Showing 21001 words to 24000 words out of 236327 words

Chapter 8 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45372

yau kika fara ganin bature ne koh miye" Cewar Yaron yana makar ƙeyarta.


Barin kallon sa tayi nan ya kama hannun ta suka wuce, dukda haka saida ta sake waigowa tana kallon ZEEYAD ɗin.



_"Yeah, babu tantama she must be a witch, who knows ma if she has an evil eye"_ ya faɗa a zuciyar sa yana kauda kai daga kallon ta.



Yarinƴa ce da ba zata wuce shekaru goma ba, ba baƙa bace sannan kuma ba fara bace ita, tana da wani irin kyau mai ɗaukar hankali, kyakkyawa ce sosai, hannun nata na riƙe cikin na yayan nata har suka 6ace wa ZEEYAD da gani bata daina kallon sa ba.


Sallama sukayi suka shiga cikin gidan mai ƙaramin ƙofa ne, amma babu laifi gidan da ɗan girman sa, sannan part biyu ne a ciki ɗaya na kallon ɗaya.


Mata matashiyar mata ce suka tarar tsakar gidan ta hura wuta a mukubur tana girki, sai dai ita ɗin fara ce sosai kamar yaron.



Yaron ne da ba zai wuce 13years ba yace "Umma kinga DEENAH har yanzu bata daina kallon mutane kamar ta samu TV ba koh?."



Ɗagowa matar tayi tace "Dama ai mai hali baya fasa halin sa, bari wataran ta samu masu yi mata duka zata dawo hayyacin ta ta daina ne, wuce ki cire uniform ɗin naki kici abinci kizo ki daka min wannan tarugun yanzu."


Wucewa tayi sum-sum ba tare da tace komai ba ta buɗe ƙofar net ɗinda akayi sa dan rufe barandar gidan inda kuma nan ne kayan kitchen ɗinsu ke ajiye a gefe guda, ɗayan gefen kuma ɗaku na ne guda biyu a jere.



Ɗayan ta shiga inda ya kasance bedroom ne ta hau cire uniform ɗin jikin ta.


Canza kayan nata tayi zuwa doguwar riga sannan tasa hula ta fito barandar.


Abinci ta ɗeba a plate kafin ta shimfiɗa tabarma ta buɗe ƙaramin fridge ɗin dake tsaye ta ɗau ruwa ɗaya.


Abinci taci Sannan ta fito ta kamawa Ummar tata aikin da ta sanƴa ta.


"Ki gama kije ki sayomin maggi a shagon Manu, nama manta Maggin ta ƙare.


Sai a sannan ta buɗi ɗan ƙaramin bakin ta tace "Toh."


Bayan ta gama ne Ummar tata ta bata Naira ɗari tace "Ki Sayomin maggin Ɗangote na hamsin star na Hamsin, kuma dan Allah ki ɗaga ƙafa ki dawo dawuri bance ki tsaya kalle-kalle ba."



Zuwa tayi ta sako Hijabin ta kafin ta sanƴa takalmin ta ta fice.



Tundaga nesa ta hango sa zaune inda suka gansa ɗazu,nan kuma ta fara aikin kallon nasa ga kuma sam bata sauri a tafiyar tata a hankali take tafiya har tazo ta wuce shi bai sani ba kasancewar kansa na kan guiwowin sa.



Sayo aiken tayi ta dawo nanma ta tarar yana nan har yanzun, lailaya ledar maggin hannun ta ta fara tana cigaba da kallon shi harda leƙe koh zata ga fuskar sa.



Ɗagowa yayi nan suka haɗa ido, mamaki ne ya cika ZEEYAD ganin kamar itace yarinƴar da ya gani da uniform ɗazu.



Kallon kallo suka shiga yi kowanne bai ɗauke idanun sa ba, ita tana yi masa kallon da ta saba yi ne idan taga mutane, shi kuwa kallon mamaki yakeyi mata wondering mai take nema a jikin sa.



Gasping tayi lokacin da ledar da take lailaiyawa ɗin ya fashe maggin ta zube a ƙasa.



Da kallo ya bita ganin yadda ta saki baki tana kallon maggin.



A zuciyar sa yace _"Ba abin ka taimake ta ba yanzu ta lashe maka ƙuruwa, Mayya"_



Hannu tasa ta ɗebi maggin ta sanƴa su cikin Hijabin ta kafin ta kallesa sannan tayi wucewar ta.


