Showing 39001 words to 42000 words out of 236327 words
su na tafiya kamar zai tashi sama tsabar sauri kasancewar abinda suka ga Uban gidan nasu nayi kenan.
Kyakkyawa ne sosai, dogo mai murɗaɗɗen jiki wanda daga gani kasan baya rabuwa da Exercise kullum, dukda fuskar sa babu fara'a hakan bai 6oye irin tsantsar kyawun da Allah yayi masa ba.
Buɗe masa glass door ɗin akayi nan suka kutsa kai ciki kafin kuma kai tsaye su nufi wurin lifter inda biyu ne kawai biye dashi sauran kuma suka tsattsaya kowanne na patrol da bindigar sa a hannu.
Kai tsaye hawa na goma sha biyu kamar yadda suka danna numbern jikin lifter ɗin ya kai su.
Suna isa kuwa ya buɗe suka fito, inda kai tsaye kuma suka nufi ƙofar dake chan ƙarshen haɗaɗɗen corridor ɗin wanda tsaya faɗar tsaruwa da haɗuwar sa 6ata lokaci ne, buɗe masa ƙofa akayi nan ya shige inda kuma ƙatuwar hall ɗin mai ɗauke da wani dogon table da kuma seats ɗin da aƙalla zasu kai talatin kowanne da mutane akai, shigowar sa yasa hall ɗin ɗaukar tsit kafin kuma ya tako zuwa ga babban seat ɗin da yafi kowanne kyau da girma a cikin su inda kuma shine yake a center suna bin sa da kallo har ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin bodyguards ɗinsa su tsaya ta kansa ɗaya a gefen hagu ɗaya a na dama.
"You're late ZEEDAN" Cewar ɗaya daga cikin mutanen dake zaune akan table ɗin.
Kallon sa wanda aka kira da ZEEDAN yayi kafin kuma ya gyara zaman sa yana fuskantar su kafin kuma ya hau ticking ɗin yatsun sa akan table ɗin, cikin zazzaƙar husky muryar sa yace "Am born to be a king, No one orders me and no one dares to command me except GOD, i can arrive at anytime i wanttt" ya faɗa cikin jan kalmar ƙarshen.
Shiru mutumin yayi kafin kuma wani ya kar6i maganar da cewa "Let's get back to business then, as we all know My company is falling apart, i mean we are going bankrupt wannan ne dalilin da yasa nake neman taimakon ku kan ku taimaka kuyi investing a Company na domin farfaɗo dashi daga faɗawa halaka."
"Am not investing, but i can buy the company idan kaso" cewar wani daga cikin su.
"Yes, i don't think i can invest too, but if you're ready to sell the company out, zan iya saya" cewar wata daga cikin su.
Nan duk kowa ya fara kawo nasa ƙorafin akan ba zaiyi investing ba sai dai ya saya.
"Alright, alright am ready to sell it out, nawa zaku saya?."
Wata ce ta fara cewa "100million."
"150million" cewar wani.
"180million."
"200million."
"210million."
Haka kowa yayi ta faɗar kuɗin da zai saya wani yana ƙara yawan kuɗin akai duk dan su samu ya sayar musu da company ɗin.
"210million shikenan kuma babu mai ƙarawa akai?" cewar mai son sayar da company ɗin.
"1billion" suka jiyo ya faɗi hakan cikin calm voice ɗin sa, nan duk suka maida duban su gare shi, nan ɗaya yayi wuff yace "3billion."
Nan kuma kowa ya sake gyara zaman shi dan ganin ƙarshen karawa tsakanin wadannan biyu da basa son raini musamman wurin harkar business inda za'a sai da wani abu kowannen su burin sa shine ace ya fitar da kuɗi dayawa, shiyasa da yawa ke son gayyatar su su biyu aduk sadda suka tashi saida wata babbar kadara tasu.
"5billion" ya faɗa.
Nan wannan ɗin kuma ya sake cewa "10billion."
Murmushin gefen baki ZEEDAN yayi dan kuwa ya riga da ya gama gano gayen nan, nan yace "100billion" yana matse fuska.
"200billion" wannan ɗinnan ya sake faɗa.
"400billion" ZEEDAN ɗin ya sake faɗa.
Shiru wannan ɗin yayi dan kuwa ba zai iya ƙara wani abu a saman 400billion ɗinnan ba.
"Da akwai wanda zai iya ƙara wani abu a kai?" cewar mai son saida companyn.
