana mai miƙewa zaune.
Kansa dake yi masa mummunar ciwo kamar zata tsage ya riƙe yanajin duniyar na yi masa juyi.
Da kyar ya samu ya lallafa ya faɗa bathroom.
Wanka yayi ya tare da ɗaura alwala ya fito.
Shiryawa yayi cikin farar jallabiya sannan ya tada sallah.
Bayan ya idda tare da yin adhkar ne ya miƙe tare da komawa falon.
Inda Telephone ke ajiye ya nufa tare da danna yin kira ya dawo cikin falon.
Ba'a ɗau lokaci ba ma'aikatan cikin hotel ɗin suka shigo ɗaya ɗauke da tray ɗin abinci a hannun sa, ɗaya kuma ɗauke da kayan shara.
Amsar order sa yayi tare da komawa ɗaki.
Zama yayi akan sofa ɗin ɗakin tare da buɗe tray ɗin abincin.
Abincin ya zubawa idanu yana kallo, abinci ne na ƴan ƙasar su wanda bansan sunan sa ba.
Rabon sa da yaci irin abincin nan tun Ummin sa na da rai, it was his favorite meal, ganin abincin ya sanƴa shi tunawa da ita, itace take zaunar dashi ta bashi abincin a baki koh da kuwa baiso hakan ba zata tilasta masa yaci, sai dai kuma gashi yau shi zai ciyar da kansa.
Hannu ya kai ya ɗau spoon kafin ya kai cikin bowl ɗin dake ɗauke da wata miya wacce bansan ta mecece ba tare da ɗebo ta ya kai baki yana yin bismillah.
Ji yayi abincin salam babu taste a bakin shi dan haka cokali ɗaya kawai yaƙara yana maida ta ya rufe.
Juice ya tsiyaya a cikin cup ya sha kaɗan tare da barin sauran kafin kuma ya ɗau tray ɗin abincin yana fitarwa falo.
Ma'aikatan hotel ɗin ya kira suka zo suka fita da tray ɗin.
Zaune yake shiru idanun sa da sukayi masa nauyi a lumshe ya rasa meke yi masa daɗi.
Haka ya kai almost 15mins yana nazari, kafin kuma a zabure ya buɗe idanun sa yana miƙewa tsaye.
"Grandma?" ya furta, kafin kuma ya zuri makullin motar sa yana yin hanƴar ficewa da sauri.
********************
________A gaban wani tsohon gida yayi parking motar sa yana mai fitowa daga ciki.
Kallo tsaf ya ƙarewa gidan, wanda ya kasance babba ne sosai, tabbas gidan ne dan kuwa bai ta6a zatan zai iya gane hanƴar ta ba.
Ya kai 5mins yana kallon gidan da yake tunanin babu kowa ganin ta garƙame da ƙatuwar kwaɗo wacce har kamar ta fara yin tsatsa ma.
Wucewar wasu samari guda biyu ya gani dan haka saurin tarar su yayi, bayan sun gaisa ne kuma cikin harshen larabci yake tambayar su inda mutanen wannan gidan suka je.
Ɗaya daga cike ne yace "Mutanen gidan nan ai sun daɗe da tashi."
"Koh zaku iya faɗamin inda suka koma?."
"Ehto naji dai kamar ance mai Martaba Sarki Abbas ne yazo ya ɗauke su tare da maida su chan cikin fada."
Zuciyar ZEEYAD ne yayi wani irin mugun faɗuwa jin an ambaci sarki Abbas, inda kuma tsoron abinda ya sanƴa shi maida kakannin sa MASARAUTA ya darsu masa.
"But...zaku iya faɗamin tun yaushe ne barin su nan?."
"Ehto, zai iya kaiwa shekaru takwas zuwa bakwai haka."
Idanu ya zaro da jin abinda suka faɗa, kenan hakan na nufin 6atar sa ya sanƴa mai Martaba maida kakannin sa cikin MASARAUTA, toh mai zaiyi musu, mai yake nema dasu, he just hope ba wani abin cutarwar yayi musu ba.
Ganin yayi shiru yana tunani ya sanƴa samarin yin tafiyar su.
"That wretched Man" ya faɗa angrily kafin kuma ya koma cikin motar sa ya jata a fusace yana barin wurin.
Sosai ransa ya 6aci he wonder mai Sarki ke nema dashi da har zai biyo iyayen mahaifiyar sa ya maida su custody ɗinsa dan kawai ya 6ace ba'a gansa ba.
