Showing 57001 words to 60000 words out of 236327 words
a idanun sa, all this abin nan da yakeyi mata dan kawai ya ringa sanƴa ta a idanun sa ne, tun ranar da ya ɗaura idanun sa akanta idanun ta sukayi captivating nasa yakejin wani abu game da ita, but he can't just tell what it is, but now yayi realizing DEENAH is part of farin cikin sa ne, and now she is getting away of his hand.
Haka nan ya gama tsayuwar sa anan wurin ya juya ya koma ciki..............
**********************
..........Office ɗin Jafar ta nufa baya ciki hakan yasa ta zaman jirar sa.
Bayan kamar Mintina goma ya shigo, ɗagowa tayi ta kallesa fuskar ta na fitar da murmushi.
"Hey, you looks happy" ya faɗa yana samun wuri ya zauna.
Murmushi tayi tace "Yaya na basa Necklace ɗinsa and he was so very happy."
"Uhm i can see that, shiyasa kema kika kasance cikin farin ciki?."
"No, am just happy ne kawai dan na rabu da nauyi."
Murmushi yayi yace "Am so happy for you, atleast kullum zaki kasance cikin farin ciki yanzu."
Murmushi tayi tare da jinjina kai tace "Yauwa yaya ni zan koma gida yanzu, idan ka tashi dawowa ka tahomin da abin daɗi sannan ka saya min waya."
Idanu ya zaro cike da mamaki yace "Phone?."
Kai ta jinjina tana murmushi.
"So finally, kinyi deciding ki fara riƙe waya?."
Kai ta jinjina cikin murmushi.
Murmushi shima yayi yace "Alright, i would make sure na sayo miki brand new Phone na yayi."
"Thank you so much blood" ta faɗa cike da jindaɗi.
"Never mind dear."
"Muje ka saya min Ice-cream sai na tafi gida."
"Toh sarkin shan ice-cream, muje mu."
Miƙewa tayi daga zaunen da take, hannu ya sanƴa a kafaɗun ta kamar wasu abokai suka fice.........
***********************
...........Zaune take kan bed ɗinta da takarda da biro a hannu.
Nazarin abinda zatayi ta fara, kafin kuma cikin zazzaƙar muryar ta ta shiga rero waƙa tana rubutawa.
_I used to think that_
_I would never fall in love_
_And then you showed me_
_That you could be everything I want_
_I gave my heart away_
_They put it on a shelf_
_And took it down only to break it into pieces_
_And then you came around_
_Picked me up off the floor_
_You put me back together_
_I couldn't believe it_
_Let me get this straight_
_You don't want to date_
_You just wanna be someone I can always turn to_
_Right until the end_
_Can you say that again?_
_I'm sorry, I just wanna make sure that I heard you_
_I waited for you my whole life_
_You don't know what you mean to me_
_If you asked me to be your wife_
_I would turn around and say_
_You mean to tell me that_
_I could have you whenever I want_
_I could tell you that I love you when you love me too_
_No more waiting, forever our love_
_But I would wait all over again_
_If it means I get you_
_I never been more sure of the unknown_
_Just wanna show you how far my love goes_
_You mean to tell me that you feel the same?_
_Then, baby, I'm here to stay ehh_
_I can't believe that I found the one_
_Yeah, my search is done now_
_When you said to me_
_Will you be my wife for the rest of my life?_
_For better or worse_
_Baby, no, these ain't just words to me_
_So take me to your home_
_We'll be forever and ever_
_Every woman deserves a king_
_You mean the world to me,_ _yeah_
_We could be everything_
_Together just us_
_I waited for you my whole life_
_You don't know what you mean to me_
_If you ask me to be your wife_
_I would turn around and say_
_You mean to tell me that_
_I could have you whenever I want_
_I could tell you that I love you when you love me too_
_No more waiting, forever our love_
_But I would wait all over again_
_If it means I get you_
_I've never been more sure of the unknown_
_Just wanna show you how far my love goes_
_You mean to tell me that you feel the same?_
_Then, baby, I'm here to stay ehn_
_Anywhere in the world_
_I would go with you_
_(I would go with you, babe)_
_We could be anywhere in the world_
_As long as I'm with you_
_(As long as I'm with you, babe)_
_And I can't wait_
_No, I can't wait for you, babe (no, I can't wait)_
_I can't wait for your love (to be with you, baby)_
_For the rest of my days, yeah (for the rest of, rest of my days)......._
Knocking ɗin da taji a bakin ƙofar ɗakin ta ne ya sanƴa ta dakatawa tana maida duban ta kan ƙofar.
