Showing 123001 words to 126000 words out of 236327 words

Chapter 42 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45313

abinda yake ƙara mata kullum sai 6acin rai.

"Miye hakan kikayi MADEENAH?" cewar Umma tana kamo bakin gashin.

Ra6a ta Umma tayi ta shigo cikin ɗakin, inda ta hau binsa da kallo ganin duk ta birkita kayan cikin closet nata ta zubo dasu, ga kuma gashin kanta da ta yanke nata yawo tsakar ɗakin.

"What the hell is this DEENAH, meke damunki ne haka?" cewar Umma tana fizgo ta.

"She is Depressed" cewar Jafar dake tsaye daga bakin ƙofa.

"What...mai kake nufi?" cewar Umma tana ƙarewa DEENAH kallo.

"Your daughter is depressed, and i hope you know that depression leads to death" ya faɗi hakan ne cikin muryar dake nuna shima haƙuri kawai yake da halin Umma ɗin.

Kallon DEENAH kawai Umma keyi ba tare da tace komai ba.

"Depression!, she is too young to suffer from depression, i mean she is not lonely."

"Ofcourse she is, you really think that zamu iya bata dukkanin farin cikin da take buƙata ne, you took someone very important away from her, and you expect her ta wanƴe lafiya ba tare da ta faɗa cikin wani hali ba, you're the cause of everything dake faruwa da DEENAH Umma, maybe idan ta mutu nan ne zaki fahimci kuskuren da kika tafka" ya faɗin hakan cikin muguwar 6acin rai kafin kuma ya fice daga ɗakin.

Fizge hannun ta DEENAH tayi daga riƙon da Umma tayi mata tana barin mata cikin ɗakin.

"DEENAH!, DEENAH?" ta faɗa tana mara mata baya.

Riƙo ta tayi tana shirin ficewa daga falo tace "Ina zaki?."

Kallon ta kawai DEENAH keyi ba tare da tace komai ba.
"Talk to me mana" ta faɗa tana kallon ta.

Shiru tayi mata haka ma bata daina kallon ta ba.

Rungumo ta Umma tayi jikin ta ta hau bubbuga bayan ta.
"Am so sorry Sweetheart, ki yafemin kinji?, i did all this for your own good, but kunƙi ku gane hakan keda ɗan uwanki."

Kwace jikin ta DEENAH tayi tana komawa cikin ɗakin ta ta sake sanƴa masa key.

Kunnen ƙashi tayi tare da ignoring dukkanin kiran da Umma keyi mata har ta gaji ta daina.



**************************



__________"So Grandma as i was telling you, the girl isn't actually my patience and ba ƴar nan ƙasar bace, she is sick aka kawo ta nan treatment, ina yawan ganin ta da wasu nurses suna fitar da ita zuwa motsa ƙafa, and i fell inlove with her, and now i don't know yadda zan sake haɗuwa da ita so i have to wait har sai sun dawo check-up, it's been a month kenan da ƴan sati kenan tun bayan komawar su i have to wait for another month da ƴan sati akai kafin na sake sanƴa ta cikin idanu na, my biggest fear is that kada tace batasona while nikuma nake kwana da ita kullum na tashi da ita, actually Grandma i never thought zan iya son wata yarinƴa kwatankwacin yadda nakejin sonta a raina, the girl is amazing, beautiful and above all she is decent, calm and has an innocent cute face, shine abinda ya birgeni tattare da ita Grandma, i really love her Granny" ya faɗa yana lafewa jikin kujerar da yake kai yana mai lumshe idanun sa.

Murmushi kawai Grandma take tunda ya fara bata labarin DEENAH, she is happy for him dan kuwa tamkar yadda ta ɗauki ZEEYAD haka ta ɗauki YAZEED, sai dai halin mahaifiyar YAZEED kaɗai ya isa ya sanƴa ka 6oye irin ƙauna da kulawar da kake yi masa, dan kuwa yanzu sai ta fassara mutum tace ana ƙoƙarin kashe mata ɗa ne koh wani abin, hakan yasa Grandma take ɗan rage wasu abubuwan daga cikin ƙaunar da takeyi masa.

Grandma ce tace "Zanso kuwa naga wannan yarinƴar, dan tunda har ka iya faɗawa tsananin tarkon sonta haka i know ta tara dukkanin qualities ɗin da ake buƙata wurin mace ta gari, ya sunan ta dama kuma ƙasar da take, dan kuwa kasan babu abinda nake da buri a kullum da ya wuce naga ranar auren ku da kai da Boy" ta ƙarashe fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon YAZEED.