Shiru meeting hall ɗin ya ɗauka hakan yasa shi juyawa ga ZEEDAN tare da yin murmushin farin ciki dan kuwa yasan ba ƙaramar riba yaci ba yace "Sold."
Murmushin gefen baki yayi yana kallon ɗayan nan, kafin kuma ya miƙa hannu wa bodyguards ɗinsa, nan suka ciro cheque da biro suna miƙa masa.
"The Documents?" ya faɗa yana kallon wanda ya saida masa company ɗin.
Da sauri ya ciro wasu takardu yana turawa gaban ZEEDAN.
Ɗauka yayi ya fara bi yana karantawa kafin kuma ya kalle sa yace "Many has regret selling their company off to me, i hope you won't fall a victim?."
Shiru mutumin yayi yana kallon sauran ƴan hole ɗin kafin kuma yace "What do you mean?."
"I mean dayawa sunyi nadamar sayar min da Company ɗinsu, ina fatan ba zaka zamto ɗaya daga cikin su ba, do you know why?, that is because zan iya farfaɗo da company ɗinda yayi shekaru goma a mace in just 3months, ina fatan ba zakayi fushi ba idan kaga yadda Companyn ka zai dawo nan da watanni uku?."
"Hahaha..mai kake faɗa ne haka ZEEDAN?, just sign the papers."
Murmushi yayi ya sanƴa hannu yayi signing, inda shima mutumin yayi signing kafin ya rubuta masa cheque ɗinsa ya basa.
Bodyguards ɗinsa ya miƙawa Documents ɗin nan suka amsa kafin ya miƙe tare da ɗaga musu hannu yana barin cikin hall ɗin............
********************
............Tsaye take a jikin window ɗin ɗakin ta tana kallon waje fuskar nan nata babu wata walwala tattare da ita.
Buɗo ƙofar ɗakin akayi akace "MADEENAH?."
Da sauri ta juya ga Umma kafin kuma cikin sanƴi tace "Na'am."
"Fito" ta faɗa tana komawa, nan ta fice itama tana binta zuwa falon ƙasa.
"Tunda kince ba zaki bar tunanin wanda baki ma san duniyar da yake ba zan tura ki gidan Mami kije kiyi mata sati biyu ki dawo koh nima na huta da wannan halin ƙuncin naki da kullum kike ciki babu walwala."
Ɗan 6ata fuska tayi tace "Umma gajiya kikayi dani?."
"Tayaya kuma zan gaji dake?, na dai gaji da halin ki ne."
"Umma amma ai rashin yaya a kusa ne yasa bana walwala."
"Ba wanin nan, mutumin dake kwana a gidan nan ya tashi a gidan nan ne ɗin kike cewa dan bakya ganin sa ne, maza tashi ki tafi kinga sai kira na take tunɗazu koh kin taho."
Miƙewa kawai tayi ta haura ɗakin ta, kafin kuma ta haɗa kayan ta cikin ɗan madaidaicin akwati wanda ya kasance duk baƙaƙe ne kuma dogin riga Arabian wears da dai English wears masu kyau da musulmi zai iya sanƴawa ya fita, sannan tayi rolling kanta da gyalen kayan jikin ta, lip balm kawai ta shafa a pink lips ɗinta, sosai tayi kyau nan taja akwatin ta ta sauƙo.
Umma ta tarar a falo nan tace "Umma na shirya ke zaki kai ni koh?, dan kinsan yaya baya nan."
"Kin ganni nan yadda na zauna anan da wadannan takardun a gaba na, toh babu inda zan motsa har sai na kammala abinda nakeyi, dama wa ya hana ki koyan motar?."
"Haba Umma ta, ni sam banason wannan aikin naki kullum cikin stress."
"Sai kizo ki sa ni ajiye shi ai, zaki tashi ki tafi ne kokuwa?."
Murmushi tayi tana miƙewa tsaye ta ja Akwatin ta tana faɗin "Toh Umma sai na dawo."
"A dawo lafiya ki gaida min dasu."
"Insha Allah" ta faɗa tana ficewa daga cikin falon.........
*************
......."Ughhh, am extremely tired and fed up with this fucking life, when ZEEYAD, when zaka bayyana ne?" ya faɗa kamar zaiyi hauka yana zagaye cikin gidan nasu tare da yin wurgi da duk wani abu da ya gani a hanƴar sa.
