Showing 183001 words to 186000 words out of 236327 words

Chapter 62 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45310

Mutane ne cike maƙil a babban Masallacin gidan sarkin Sokoto, duk inda ka waiga manƴa-manƴan motoci kawai kake gani kai kace auren ƴar gidan gwamna koh sarkin ake ɗaurawa sabida irin manƴan mutanen da suka halarci ɗaurin auren.

Ana idar da sallahr Jumma'ah, aka nemi awallin kowane ɗaya daga cikin su, inda Dadyn Khairat ya kasance awwalin ZEEYAD, Abban su Amirah kuma na DEENAH.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura auren *ZEEYAD IBN ABBAS* da kuma amaryar sa *MADEENAH ABDULSALAM* akan sadaki dubu Hamsin kacal kamar yadda Abban su Khadija ya buƙata sabida aure da sadaki kaɗan yafi albarka.

Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ZEEYAD dake sanƴe cikin shigar fararen kaya irin tasu ta larabawa ya ɗaura brown alkyabba mai matuƙar kyau da tsada akan sa, yanajin wani irin farin ciki da annashuwa na ratsa kowacce saƙo na jinin jikin sa, yana mai nana ta kalmar Alhamdulillah tare da sake miƙa dubbun godiyar sa ga Allah na cika masa burin sa da yayi a cikin zuciyar sa.

Dafa kafaɗun shi Sadeeq dake kusa dashi yayi shima cike da tsantsar murna a hankali yace "Finally, Congratulations bro."

Murmushi ZEEYAD ya saki tare da jinjina masa kai dan kuwa baya tunanin zai iya buɗar baki magana sabida irin farin cikin da yake ciki.

Albarka manƴan wurin suka sanƴa masa da amaryar tasa tare da sanƴawa rayuwar auren su albarka, mai Martaba kam dama bai zo dan kuwa zai tsaya ne a wurin ɗaurin auren YAZEED dan nuna masa ƙauna da kulawa shima.

Mutane ne suka fara fitowa bayan an ɗaura auren, Jafar ne ya ƙaraso gun ZEEYAD tare da rungume sa a hankali yake faɗin "I know you're a good Man with a kind heart, and i know ba zakayi abinda bai dace ba, i trust you completely banida wani tantama akanka, i know DEENAH tayi dacen miji, please take a very good care of my sister fiye da yadda ka nuna mata a dah, don't let her shed tears da sunan kewar mu, ita ɗin amana ce a gareka and i do hope ka riƙe amanar ta da kyau" ya faɗa yana ɗagowa cikin sanƴin jiki dan kuwa sosai yakejin zaiyi kewar ƴar ƙanwar tasa, she means alot to him and gashi yau zatayi nesa dashi zuwa wani wurin, wanda bai kuma sanin taƙaitaccen ranar sake haɗuwar su ba, ji yake tamkar su koma rayuwar su ta dah lokacin da suke ƙanana, baisan yadda zai iya misalta yadda yakejin kewarta cikin zuciyar sa ba.

Murmushi ZEEYAD yayi cikin sanƴi da tausayin Jafar ɗin ya dafa kafaɗun sa yace "I promise to take good care of her fiye da yadda zan baiwa kaina kulawa, trust me."

"I trust you" ya faɗa kafin ya ɗaura da faɗin "We should get going, don't you wanna see your Bride?."

"Ofcourse he does, he is very eager ma kuwa" faɗin Sadeeq cikin ɗan dariya.

Duk jerawa sukayi suka fito kamar wasu ƙuda haka securities da fadawa suka mara musu baya har izuwa motocin su, kafin su jera duka zuwa gidan su amarya.


*************************


_________Sosai ta haɗe cikin tsadaddiyar doguwar farar wedding gown da yake ja mata har ƙasa, kyawu irin wanda DEENAH tayi a wannan rana ba zai kwatantu ba, duk da kuwa fuskar ta a matuƙar tsuke take babu walwala kamar yadda zakaga wasu amaren amma hakan bai hana irin kyawun da tayi fitowa ba.

Sosai take sake kallon family picture ɗin nasu tana sake jin kewar mahaifiyar ta da ɗan uwanta na ratsa ta.


Buɗo ƙofar ɗakin akayi aka shigo, tsaye Amirah da tayi matuƙar haɗuwa cikin shigar leshi tayi tana kallon ta kafin kuma ta buɗi baki tace "DEENAH sun ƙaraso fah wai kizo kije ki gaida manƴan baƙin."

