Showing 219001 words to 222000 words out of 236327 words

Chapter 74 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45303

sosai suka jigata Rahinah da Sairah sai kuka suke ganin girman falon amma koh tausaya musu baiyi ba gashi kuma dama ba sabawa sukayi ba, sosai sukejin kamar bayan su zai 6alle ya faɗi.

Sai da yaga gidan ya fita tass kafin ya miƙe yace "Ku tabbatar kun gyara mata ɗakin da zata sauƙa idan tazo, muddin kuma naga koh da tsakuren datti ne kuyi kuka da kanku" yana faɗin haka ya fice a fusace.


**********************

_______Sosai hankalin DEENAH da na Grandma ya tashi ganin abinda su Hafeezah sukayi wa JALILAH.

DEENAH ce cikin kuka tace "Grandma they won't stop at nothing har sai sunga bayan babyn jiki na, sai dai ba zan ta6a bari hakan ya faru ba kafin su ga bayan mu ni sai na kawo ƙarshen su."

"DEENAH tayaya, just take a look akan abinda suka yiwa JALILAH think of abinda zasu yi miki ke da suke farauta, cikin ki watar sa biyar ne kawai da ƴan kai, am sure ba zasu sarara ba har sai sunga bayan shi."

Dafe cikin tayi lokacin da taji motsin sa, cikin kuka ta runtse idanun ta tana samun kujera ta zauna, kafin ta shiga girgiza kai tana faɗin "Sunga bayan mahaifin shi nikuma ba zan bari suga bayan shi ba, mai suke nema ne damu, ba dama mahaifin sa suke so ba kuma sun raba mu dashi, why kuma yanzu suke sake harin mu nida ɗana" ta faɗa cikin kuka tana rungume cikin nata.

Cike da tausayin ta Grandma ta zauna a gefen ta tana faɗin "DEENAH har abada kada ki gaji da neman addu'ar tsari daga wurin Ubangiji, ni inaji a jiki na ba zasu ta6a yin nasara akanku ba komin asiri da tsafin su Allah ba zai ta6a basu galaba akanku ba, ya kama ta ki zamto mai dauriya, jajiratacciya dama kuma jaruma koh dan saboda ɗan dake cikin ki ma, muddin kina son ɗaukar fansar ran mahaifin sa then yakamata ki rage rauni dama kuma yawan shiga wannan ƙuncin ki nuna musu cewa ke bakya tsoro sannan babu abinda zasu iya yi miki keda ɗan cikin ki."

"Grandma is right DEENAH, lokaci yayi da yakamata kema ki nuna musu cewa a shirye kike da ki kare kanki da ɗanki, ki kuma nuna musu cewa Allah yana tare daku and no harm can come to you, zamu goya miki baya akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke" cewar JALILAH da har anyi mata dressing ɗin ƙafar tata.

Grandma ce tace "Kwarai kuwa DEENAH, idan suna taƙama su su uku ne zasu iya ja damu ai mu mun fisu yawa, kinga da ɗan cikin ki mu huɗu kenan, mu nuna musu cewa muma fah ƴan iskan kanmu ne sannan ba zamu sake kar6ar wani rashin mutunci koh nuna tsoron su a fili dama kuma zuciya ba, na tabbata ɗan cikin ki shima yana goyon bayan mu a wannan harkar dan nasan shima ba zai so ayi babu shi ba wurin ɗaukar fansar ran mahaifin sa."

Dariyar da batasan da zuwan sa ba tayi jin abinda Grandma ke faɗi, murmushi Grandma tayi ganin DEENAH ɗin tayi dariya nan tace "Ehmana ai gaskiya ne duk zamuyi maganin su ɗaya bayan ɗaya da izinin Allah."

Murmushi sukayi dukan su kafin kuma su rungume juna.






*Yawan Comment, Yawan Typing*







*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[9/6, 10:49 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*QUARTER FINAL*





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*053...*




_Ku tanadi Hanky tukun kafin ku fara karatun😭_



________"Ni fah wannan mahaukacin Sooraj ɗin bai daki banza ba wallahi, sai na rama duk wani rauni da yayi min akan ƙanwar tasa na nuna masa cewa nima fah da tawa gatar, dan aure ya kawo ni wannan MASARAUTAR ba shi ke nufin koh banida gata bane sannan wani banza chan ya ta6a min lafiyar jiki kuma ya wanƴe lafiya, sai na tabbatar na ɗau fansa ta akan ƙanwar tasa idan yaso koh kashe ni zaiyi sai dai ya kashe ni" ta ƙarashe cike da fusatar da take ciki.