Ajiye takarda da Biron tayi tana miƙewa daga kan gadon ta sauƙo.
Zuwa tayi ta buɗe ƙofar nan taga Umma tsaye.
Murmushi tayi tace "Umma, yaushe kika dawo?."
"Ina zaki san yaushe na dawo, ace mutum kullum yana cikin ɗaki maƙale yawa sabuwar amarya, fito kizo kije cikin gari ki iyo mana siyayya gobe zamuyi baƙi" ta faɗa tana komawa.
Bin ta DEENAH tayi tace "Baƙi kuma ummi, su waye zasu zo?."
"Ke ni kinga banason surutu, ɗauko biro da takarda kizo kiyi list kada ki manta."
"Toh" kawai ta faɗa tana komawa cikin ɗaki.
Paper ta tsinka tare da ɗaukar biro ta fito.
Zama tayi kusada Umma tace "Umma mai da mai za'a saya?."
"Kiyi figuring abinda yakamata ayi musu kawai sai ki iyo siyayyar."
Tunani ta shiga yi kafin tace "shikenan toh, ki kawo kuɗin."
ATM Umma ta ciro ta miƙa mata tace "Ki sayo da Stock fish bamu dashi a gida kizo kiyi mana faten doya muci da rana."
"Toh Umma, bara naje na shirya" ta faɗa tana tashi ta shige ciki...........
********************
............Tsaye take a kitchen tana girki ƙamshi sai tashi yake, Umma ce ta leƙo tace "Ohh ni Faɗimatu, har yanzu abincin nan baiyi ba sai ƴunwa ta gama kwaƙule min ciki?."
"Umma saura kaɗan yanzun nan zaiyi."
"Toh ai shikenan, dan Allah dai kiyi sauri."
"Toh Umma" ta faɗa tana jujjuya abincin nata.
Bayan ta kammala ne ta zuba a cikin warmer mai kyau ta kai musu shi falo.
Komawa tayi ta ɗauko plate da spoon, kafin ta wuce fridge ta ɗauko musu ruwa da drinks.
Serving tayi a plate ta ajiyewa Umma nata kafin itama ta ɗeba akan plate ta fara ci.
"Umma" ta faɗa.
Ɗagowa Umma tayi ta kalle ta nan tace "Umma, ki canza min makaranta."
Kallon ta Umma take kafin tace "Maiyasa?."
"Ni makarantar baya burgeni, ki nema min transfer zuwa wani."
"Toh shikuma first semester ɗin da kikayi fah?."
"Umma nidai kawai banason makarantar ne, nafison kawai ki maida ni University banason Nursing ɗinnan" ta faɗa cikin tsuke fuska alamun dgsk bata so ɗin.
"Toh shikenan ai, bari yayan ki ya dawo."
Cike da jindaɗi tace "Yauwa Umma ta, shiyasa nake Ƙaunar ki."...........
*********************
*TWO WEEKS AFTER*
............Wayar ta dake ajiye kan Dressing mirror ɗinta ne ya hau ruri.
Da sauri ta shigo cikin ɗakin nata tana ɗagawa taga sunan dake yawo a jiki take fuskar ta ta sauya zuwa 6acin rai.
Har ta tsinke bata ɗaga, nan ta sanƴa wayar a silent dan kuwa tasan indai bata ɗaga ba, ba zai ta6a gajiya da kiran ta ba, musamman ma da yake bashida zuciya koh kaɗan, itakuwa sam batason hayaniya.
