Showing 186001 words to 189000 words out of 236327 words
tayi kyau sosai fiye da dah, koh ina ka wulga mutane ne ke ta sabgogin gaban su kamar ba dare ba.
Cikin minti talatin suka ƙaraso cikin MASARAUTA inda ɗumbin jama'a suka taru dan shaida amaryar Yarima ZEEYAD ɗin.
Part ɗin Grandma aka wuce dasu kamar yadda ya buƙata, sauƙar su keda wuya Grandma ta fito da wasu kuyangu a bayan ta hannayen su riƙe da wasu abubuwan da bansan koh menene ba.
Cike da farin ciki ZEEYAD ya fito daga motar yana zuwa ya rungume Grandma cike da tsantsar farin cikin da yake ciki.
"Masha Allah, masha Allah kyakkyawan yaro na ya zama babban mutum, ni yanzu matsamin tukun naga ƴar kyakkyawar jikar tawa, ƴar amana" ta faɗa tana jaye shi daga gaban ta kafin ta nufi motar da sauri tana buɗe 6angaren inda DEENAH take.
Wani ƙayataccen murmushi Grandma ta saki tana riƙo hannun DEENAH ta fito daga cikin motar, rungumar ta tayi tightly kafin ta ɗaga ta manna mata kiss a duka ƙuncin ta dama kuma goshin ta tana cupping fuskar ta a hannu tace "Barakillah feek."
Ɗan murmusawa DEENAH tayi tana sadda kanta ƙasa, juyowa Grandma tayi tana kallon kuyangun tace ku matso nan.
Takowa sukayi inda take tsaye kafin ta kar6i wani farin mayafi mai kyau tana rufawa DEENAH akai ya rufe mata har fuska kafin ta juya ga ɗayar ta amshi wani abu kamar burner tare da kunna shi wani irin hayaƙi mai daɗin ƙamshi sosai ya fara fitowa daga 6uli-6uli abin, turarawa DEENAH tayi tana faɗin "Allah ya raba ki da sharrin dukkanin wani mugun abu walau mutum ne koh aljan, wannan turaren da kike gani haɗe yake da maganin mayu dama kuma na asiri, komin sharrin mutum akanki sai dai ya koma kansu, kaima zo nan na turara maka shi" ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD dake tsaye gefen ta.
Murmushi yayi yace "Grandma zaki sanƴa mata mura da wannan hayaƙin naki, you know banason wani abu ya same ta koh?" ya faɗa yana ƙarasawa kusa da DEENAH yana rungume kafaɗun ta.
"Kaji min ja'irin yaro, ni zaka nunawa salawaitun gantalewa, toh kaima da kake ƙarami kullum sai na turara maka ita, koh yanzu duk wani turare da ake sanƴa maka a 6angaren ka haɗe yake da wannan maganin, ni yanzu dai ka barmin ƴa mu shiga ciki haka nan nasan ba ƙaramin gajiya ta kwaso ba" ta faɗa tana maidawa ɗayar kuyangar burner ɗin hannun ta kafin ta kamo hannun DEENAH su shiga ciki da ita.
Daga inda suke tsaye suke leƙe Kiki tace "Ranki ya daɗe ni fah banga fuskar matar tasa ba."
"Zo muje kawai, koma dai wacece gobe da safe ma ganta a fada" tana faɗin haka ta janƴo mayafin kanta yana rufe mata fuska ta bar wurin nan Kiki tayi saurin mara mata baya.
*************************
_________Washe gari da sassafe Grandma ta shigo ɗakin da DEENAH take, zaune ta same ta ta kafe wuri ɗaua da ido, shigowar su ne ya sanƴa ta saurin dawowa hankalin ta tana miƙewa tsaye tare da ƙarasawa gun Grandma ɗin tana gaida ta.
"Allah yayi miki albarka ƴar nan, dafatan dai kin kwana lafiya?."
"Lafiya ƙalau" ta amsa tana sadda kai ƙasa.
"Masha Allah naji daɗin jin hakan, kai ku kuma zaku ajiye karin kumallon ne kokuma zaku tsaya kallon ta ne, kokuwa dai baku ta6a ganin kyakkyawa bane a rayuwar ku, magulmatan banza saura kuma akai gaba."