But a yanzu yana ganin it's high time da yakamata ya koma cikin MASARAUTAR sannan kuma yayi maganin duk wani tantiri da ɗan iskan dake jin kansa cewa shi ɗan iskan gaske ne, he would make sure ya koyawa kowanne daga cikin su hankali ta haka ne kaɗai zaiji ransa ya ɗan kwanta da irin abubuwan da sukayi masa, ya za6i ya ajiye batun wata DEENAH a gefe muddin yanason yayi achieving goals nasa, dan sunci galaba akansa wancan karon ba hakan ke nufi zai sake basu wani damar bane yanzu har ma su samu nasarar ta6a kakannin sa, ba wai dan ya manta dasu bane ya sanƴa shi baije wurin su tun farko ba, sai dai yayi hakan ne dan yin nesa da azzaluman da suka cika PALACE ɗin nasu, and now lokaci yayi da zai nunawa kowannen su wurin zaman sa.
Da wannan tunanin ya ƙarasa Babban hotel ɗin.
Bathroom ya shige ya sake iyo wani wankan ya fito.
Gaban mirror yazo ya zauna tare da gyara baƙar sumar kansa sai tada ƙamshi da sheƙi take.
Zuwa yayi ya buɗe closet ɗin ɗakin ya fito da wata kwali mai ɗan faɗi.
Ajiye ta yayi akan gado sannan yayi unwrapping nata yana buɗe ta.
Take wata baƙar suit dama kuma complete abubuwan da za'a yi dressing ɗin dashi ya bayyana.
Ciro ta yayi yana ƙare mata kallo, shi kanshi yasan ba ƙaramar kuɗi ya 6arar akanta ba, dan haka ba tare da 6acin lokaci ba ya shirya cikin ta.
Komai baƙi ne kama daga kan kayan jikin sa zuwa kan tsadaddar takalmin sa, except fatar jikin sa dama kuma rigar ciki da yakasance fari.
Gaban mirror ɗin yazo yana gyara zaman coat ɗin jikin sa, shi kansa yasan bai ta6a yin kyau kamar wannan rana ba dukda kuwa fuskar sa tamau take babu fara'a koh kaɗan.
Feshe jikin sa yayi da turarukan maza masu kyau da matuƙar tsada sai tada masifaffen ƙamshi mai kwantar da rai yake, sannan ya ɗauka baƙar shade tare da mannawa a fuskar sa.
Sosai yayi looking hot a wannan shiga, dan kuwa dama shi ɗin ba baya bane wurin iya ɗaukar wanka ga kuma iriyar kyakkyawar haliitar sa da ta dace da shigar sa, everything is perfect about him, except one thing wato *FARIN CIKI*
Card, waya dama kuma makullin motar sa ya ɗauka yana ficewa daga ɗakin.
Motar sa ya shiga tare da janta ya bar cikin hotel ɗin.
Tafiya mai nisa yayi kafin ya iso wani kamfanin saida motoci na ɗaukar hankali da ƙece raini.
Parking motar sa yayi yana fitowa.
Wani mutumi ne ya tunkaro shi ba tare da 6ata lokaci ba sukayi musabaha kafin ZEEYAD yace "I come to claim what i ordered."
"This way Sir" ya faɗa yana nuna masa hanƴa nan suka jera har zuwa cikin wani ƙaton ɗaki da za'a iya kiran sa da garage, wanda ke ƙawace da manƴa-manƴan zafafan motoci na masu manƴan ragamar mulki.
Leading ɗinsa yayi zuwa wurin wata tsadaddiyar baƙar *Bugatti la voiture noire* sai sheƙi da ɗaukar hankali take.
"Here it is sir" cewar mutumin cikin girmamawa.
Kallon motar ZEEYAD keyi kafin kuma yace "Alright, here is my card, ka ɗau haƙƙin ka and return the card to me."
Amsa mutumin yayi tare da furta "Sure, Sir."
Yaran sa mutumin ya ƙira kafin su fito da motar waje tare da sake kwaskware ta da yin sauraran abubuwan da yakamata.
Takardun motar dama kuma key ɗinta mutumin ya bashi haɗi da card ɗinsa.
Amsa yayi tare da yin godiya, sannan ya buɗe motar, cikin motar kaɗai abar kallo ce.
Addu'ar yayi tare da shigewa yana rufo ta, kafin kuma ya tada ta yana ficewa da gudu daga cikin Company ɗin.
Tafiya yake yana duba location ɗin wayar tasa har ya iso Ungwar da PALACE ɗinsu yake.
