Showing 153001 words to 156000 words out of 236327 words

Chapter 52 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45350

Umma yake da kallo, hakan ya sanƴa jikin su yin sanƴi ganin su tsakiyar wasu ƙabilu.

Umma ce ta ƙaraso inda DEENAH da YAZEED ke tsaye tana kamo ta ta yadda babu wanda zai ji mai take cemata tace "DEENAH, ban fah gane komai ba, i mean such a big Mansion kamar wannan..."

"Umma am also nervous, just look at yadda kowa ke kallo na, maybe idan aka tashi taron nan su fayyace mana komai, ki koma wurin Grandma."

"Don't be nervous dear, Okay?, ni bari naje" ta faɗa tana komawa wurin Grandma kafin ta shiga introducing ɗinta ga ƴan uwa da abokan arziki.

Kallon DEENAH YAZEED yayi yace "Are you...alright?."

Murmushi tayi tare da jinjina masa kai tace "Yeah, yeah am fine."

"Come on, thats my Mom over there, you should meet her" ya faɗa yana nuna mata saitin inda Sarauniya Hafeezah da wasu matan ke tsaye suna gaisawa.

Kallon sa tayi nan yace "No ki saki jikin ki, Okay?."

Kai ta jinjina masa kafin tabi bayan sa zuwa gun mahaifiyar tasa.

Haka kawai DEENAH taji tsoron matar ya darsar mata a zuciya, ga kuma fargabar tunkarar ta da take.

Suna isa ya kira sunan ta "Ummie?" fuskar sa a ɗaure dan kar ma ta sami damar kawo masa wasa.

Kallon sa Sarauniya Hafeezah da hankalin ta ke kan aminan ta tayi tare da sakar masa murmushi tana kamo sa tace "My boy, ka gaisa da Aminai na suma iyayen ka ne, wannan shine YAZEED ɗana ne" ta faɗa cikin murmushi tana introducing ɗinsa garesu.

Duk kallon sa mata ukun sukayi suna faɗin "Masha Allah."
Ɗaya ce tace "Lallai kin iya haihuwa Hafeezah, wannan santalelen saurayi haka?."

Murmushi tayi jin yadda suke ta yabon YAZEED ɗin.

"Wannan kyakkywar yarinƴar dake tare dashi fah, kodai itace amaryar tasa?" cewar ɗaya daga cikin su wacce daga gani ita ce mai sauƙin kai.
Juyowa Sarauniya Hafeezah tayi tana sauƙe duban ta kan DEENAH da sai yanzu ma ta lura da existing ɗinta a wurin, kallon ta ƙare mata daga sama har zuwa ƙasa yayin da murmushin fuskar ta ke gushewa.




*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽*



[8/13, 5:26 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```







*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*







*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*041...*


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





_*NOT EDITED*_





_________Sosai DEENAH tasha jinin jikin ta da ganin expression ɗin fuskar mahaifiyar YAZEED, hakan ya sanƴa ta sunkuyar da kanta zuciyar ta na bugu.

Sosai Sarauniya Hafeezah ta gimtse fuska tana bin DEENAH da wani irin wulaƙantaccen kallo kai kace ba mutum bane a gaban ta.

"What is this?" ta faɗa tana kallon YAZEED.

Kallon DEENAH YAZEED yayi kafin ya kalli mahaifiyar sa yace "DEENAH?, meet my Mom please."

Da kyar DEENAH ta iya ɗagowa tare da buɗar baki tace "Good day Aunt."

"What is good about this day young lady?" ta faɗa cikin gimtsewar fuska tana kallon DEENAH.

Cikin kwantar da murya YAZEED yace "Ummie what are you doing?, she is..."

"Don't tell me wannan ce abar da kake son kawomin a matsayin suruka YAZEED."

Cize baki YAZEED yayi ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu yace "Ummie please don't try to create a scene here, please i beg you don't said anything stupid da zaiyi annoying DEENAH anan wurin" ya faɗa pleadingly cikin kwantar da murya.

Murmushi tayi kafin tace "Hm, mai na faɗamaka tun farko YAZEED?, ban cemaka kada ka ɗauko min ƴar talakawa a matsayin suruka ba, so duk wani abu da ya faru anan kai ka jawa kanka."

DEENAH da batasan abinda suke cewa ba, amma dai tasan akanta ne suke magana dan kuwa sam bataga alamun jindaɗin ganin ta a fuskar mahaifiyar YAZEED ba, sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi da hakan.

"Listen Young lady, ina iyayen ki suke?" ta faɗa tana kallon DEENAH.

Ɗagowa DEENAH da idanun ta suka fara tara kwalla tayi tare da faɗin "My...my Mom is here" ta faɗa tana ciccila idanun ta a inda zata hango Umma.

"So you're here with your Mom, hoping cewa za'a yi accepting ɗinku zuwa cikin family ɗinnan, who the hell ma ya barku kuka shigo cikin MASARAUTAR nan har ma cikin wannan fadar?, talakawa irin ku aren't worth that."