Rahinah ce tace "Ke ki raba kanki da Sooraj wallahi bayida hankali koh kaɗan ni kunga tattara inawa-inawa zanyi na koma London da zaran na ɗan ƙara jin sauƙi ban isa ya kashe ni a banza ba tare da na gama more rayuwa ta ba."

Shiru Hafeezah dake ta kai komo cikin ɗakin tayi tana saurarar su.

Katse su tayi da faɗin "We must get rid of DEENAH's baby."

Wani irin kallo Sairah tayi mata kafin tace "Just look at our condition, koh nuna alamun kin damu bakiyi ba, kedai kawai akan burin ki hankalin ki ya karkata baki damu da kiyi mana jajen abinda ta6a66en nan yayi mana ba, and kinzo kina maganar wata banzar DEENAH chan daban."

Kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "Kuma dan Sooraj yayi muku lahani sai hakan ya dakatar dani daga aiwatar da niyya ta komiye kike nufi, this is for your own good ke gaki nan koh cikin bakiyi ba and YAZEED ne zai zamto sarki nan ba da jimawa ba, muddin muka bari DEENAH ta haihu then komin daren daɗewa sai abinda ta haifa ya gaji mulki muddin ya kasance namiji ne."

Shiru tayi tana tunani sai yanzu take ganin wautar ta tun farko da ta kada seducing YAZEED, nan ta miƙe tsaye tana kallon Hafeezah tare da faɗin "What do we do then?."

Murmushi Hafeezah tayi tare da faɗin "We kill the unborn child."

"But how, tayaya JALILAH is our only hope and mahaukacin yayan ta won't let us rest muddin muka sake yunƙurin yi mata wani abin."

Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Wayo zamuyi mata da daɗin baki mu janƴo ta cikin mu."

"That won't be easy, zuciyar ta gauraye take da imani, ba zata ta6a yarda damu ba har ta iya bamu haɗin kai, and besides kishiya ce a gareni there is no way zan haɗa inuwa ɗaya da ita a matsayin team, we all want her dead sabida ya kasance ni kaɗai na rage matar YAZEED why kuma zamu jawo ta cikin mu?."

"Kina tunanin koh nima kaina ina ƙaunar ta da YAZEED ne, ke kaɗai ce matar YAZEED sannan kece zaki zamto Sarauniya ga wannan ƙasa ba da wata ba, da zaran ta gama yi mana amfani sai kuma muga bayan ta."

Murmushi Sairah tayi kafin tace "Yanzu kikayi magana, ta ina yakamata mu fara yanzu?."


***********************


__________DEENAH ce tsaye bakin mirror ta ƙurawa cikin nata ido, hannu ta kai ta shafi cikin tanajin yadda yake yi mata motsi a ciki.

Murmushi tayi kafin tace "You're my only happiness now and i will do everything it takes dan ganin kazo duniyar nan da ranka, i can give my life dan ganin kai ka rayu, no enemy da ya isa yayi galaba akanka, this is my promise to you little ZEEYAD."

Rolling ɗin gyalen hannun ta tayi akanta tana gyara dressing ɗin jikin ta kafin kuma ta fice daga ɗakin.

Tundaga sauƙowar ta kuyangu matan suke binta da ido har tsayawa sukayi suna kallon ta, DEENAH tamƙe fuska tayi tamkar bata ta6a yin dariya ba ganin yadda har wasun su sun fara ƙus-ƙus ƙasa-ƙasa.

Har ta fice daga part ɗin Grandma basu daina binta da kallo ba, tana fita kai tsaye hanƴar fadar mai Martaba ta nufa sam bata damu da kallon da kowa ke bin ta dashi ba duk inda ta ratsa, a haka har ta iso ƙofar fadar.

"What a beautiful being" ta tsinkayo murya daga bayan ta hakan ya sanƴa ta dakatawa ba tare da ta juyo ba.

Ayaan dake binta da tsinannen kallo ƙarasowa wurin yayi kafin ya shiga zagaye ta yana binta da kallo, dakatawa yayi a gaban ta kafin yayi murmushi yace "You look more beautiful fiye da yadda ake kwatancen ki."