Da sauri suka rissina suna gaida DEENAH kafin su nufi kan wani table dake tsakiyar ɗakin suna ajiye tray ɗin hannun su.
Kamo ta Grandma tayi tana zaunar da ita bakin bed kafin tace "Ni na girka miki abincin nan da kaina, sabida kinsan halin mutanen cikin MASARAUTAR nan duk munafukai da annamimai aka tara sai mutum yana takatsantsan, amma ke kam kar ki wani damu da izinin Allah turaren da nayi miki jiya koh maƙiyi sai yaji tsoron haɗa idanu dake, yanzu kici abincin nan ki shirya sabida yau za'a je fada duk kuje ku gaida Sarki" ta faɗa tana ɗauko plate ɗin abincin.
Wani irin abinci ne kamar fankasau sai dai shi ɗin nama ne birjik a tsakiyar sa, tauna ɗaya DEENAH tayi masa taji yayi mata daɗi sosai.
Murmushi Grandma tayi tace "Yayi miki daɗi sosai koh, ai nasan zaki so shi shiyasa nayi miki shi, kada ki damu a hankali zan koya miki irin girkunan mu na nan, sannan a hankali zaki koyi cin wasu."
Ita dai DEENAH kawai murmushi take tana saurarar ta.
Bayan ta gama breakfast ɗinne Grandma da kanta ta haɗa mata ruwan wanka gudun wai kar a sanƴa wani abin cutarwa a cikin ruwan, bayan DEENAH ta fito daga wankan ne kuma ta tadda wani dogon gown ɗin kuma mai kyau akan bed, ta komai nasa, kallon ta Grandma tayi tace "Masha Allah, wannan shine kayan da zaki saka bari na bar ki ki shirya cikin kwanciyar hankali, ni zan fita yanzun nan zan dawo kafin ki kammala.
Kai DEENAH ta jinjina mata cikin murmushi tana binta da kallo ta fice daga ɗakin tare da rufo mata ƙofar.
Maida duban ta tayi kan kayan kafin ta sake maida duban ta kan mirror ɗin dake shaƙe da kayan kwalliya kama daga kan lotions ɗin shafawa da dai sauran su, ɗakin ta kuma ƙarewa kallo tana sake jinjina girma dama kuma haɗuwar sa ganin irin dukiyar da aka sheƙa mata a ciki.
A hankali taja kujera tana zama gaban dressing mirror ɗin kafin ta ɗau lotion mai kyau daga ciki ta shiga shafawa a jikin ta, dukda kuwa batasan koh zai kar6e ta ba dan kuwa sam ba irin company ɗin da take amfani dasu bane a wurin.
Gashin kanta da ya sha ƙananun kitso ta sake feffesawa spray mai daɗin ƙamshi tare da sanƴa gashi walƙi, kwalli kawai tasa tare da shafa glowing lip-gloss a bakin ta.
Miƙewa tayi ta shirya cikin inner-wears ɗinta da suka kasance irin kayan ne kafin kuma ta ɗau doguwar rigar tana jujjuya ta a hannu tana sake yaba irin kyawun sa.
Tana cikin haka ne taji an buɗo ƙofar an shigo, saurin juyawa tayi tana sauƙe idanun sa cikin nashi, da sauri ta ɗaga rigar tana kare kanta dashi.
Murmushi yayi yana kallon ta kafin yace "I promise i didn't saw anything."
6ata fuska tayi tace "What are you doing here?."
"I...i..." shiru yayi yana kallon ta.
"Get out and let me get dressed."
Tsaye yayi yana sake dafe bakin ƙofar yace "No."
Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "Please."
"I can get you dressed" ya faɗa cikin ɗaga mata gira.
"No, get out please."
Sake gyara tsayuwar sa yayi kafin yace "I really wanna see you get dressed, go on."
"This isn't right" ta faɗa.
"What is not right here, seeing my wife get dressed infront of me?, strange."
A hankali ta shiga ja da baya, tana targetting ƙofar bathroom ɗin bayan ta, a hankali shima ya shiga takowa hannayen sa sarƙe cikin aljihu yana ƙare mata kallo.