Ficewa tayi daga ɗakin tana 6ata fuska taje ta cigaba da gyare-gyaren da takeyi a falo.
Tana cikin gyarar ne Jafar ya fito daga ɗakin sa yace "DEENAH?."
Ɗagowa tayi ta kallesa nan yace "Maiyasa ana kiran ki bakya picking call?."
"Babu" kawai ta faɗa tana cigaba da aikin ta.
"Look DEENAH maiyasa kikeyin haka, atleast yakamata ki basa dama ku fahimci juna right?."
"Yaya ni nace banaso, ni banason sa ya daina kira na" ta faɗa kamar zatayi kuka.
"DEENAH, what's wrong with you, idan bakyason shi then waye kike so?, yakamata ki fahimce shi kinsan fah babu kyau wulaƙanci koh?."
Shiru kawai tayi ta tsaya tana kallon shi.
"DEENAH bansanki da haka ba, dan Allah ki saurare shi kinji?."
"Sabida kawai ka haɗa ni da Allah zanyi" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin ta.
Wayar tata ta ɗauka nan taga almost ten missed calls, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa.
Picking tayi tare da karawa a kunnen ta, ajiyar zuciya taji ya sauƙe tare da yi mata sallama.
"Wa'alaika salam" ta amsa a takaice.
"Ina ƙofar gidan ku" kawai yace tare da katse kiran.
Da wani irin mugun harara tabi wayar kamar ta fashe da kuka haka takeji.
Dogon Hijabin ta kawai ta zura tana ficewa daga cikin ɗakin.
Cikin gidan kawai ta fito taje wurin mai gadi gaisawa sukayi kafin tace "Tijjani dan Allah ka leƙa waje zakaga wani kace dashi ya shigo."
"Toh ranki ya daɗe" ya faɗa yana ficewa zuwa waje.
Ba'a jima ba ya dawo tare da wanda yaje ɗaukowa ɗin.
Kallo ɗaya tayi masa kawai ta kauda idonta kafin ta fara tafiya.
Murmushi yayi ya mara mata baya.
A tsakar gidan ta fito da plastic chairs ta ajiye da table, kafin ta koma cikin gidan.
Abubuwan ciye da sha ta jero masa akan tray ta fito fuskar nan tata a matukar tsuke.
Akan table ɗin ta ajiye, kafin taja ɗayan kujeran ta zauna.
Kallon ta guy ɗin yayi murmushi ɗauke akan fuskar sa, kyakkyawa ne babu laifi sannan kuma yana da ɗan haske ya haɗe cikin brown ɗin shadda sai zuba ƙamshi yake.
"Ina yini Hajiya?" ya faɗa yana kallon ta.
Tsaki taja a ranta jin ya kira ta da Hajiya "Lafiya" kawai ta amsa tana sake kauda kai tare da tsuke fuska.
"DEENAH, mai nayi miki ne haka kika tsane ni?."
"Ni ban tsaneka ba" ta faɗa.
Murmushi yayi yace "Amma gashi nan bakya son gani na, kuma idan na kira ki bakya son ɗagawa, haka ma idan nayi miki magana ta whatsapp bakya replying, i don't know why."
Shiru tayi kafin tace "Banida lokaci ne."
Murmushi yayi yace "Please DEENAH na roƙeki da Allah ki bani dama na gwada miki sirrin dake cikin zuciya ta, i fell inlove with you at first sight, tun ranar nan da na ganki naji na kasa samun nutsuwa a raina, dan Allah ki bani dama nikuma nayi miki alƙawarin ba zakiyi regretting damƙa min zuciyar ki ba."
Shiru tayi bata basa amsa ba, dan kuwa koh muryar sa haushi take bata bale kuma tace zata kula sa.
"Please DEENAH, ni mai ƙaunar ki ne tsakani da Allah, ki bani dama nikuma nayimiki alƙawarin shayar dake farin ciki, DEENAH kaso mai sonka yafi kaso mai ƙin ka."
Shiru tayi kafin kuma tace "Naji, bakomai na baka dama, ka shayar dani farin ciki kamar yadda ka faɗa ɗin."