Bata kallesa ba haka ma kuma bata kulasa ba.

Baki ya lashe yana sake matsowa kusa da ita kafin yace "Sai dai koh kaɗan baki dace da ciki a jikin ki ba, i mean ZEEYAD is already dead why keeping abinda ya bari har yanzu cikin mahaifar ki, you deserve a better life like this carrying a dead persons heir in your womb..."

Kallon da tayi masa ne ya sanƴa shi haɗiye sauran maganar, sosai maganar da yayi yayi mata zafi har wani irin huci ta shiga fitarwa cike da 6acin rai.

Hannaye ya ɗaga sama tare da faɗin "Oops those that hurt you?" kafin kuma ya sauƙe hannun cikin murmushin ƙeta yace "Seriously DEENAH you're much younger than your age and more beautiful than your expectation ZEEYAD is dead... why don't you give me a chance?" ya faɗa cikin ɗaga mata gira ɗaya.

Hannu ta ɗaga tare da wanke fuskar sa da mari, dafe ƙunci yayi yana juyowa ya kalleta cikin tsananin 6acin rai idanun sa na canza launi.

"How dare you?" ya faɗa yana ture ta da ƙarfi.

Tangal-tangal ta tafi zata faɗi kafin tayi saurin riƙe wani ƙarfe dake bayan ta yanw tsaida ta, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana riƙe cikin ta kafin kuma ta sauƙe numfashi ganin tana runtse idanun ta.

Ƙarasowa yayi inda take tare da fizgo ta tana kallon sa, murmushi yayi kafin yace "You think ana ta6a lafiyar jiki na kuma a wanƴe lafiya ne?" ya faɗa yana shafa kafaɗun ta cikin salon iskanci.

Su dai guards ɗin koh motsawa basuyi ba bale su tanka abin dake faruwa haka suka ƙame a wurin tamkar gumaka.

Ganin yadda yake shafa mata jiki ne ya sanƴa ta tattarar dukkanin karfin ta tana tura shi.

Baya yayi yana ja ya tsaya, dariya ya saki yana sake binta da wani irin kallo.

Saurin nufar ƙofar fadar tayi nan taga ya sake ɗaura mata hannu a kafaɗa wurin tsaida ta.

Idanun ta ne suka sauƙa kan wani ɗan guntun takobin dake maƙale gefen wandon ɗaya daga cikin guards ɗin, ai kuwa batayi wata-wata ba tayi saurin kai hannu tana zaro kafin ta juyo a fusace tana fille masa hannu da wannan takobin har jini na 6ata mata fuska.

Wani irin ƙara Ayaan ya saki cike da mugun firgita yana ja da baya tare da faɗi ƙasa ganin damtsen hannun sa guntule a ƙasa ga kuma yadda jini ke ta bulala tamkar an buɗe shower.

Ihu kawai yakeyi sai a sannan ne guards ɗin suka iyo kansa, kan kace miye kuma har mutane sun fara taruwa kowa na zuwa ganewa idanun sa abin dake faruwa ganin yadda Ayaan ɗin ke ta ihu har yanzu tamkar zai zauce.

"Arrest her" ɗaya daga cikin guards ɗin ya faɗa da ƙarfi yana nuna DEENAH dake tsaye tana ta faman sakin huci tamkar ranta zai fito.

Kanta wasu guards ɗin sukayi suna sanƴa mata handcuff a hannu, sam koh kaɗan bataji wani tsoro koh fargaba cikin ranta ba sai ma ji take da tayi dai-dai, sannan duk wani wanda yayi yunƙurin shiga gonar ta a shirye take da ta fuskanci wannan mutumin, yanke hannun Ayaan da tayi a yanzu ji tayi wani irin jarumta tazo mata, da mugun kallo take binsa har suka wuce shi kafin ta saki wani irin murmushin gefen baki.

Kaita akayi aka rufe cikin cell sam bata damu ba dan kuwa tasan komin daren daɗewa dai sai ta fita dan ba zata dauwama cikin nan ba.

Wuri ta samu ta zauna tanajin zuciyar sa fes koh bakomai ta ɗau fansar ta6a mata jiki da yayi.