Shiru DEENAH tayi mata bata tanka mata ba, ganin taƙi kula ta ne ya sanƴa ta ficewa.

Ba'a ɗau lokaci ba Mami ta leƙo a karo na ba adadi wannan karon cike da masifa take faɗin "Wai ba zaki tashi daga wannan gun bane nikam, akanki aka fara aure ne komiye, kowa fah da kika ganshi da aure haka yayi passing level ɗinnan ya wuce ba dan yaso ya bar gidan iyayen sa ba, zaki tashi ki fito ne dai kokuwa sai ranki ya 6aci, ayi tayi miki magana ɗaya tunɗazu sai kace yarinƴa ƙarama, kin bar mutane nata faman jiran ki sai kace wasu sa'annin ki, maza tashi ki wuco mu tafi."

Miƙewa tsaye DEENAH da ta turo ƙaramin bakin ta tayi idanun ta cike taf da kwalla ƙiris ya rage ta fashe ta tattari gown ɗinta a hannu tana bin bayan Mami ɗin da riga da tayi gaba.

Ɗakin Umma ta fara kaita inda ƴan office ɗin Umma ɗin suke ta gaida su, sai yaba ta suke kamar su ari baki, kafin kuma Mami ɗin ta ɗauko wani farin mayafi tana rufa mata akai tare da riƙo hannun ta sukayi falon baƙi.

Su Daddyn Khairat ne da Abban su Khadija dama kuma uku daga cikin manƴan ministocin fada, sai kuma mataimakin gwamna dama kuma ƙarin wasu manƴan mutane uku.

Durƙushewa DEENAH tayi a gaban su tana sake jan mayafin jikin ta, kafin ta buɗi baki dakyar ta gaida su.

Duk cike da fara'a suka amsa mata gaisuwar fuskar su washe.

Addu'a sukayi mata da fatan alkhairi dama kuma samun rayuwa mai inganci cikin rayuwar ta, kafin su ɗaura mata da nasiha dai-dai iya gwargwadon abinda zasu iya faɗa mata sannan sukayi mata kyaututtuka.

Hawaye kawai DEENAH keyi bata ma iya yi musu godiya ba Mami ta ɗaga ta suka fice.

Falon su ta kawo ta nanma ta gaida baƙin da sukayi suma sai yaba ta suke kafin ta maida ta ɗakin Jafar inda ta ɗauko ta tana faɗin "Ki zauna anan, idan kina buƙatar wani abin ki kira ni a waya, ina dai akwai waya a hannun ki koh?."

Kai ta jinjina mata alamun eh tana nuna mata inda wayar take ajiye.
"Yauwa toh, kuma dan Allah banda kuka, kukan nan ya isa haka, mu zamu je mu cigaba da shirye-shiryen tafiyar taku, dan naji labarin shi mijin naki ma sun iso suna waje."

Zuciyar DEENAH ne ya tsinke nan tace "Shirye-shiryen tafiya ina?."

"Bangane shirye-shiryen tafiya ina ba, dah so kike mu saki a gaba muna ta kallo komiye, tafiya mana da mijin ki."

Shiru tayi ta kasa cewa komai nan Mami taja ƙafafuwan ta ta fice, DEENAH sam batayi zaton yau ne zata bar gidan su ba.

Kamar wacce aka tsikara haka ta sake fashewa da wani kukan harda shessheƙa.

Hoton nasu ta ɗauko tana cigaba da kallo duk hawaye ya 6ata fuskar hoton.

A haka Jafar ya shigo ɗakin nasa ya sameta zaune sai kuka take, tsayawa yayi kallon ta for about some minutes kafin ya taka ƙafar sa cikin sanƴin jiki ya ƙaraso.

"DEENAH?" ya kirayi sunan ta a hankali.

Tsagaitawa tayi da kukan da takeyi ɗin tana juyowa ta zuba masa idanun ta da fuskar ta da yayi cha6a-cha6a da hawaye.

Ji yayi jikin sa ya ƙarayin sanƴi sosai fiye da dah, a hankali ya buɗi yace "It's time."

A hankali ta shiga miƙewa tsaye tana kallon shi kafin ya ƙare cewa "Everyone is waiting."

Da gudu tazo ta shige jikin shi tana ƙanƙame sa tare da sake fashewa da wani kukan.

Jafar ji yayi shima kukan na zuwan masa dan haka saurin runtse idanun sa yayi yana bata tight hug shima.