"S...s..s..stop right there, don't you dare come closer" ta faɗa cikin rawar harshe.
"I really can't imagine this, my own wife forbidding me from watching her get dressed."
"Please Abyad, ka tsaya a inda kake, baikamata ka kalle ni haka ba."
Ganin tana yi kamar wacce zatayi kuka ne ya sanƴa shi dakatawa yace "Fine then, five minutes ki gama shiryawa or else zan dawo idan na dawo kuma ba zan fita ba."
Saurin jinjina masa kai tayi nan ya saki murmushi yana juyawa ya fice daga ɗakin tare da rufo mata ƙofa.
Ajiyar zuciya ta sauƙe a hankali tace "He is unbelievable" kafin ta shiga sanƴa kayan.
Sosai ya zauna mata ɗarass a jiki kamar wanda an gwada ta kafin a haɗa shi.
Mayafin sa da ɗankwalin sa ta gani nan ta ɗau ɗankwalin ta shiga ɗaurawa akanta.
"Ba haka ake ɗaura shi ba" ta sake jiyo muryar sa yana buɗo ɗakin ya shigo.
Mamaki ne ya cika ta nan ta saki baki tana kallon sa, murmushi yayi yana ƙarasowa tare da amsar ɗankwalin a hannun ta.
Ganin yadda take yi masa kallon tuhuma ne ya sanƴa shi faɗin "I promise ban leƙe ki ba."
"Really?, ban fah tambaye ka ba tukun, that means la6ewa kayi kana kallo na kenan koh?."
"Ahm well, maybe" ya faɗa.
Tsuke fuska tayi kawai tana cigaba da kallon sa.
Nan ya sake faɗin "By the way you have an attractive body shape."
Sake tsuke fuska tayi mamakin sa fal cikin zuciyar ta, ashe haka yake bayida kunƴa take faɗa a zuciyar ta.
Murmushi yayi ganin yadda take kallon nasa, ɗankwali ya shiga ɗaura mata irin yadda ake yi.
Kafin ya ɗauko mayafin ya shiga yi mata rolling ɗinsa irin yadda sukeyi.
Dube-dube ya fara nan tace "What are you looking for?."
"Pins" ya bata amsa.
Hannu tayi masa pointing gaban mirror still fuskar ta a tsuke shi dariya ma ta bashi daukar pin ɗin yayi ya shiga tying mata.
Sosai tayi kyau kayan ya kar6e ta kamar wata Balarabiyar.
Grandma ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Ƴar nan kiyi haƙu..." kasa idda maganar tayi kafin kuma tace "Kai mai kakeyi anan?."
"Ohh me?" ya faɗa yana nuna kansa.
"A'a wancan" ta faɗa tana pointing reflection ɗinsa na jikin mirror.
Murmushin da batayi niyya bane ya su6uce mata, kallon ta Grandma tayi kafin tace "Masha Allah kiyi kyau sosai, wa ya ɗaura miki wannan gyalen lallai yayi kyau sosai."
Murmushi tayi tana kallon ZEEYAD da shima murmushin yake.
Takalmin mai ɗan tsayi Grandma ta ɗauko mata tare da bata ta sanƴa, kallon ZEEYAD tayi tace "Zaka wuce kaje ka shirya ne koh yaya."
Murmushi yayi idanun sa kan DEENAH ya bar ɗakin.
Taimaka mata da sauran shirin Grandma tayi, nan ta fito tayi kyau sosai.
************************
________Zaune suke a fadar inda ya tara manƴan baƙi dama kuma Family baki ɗaya.
YAZEED na hango zaune cikin kyakkyawar shigar sa da tayi masa matuƙar kyau, gefe da gefen sa kuma matan nasa ne, sosai fuskar sa ke a matuƙar ɗaure babu walwala koh kaɗan.
Ita ma Jalilah sam fuskar ta babu wata wadatacciyar walwala, sam bata yarda ta kalli inda DEENAH da ZEEYAD ke zaune ba, dan kuwa tunda har aka ɗaura auren ta da YAZEED ta cire sa daga ranta.