Ɗagowa YAZEED yayi yana murmushi yace "Her name is DEENAH and ita ɗin ƴar Nigeria ce."

"Masha Allah, nasha jin labarin matan Nigeria, tabbas ba za'a nuna musu komai wurin iya zaman aure da kulawa da miji ba, uwa uba akwai girmama baƙi da nuna musu tsantsar ƙauna, zanso naga wannan jikar tawa yadda naga kake ta rawar ƙafa akanta ɗinnan."

Murmushi YAZEED yayi cike da farim ciki kafin yace "Don't you worry Grandma, soon zan kawo ta ki ganta."

Murmushi Grandma tayi tace "Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin."

Da "Aameen" ya amsa yana murmushi.

"Grandma?" cewar ZEEYAD dake tsaye kan stairs yana kallon ta cikin shagwa6e fuska.

"Au har ka tashi daga baccin?, toh ƙaraso mana" cewar Grandma tana kallon sa.

Sauƙowa ZEEYAD yayi yana zuwa ya rungume ta yace "Grandma, na fara missing naki."

"Ai duk kewar da zakayi ba zai kai wanda zanyi maka ba Habibi."

Ƙara rungume ta yayi yace "Grandma, why not ba zamuje tare dake ba?."

"A'a nikam ka ganni nan banga dalilin da zai sanƴa ni barin ƙasa ta ta haihuwa zuwa wata ba, ka ma bar yimin maganar tafiya tare dani, banga dalili ba."

"Where are you going?" cewar YAZEED.
Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa yace "Am going to found the love of my life."

Ɗan zaro idanu YAZEED yayi yana tasowa yazo kusa da ZEEYAD ɗin yace "Really?, tell me more about her."

"What about her?."
"I mean, everything about her, i want to know the lucky girl."

Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "Well you need to work alot before samun ganin ta."

"What, this is serious."

"Yeah it is" ya faɗa cikin murmushi.

Grandma ce tace "Nima fah na kasa kunne naji koh wacece wannan" ta faɗa tana kallon ZEEYAD.

Kallon ta ZEEYAD yayi tare da ɗan yin murmushi kafin yace "Duk kunason ganin ta then work hard."

"Work hard?" duk suka faɗa wurin haɗa baki.

"Yep" ya faɗa.

"Who is she da har sai munyi working hard zamu iya ganin ta?."

Murmushi yayi yana kallon su yace "What do you think she is other than Money?."

Duka Grandma ta kai masa yana kaucewa, inda YAZEED kuma yayi dariya tare da faɗin "But seriously am so eager to know the lucky girl."

"Wa kake tunanin will be the lucky girl other than Jalilah?" cewar Grandma.
Murmushi YAZEED yayi yace "Really?, the girl is cool yeah."

Duk kallon su yayi kafin yace "Grandma, stop it who told you cewa inason Jalilah?."

"Kenan dagaske ne kanason nata kenan, tunda babu wanda ya faɗamin ni na fahimci hakan da kaina."

Kallon ta ya tsaya yi kafin kuma ya 6ata fuska yana kauda kai.

"I know it ai, kaga yayi shiru koh, he loves her" cewar Grandma.

"No Grandma i don't."

"Toh ai sai kuma kayi koma dai menene ai gaskiya zatayi halin ta, mudai namu ido, koh ya kace YAZEED?."

"Ofcourse Granny, but do you really think dagaske yana son nata, i mean banga hakan tattare dashi ba."

"Kai ka kyale ja'iri mana, he is just trying to hide his feelings, bai san na gano komai ba."

Jinsu kawai ZEEYAD keyi bai tanka musu, dan kuwa shi baiga dalilin da zai sanƴa shi son Jalilah ba.

"Ya bani labarin komai daga cikin rayuwar sa amma ya 6oyemin labarin soyayyar sa sabida bayason na sani" cewar Grandma.

"Maybe then, the girl broked his heart" cewar YAZEED.

"Kai no way, i pretty know babu yarinƴar da zata yaudari Boy, wannan santalelen Saurayi ai duk wacce ta barshi ya ku6uce mata ta tafka babbar asara" cewar Grandma cikin koɗa jikan nata.

"Exactly Grandma, then maybe da akwai abinda shi ya barwa kansa sani."

"Koma dai menene ai in tayi tsami zamuji."