"Sooraj ana neman ka a waje?" cewar wani dogare yana idda shigowa cikin gidan nasu.
"You son of a bitch!" ya faɗa yana shaƙo wannan dogarin ya hau jibgar sa.
Ihu da ƙururuwar neman taimako wannan dogari ya fara dan kuwa ba ƙaramar shaƙa Sooraj da ya murɗe ya zama ƙato yayi masa ba.
"How dare you, har yaushe aka haife ka, yaushe ka girma da zaka dinga yi min magana garangatsai haka babu respect, sai na tabbatar na gyara muku zama dukkanin ku ɗaya bayan ɗaya, move your fucking legs out of here" ya faɗa yana yin ball dashi, kafin kuma ya biyo bayan sa ya fito a fusace dan ganin wane banzan ne ke neman sa.
Sadeeq ya gani tsaye cikin shigar sa ta alfarma, nan yace "This Asshole, naji labarin ance ya zama likita, yana ɗan talakawa but look at me, nida na riga sa fara makarantar wai yau shine ya zama wani, koh mai yazo yi a wuri na?" ya faɗa yana ƙarasawa gaban Sadeeq ɗin ya tsaya.
Nan yace "Kai ne kake nema na, mai ya kawo ka toh, bayan kai ba aboki na bane."
Murmushi Sadeeq da ya zama Handsome guy kamar ka ɗauke shi ka gudu yayi yace "No, bakomai nazo ne kawai na tunatar maka da cewa a yau ZEEYAD ya cika shekaru goma da 6ata, sannan kuma har yanzu ba'a san inda yake ba koh labarin sa babu, sannan kuma na tunatar maka da cewa kaima ka kusa yin shekaru goma a wannan wuri, nazo ne na tunatar maka in case idan ka manta kokuma kanason throwing party shine nazo na tunatar maka idan ka tashi shirya liyafar kada ka manta da gayyata ta a matsayi na na aminini ga ZEEYAD."
Sosai Sooraj ke huci kamar ya haɗiyi bishiya yace, dan kuwa dama Sadeeq yazo ya ɗura masa baƙin ciki ne kuma yayi nasara.
"Kai har waye kai, kai har ka isa kazo nan gaba na ka faɗamin maganar banza?" ya faɗa kamar ya buge Sadeeq ɗin yana kukan kura.
"Ni ba kowa bane, sai dai inaso ka sani a yanzu ni na fika nesa ba kusa ba, then just imagine a wane matsayi ZEEYAD yake yanzu indai har ni na kai wannan matsayin."
"Noooooooooo" ya faɗa cikin ihu kafin yace "Ƙarya kake ɗan matsiyata, ZEEYAD ba zai ta6a zama wani ba bai isa ya kai wannan matsayin ba, dan kuwa na tabbata har yanzu takalmin ƙafa ta ta fisa daraja, idan ya isa ya dawo nan indai har ya zama wani abu, maganar banza ma kake faɗi dan kuwa ZEEYAD ya daɗe da mutuwa."
Murmushi Sadeeq yayi dan dama abinda yakeso kenan, ya ɗurawa Sooraj baƙin ciki kuma yayi nasara, nan yace "Kana ganin ba zai dawo bane?, kada ka damu tunda har ka iya haƙurin shekaru goma kana jiran dawowar sa ai kamar yau ne zakaga ya dawo, what's the haste for?, anyways ni nan bari naje na duba jikin mai Martaba, dama nazo na duba ka ne kawai naga ya kake, and yes kada ka manta ZEEYAD ya cika shekaru goma yau incase kanason haɗa liyafa" yana faɗin haka yayi murmushi ya wuce.
Sosai Sooraj ke huci idanun sa sunyi matuƙar yin jaa, fuskar nan a cunkushe yana fitar da wata iriyar huci yace "Koh da abinda wannan wawan ya faɗa ya tabbata dagaske ne, toh na rantse ZEEYAD ni ne ajalin ka.".................