Sun ɗan jima a haka DEENAH bata bar kukan ba, a haka Mami ta shigo ta same su.

Ji tayi duk tausayin su ya kama ta, ƙarasowa wurin su tayi tare da faɗin ''Ai ya isa haka nan koh, sai kace wanda za'ayi rabuwa ta har abada."

Ɗago DEENAH yayi ba tare da ya kuma kallon ta ba ya fice daga ɗakin da sauri.

Riƙo ta Mami tayi ta shiga share mata hawayen "Haba kekuwa DEENAH haƙuri fah zakiyi wannan kuka dai ai yakamata ace kin dakatar dashi haka nan, ace tun shekaran jiya bakida aiki sai abu ɗaya kuka, kiga duk kinbi ma kin 6ata kwalliyar fuskar taki da wannan kukan, ya isa haka nan kinji insha Allah muma zamu ke kawo miki ziyara kar ki damu kinji?."

Kai kawai ta iya jinjinawa tana sassauta kukan nata, a haka suka ƙarasa ɗakin Umma.

A bakin bed aka zaunar da DEENAH, kallon Umma da ta sunkuyar da kai Mami tayi tace "Toh ga ƴar taki nan, sai kizo kiyi mata nasiha irin ta uwa dan gashi chan suna ta jira za'a tafi, ga Alhaji ma tunɗazu yake ta damu da ƙira ayi a fito.

Umma da duk jikin ta yayi sanƴi kasa kallon DEENAH tayi dan kuwa ji take kamar ta fashe da kuka, sam bata zaci DEENAH zata bar gidan nan zuwa gidan auren ta soon haka ba.

Da kyar ta iya miƙewa daga inda take tazo kusa da DEENAH ta zauna tare da rungumo ta tace "Allah yayi miki albarka, Allah ya sanƴa albarka cikin rayuwar auren ki, Allah ya albarkaci zuri'ar da zaku tara nan gaba, ki ɗauke ta kuje kawai Yaya ni banida ta cewa, Allah Ubangiji ya tsare ku ya sauƙe ku lafiya ya kare ku daga dukkanin sharrin masu sharri."

Zama Mami ma tayi suka sanƴa DEENAH dake rungume da Umma sai kuka take a tsakiya kafin ta kira yi sunan DEENAH har sau uku.

Tsagaitawa DEENAH tayi da kukan nata tana sauraran yadda Mami ke ta zuba mata nasiha mai rastsa jiki ƙawayen Umma na taya ta, sosai suke sake ƙara mata kewar Umma har takejin kamar ba zata iya barin su ba.

Amirah ce ta shigo ɗakin tace "Wai ma inji Abba ayi sauri ya isa haka nan."

Kallon ta Mami tayi tace "Ina Khadija fah?."

"Tana ɗaki tare da ƙawayen ta."

Kuje a sake gyara mata kwalliyar nan tukun kafin a tafi ɗin."

Ƙanƙame Umma DEENAH tayi tana kuka sosai take faɗin "Umma na dan Allah kar ki bar ni."

Rungume ta Umma tayi sosai ita ma tana sharar hawayen kewar ƴar tata.

"Ki ɗauke ta kuje Yaya" ta faɗa cikin muryar kukan dake zuwan mata.

Kama DEENAH da ta riƙe Umma ƙamƙam Mami tayi tana faɗin "Umma na dan Allah kar ki bari su tafi dani, banason rabuwa dake, dan Allah Mami ki sake ni."

A haka aka fitar da ita zuwa ɗakin su, Anty Khadija dake zaune da ƙawayen ta suna cin abinci ne ta miƙe tsaye tana faɗin "Lafiya?" ganin yadda DEENAH ke ta kuka ɗin.

"Tafiya zasuyi mana ke kinzo nan sai ɗirkawa cikin ki abinci kike" cewar Amirah.

"Yau kuma?" ta faɗa cikin waro idanu.

"Dan Allah banson surutu, maza gyara mata kwalliyar nan gayi chan suna ta jira tunɗazu" cewar Mami tana zaunar da DEENAH.

Kallon DEENAH dake ta zabga kuka tayi kafin kuma ta wuce toilet ta wanko hannun ta ta fito.

Kit ɗin kayan kwalliyar ta ta ɗauko ta hau gyarawa DEENAH kwalliyar tata.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala, kallon Mami tayi tace "Mami taci abinci kuwa?."

"Kamarya taci abinci baku bata abinci bane?."