Ɗayan gefen kuwa wata ƴar budurwa ce itama ba laifi da ɗan kyawun ta sai dai koh kaɗan bata kamo ƙafar Jalilah ba.
Fitowar sarki ya sanƴa kowanne daga cikin su nutsuwa inda take surutun da akeyi yayi ƙasa.
Zama mai Martaba yayi yana kallon ƴaƴan nasa cike da ƙaunar su, kafin kuma yayi gyaran murya ya fara faɗin "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, this is indeed a happy day for me, ganin yara mafi soyuwa a gareni sun mallaki nasu iyalan, babu abinda zan iya cewa sai Allah yayi muku albarka ya kuma sanƴa albarka cikin rayuwar auren ku."
Duk da Aameen wasu daga ciki suka amsa, murmushi yayi yana kallon ZEEYAD da DEENAH kafin ya maida duban sa kan YAZEED da matan nasa, duk sai yaji zuciyar sa babu daɗi ganin babu wata annashuwa akan fuskar YAZEED ɗin.
Kowane ango na kasancewa cikin farin ciki ne a ranar auren sa ba amma sai gashi YAZEED baya farin ciki da hakan which is all because of son rai irin na mahaifiyar sa.
Gyaran murya yayi kafin ya kalli ɗaya daga cikin ministoci tare da kiran sunan sa yace "Ka gabatar musu da kyaututtukan wa amaren nasu."
Duƙar da kai yayi cike da girmamawa kafin kuma cikin ɗagun murya ya fara faɗin "Mai Martaba adalin sarkin mu yana maraba da surukan sa hakan ya sanƴa shi yiwa kowacce daga cikin matan ƴaƴan nasa kyauta mai tsoka, amaryar Yarima ZEEYAD wanda yake shi ne babba daga kanta za'a fara, mai Martaba ya mallaka mata biyar daga cikin manƴan raƙumar sa haɗi da kujerar Hajji ta wannan shekara."
Ɗago da idanu DEENAH tayi tana sake damƙe hannayen ta dake cikin na ZEEYAD, she can't believe her ears.
"Yayin da kuma amaren Yarima YAZEED kowacce daga cikin su itama tana da kyautar raƙuma biyar haɗi da kujerar Hajji, baya ga haka kuma Sarki yayi wa Uwargidan Yarima YAZEED kyauta ta musamman wato kyautar santaleliyar mota ta miliyan goma sha takwas, yayin da amaryar sa kuma akayi mata kyautar babban fili dake a wajen MASARAUTA."
Wani irin gimtse fuska yarinƴar tayi da jin kyautar da akayi mata, above all abubuwan kyalli-kyallin duniyar nan sai a rasa kyautar abinda za'a yi mata sai na fili?
"Wannan shine dalilin tara ku anan da akayi kowa yaga sabbin amaren sannan kowa ya shaida kyautar da sarki yayi musu dan haka zaku iya watsewa."
Wani ne ya gaya masa magana a kunne nan yayi saurin dakatar da mutanen dake shirin tafiya da faɗin "Ku ɗan jinkirta kaɗan da akwai manƴan baƙi dake son yiwa amaren kyautar ban girma."
Kallon ZEEYAD DEENAH dake jin ta kamar a ƙaya tayi, duk a takure take gani take ita kaɗai ce bare a cikin su sabida babu ƴan uwanta koh ɗaya a wannan wurin, a hankali tace "Abyad?."
Kallon ta yayi yace "are you Okay?."
"Zamu iya tafiya?."
Damƙe hannun ta yayi cikin nasa yace "Don't panic please am here."
Shiru tayi kawai bata sake cewa komai ba.
Baƙin dake wurin ne suka fara zuwa suna presenting gifts ɗinsu a gaban amaren, sosai DEENAH da Jalilah suka kwashi gifts masu yawa inda dukkanin su murmushin yaƙe kawai sukeyi.
Sarauniya Nazeerah ce itama ta taho da kuyangun ta a baya suna riƙe da abubuwan da zatayi wa amaren kyauta dashi.
Gun DEENAH ta fara nufa, ɗago da ha6ar DEENAH tayi tana kallon ta tace "You're such a cutie Darling."