_*MUJE ZUWA......YANZU WASAN ZAI FARA😅*_
*Ba kwa comment koh?😩, Allah zanyi fushi ba zan sake typing ba sai bayan 2weeks😒*
*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Masha Allah Readers sun roƙeni alfarmar na dinga yi musu post sau biyu a rana😃, insha Allah zan ƙoƙarta sai dai banyi muku alƙawarin zaku dinga samun pages biyu kullum a rana ba, haƙiƙa kun matuƙar nuna min Ƙauna a wannan littafi na ZEEYAD dan haka nima dole na faranta muku, Allah Ubangiji ya bar Ƙauna tsakanin mu, yayi wa rayuwar albarka🥰❤️ , Ku dinga suburbuɗo min zafafan comments nikuma na cigaba da suburbuɗo muku post ɗin 2pages kullum Non-stoppable💃🏽🤘🏼😂_
*014...*
..............Da sallama ɗauke a bakin ta ta ƙarasa shigowa babban falon gidan, sai dai babu kowa a ciki.
Wuri ta samu ta zauna tana ajiye akwatin ta a gefen ta.
Ji tayi an rufe mata ido ta baya, murmushi ta saki tana kai hannu ta ta6a na wanda ya rufe mata fuskar.
"Wanene" ta faɗa cikin sweet calm voice ɗin ta.
Shiru akayi ba'a bata amsa ba nan ta sake cewa "Please wanene?."
"Yeeehhhh, nice bata gane ni ba" faɗin budurwar da ba zata wuci sa'ar MADEENAH ba tana buga tsalle, kafin tazo ta rungumo ta tace "You're welcome sis, yau dai gaki nan a gidan mu yin hutu, amma mu kullum sai dai muje ke bakya zuwa."
Murmushi tayi tace "Ina zuwa mana, ba gani nazo ba
yanzu."
"Ba wani nan, ai nasan ba yin kanki bane, Anty ce ta tilasta ki."
"Shikenan toh tunda baki yarda ba" ta faɗa to cut the conversation short, dan kuwa sam batason surutu da yawan magana, ga kuma ƴan matan gidan nan ɗin ba dai surutun tsiya ba, shiyasa sam batason zuwa, tafison rayuwa ita kaɗai kawai tayi ta tunanin sa.
"Ku jita wai ita a dole batason surutu."
"Ina Mami fah?."
"Mami ta fita ungwa, zo muje na kai miki akwatin naki ciki" ta faɗa tana miƙewa tsaye ta kamo hannun MADEENAH.
Babu musu ta tashi ta bita zuwa ɗakin nasu.
Kayan akwatin ta ta jere mata a cikin ƙaton wardrobe ɗin ɗakin kafin ta ɗaura akwatin a sama.
Wata budurwa ce ta fito daga Bathroom da alamu wanka tayi ta fito, ganin MADEENAH yasa ta daka tsalle cike da farin ciki tana rungume ta tace "Yau wa nake gani a gidan mu, kodai mafarki nakeyi ne" ta faɗa tana murza idanun ta.
"Wace kuwa idan ba DEENAH ba" cewar ɗayan.
"Amma tare suka zo da Anty koh?."
"Ita kaɗai, bakiga harda akwatin ta ba."
"Dan Allah kice kwana zamuyi?."
"2weeks Umma tace nayi muku na komo" ta faɗa tana kallon su cikin murmushi.
"Kai sis 2weeks, sai kace nan ɗin ba gida ba?."
"Ke bakisan MADEENAH da baƙin hali ba kenan, sam batason shiga mutane, kullum tafison ke6ewa ita kaɗai, tayi ta rubuta emotional waƙoƙin ta n da ta saba, ni dan Allah ɗan rera min ɗaya ma naji daga ciki" ta faɗa tana zama kusada ita.
Murmushi tayi tace "Ni ki rabu dani dan Allah, ba zanyi ba" ta faɗa tana sunce rolling ɗin kanta.
Shafa dogon gashin kanta ɗayar tayi tace "Kekam DEENAH yaushe ne zaki fara kitso a rayuwar ki?."
"Ke ki rabu da ita taga gashin baya zubewa ne shiyasa take iskanci, ni da nawa ya fara ƙwaiƙwayewa ta ƙeya ai tuni na nemi gidan kitso."
Haka nan suka cigaba da hirar su DEENAH bata tanka musu ba, sai ma ficewa kawai da tayi ta bar musu ɗakin.................
********************
...............Zaune yake cikin ash color ɗin sport wears wanda suka bayyanar da fararen murɗaɗɗun muscles ɗinsa, wanda da alama bai daɗe da idda motsa jiki ba, fuskar nan tasa manne da baƙar shade, inda hannun sa ke riƙe da mug ɗin coffee kafafun sa kan table ɗin gaban sa yana sipping a hankali.