Amirah ce tayi caraff take "An bata taƙi ci, da kaina na kai mata ɗakin Yaya Jafar amma tace ba zata ci ba."

"Shikenan ai, maza tashi muje" cewar Mami tana ɗago ta tare da kama ta suka fice daga ɗakin.

ZEEYAD dake zaune a motar ƙafar sa ɗaya a waje idanun sa kafe a hanƴar fitowa daga falon nasu tunda aka ce musu yanzu za'a fito su tafi, miƙewa yayi ya fice daga cikin motar lokacin da idanun sa suka sauƙa akan DEENAH da ake fitowa da ita, zuciyar sa cike da tsantsar farin ciki ya ƙarasa inda suke, sake DEENAH su Mami sukayi inda shi kuma ya rungumo ta so tightly yana rufa mata alkyabar jikin sa haɗi da lumshe idanun sa yana sauƙe wata iriyar 6oyayyiyar ajiyar zuciya.

Fuskar kowa washe da murmushi yake kallon su.

DEENAH wata iriyar ajiyar zuciya ta sauƙe lokacin da taji ta manne cikin faffaɗar ƙirjin sa, inda ƙamshin sa na musamman taji na dausar mata da wata iriyar nutsuwa cikin zuciyar ta.

Kiss ya manna mata a forehead yana sake shigar da ita jikin shi.

"Alright, i think you guys should get going by now" faɗin Abban su Amirah da suke tsaye suna kallon su.

Ɗago da DEENAH yayi ya shiga share mata hawayen kan fuskar ta, kafin kuma ya riƙo hannun ta suna juyawa su fara tafiya, dakatawa yayi tare da juyowa ya kalli su Mami dake tsaye sun zuba musu idanu, ɗan duƙar da kai yayi tare da furta "Thank you so much Aunt."

Murmushi Mami ta saki kafin ya juya su cigaba da tafiya.

Da kansa ya buɗe mata murfin motar tana shigewa tare da tattare mata jelar gown ɗin nata ya rufe, kafin ya zaga zuwa ɗayan 6angaren ya buɗe ya shige.

Shigar sa keda wuya suma duk sauran fadawa da ma kuma securities ɗin da suka taho daga Egypt dama sauran mutane duk suka bubbuɗe motocin su suka shige, already dama gate a wangale take dan haka a hankali suka fara kutsa kai suna ficewa daga cikin gidan.

DEENAH juyawa tayi tare da dafa seats ɗin da take tana kallon ƴan uwanta dake ta waving da hannayen su dama kuma gidan nasu baki ɗaya.

Ta lura bata sake ganin Jafar ba har suka fice daga gidan a hankali ta furta "Yaya?" idanun ta na sake tara wasu sabbin hawayen.

Ganin haka ya sanƴa ZEEYAD riƙo hannayen ta da suka sha baƙin lalle da jaa irin na amaren zamani a hankali ya furta "You will see him again oneday."

Jaye hannayen ta tayi daga cikin nashi tana kauda fuskar ta idanun ta kan glasses ɗin motar.

Matsowa kusa da ita yayi giving her a warm hug yace "It's alright, am here" ya faɗa tare da bata light peck a gefen ido.

Kwantar da kanta tayi kan faffaɗar ƙirjin sa tana lumshe idanun ta.

A haka suka ƙaraso Airport, kasancewar Private Jet nasu na kansu ne wanda already yana jiran su ya sanƴa babu wani 6ata lokaci motocin suka ƙarasa kusa da jirgin.

Da kansa ya buɗe ƙofar ya fito yana saurin dakatar dogarin da yazo da niyyar buɗe ƙofar ya buɗe da kansa tare da riƙo hannayen ta ta fito.

A haka suka ƙarasa matattakalar benin yana tattare mata gown ɗin har suka shige.

Inda aka ware wurin zaman VIPs suka nufa ya taimaka mata ta zauna, kafin shima ya zauna kusa da ita yana kamo hannun ta ya sarƙe da nashi tare da ƙurawa ƙunshin hannun ta da yayi bala'in tafiya da imanin sa idanu yana kallo.

Kanta ta ɗaura kan kafaɗun sa tana lumshe idanun ta, sun ɗau almost 10mins kafin jirgin ya fara ƙoƙarin ɗagawa, ƙanƙame sa tayi dukda kuwa seat-belt ɗin da ta sanƴa har sai da jirgin ya ɗaga sama tafiyar sa ta saitu kafin ta sassauta riƙon da tayi masa ɗin.