Murmushi ya sake cike da farin ciki ya hau yi mata godiya.
"Kada ka godemin tukun, ka bari har sai na fara sonka kamar yadda kake sona kafin ka godemin sannan kuma kayi farin ciki."
Kai ya jinjina yace "Insha Allah wannan ma ba zata gagara ba, insha Allah zaki soni kamar yadda nakeson ki, sai dai fah idan kin tashi sona ɗin kada kiyimin wanda zai zarce wanda nakeyi miki, idan ba haka ba kuma babu ruwan Abdul."
Ji tayi wani irin haushi ya turnuƙe ta "Allah ma ya kiyaye, sai anjima" ta faɗa tana tashi ta koma ciki.
Da kallo yabi ta tare da yin murmushin farin ciki kafin kuma shima ya miƙe ya tafi..............
*Kun ganshi kaɗan koh?, zan cigaba anjima*
*Yawan Commew, yawan Typing*
*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*020...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
..............Zaune yake idanun sa akan fakeken plasma TV ɗin dake manne jikin bangon office ɗin nasa, kallo kawai yake sai dai sam tunanin sa da hankalin sa na wani wurin daban.
Sosai fuskar sa take matuƙar ɗaure yawa wanda yaci guna.
Ƙofar office ɗin ce ta buɗe wani ya shigo hannayen sa riƙe da wasu documents.
"Good afternoon sir" ya faɗa.
Hannu kawai ya ɗaga masa alamun amsawa ba tare da ya juyo ya kallesa ba.
Rissinawa yayi yace "Sir, ga nan files ɗin nan komai ya kammala, sa hannun ka ne kaɗai ya rage" ya faɗa cikin tura masa files ɗin.
"Alright" kawai ya faɗa ba tare da ya ɗago ɗin ba.
Rissinawa ya sake yi tare da ficewa daga cikin office ɗin.
Idanun sa ya maida ya lumshe yana ɗan jujjuyawa akan kujerar da yake gefe da gefe.
Karar buɗewar ƙofar da ya sake ji ne ya sanƴa sa buɗe idanun sa, inda fitinannen turaren ta ya dako masa hanci.
Sanƴe take cikin jan riga da black trouser wanda sukayi matuƙar amsar jikin ta tare da bayyanar da duk wata sura ta jikin ta, fuskar ta manne da ƙatuwar baƙar shade bakin nan nata ya sha red lipstick sai yalƙi yake, kyakkyawa ce sosai.
"Hello honey" ta faɗa.
Bai ɗago ya kalle ta ba sai ma yi da yayi kamar baisan da wanzuwar ta ba a wurin, dan kuwa a yanzu yaji yayi mugun tsanar ta, sai dai har yanzu taƙi rabuwa dashi yana ɗaga mata ƙafa ne kawai domin mahaifin ta.
Kujera taja ta zauna tana kallon sa tace "Honey?."
Juyo da kujerar yayi ya zamto yana fuskantar ta.
Kallon da yakeyi mata ne ya sanƴa ta shan jinin jikin ta, sai dai da yake gogaggiya ce ita ta dake tana sake gyara zamar ta ba tare da ta sake kallon sa ba, dan kuwa a duk sadda yakeyi mata wannan kallon bata ta6a iya haɗa idanu dashi komin iskancin ta, dan kuwa da zarar ta haɗa idanu dashi zataji ba zata iya yi masa komai ba, shiyasa duk wani abu da zata yi masa sai dai ta kalli fuskar sa ba dai cikin idanun sa ba.
Wani abu ya danna, cikin abinda bai wuci minti.ɗaya ba ƙofar ta buɗe Secretary ya shigo.
"Yes sir" ya faɗa cike da girmamawa.
"Get her out of my sight" kawai ya faɗa yana komawa ya jinginu da kujerar da yake kai tare da lumshe idanun sa.