Sallama tayi ta shigo gidan tare da miƙawa Ummar tata aiken,tsaye kawai tayi tana kallon ta tsabar takaici ace a aiki mutum tunɗazu kamar wanda ba'a yi masa warning ba sai yanzu yake dawowa.



"Kin kyauta ai" kawai ta faɗa tana amsar maggin.



Zama tayi kan dakalin bakin part ɗin nasu tana kallon Ummar ta dake girki.


"Kinci abincin ne?" ta tsinkayo muryar Mahaifiyar tata.


Kai ta ɗaga mata kawai kafin kuma tace "Umma akwai wani almajiri a waje, na ɗau sauran abincin na kai masa?."


Kallon ta tayi tace "Ki duba idan yayan naki yaci nashi sai ki ɗauka ki kai masa."



Da sauri ta miƙe ta shige tare da buɗe tukunƴar abincin, juyawa tayi ga yayanta dake cin nasa abincin kafin kuma ta ɗau kula da murfin sa ta juye sauran a ciki ta ɗau cokali tare da ɗaukar ruwa ɗaya a fridge ta ɗaura akanta ta fito.


Mamaki ne ya cika mamar tace "Ke kuma ina zaki da kula?."


"Umma ai almajirin yana ta wurin islamiyyar mu ne zan kai masa ya juye sai na dawo da kulan."


"Yi sauri toh karki daɗe,kinga dai Magrib ta gabato koh?."



Ficewa tayi da sauri dan kar ya tashi ta isa gareshi.



Tsaye tayi a kansa tana kallon sa ba tare da tace komai ba.


Ɗagowa yayi jin kamar tsayuwar mutum akansa, it's that same girl dai.



Bai san sadda ya haɗe rai murtuƙ ba yace "What?."



Kular abincin ta miƙa masa ɗauke da ruwa a kai, da kallo yake bin kular hannun nata da kallo nan yace "No thanks" ya faɗa yana kauda kai daga kallon da take masa.


Sake tura masa kular tayi, nan ya ɗago ya kalleta yace "I don't trust you, so i won't eat this food, take it away."



Sake tura masa kular tayi kamar zata sa masa a baki,a fusace kuma cikin tsawa yace da ita "I said i don't want it."


Da mugun tsoro taja baya jin yadda yayi mata maganar ransa na 6aci wanda ya sanƴa ta yar da kular hannun nata abincin ya zube.


Da mugun kallo ya bita kafin kuma ya tashi yana ɗaukar ledar sa ya barta nan tsaye kamar zatayi kuka...............




*Babu Posting On Week days*




*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*009...*





_So i decided nayi posting yau ganin yadda kuke ta tambayar ZEEYAD, So here is he now, enjoy😉_




_Banyi editing ba_




.............Hannu tasa ta ɗau kular ta kafin ta bisa da kallo idanun ta na tara hawaye.


Tafiya ta fara nan taji yace "Hey."



Tsayawa tayi tana kallon sa daga inda yake zaune nan yace da ita "Am sorry" dan kuwa yaga kamar ranta ya 6aci, shi kuma ba zai so ya zamto sanadiyyar 6acin ran wani ba dukda kuwa taimakon sa tayi niyar yi sai dai yayi alƙawarin ba zai sake yarda da wani ba a rayuwar sa dan kuwa duk gur6atattun mutane yake haɗuwa dasu, ita ɗinma kallon mayya yake yi mata dan kuwa bai yarda da cewa wannan kallon nata na lafiya bane.



Juyawa tayi a hankali kawai ta cigaba da tafiyar ta dan kuwa ta fahimci mai yace mata, haƙuri ya bata dan haka sai taji ta daina fushin ta nufi gida.



Shigar ta gidan aka shiga kiran sallahr Magrib, dan haka buta ta ɗauka tayi alwala sannan ta shige ciki.



Ɗayan ɗakin ta shiga inda ya kasance falo ne masha Allah mai kyau dashi babu laifi sai tada ƙamshin turaren wuta mai daɗi yake.



Sallaya ta ɗauka ta tada sallah tana cikin yi Ummar ta tazo itama ta tada nata sallahn kusa da ita.



Suna idarwa sukayi addu'o'i kafin Mahaifiyar tata ta kar6i haddar karatun da take ɗaura mata a gida,kuma Alhamdulillah duka ta kawo su daidai.


Murmushi mahaifiyar tata tayi dan kuwa Allah ya bata ƴaƴa masu albarka, ilimi dama kuma kaifin basira nan tace "Masha Allah, Allah yayi miki albarka DEENAH ta."