Ɗan ɗago kanta tayi tana kallon fuskar sa taga shima ita yake kallo, murmushi ya sakar mata kafin ta sake maida kanta.

Suna nan zaune masu aikin cikin jirgin suka kawo musu abinci tare da jera musu a gaban su.

Ɗan motsa ƙafaɗar sa yayi nan ta ɗago tana kallon sa, da ido yayi mata nuni da abincin, nan ta maida hankalin ta kan abincin kafin kuma ta ɗan yatsine fuska tace "Na ƙoshi."

Ɗan janƴo table ɗin abincin yayi tare da buɗe plate ɗin chips ya ɗau fork ya cakalo chips ɗin a jiki yace "I promised your Family to take good care of you, and i know you're hungry right now, so haaa" ya faɗa yana kaiwa saitin bakin ta.

Kallon sa take kafin ta buɗi baki a hankali yana sanƴa mata a baki, wasu siraran hawaye ne suka biyo mata ƙunci nan ya shiga girgiza mata kai yana faɗin "Please, i don't want to see those tears again, everything will be alright, i promise" ya faɗa cikin riƙe ha6ar ta yana kallon fuskar ta.

Sauƙe idanu tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan nata, a haka ya cigaba da bata abincin tana kar6a har sai da taci kusan rabi tukun kafin tace masa ta ƙoshi, juice ya tsiyaya mata a kofi tare da bata ta sha, kafin ya ɗau tissue sheet ya goge mata bakin dashi tare da sakar mata da murmushi.

Ji tayi hankalin ta ya ɗan kwanta da abincin nan da taci, ganin yana ta kallon ta ne ya sanƴa ta kauda idanun ta tana tsuke fuska.

Murmushi yayi kafin yace "I don't know ranar da zan gaji da kallon face naki, your gorgeous face is like a charm that captivate my eyes" ya ƙarashe yana leƙa fuskar ta da take ta kawar masa tun ɗazun.

Murmushi ya saki kafin yace "I know you're tired so come on, rest here" ya faɗa yana buɗa mata hannayen sa.

Kallon sa tayi kafin kuma ta sake kawar da kai tana 6ata face, ya lura she is moody but nan da ƴan kwanaki zata warware ne.

Jinginuwa tayi a jikin seat ɗinta tana lumshe idanu, ta ɗan jima a haka kafin bacci ya ɗauke ta.

Ganin kamar tayi bacci ne ya sanƴa shi matsawa daf da ita yana gyara mata kwanciya kan faffaɗar ƙirjin sa tare da bata peck a goshi.


************************


__________Hancin ta da taji ana ɗan lakuta mata shi ne ya sanƴa ta fara buɗe idanun ta a hankali tana ware su kan kyakkyawar fuskar sa da yayi tagumi da hannayen sa yana kallon ta daga ɗaya seat ɗin dake facing wanda take.

Idda ware idanun nata tayi tana gyara zaman ta tare da ƙarewa cikin jirgin kallo ganin kamar ya tsaya.

Kallon sa tayi tace "Mun zo?."

Kai ya jinjina mata ba tare da ya ɗauke idanun sa daga kanta ba.

"Ƙarfe nawa?" ta tambaye sa.

Wayar sa ya ciro tare da dubawa kafin yace "It's 8pm."

Ɗan waro idanu tayi kafin kuma ta shagwa6e fuska tana faɗin "Ni na gaji, wannan kayan yana takura min."

Miƙewa yayi tsaye daga zaunen da yake yana takowa gaban ta tare da miƙa mata hannu.

Nata hannun ta sanƴa cikin nasa kafin ya taimaka mata ta tashi suka fice daga wurin.

A hankali suke takowa daga kan matattakalar benin tanajin wani irin iska mai sanƴi na hura ta, wasu baƙaƙen zafafan motoci ta hango tsattsaye da alama dai jiran fitowar su suke.

Buɗe ƙofar motar yayi mata tana shigewa ciki kafin ya zaga ta ɗayan side ɗin shima ya shige.

Nan aka ja duka motocin tare da barin cikin airport ɗin.


**********************


_________Tsaye Grandma take cikin tsadaddiyar shirin ta na alfarma, sosai tasha kyau kamar babu gobe, jin Boy ɗinta da DEENAH na hanƴar tahowa MASARAUTA duk sai takejin ta cikin wani irin tsantsar farin cikin da ba zata iya musalta shi ba.

Sosai aka gyara MASARAUTAR inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login