Tashi ZEEYAD yayi ya bar musu cikin falon, inda duk suka bisa da kallon mamaki, ganin yadda mood ɗinsa ya canza fiye da kullum.

Part ɗinsa ya koma yana zuwa ya zauna bakin bed tare da kafe wuri ɗaya da ido yana mai damƙe hannun sa ɗaya, sosai yanayin fuskar sa ya canza zuwa 6acin rai dan kuwa ba zai ta6a manta yadda Umma taci masa mutunci akan dan yaso ƴarta ba, bai so DEENAH bane sabida wani abu nata, haka kuma bai ƙi ta sabida wani naƙasu da ta samu lokacin da take kwance babu lafiya ba, hasalima ya sha haɗuwa da mata iri-iri a rayuwar sa sai dai haɗuwar sa da DEENAH na ɗaya daga cikin tarihin rayuwar sa ne hakan yasa ba zai ta6a manta ta ba, but aduk sadda yayi nisa da cire ta daga cikin kwakwalwar sa sai Grandma koh YAZEED sun ɗauko masa maganar da zai sanƴa shi tunawa da ita, ba ƙaramin fama yasha ba wurin cire soyayyar DEENAH a ransa shi kaɗai yasan halin da ya shiga, koh shi a yanzu yanajin daɗin rayuwar sa without her but baisan maiyasa aduk sadda aka tuno masa da ita yakan ji ƙunci da 6acin rai tattare dashi ba, yasan tayi masa nisa yanzu haka shima yayi mata nisa tunda har ya yanke dukkanin wata alaƙar sa da family ɗinta sabida gudun sake tunato ta, he wants to live a new life ba tare da DEENAH ba, but da wata daban?...

Dakatawa yayi da tunanin da yakeyi, tabbas he wants to live a new life tunda gashi nan cikin new world ɗin da babu DEENAH or any of her family, but koh da yace zaiyi sabuwar rayuwa ya mance da ta baya, baya tunanin zaiji soyayyar wata mace daban kamar DEENAH.

Tashi tsaye yayi tare da zuba hannaye cikin aljihu ya hau yin safa da marwa cikin ɗakin nasa, yana mai tunanin yadda yakamata ya tafiyar da rayuwar sa.

Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofar sa ne ya sashi dakatawa da tunanin da yakeyi, kafin ya taka zuwa bakin ƙofar yana buɗewa tare da leƙa kansa.

Wata kuyanga ya gani tsaye kanta a ƙasa kafin cikin girmamawa ta fara faɗin "Afuwan babban Yarima, nasan ka haramta mana zuwa koh da kusa da bakin ƙofar ɗakin ka ne."

Kallon tsaf ya ƙare mata kamar ba zaiyi magana ba, kafin kuma yace "Uhum?."

"Dama Jalilah ce tace nayi mata iso zuwa gunka, nace mata hakan ba zaiyiwu ba..."

Lumshe idanu ZEEYAD yayi ya sake buɗewa cike da ƙosawa yace "Let her in" yana faɗin haka ya koma ciki ba tare da ya jirayi cewar ta ba.

"What does she want again, i thought she fractured her leg" ya faɗi hakan yana mai zama bakin bed ɗinsa.

Bayan kamar mintina biyar ya sake jiyo ƙarar knocking, lumshe idanu yayi cike da ƙosawa kafin kuma ya tashi yaje ya buɗe.

Idanu ya ɗan waro ganin ta tsaye tana yi masa murmushi.

Kallo ya bita dashi tundaga ƙasa, tana sanƴe ne cikin light-blue ɗin gown, fuskar ta ɗauke da light make-up ɗin da yayi matuƙar amsar cute face nata, inda kuma dogon gashin kanta da babu koh da ɗankwali kamar kullum yasha style da gyara mai kyau wanda ya sake taimaka wa wurin fito da tsantsar kyawun ta.

Da kyar ya iya ɗauke idanu akanta yana wani irin murtuƙe fuska ganin yana neman bada kansa a gaban ta.

Barin bakin ƙofar yayi yana komawa cikin ɗakin ya zauna kan couch.

Da ɗingishin ta ta idda shigowa cikin ɗakin tana maida ƙofar ta rufe.

Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da yace mata komai ba.
Ganin kallon da yakeyi mata ne yasa ta faɗin "I...am sorry i know baka tsanmaci zuwa na ba, but ƙafar tawa ta ɗanji sauƙi ina iya taka ta, shine nace bari nazo na sake yi maka godiya, Nagode sosai Akhi."