********************

________Sosai Hafeezah ke wani irin mugun kuka a gaban ɗan nata ganin hannun sa a yanke, musamman da taji wacce ta aikata masa hakan ba ƙaramin fusata tayi ba, ji take zata iya kashe DEENAH muddin ta haɗa idanu da ita, sai ta ɗau fansar cire mata hannun yaro da tayi sai dai uwarta ta haifo wata amma ba dai ita ba.

Ganin mai Martaba baiyi magana bane ya sanƴa ta nufar sa a mugun fusace tana faɗin "Kaga abinda matar wancan mataccen ɗan naka tayi wa ɗana amma har yanzu ka kasa cewa komai, banji ka bada umarnin aje a yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata ba, ta cire min hannun yaro amma kayi shiru tamkar wanda ba ɗanka bane shi ɗin, maiyasa ba zaka ɗau mataki akanta ba?."

A tsawace mai Martaba yace da ita "DEENAH have done the right thing, your son here tries to humiliate her ba tare da yayi tunanin ita ɗin matar wansa bane ba, koh a dokar ƙasa laifi ɗaya ta aikata shine na ɗaukar mataki da hannun ta..."

Cikin kuka ta katse shi da faɗin "Ni zaka dubi idanu na kacemin ta aikata dai-dai, kasan ciwon da nakeji cikin zuciya ta na ganin yaro na babu hannu ɗaya?, ta maida min yaro miskini cikin ƙanƙanin lokaci dan haka nima ba zanyi ƙasa a guiwa wurin ɗaukar fansa wa yaro na ba, muddin kai ba zaka ɗauki mataki ba ni nan zan ɗauka" ta faɗa a haukace tana nufar hanƴar ficewa, kwala mata kira mai Martaba keyi sai dai inaa koh ta juyo ta kallesa balle yasa ran zata amsa har ma ta tsaya.

Bata tsaya koh ina ba sai part ɗin Grandma saurin miƙewa tsaye duk sukayi ganin yadda Hafeezah ta faɗo cikin falon nasu hannun ta ɗauke da takobi tamkar zata tashi sama.

Kai tsaye kan DEENAH ta iyo cike da fusata ba tare da tunanin komai ba idanun ta sunyi matuƙar rufewa da tsanar DEENAH ta ɗaga takobin, DEENAH saurin runtse idanun ta tayi tana jiran shigar takobin cikin cikin ta sai dai taji shiru, ihun JALILAH da taji ne ya sanƴa ta saurin ware idanun ta tana sauƙe su a bayan sa.

Duk mutanen cikin wurin idanu suka zaro cike da mugun tashin hankali ganin wanda wuƙar ya soka.

Da sauri Hafeezah ta saki takobin tana ja da baya a mugun razane tare da sakin wani irin ƙara tana ware idanun ta kan wanda takobin ke jikin shi.

Ɗago da idanun sa da sukayi matuƙar kaɗawa YAZEED yayi daga kan takobin yana kallon mahaifiyar tasa, zuciyar sa cike da tsantsar baƙin ciki, baƙin cikin da ba zai ta6a gushewa daga ransa ba har izuwa ranar da za'a busa ƙaho.

A hankali ya furta "Um... mie..." yana zubewa kan guiwowin sa wasu irin hawaye na biyowa ƙuncin sa.

DEENAH ji tayi zuciyar ta na breaking into tiny-tiny pieces sakamakon ganin YAZEED da tayi cikin sa soke da takobin da mahaifiyar sa tayi niyyar kashe ta dashi.

Bata koh iya motsa koh da ƴar yatsar ta bane wasu irin zafafan hawaye na biyo mata ƙunci.

Grandma kuwa zubewa tayi kan kujera itama tamkar wacce aka zarewa ruhin ta daga jikin ta.

Cikin maganar sa da bata fitowa mai kyau yake kallon mahaifiyar tasa yace "Are... you... happy now?."

Kai kawai Hafeezah ke girgizawa cike da tashin hankali hawaye na biyo mata ƙunci.

Babu wanda ya iya tunkarar YAZEED sakamakon wani irin shock da ya ziyarci kowannen su, cikin kuka ya sake faɗin "Are you happy now... Ummie?" yana zubewa kwance a wurin inda kuma jini ya shiga wanke wurin.