Ɗan murmusawa kawai DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa, kar6ar kwalin hannun ɗaya daga cikin su tayi tana ajiyewa DEENAH a gaban ta tace "This is for you dear, for the first time i saw you that day na tabbatar da wadannan awarwaro zasuyi miki kyau, accept them from me please" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon ta.
Kai DEENAH ta jinjina mata nan ta buɗe kwalin inda wani set ɗin hand Bangles na gold masu bala'in kyau da tsada suka bayyana.
Waro idanu amarya YAZEED tayi ganin irin babban kyautar da Sarauniya Nazeerah ke baiwa DEENAH, she just hope ace nata ma kamar hakanne koh fiye dashi ma.
Hannun DEENAH ta kama ta sanƴa mata awarwaron inda suka zauna mata ɗas sukayi mata kyau sosai a hannu, murmushi tayi tace "Masha Allah, Allah yayi wa rayuwar ki albarka."
"Nagode sosai" cewar DEENAH.
Kallon ZEEYAD da fuskar sa ke a matuƙar tsuke Nazeerah tayi bata ce dashi komai ba ta miƙe ta nufi wurin Jalilah, Itanma Bangles ɗin GOLD mai kyau da tsada tayi mata, sai dai design ɗin nata ya banbanta da na DEENAH.
Kafin kuma ta nufi gun amaryar YAZEED nan tace mata "Tun farkon gani da nayi miki ba zan 6oye miki ba jini na bai ɗauke ki ba, so accept this little gift from me please, don't be offended" ta faɗa tana miƙa mata kwalin sarƙa da ƴan kunne.
Amsa tayi kafin a hankali tace "Are they GOLD?."
Murmushi Nazeerah tayi kafin tace "Kwarai kuwa gwal ce, kin ta6a ganin inda matar sarki tayi kyautar da ba gwal ba, sai dai Let me be honest with you naki bai kai nasu kyau da tsada ba" tana faɗin haka ta miƙe ta bar ta nan zaune.
Sosai zuciyar yarinƴar ya shiga burning ganin duk kowa yafi nunawa Jalilah ƙauna akan ta most especially DEENAH wanda ta rasa abinda suka gani a jikin ta da suke ta rububin ta haka, kallon tulin kyaututtukan dake gaban DEENAH tayi tanajin zuciyar ta na ɗaci, kafin ta maida duban ta kan fuskar DEENAH ɗin.
Mistakenly DEENAH ta ɗago tana sauƙe idanun ta cikin na yarinƴar taji gaban ta yayi wani irin mummunar faɗuwa.
*Yawan Comment, Yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR..................✍🏽*
[8/28, 7:58 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*048...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
_________Saurin sadda kai DEENAH tayi tana runtse idanun ta zuciyar ta na dukan tara-tara.
Motsa hannun sa ZEEYAD yayi nan ta ɗan ɗago ta kallesa, alamun yayi mata da meke damun ta inda tayi saurin girgiza masa komai kan bakomai tana maida kanta ƙasa.
Kauda kanta amaryar YAZEED tayi tana wani irin tsuke fuska haɗi da hura hanci.
Kallon inda ZEEYAD da DEENAH ke zaune Sarauniya Hafeezah tayi kafin ta miƙe daga kan kujerar ta, Rahina ce tayi saurin faɗin "Ummie ina zaki?."
Hafeezah bata kula ta ba tazo tsakiyar wurin ta tsaya inda kowa ya tsaya yana kallon ta nan, idanun ta kan DEENAH take faɗin "Your Highness how on earth zaka yarjewa ɗanka auren wannan yarinƴar, she was his brothers Ex, am definitely sure da wani mummunar ƙudirin ta shigo cikin MASARAUTAR nan, tayi soyayya da YAZEED ganin burin ta ba zai cika akansa bane kuma tayi dukkanin yadda zatayi ta koma soyayya da ɗanka, ba wai ina faɗin haka bane sabida na damu da ZEEYAD but sabida ina da ƴaƴa cikin wannan MASARAUTAR and GOD knows abinda zata aikata muddin ta zamto Sarauniyar ga wannan fadar..."
"Hafeezah!" mai Martaba ya katse ta a tsawace.
Juyawa tayi tana kallon sa kafin