Kallon tsaf ya ƙare mata kafin kuma ya miƙe tsaye yace "Thank you for what?" ya faɗa yana kallon ta.

Sunkuyar da kai tayi ganin yadda yake kallon ta, tana wasa da yatsun hannun ta tace "Dah ba dan kai ba then Allah ne kaɗai yasan abinda Sooraj zaiyi min yau, sabida nasan babu abinda zai hana shi aikata abinda ya faɗa koh fiye da hakan ma."

Tausayi ta basa nan yace "You don't have to worry Okay?, i promise Sooraj ba zai sake yi miki wani mummunan abu ba kuma, uhm?."

Kai ta jinjina cikin murmushi kanta a ƙasa.

"I should be going now" ta faɗa.

Kallon ta yayi kafin kuma ya jinjina mata kai.

"Naji Grandma tace zakayi tafiya gobe, would you mind idan na haɗa maka chips-cracker, i know you will love it, zaka iya ajiyewa kana ci kullum ba zai 6aci ba."

Ɗan waro idanu yayi yace "Really?."

Kai ta jinjina masa nan yace "Ofcourse i will love it."

Ɗagowa tana yi masa murmushi kafin tace "Alright, zan haɗo maka shi zuwa anjima koh gobe."

Kai ya jinjina mata kawai kafin tace "Ni zan wuce."

"Bye" kawai yace kafin kuma ta fice daga cikin ɗakin yana binta da kallo.

Idanu ya lumshe yana komawa ya zauna kan couch ɗin yana cize baki.

Ɗan ƙaramin tsaki yaja dan kuwa yaga ta fara shigewa gonar sa dayawa, dole ne ya taka mata burki tun kafin ta zaci shima sonta yake yasa yake barin take ra6ar sa, alhalin shi kawai tausayin ta yakeji haka kurum.



************************



___________Da dare bayan ya gama hirar sa da Grandma ya koma part nasa, idda shirya kayayyakin sa yayi kafin kuma yabi lafiyar gado.


************************

__________Washe gari ƙarfe takwas na safe ya gama shirin sa, dan haka part ɗin Grandma kawai ya wuce dan yi mata sallama.

Sosai Grandma tasha kuka ganin fah dagaske tafiyar zaiyi ya sanƴa ta cewa ta canza ra'ayin ta kan cewar babu inda zaije shi.

Sai da ya rarrashe ta sosai tukun kafin ta kwantar da hankalin ta.

Da kanta ta raka sa part ɗin mai Martaba dan yi masa sallama, a cikin fada ya same shi zaune akan Throne nasa kamar kullum da manƴan mutane suma Zazzaune.

Hango Grandma da ZEEYAD ne yasa shi miƙewa tsaye daga kan Throne ɗinsa yana tako ƴar matattakalar da akayiwa wurin ya sauƙo.

Gaisuwar mutunci sukayi da Grandma kafin ya maida duban sa kan ZEEYAD dake kallon sa yana yi masa murmushi.

Ɗan murmusawa shima ZEEYAD yayi yana kuma harɗe fuska lokaci guda.

"Boy yazo yayi maka sallamar tafiyar tasa ta yau ne."

Da mamaki mai Martaba ke kallon su kafin yace "Tafiya?."

"Kwarai kuwa, bai sanar da kai bane?" cewar Grandma.

Kallon sa sarki yayi kafin yace "Tabbas ya sanar dani."

Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, kafin Grandma tace "Ai yau ce tafiyar tasa, watanni biyu kawai zaiyi ya dawo, nasan kaima ba ƙaramin tashin hankali ka shiga da ya sanar da kai hakan ba, amma ya muka iya tunda harkar kasuwancin sa ce zata kaishi."

Sosai yanayin fuskar mai Martaba ya canza da jin abinda Grandma ke faɗi cewar ZEEYAD zaiyi tafiya har ma yayi watanni biyu, alhalin bai sanar dashi hakan ba, murmushi mai Martaba ya ƙaƙalo yace "Hakane" kallon ZEEYAD yayi yace "Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, inaso ka manta da dukkanin abinda ya faru a baya ka ɗauka nan ɗin gidan ka ne sannan bakada inda ya fishi, ka dawo lafiya ɗana" cewar mai Martaba yana ɗaura hannaye kan kafaɗun ZEEYAD ɗin.