Magana Secretary zaiyi mata nan ta wani daka masa tsawa tare da wurga masa harara tace "Notin kanka ya kunce ne, yace ka fitar dani daga nan kuma dayake bakada kunƴa sai kuma kace zaka buɗi baki kacemin na fita, let's see uban wanda ya isa ya fitar dani daga office ɗinnan mtssswww" ta karashe cikin jan doguwar tsaki.
Shan jinin jikin sa Secretary yayi, dan kuwa mugun tsoron ta yakeji yasan koh kaɗan batada mutunci ba ƙaramin aikin ta bane yanzun nan ta tsitsinka masa mari tayi disgracing ɗinsa.
Duk abinda sukeyi ɗinnan ZEEDAN bai buɗe idanun sa ba.
"ZEEDAN, kai ne yakamata ka fitar dani ba wannan ƙasƙantaccen ba" ta faɗa tana wurgawa Secretary muguwar harara.
Buɗe idanu ZEEDAN yayi lokacin da yaji ta ambaci ƙasƙantacce.
Tashi ZEEDAN yayi daga kan kujerar da yake tare da zuwa ya ɗauki coat ɗinsa akan hanger ɗin dake ajiye a office ɗin nasa ya sanƴa akan kayan sa tare da ficewa daga office ɗin.
Tashi tayi haɗi da wurgawa Secretary harara kafin taja doguwar tsuka ta fice tare da mara masa baya.
Tafiya take but koh ina na jikin ta na shaking, inda kuma kowa sai bin ta yake da kallo yana haɗiye ƴawu.
Lifter yake shirin shiga nan tayi saurin kiran sunan sa da ƙarfi "ZEEDAN?."
Cikin sauri ta ƙarasa wurin sa ta tsaya ta bayan sa tace "It's been a year kenan rabo na da Nigeria, but tunda na tafi outside dan gabatar da final exams ɗina koh ƙira na baka ta6a yi ba, a hakan kenan kake tunanin riƙe amanar da aka damƙa maka?."
Juyowa yayi gare ta yace "Babu wanda ya bar min amanar ki, stop deceiving yourself" ya faɗa cike da 6acin rai idanun sa na yin ja.
Hannu ta harɗe a ƙirji tace "Bakada ikon yi min tsawa ZEEDAN, yakamata ka girmama ni a matsayi na ta ƴa ga mai gidan ka."
Cize baki yayi yana kaɗa kai cike da muguwar taƙaici yayin da 6acin rai ke sake tsattsafo masa akan fuska dama kuma zuciya.
"Kada kuma ka manta da cewa we're getting ENGAGED next week, ZEEDAN koh kaƙi koh kaso ni Khairat sai nayi rayuwa da kai, kasan kuma maiyasa nace hakan?, sabida mahaifi na, ina da tabbacin ba zaka iya ja dashi ba sabida irin halarcin da yayi maka a rayuwa ya ciro ka daga tsumma ya maida ka cikakken mutum har ka zama abinda ka zama yau, ɗaya daga cikin manƴan Artist ɗin da akeji dasu a duniyar zane, ZEEDAN my love, ka daina 6atawa kanka lokaci sabida na tsani ganin wannan kyakkyawar fuskar taka cikin fushi dukda kuwa yana yi maka kyau sai dai ba ƙaramin tsorata ni yakeyi ba" ta faɗa tana kai hannu da niyyar shafo gefen fuskar sa.
Riƙe hannun nata yayi, sam dukan mace ba zai bada wani ma'ana koh armashi ba, idan ba haka ba babu abinda zai hana sa lakaɗawa Khairat duka a yanzun, sosai yaji daɗin nisan da tayi masa, but a yanzu da ta dawo dole ne ta zame masa ƙarfen ƙafa ta kuma hana sa sukuni, duk inda yaje tana biye dashi, duk macen da ta ra6e sa kuwa koh da ma'aikaciya ce babu abinda zai hana ta sanƴa guards ɗinta yi mata dukan cin mutunci, daɗi ɗaya zaiji na dawowar ta wato tayi maganin Surayya ma dake maƙale dashi kullum yawa chewing gum batason rabuwa dashi, but bayan wannan kuma babu wani abin so koh sha'awa tattare