Da gudu Hafeezah ta iyo kanshi mai Martaba ya daka mata wani irin tsawa "Don't you dare go near my Son Hafeezah."

Amma inaa bata saurare sa ba tayi kan YAZEED ɗin sai gurzar kuka take tamkar ranta zai fita.

"Oh no!, no... my lovely son YAZEED, i killed you, i killed my own Son, na shiga uku na lalace na kashe YAZEED ɗana..."

"Sieze her" cewar mai Martaba ɗin ai basuyi wata-wata ba guards ɗin suka iyo kanta suna ɗagota, hannun YAZEED ɗin ta riƙo gam babu abinda take sai kuka shikenan ta kashe ɗanta da kanta a garin son zuciya da baƙar zuciya irin tata.

Dakyar suka iya kwace YAZEED daga hannun ta, da gudu JALILAH ta iyo kansa bata ma damu da ciwon ƙafarta ba dan kuwa tama daina jinsa baki ɗaya ne a jikin ta tana ɗagoshi, sosai take kuka tana girgiza masa kai.

Murmushi yayi mata kafin yace "Don't... cry."

Kai kawai take girgiza masa tana kuka.
"Please...please i beg you kada ka mutu ka barni, ba zaka mutu yanzu ba baikamata ace ka mutu ba, no... no please, please" ta faɗa da ƙarfi cikin kuka tana ɗan bubbuga fuskar sa ganin idanun sa na neman rufewa.

Riƙo hannayen ta yayi yana kallon fuskar ta kafin yace "Am sorry..."

"No...ba zaka mutu ba, ba zaiyiwu kaima mu rasa ka ba, dan Allah kada ka mutu na roƙeka, dan Allah..."

Shafa fuskar ta yayi yana share mata hawayen dake biyo mata fuskar, "Please forgive me..." ya faɗa cikin rarrabewar harshe.

Kallon DEENAH dake tsaye akansu tana hawaye yayi kafin yace "Z...EE...ZEE..." bai ƙarasar da zancen nasa ba jami'an dake aiki da emergency Ambulance suka zo suka ɗauke shi.

Cakumo ɗaya sarki yayi yace "Save him... Save my son please shi kaɗai ne ya rage min..."

Kwacewa mutumin yayi daga riƙon da yayi masa kafin yayi saurin marawa ƴan uwan sa baya.

Tari mai ƙarfin gaske ne ya sarƙe mai Martaba ɗin, take shima cikin gaggawa aka ɗauke sa suka fice.

Sosai JALILAH ke kuka tamkar zata shiɗe tana kallon hannun ta da yake kaca-kaca da jinin YAZEED haka ma kayan jikin ta.

Tashin hankalin da DEENAH da Grandma ke a ciki baya misaltuwa, dukkanin su kuka suke an rasa mai rarrashin wani, jikin DEENAH har rawa yake, tasan itace tayi sanadiyyar mutuwar YAZEED da ace bata tankawa Ayaan ba dah Hafeezah bata haukace tazo da niyyar kashe ta abin ya faɗa kan YAZEED ba.

Zubewa tayi akan kujerar dake bayan ta tana shessheƙa mai cin rai, sosai take cikin shock ɗin ganin mutuwar YAZEED a gaban ta, shikenan JALILAH ta zama ƙaramar bazawar kamar ita though ita tana da magajin da zata dinga tuna mijin ta dashi but JALILAH fah yanzu ne ma sabo ya soma shiga tsakanin ta da YAZEED gashi kuma ya tafi ya bar ta, this is very shocking, sam bata tsanmaci zuwan wannan incident ba, sosai zuciyar ta ke rawa, sosai take baiwa kanta laifin afkuwar wannan lamari, tasan YAZEED ba zai rayu ba shikenan shima ya tafi tamkar yadda ZEEYAD ya yafi tsawon watanni biyar kenan bata ga ya dawo ba, haka shima YAZEED ɗin zai tafi ba zai dawo ba har abada dan kuwa bata tunanin zai rayu, sosai takejin tausayin mai Martaba ma ace ya rasa ƴaƴan sa matasa wadanda zasuyi gadon mulkin sa, bashida wani magaji na kirki kuma da har za'a iya bashi mulkin ƙasar ya riƙe, gashi shima dama bai gama farfaɗowa daga shock ɗin da ya shiga na mutuwar ZEEYAD ba ga kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login