Riƙo Ummien nasa yayi yace "Ummie let's talk this out please."

Kwace hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata cikin fushi take kallon DEENAH "Listen Young lady, kije ki nemi mahaifiyar ki ku bar cikin MASARAUTAR nan da gaggawa tun kafin na wulaƙanta ku anan wurin."

Juyawa YAZEED da idanun sa suka canza launi sabida 6acin rai yayi ga DEENAH tare da faɗin "Listen DEENAH please kada ki ɗau wani abu da mahaifiya ta zata faɗamiki da zafi, am really really sorry okay?" ya faɗin hakan kamar zaiyi kuka tsabar taƙaici.

Kai kawai DEENAH ke jinjina masa tana ƙoƙarin controlling hawayen ta.

Ɗaya daga cikin ƙawayen Sarauniya Hafeezah ne cikin sigar ziga tace "Your Son is Handsome and wealthy, mai zaiyi da yarinƴar nan, just look at her she isn't not just his type."

Hakan ba ƙaramin sake tunzura Sarauniya Hafeezah yayi ba, a tsawace tace "Get this piece of trash out of my sight now YAZEED."

Nan duk fah hankalin kowa ya dawo kansu, kowa ya tsaya kallon su.

DEENAH wani irin gumi ne ya shiga ƙeto mata kanta a ƙasa, jikin ta inbanda rawa babu abinda yakeyi, a rayuwa babu abinda ta tsana kuma take tsoron faɗawa ciki kamar tozarci da humiliation.

A tsawace YAZEED da ransa yayi mugun 6aci yace "Stop this Ummie, what's wrong with you, maiyasa kike yimin haka ne, mai kike nema ne haka da kullum burin ki bai wuce ki 6ata min rai ba?."

"Your Mom is right YAZEED, i mean wannan yarinƴar sam ba tsarin ka bace, kalli fah kayan jikin ta, such a cheap dress..."

"Enough, wannan tsakani na ne da mahaifiya ta, babu wanda ya nemi magantuwar ki a ciki."

"YAZEED stop it, she is like a Mom to..."

"No she is not, why not ba zata riƙe girman ta ba, must she interfere?."

Babu abinda kakeji sai maganar mutane ƙasa-ƙasa.

Kallon DEENAH tayi kafin kuma yadda kowa zai ji ta fara magana "My son here sai ya rasa wacce zai so sai wannan abar, i mean just look at her, a middle class girl like her itace zan yarda ɗana ya aura?, and ina kika samo wannan kaya mai arha haka wanda koh bayin da suke yimin aikace-aikace basu sanƴa kaya irin wadannan na ƙazaman talakawa."

Nan fah wurin ya kacame da dariyar masu hali irin na Sarauniya Hafeezah, suma suna tofa albarkacin bakin su.

Wata ce tace "YAZEED needs a good looking princess, not a poor brat like her."

"And naji ance tana tare ne da mahaifiyar ta, where is your Mom girl?, she needs to stand for you."

DEENAH tuni ta fashe da kuka tana jin kamar ta nutse a wurin tsabar kunƴar da suka ya6a mata, YAZEED kawai tsayawa yayi yama rasa abinda zaiyi, idan ransa yayi dubu toh ya 6aci.

Sarauniya Nazeerah dake tsaye gefe tana kallon abin dake faruwa a ranta taji babu daɗin abinda akeyiwa DEENAH, sai dai sam ba zata yi interfering ba sabida bata shiga abinda bai shafe ta ba.

Sarauniya Naseeba dake tsaye a gefe ta6e baki kawai tayi dan kuwa ba tasu take ba, idanu kawai take ta cillawa koh zata hango inda ZEEYAD da JALILAH suke ta samu ta aiwatar da ƙudirin dake ranta.

YAZEED da baisan mai zaiyi wanda ya wuce roƙon mahaifiyar tasa bane yace "Ummie please, stop all this baikamata ba, you're making her cry."

"Let her cry all her tears out, who even cares, kwaɗayin su da son abin duniya da kuma bin ƴaƴan masu kuɗi ya jawo mata, banason jin komai daga bakin ka YAZEED, the more ka ɗaga min murya nikuma the more zan cigaba da tozarta ta, the best thing da zakayi shine ka ɗauke ta ka fitar da ita daga nan wurin, muddin bakason ganin hawayen ta."

"DEENAH am sorry please, kiyi haƙuri and let's go from here."

"No, you won't go anywhere with her, i want her to leave by herself."

Bai kula mahaifiyar tasa ba sai ma hanƴa da ya nunawa DEENAH yace "Kiyi haƙuri DEENAH, muje please am so sorry on my mom's behalf..."

"Stop begging her on my behalf YAZEED, ka ta6a ganin inda na baiwa wani haƙuri bale kuma wannan kucakar da ka ɗebo min?."