Yatsun hannun sa na hagu ya fara tausawa a hankali suna bada ƙara kan kuma ya duba rolex watch ɗin dake manne a wrist ɗinsa yana duba time.
9:00am yake da meeting and yanzu bakwai ta ɗan wuce, hakan yasa shi ajiye mug ɗin hannun sa yana tashi tsaye tare da zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa yana tafiya cike da muguwar ƙasaita.
Fresh korayen shukoki ne zagaye da wurin kala daban-daban inda sukayi mugun ƙawata wurin sosai.
Tsaya faɗin haɗuwa dama kuma tsaruwa irin na wannan gida 6ata lokaci ne, dan kuwa haka take mansion guda wanda daga gani ba ƙaramin kuɗi aka zuba mata ba.
Cikin katafaren falon ya shigo kafin kuma ya nufi left handside ɗinsa ya haura stairs.
A bakin ƙofar wani ɗaki ya ja ya tsaya kafin kuma ya tura ta ya shiga, ɗakin akwai duhu sai dai ba sosai ba tunda ana iya ganin abubuwan dake ciki.
Wasu abubuwa ne kamar standing boards haka suke a tsaye kowanne rufe da farar kyalle, wanda aƙalla zasu kai ashirin koh sama da hakan.
Tsayawa yayi yana bin kowanne da kallo kafin kuma idanun sa su faɗa kan ɗaya dake ta hannun damar sa.
A hankali ya taka zuwa wurin kafin kuma ya sanƴa hannu ya yaye farin kyallen dake rufe dashi, take kuma kyakkyawar hoton ta ya bayyana fuskar ta ɗauke da murmushi.
Sai dai shi wannan ba zaka ta6a ce masa zane bane sabida yadda fuskar ta ta fito sosai, kamar ita aka ɗauko aka manna jikin board ɗin.
Yatsar sa ya kai yana shafar dimple ɗin ha6ar ta trying to get rid of all the old memories da suka riga da suka wuce.
"Atleast yakamata yau ka faɗamin wacece yarinƴar nan dama kuma matsayin ta a wurin ka" ya jiyo an faɗi hakan ta bayan sa.
Sosai fuskar sa ya sake tamƙe ta jin muryar ta, nan ya juyo gareta yace "What are you doing here?."
Kyakkyawar budurwa ce fara wanda daga gani kasan hutu da Naira sun zauna mata.
Murmushi tayi tana ƙarasowa wurin sa tace "Ni ɗin, har sai na nemi izinin shigowa cikin gidan ka kenan?, we are in a relationship so zan iya shigowa cikin gidan nan duk sadda naga dama."
Juyawa yayi tare da ɗaukar farar kyallen yana shirin rufe hoton ne ta sake faɗin "Yakamata yau ka faɗamin wacece yarinƴar nan, sannan kuma maiyasa kake son zana ta a duk sadda kake zaune?."
"That is non of your business."
"Really, but why dama baikamata ace nasan komai game da kai bane?."
"Bakisan komai game dani ba Surayya, so just ki tsaya a matsayin ki."
"What do you mean, a matsayi na ta budurwar ka dama baikamata nasan komai bane?."
Shiru yayi ya rufe hoton ya fice daga ɗakin ya bar ta nan tsaye.
Mara masa baya tayi zuwa cikin tafkeken falon tare da kiran sunan sa "ZEEDAN?."
Tsayawa yayi nan ta ƙaraso gaban sa tace "Maiyasa kakeyi min haka ne duk sadda nayimaka maganar yarinƴar nan sai ka 6ata rai ka kama fushi dani?."
"Sabida babu ruwanki da sanin koh wacece ita, she mean nothing to me, Infact i hate her, so Stop disturbing your Peace and asking to know who she is, hakan ba zai amfane ki da komai ba."
"You hate her, but why?, she is such a cutie" ta faɗa cikin ɗan murmushi.
"That's non of your business" ya faɗa yana ra6a ta ya wuce.
Saurin shan gaban sa tayi, nan yace "What again?."
"Please yau ɗaya dai kam kazo mu fita shaƙatawa, it's been long da ka ɗauke ni muka fita, why are you behaving as if baka sona yanzu?" ta faɗa kamar wacce zatayi kuka.
"Don't say that, you know i love you and dan bamu fita tare ba that doesn't mean kiyi irin tunanin nan."
"Alright then, ka faɗamin yaushe ne zamu fita tare?."
Shiru yayi kafin kuma yace "On Sunday Evening."
"Wow that would surely be