Tabbas ya gane nan wurin daga nan zai iya kai kansa har cikin PALACE ɗin.
Sosai yaga arear ta canza masa an sake gyara ta sosai kai kace duka ungwar ce cikin PALACE ɗin tsabar haɗuwa da tsaruwar ta.
Ɗan sassauta gudun motar tasa yayi lokacin da ya shigo layin da ƙatuwar PALACE ɗin tasu take.
Gabaɗaya layin cike take da jami'an tsaro koh ta ina sai patrol suke, inda girman PALACE ɗin ya fara daga farkon layin har izuwa ƙarshen ta ne, tsayawa faɗin haɗuwa dama kuma tsaruwar ta 6ata lokaci ne.
Kallo ya ƙare musu tundaga nesa, lallai ba ƙaramin wulaƙanci aka ƙaro ba a wannan MASARAUTA.
Kallon tafkekiyar gate ɗin MASARAUTAR wacce ke facing inda yake yayi, kafin kuma ya ɗau Mask ɗinsa tare da sanƴawa, yana mai ɗaura seat belt ɗinsa tare da tightning ɗinsa sosai.
"Let's see if you can try and stop me" ya faɗa lokacin da yake ƙure dukkanin iya speed ɗin motar ya nufi hanƴar ƙofar.
Jami'an duk watsewa sukayi ganin yadda motar ta iyo kansu da bala'in gudu kamar zata tashi sama.
Ɗan murmusawa yayi yana maida duban sa kan hanƴa tare da furta "Rascals."
At high speed yazo tare da buge gate ɗin PALACE ɗin yana shigewa ciki.
Ƙarar da hakan ya bayar ne ya janƴo hankalin mutane da dama dake ta kai kawo a cikin MASARAUTAR izuwa inda abin ya faru.
Da kyar ya samu yayi controlling ɗin motar yana zuwa ya buge wani Statue dake cikin tsakiyar PALACE ɗin kafin motar ta tsaya.
Babu abinda kake gani sai tashin hayaƙin da ya cika wurin sakamakon irin tuƙin da yayi wa motar dama kuma abinda ya buga.
Kan kace miye dogarai sun taru a wurin inda kowa ya saita kwari da bakar sa izuwa saitin motar dan ganin wane mai son ƙare rayuwar sa a gidan yarin ne yayi aika-aikar nan.
Haka ma jami'an tsaro dukkanin su suka zo suka zagaye motar riƙe da bindigogin su suna jiran fitowar wanda ke cikin motar.
Ta cikin tinted glass ɗinsa yake kallon su, hakan yasa shi sakin murmushi mai ɗan sauti ganin duk yadda sukayi ready ɗin harbi suna jiran fitowar sa.
"Silly guards" ya faɗa hannayen sa kan steering ɗin motar yana ticking.
Babban daga cikin jami'an aka ɗaukowa micro-phone nan ya fara magana ta yadda na cikin motar zai ji da kyau "Koma wanene kai, kayi gaggawar miƙa wuya ba tare da ka wahalar da hukuma ba, sabida mummunar laifin da ka aikata, ka miƙa wuya yanzun nan" ya faɗi hakan har sau uku sai dai wanda ke cikin bai fito ba.
Kallon ɗaya daga cikin yaran sa yayi kafin yayi masa alama da kai akan yaje ya duba motar.
Ƙara saita bindigar sa yayi yana tunkarar motar.
Hannu ya kai tare da buɗe motar inda bai kai ga ganin wanda ke ciki ba, sai jinsa yayi a yashe a gefe sakamakon wani irin blow da aka bashi da ƙafa, hakan kuma ya sake sanƴa sauran saurin maida duban su kan motar baki sake suna sake saita bindigar su da kibiyar su.
Farar ƙafar sa da tasha baƙar tsaddadar takalmi ya fara zurowa, kafin ya dafa murfin motar da hannun sa da tasha tsadaddiyar diamond ring sai walƙi take kafin kuma ya idda fitowa fuskar nan tasa tayi wani irin murtuƙewar da bai ta6a yi mata ba.
Tun daga ƙasa suka fara kallon sa har izuwa kan ɗaurarriyar kyakkyawar fuskar sa.
Maida murfin motar yayi ya rufe ta kafin ya zaga zuwa gaban motar yana kallon inda ya bige da ta lotsa kafin ya maida duban sa kan statue ɗin da ta faɗi ƙasa ta 6antare gida biyu.
Motar tasa ya shiga shafawa tare da furta "Oh my poor *Bugatti la voiture noire*."