"Aameen Ummah na" ta faɗa tana sakin murmushin jindaɗi wanda ya sanƴa dimple ɗin ha6ar ta lotsawa.


Basu tashi a wurin ba sai da sukayi sallahr Isha'i, ta sake ɗaura mata wani karatun a lokacin kuma yayan DEENAH ɗin ya dawo shima daga masallaci yazo ya jona su.


Nan shima aka kar6i tasa haddar inda ya kawo ta dai-dai, hakan ba ƙaramin faranta ran mahaifiyar su yake ba, dan kuwa Allah ya cika mata burin ta da ya bata ƴaƴa masu albarka, tarbiyya dama kuma nutsuwa.


"Allah yayi muku albarka" ta faɗa.



Amsawa sukayi da "Aameen" kafin kuma ta haɗa litattafan karatun cikin wani jaka tace "Jafar kai Jakar ɗaki bari na zubo mana abinci koh?."



Cikin girmamawa yace "Toh Umma" kafin ya ɗau jakar ya fice zuwa ɗaki ya kai ya ajiye sannan ya dawo falon ya zauna.



TV ya kunna ya kai tashar Cartoon Network inda aka sanƴa film ɗin *Tom and Jerry*, nan duk suka gyara zama suna kallo fuskar su na fidda murmushi.



Shigowa tayi da ɗan madaidaicin tray mai kyau ta iyo musu serving ɗin jellof rice sai fidda ƙamshi da tururi yakeyi, ajiyewa tayi kafin ta fice ta ɗauko musu ruwa akan plate ta dawo.



"Toh ni kun cika min kunne da dariya, maza ku sauƙo kuci abinci."



Sauƙowa sukayi suka zauna tare da maida hankalin kan abincin suna ɗaukan cokali tare da yin bismillah suka fara ci.



Shiru falon ya ɗauka babu abinda kakeji sai Ƙarar hayaniyan TV ɗinda Tom da Jerry keyi.



Faɗo mata yayi a rai lokacin da take shirin kai cokalin abincin bakin ta, _"koh yanzu ya ci abinci?"_ ta faɗa a ranta dan kuwa taga kamar bashida kowa basuda gida.



Bayan sun idda cin abincin ne kuma Jafar ya kwashe kwanukan ya fitar baranda ya ajiye a robar kayan wanke-wanke, sannan suka cigaba da kallon su dukkan su inda Ummar su kuma ta fice zuwa ɗaki.



Kallon sa tayi tare da matsowa kusada shi tana ta6a sa tace "Yaya."



"Miye?" ya faɗa yana kallon ta.


"Yaya kaga wannan ɗin nan na ɗazu?."


"Waye?."


"Wannan mai kama da indiyawan da muka gani ɗazu ɗinnan."



"Ni nasan miki shi" ya faɗa yana maida hankalin sa kan TV.


"Yaya har kacemin na daina kallon sa."


"Eh natuna, menene?."


"Ɗazu ma da Umma ya aike ni sayan maggi ai na ganshi a wurin zaune, kuma shine wanda na kaiwa abinci."



"Toh sai akayi yaya kuma dan kin kai masa abinci?."


"Naga kamar bashida kowa kuma basuda gida."



"Ke kam ina ruwan ki dashi, wallahi gara kin shiga taitayin ki dan yanzu ba kowa bane abin yarda kin dai ga yadda ake ta sace yara koh?."



Manƴan Idanun ta ta zaro jin abinda ya faɗa,nan ta koma wurin zaman ta tana cigaba da tunani har bacci ya ɗauketa a wurin.



6angaren ZEEYAD kuwa Kan Varender ɗin islamiyyar ya samu ya kwanta, dukda uban sauron dake cizon sa haka nan yayi haƙuri har gari ya waye.



Gindin bishiyar nan dai ya sake komawa ya zauna yana ganin fice da shigen ɗaiɗaikun mutane da alama dai aiki zasu.



Yana nan zaune har takwas na safe kafin kuma ya fara hango zuwan yara da irin kayan islamiyyar jiya.



Sai a sannan kuma ta faɗo masa a rai nan yace "That witch must be on her way."



Mintina talatin mai kyau bai ƙara a zaune ba sai gata sun shawo kwana itada yayan ta.



Kallon ta yake dan yaga kamar bata gansa ba yau ɗin kafin kuma ya kauda kansa yana yatsine fuska.