Karo na farko kenan da yaji mahaifin nasa ya bashi tausayi dan haka murmushi kawai yayi tare da jinjina kai kafin kuma ya rungume shi.

Sosai mai Martaba ya cika da farin ciki dan kuwa bai tsanmaci zuwan wannan runguma ba, bubbuga bayan ZEEYAD yayi yana murmushi kafin yace "Allah yayi maka albarka."

Ɗagowa ZEEYAD yayi yace "I promise you zan dawo."

Duk murmushi sukayi kafin kuma ya kama hannun Grandma yace "Grandma, jirgi na ƙarfe goma zai ɗaga, i should be going."

Kai ta jinjina masa tana rungume kafin ta ɗago tana bashi kiss a forehead tace "Muje."

Kallon mahaifin nasa ya sake yi, ɗan murmusa masa yayi kafin kuma ya kama hannun Grandma su fice daga fadar.

Da kallo mai Martaba ya bisu har suka fice, kafin ya sanƴa hannu ya goge ƴar siririyar hawayen da ta zubo masa, yana juyawa ya koma kan Throne ɗinsa.


************************

__________YAZEED, Sadeeq, Grandma dama kuma ZEEYAD ɗinne tsaye a gaban wasu danƙara-danƙaran motoci na azo a gani da alama duk rakiya zasuyi masa.

"What are we waiting for, ba cewa kayi 10 jirgin ka zai tashi ba?" cewar Sadeeq.

Kallon agogon hannun sa ZEEYAD yayi yace "She must be on her way."

"Who?" duk suka haɗa baki wurin faɗa.

Hango ta da yayi tana zuwa ne yasa shi faɗin "There she is."
Duk maida duban su sukayi gun Jalilah dake zuwa tana ɗan sauri hannun ta riƙe da silver lunch box tana ƙarasowa wurin.

"Ku gafarce ni, nayi latti."

"Oh come on, muje kada mu sashi ya rasa jirgin" cewar Grandma.

Duk buɗe ƙofar akayi musu suka shige, ZEEYAD da bai shiga bane ya juyo yana kallon Jalilah dake tsaye tana kallon sa yace "Aren't you going?."

Kai ta girgiza masa kafin kuma ta miƙa masa box ɗin tace "Here, abinda nayi maka alƙawari ne, i just hope zakaji daɗin shi."

Kallon ta yake kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "I appreciate it."

Ɗan murmusawa kawai tayi tana controlling hawayen dake son kawo mata.

"Are you going to cry?" ya faɗa yana kallon ta.

Saurin girgiza masa kai tayi tana sunkuyar da kai ƙasa.

"Mai zai hana a ƙarasa tattauna dukkanin abinda ake son faɗa a waya?" cewar Grandma cikin ɗagun murya.

Duk dariya su Sadeeq sukayi.

Kallon ta Jalilah ZEEYAD yayi yace "Bye."

Ɗagowa tayi tana kallon sa da Idanun ta da suka cika taf da kwalla, shigewa motar yayi inda aka maida murfin aka rufe.

Sai da motar taga ficewar motar daga arear wurin kafin ta juya cikin sanƴin jiki ta koma.


**********************


_________"What do you mean na ƙara trying?, that boy almost got me killed a wannan ranar, i wonder maiyasa na kasa samun nasarar ganin bayan sa har yanzu, abinda yafi bani mamaki yake kuma ɗaure min bai wuce yadda akayi ya fahimci nice wannan magen ba."

Dariya bokan nata ya sanƴa kafin ya tsagaita yace "I warned you didn't i?, muddin kika takurawa kanki na cewar sai kinga bayan Yarima ZEEYAD toh tabbas zaki iya aikata babban kuskuren da zai kai ki ga kashe Yarima YAZEED maimakon shi, amma kece kika tilasta nikuma banida wata hanƴar da ta wuce wannan da na faɗa miki, muddin kika samu kika cize sa toh tabbas gubar dake jikin haƙorin kuliyar zata yaɗu zuwa chan cikin zuciyar sa ne, a haka zaiyi ta fama har lokacin sa yayi, amma kin kasa hakan, kaɗan daga cikin alamun ba zaki ta6a yin nasara akansa ba kenan."

Sosai zuciyar Sarauniya Hafeezah ya cika da mugun 6acin rai nan tace "Tabbas sai nayi nasara akansa tamkar yadda nayi akan Uwar sa, ni Hafeezah banta6a cin burin aiwatar da abu kuma abin yazo ya gagare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login