"Hey" yaji an daka masa tsawa hakan yasa shi saurin runtse idanu yana ayyana irin hukuncin da zaiyiwa koma wane mai ru6a66en bakin ne wannan.
"Who the hell are you, and where did you come from?" yaji an sake jefo masa tambaya.
Sosai yaji tambayar ta 6ata masa rai, babu makawa idan ya kama mai maganar nan ya fara gurza bakin sa a ƙasa sai yayi nadama.
Juyowa yayi garesu yana zura hannaye cikin aljihu, kafin kuma ya lankwasar da wuya gefe yace "Wane mai dolphin mouth ɗinne yayi maganar nan a cikin ku?."
Duk kallon juna sukayi suna mamakin iriyar tantiran ci da isa irin na gayen nan, wanda zagaye yake da bindigogi da kibiyu ta koh ina amma har yana da bakin da zai iya zagin wani a cikin su.
"Sir seems like wannan fah baisan a inda yake ba" cewar ɗaya daga cikin dogaran.
"Surrender yourself, now" cewar babban nasu.
Maida duban sa ZEEYAD yayi kansa yace "Ohh i see, kaine kake magana, i got you."
"Soldiers, get ready to shoot indai har ba zaiyi surrending kanshi ba."
Ta6e baki ZEEYAD yayi yana mai gyara zaman glass ɗin idon sa.
Duk sake shirin harbi sukayi suna kallon ZEEYAD dake tunkaro su.
"Stay right there or else i will shoot."
"Really, what are you waiting for then?" ya faɗa still yana tunkaro su ba tare da ya tsaya ba.
"What the hell is going on here?" ta faɗa cikin tsawa.
Dakatawa ZEEYAD yayi lokacin da yaji amon muryar ta cikin kunnen sa.
Duk buɗa mata sukayi, tsaye take cikin doguwar rigar ta dake jan ƙasa bayin ta na take mata baya.
Idanun ta ne suka sauƙa akan murɗaɗɗen saurayin dake tsaye a gaban ta inda zuciyar tayi wani irin faɗuwa tana kallon sa.
"My queen, he caused some damages to the PALACE while driving recklessly, sannan babu wanda ya san shi koh ya san daga inda yake, ya aikata mummunar laifi ya zama dole a hukunta shi koh shi waye."
Zuciyar ta ce ke ta up and down still idanun ta a kansa.
Takowa ZEEYAD da zuciyar sa ta gama munana sabida ganin ta da yayi zuwa gaban ta, kafin kuma ya saki wani irin killer smile yace "QUEEN NASEEBA."
Dum-dum haka taji zuciyar ta ta bada wata iriyar mummunan sauti tana zaro manƴan idanun ta.
Cikin tsukewar face yace "It's been Long."
Cikin rawar harshe da mummunar faɗuwar gaban da take ciki tace "Z...Z...ZEE...ZEEYAD?."
Slight murmushin da ya saki ne yasa ta gasgata abinda tunanin ta ya bata, sai kuma a lokacin ne kammanin sa suka dawo mata cikin kwakwalwa.
"ZEEYAD?" Ta sake faɗa idanun ta kamar zasu faɗo daga ramin su.
Da sauri ta kai hannu zata shafi fuskar sa sai dai wani mugun kallon da ya watsa mata da ganin yanayin fuskar sa ne yasa ta saurin tsaida hannun nata tana sauƙewa ƙasa.
Duk da kallo dogarai dama securities ke bin juna dashi, sakamakon basu fahimci abin dake faruwa ba.
"ZEEYAD" ta sake faɗa yayin da wani irin farin ciki dama kuma tsoro suka darsu mata duk lokaci guda.
Sake tsuke face yayi ganin yadda take ta bin sa da kallo kamar zata haɗiye shi.
"Surprise, surprise Naseeba" ya faɗa cikin calm voice ɗinsa wanda ya sake gigita Sarauniya Naseeba..
Saurin juyawa tayi ga dogaran tace "Put your guns down now, he..he is the lost prince" ta faɗa.
Mamaki ne ya cika mutanen wurin baki ɗaya, inda kuma baki sake suke bin ZEEYAD da kallo.
"Put your weapons down...now" ta sake faɗa da ƙarfi, hakan ya sanƴa su fara sauƙe makaman su, kafin ta juyo ga ZEEYAD cikin murmushi tace "My Sweet Boy..." tana kai hannu zata shafi fuskar sa.
Saurin riƙe hannun ta yayi cikin kakkausar murya yace "Not anymore Naseeba" ya faɗa tare da sakin hannun nata yana ra6a ta ya wuce.