"Assalamu Alaikum" yaji muryar yaro yayi masa sallama, ɗagowa yayi ya amsa da "wa'alaika Assalam" yana kallon Jafar.



Jakarsa ya buɗe ya ciro Wata ƴar ƙaramar lunch box yana miƙa masa yace "My sister asked me to give you this."



Da kallo yabi Jafar ɗin dashi kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "Jazakallahu Khair."



"Aameen" ya amsa kafin kuma ya ciro ruwan pure water biyu ya ajiye masa sannan ya juya ya tafi.



Da kallo ZEEYAD ya bishi kafin kuma ya maida duban sa ga kular yace "Wato dai basuda wata hanƴar da zasu yaudare ni sai wannan, No i won't easily fall into their trap" ya faɗa yana maida abincin gefe.


Misalin sha biyu suka fito break inda kuma kowane yaro ya fito da lunch box ɗinsa yana cin abincin sa, yayin da wasu ke ta wasan su.


Wucewa tazo yi zata koma gida, nan tagan sa kwance yana bacci yayin da lunch box ɗin ke gefe a ajiye.



Lalla6awa tayi taje ta bayan bishiyar tare da ɗaukar ganƴen maina ta zuge Leaves ɗin jiki sannan ta shiga sanƴa masa a kunne tana yi masa tafiyar tsutsa dashi a fuska.



Saurin kawo hannun sa yayi yana korarwa dan kuwa ya ɗauka koh wani ƙwaron ne.



Dariyar dake son kawo mata ta gimtse tana toshe bakin ta.



Sake kai tsinken tayi a karo na biyu tana sosa masa kunne.



Hannu ya sake kaiwa da sauri ya buge yana korarwa da hannun sa.



Gimtse dariyar ta tayi sai da tayi mai isarta kafin kuma ta sake kai tsinken saitin fuskar sa zuwa hancin sa.



Furzar da hanci ya fara yana goge fuskar sa, dariyar ta da ta kusan fitowa fili ta gimtse,kan kuma ta sake kai tsinken a karo na huɗu.



Caraff ya cafke hannun nata yana buɗe idanun sa, idanu ta waro kafin ta fara jan hannun nata sai dai ta kasa ƙwata.



"Kayi haƙuri dan Allah" yaji ta faɗa cikin zazzaƙar muryar ta



Jawo ta yayi ta fito daga bayan bishiyar nan yace "Ke kika san abinda kike faɗa, what are you doing here?" ya faɗa cikin tsare ta.



"Bakomai fah...nothing."



"Ohh zuwa kikayi ki lashe ni, dama nasan shiryawa kukayi dake da wancan yayan naki dukda dai naga kamar shi salihi ne Unlike you da nake tunanin mayya ce."



Sosai idanun ta yayi zuru-zuru, bata ta6a tsokalar wani koh wata ba sai akansa gashi kuma asirin ta ya tonu dan itama batasan maiyasa taji tana son aikata masa hakan ba.


"Your eyes are so large and Scary, you Look exactly like a 100years witch, who even knows if you're one, what do you want from me?" ya faɗa yana cika hannun nata.


Kallon sa kawai take idanun ta na tara hawaye dan ta fahimci zagin ta yakeyi dukda abubuwa kaɗan kaɗan take tsinta cikin maganar tasa, tasan miye ma'anar witch kenan mayya ya ɗauke ta kenan.



"Take this i don't want it, Okay?" ya faɗa yana ɗauko kular Lunch box ɗin ya dire a gaban ta sannan yace "Get out of here."



Buɗe kular tayi nan taga bai koh buɗe abincin ba balle ya ta6a, doya ne soyayye da kwai sai yaji a gefe, ɗaya ta ɗauka tare da yin bismillah ta kai bakin ta ta fara ci.



"Oh girl, i have escaped millions of traps before, so what made you think that your silly plan would make me fall for your stupid trap?, get out of here, i don't want to see your face."



Da watery eyes ɗinta kawai take kallon sa hakan ya sanƴa shi kauda fuskar sa daga kallon ta yana jin kamar ya make ta nan wurin dan haushi da takaici.



A haka ta gama cinƴe abincin ta ta tashi tayi hanƴar islamiyyar su zuciyar ta babu daɗi, sabida taga kamar bayason taimakon ta.



Da kallo ya bita yana furta "Thank GOD" kafin kuma ya koma yayi kwanciyar sa.



Yau ma da yamma bayan an tashe su daga islamiyya yana nan zaune inda yake suka zo wucewa itada Jafar.



Ɗauke kansa yayi daga kallon da takeyi masa nan Jafar yace da ita "Ke dallah wai ba zaki daina kallon shi bane?."



Ɗauke idon ta tayi tana maidawa kan Jafar ɗin nan kuma yace "Ni bance ki kalle ni ba, cewa nayi ki daina kallon sa" ya faɗa yana kama hannun ta suyi gaba da sauri.



Kamar kullum sallama sukayi suka shiga gidan nan suka tarar da Ummah su tsaye da wani mutumi, take kuma fuskar Jafar ya canza yana 6ata rai, kamar jiran su yake nan yace "Yauwa kuma wadannan gantallallun yaran naki suma kisan yadda zakiyi dasu, indai ba zaki biya ni kuɗin haya nan da ƙarshen sati ba toh ki tabbata kinsan inda dare tayi miki" ya ƙarashe cikin kumfar baki.



Shiru Mahaifiyar tasu tayi tana sauraron sa kafin kuma tace "Dan Allah Alhaji kayi haƙuri, ka ƙaramin zuwa ƙarshen wata insha Allahu da zaran an biya albashi zan tabbatar da na baka kuɗin ka a cike, ai ba sai ka tona min asiri a gaban yara ba, kuma dan Allah ka daina aibata min ƴaƴa dan kuwa bakasan wahalar da nasha wurin tarbiyantar dasu ba, indai kuɗin ka ne insha Allah nayimaka alƙawarin biyan ka zuwa nan da ƙarshen wata."



"Oho dai koma dai menene ki tabbatar da kin tanadi kuɗin nan dubu goma sha biyar cir tun kafin na haɗa ki da hukuma wallahi, haka kurum kaida haƙƙin ka ka riƙe a hana ka" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗayan part ɗin ya shige.



Nan tace "Haƙƙin marayu dai, koh ka manta ne?."



Nan ya dawo da wuri yace "Mai kika ce?."


Bata kula sa ba ta haɗa kan ƴaƴan ta tace "Muje."



Nan suka shige part ɗinsu suna rufo ƙofa,kwafa yayi yace "Zamu gamu ne" yana komawa ciki.



"Umma wa maiyasa kawu Sale yake yi miki haka ne, koh dama ba Abban mu bane ya gina gidan nan?."



"Toh nikam ya na iya ne dashi dan Allah Jafar, ai dama idan mutum yafi ƙarfin ka kawai ka kai kukan ga Allah shi zaiyi maganin azzalumai, idan ni banida yadda zanyi na kwato muku haƙƙin ku da dukiyar ku da ya cinƴe ai akwai Allah kuma yana ganin komai, shine wanda zai kwatar muku sabida babu wanda yafi ƙarfin sa, kuje ku ɗau abincin ku kuci" ta faɗa tana ficewa zuwa ɗaki ta barsu nan falon idanun ta na tara hawaye.



Da kallo duk suka bita suna mai jin tausayin Mahaifiyar tasu matuƙa a zuciyar su, dan kuwa ba ƙaramin ƙoƙari takeyi akansu ba na ganin ta inganta rayuwar su, tana iya sadaukar da komai nata akansu burin ta shine rayuwar su ta inganta tayi kyau, bata ta6a barin su sunyi kukan rashin uba ba, itace ta zame musu Uwa sannan kuma Uba, duk wani abu da Uba yakamata yayi itace keyi musu dukda kuwa ɗan uwan mahaifin su na raye sai dai babu abinda yakeyi musu, dukiyar da Mahaifin su ya bari ma yayi nake-nake akai a cewar sa zai kula da rayuwar ƴaƴan da ya bari, wanda hatta gidan da suke ciki na mahaifin su ne ya gina ta sai dai dukda haka wai sai sun biya kuɗin haya, sannan daidai da Naira biyar bai ta6a kashe musu cikin wannan kuɗin ba, komai Mahaifiyar su ce keyi musu kasancewar tana aikin gwamnati kuma albashin ta babu laifi, dashi takeyi musu dukkanin buƙatun su kafin tayi na kanta, shiyasa suma suke burin wataran su girma su sanƴa mahaifiyar su farin ciki fiye da wanda ta basu.



Jafar ne yabi ta ɗaki dan kuwa yasan kuka takeyi, DEENAH kuwa kula ta ɗauka ta ɗebi abinci a ciki tayi ficewar ta.



Kwance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login