Sosai ranta yayi mugun 6aci sakamakon dizga ta da yayi gaban ɗumbin bayin ta, juyawa tayi tana kallon bayan sa, kafin ta bisu da kallo ta ƙasan ido cike da masifa kuma tace "Get back to your work now."
Nan duk suka shiga watsewa kowa na kama hanƴar sa, inda dayawa ke tattauna akan Yarima ZEEYAD da ya 6ata shekaru goma da suka wuce ace ya dawo.
Cikin takun ƙasaita irin tasa ya ƙaraso babbar ƙofar shiga cikin fada wanda shima ba ƙaramin ƙawata aka sake yi ba.
Tundaga nesa dogaran suka sanƴa dogin takoban su tare da toshe hanƴar.
Ta6e baki ZEEYAD yayi dan kuwa yaga kamar har yanzu wasu dokokin na cikin MASARAUTAR are still intact.
Ja yayi ya tsaya yana kallon su yadda suka wani ƙame wuri ɗaya basa kwakkwaran motsi duk a cikin sunan gadin fadar sarki.
Kallo ya ƙare musu tsaf tabbas ƙarfafa ne sai dai koh kaɗan basu bashi tsoro ba.
Kan ya buɗi baki yayi magana wani dogari yayi saurin ƙarasowa wurin yana yin wurin masu tsaron tare da raɗa wa ɗaya daga cikin su abu a kunne.
Zaro idanu yayi yana kallon ZEEYAD dake tsaye yana kallon su.
Ƙarasawa yayi wurin ɗayan nasa ya faɗa masa abinda aka faɗa masa a kunne nan duk suka sake maido duban su kanshi suna kallon sa.
Kauda kai yayi yana yatsine fuska kafin kuma a buɗe masa doguwar ƙofar cikin girmamawa kuma suka ce "We apologise for our misdeeds the great prince."
Kallon su yayi tsaf kafin kuma ya ɗaga ƙafarsa tare da takawa zuwa bakin ƙofar ba tare da ya shige ba, yana mai bin katafariyar fadar da girman ta kaɗai ya isa a gina ɗakuna huɗu a ciki banda tsaruwar ta da ba'a iya cewa komai.
Doguwar ajiyar zuciya yaja idan ya tuna cewa zai ga mahaifin sa, sai dai wannan karon ba zai lamunci duk wani rashin mutunci koh rashin daraja daga gareshi ba.
Idda shigewa yayi kafin su maida ƙofar su rufe, shiru fadar take babu kowa a cikin ta.
Takawa yayi ya ƙarasa zuwa tsakiyar falon, kafin kuma cikin ɗagun murya ya fara kiran sunan "Grandma!."
************************
Zaune yake kamar kullum gaban hoton ta yana kallo.
Tun safiyar yau yakejin wata iriyar faɗuwar gaba wacce ba zai iya kwatanta yadda yakejin ta ba.
Kamar daga sama ya jiyo muryar da ya sanƴa shi ware idanun sa daga lumshe su da suke, inda kuma ya darsar masa da wata iriyar faɗuwar gaba, amon grandma da ya jiyo ne ya sanƴa sa miƙewa tsaye yana maida duban sa zuwa bakin ƙofa.
ZEEYAD bai damu da mutanen da suka fiffto suna kallon sa ba, sakamakon duk sabbin fuska ne a wurin sa, babu abinda yake kira sai "Grandma."
"Grandma, where are you?."
Duk da kallo suke binsa, suna mamakin daga inda ya fito.
Miƙewa yayi daga kan kujerar da yake haɗi da ɗaukar kyakkyawar sandar dake taimaka masa wurin tafiya ya fito.
Tundaga saman stairs yake hango bayan shi, har ya sauƙo izuwa farfajiyar falon staring at him.
Sarauniya Nazeerah da Hafeezah ma fitowar su kenan suna kallon ikon Allah, inda duk suke Allah-Allah suka wanene wannan ɗin.
Juyowa yayi yana kiran "Grand..." maganar sa ce ta ƙaƙare sakamakon idanun sa da suka sauƙa cikin na mai Martaba.
Ji yayi gaban sa yayi wani irin mummunar faɗuwa, kafin kuma ya haɗe rai tamau kamar wanda yaci guna yana ƙarasowa gaban sa kamar wanda bai san shi ba yace "Tell me...ina ka kaimin Grandma?."
Baki mai Martaba ya saki yana kallon haɗaɗɗen saurayin dake gaban