"Let's go DEENAH."

"Don't you dare take a step or else nothing would stop me from cursing you."

Cakk yaja ya tsaya da jin abinda mahaifiyar tasa ta faɗa yana runtse idanun sa.

Kallon sa DEENAH tayi tace "You don't have to worry about me...i...zanje na nemi Umma ta kawai mu tafi."

"Am sorry DEENAH."

"Hafeezah, abinda kikeyi sam bai dace ba, bai zama dole kai zaka yankewa ƴaƴan ka wasu abubuwan game da rayuwar su ba, suma suna da ikon za6ar abinda suka ga ya fiye musu, but ki rage tsanantawa ɗanki haka, abinda kikayi yanzu sam bai dace ba ya kike tunanin yarinƴar nan zataji a zuciyar ta?" faɗin ƙawar ta ta farkon.

Wani irin wulaƙantaccen kallo Sarauniya Hafeezah ta wurga mata kafin tace "Ke fah shiyasa bana buƙatar sako ki cikin wasu abubuwan Zakiyya, sabida sam bakisan ina ne ma yakeyi miki ciwo ba bale har kisan abinda yake dai-dai da wanda ba dai dai ba, wannan Ƙazamar yarinƴar kike tunanin zan bar ɗana ya aura?, why not ki bata ɗanki tunda kema mai arzikin ce."

Kallon DEENAH matar tayi tace "Banga wani aibu tattare da yarinƴar nan ba Hafeezah, kuma ai da ɗana zai ganta yace yana so kuma ya kawomin ita matsayin suruka babu abinda zai hanani amincewa da hakan."

Rolling idanu Hafeezah tayi cike da takaicin halin ƙawar tata, kallon DEENAH dake tsaye har yanzu tayi tace "What is she still doing here, get her out of my sight, and you YAZEED kaji abin da nacemaka idan ka kuskura kayi wani yunƙuri wurin kareta then babu abinda zai hanani buɗar baki na kwashe maka albarka, get out of here lady" ta ƙarashe a tsawace tana aikawa DEENAH da ta kasa motsa koh da ƴar yatsar ta ce mugun kallo.

DEENAH fashewa tayi da kuka sosai, tana danasanin amincewa da tayi na zuwa wannan gidan da basu san darajar mutane ba, gashi bata ga Umma koh ZEEYAD a kusa ba, kenan babu mai tsaya mata sai shi YAZEED ɗin, kuma shima mahaifiyar tasa na neman tsine masa muddin yayi yunƙurin sake tankawa.

YAZEED can't stand the humiliation da akeyiwa DEENAH dan haka barin wurin yayi zuwa ɗakin mai Martaba yaji dalilin da ya hana shi fitowa har yanzun, da kallo DEENAH ta bisa tausayin kanta na kama ta, ta san shikenan tata ta ƙare tunda har ya bar ta tsakiyar wadannan awakin.

Murmushin jindaɗin barin sa wurin Sarauniya Hafeezah tayi, dan kuwa daga yau ta sami kalmar faɗa aduk sadda yayi yunƙurin yi mata gardama akan abinda ta sanƴa shi.

Wata ƴar budurwa ce ta ƙaraso kusa da DEENAH tana ta6a material ɗin kayan jikin ta, kafin ta kalle ta tace "Irin kayan nan ai koh karen da nake kiwon sa bana sanƴa masa kaya masu arha haka nan."

Duk dariya shaiɗanun wurin suka sanƴa.

"Aunt Hafeezah, kada kiyi gaggawar fitar da ita daga fadar nan tukun har sai mun tozarta ta iya son ranmu wanda nan gaba koh motar masu arziƙi ba zata iya ɗaga ido ta kalla ba."

Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi kafin tace "Na baku damar hakan, ku koya mata hankali yadda yakamata."

Hannu yarinƴar ta kai da niyyar fuzge ɗaurin kan DEENAH sai dai ta kasa hakan sakamakon muryar sa da taji.

"What's going on here?" ya faɗa yana bin kowannen su da kallo.

DEENAH buɗe idanun ta da ta runtse tayi sakamakon jin muryar sa da tayi a bayan ta dan haka da sauri ta juya tana kallon sa da fuskar ta da ya 6aci da hawaye sha6e-sha6e.

"DEENAH?" ya kira sunan ta yana ɗan waro idanun sa cike da mamakin ganin hawaye kan fuskar ta.

DEENAH sai yanzu ta ɗanji relief dan haka da gudun ta taje tana faɗawa jikin sa tana ƙanƙame shi tare da sakin wani sabon kukan fiye da na dah.

Hankalin sa tashe ya ɗago da fuskar ta yana tambayar ta abinda ya same ta.
"Tell me DEENAH, mai ya sameki, did something happened to you? tell me wa ya saki kuka?" ya faɗa cikin 6acin rai idanun sa na canza launi.

Kuka kawai DEENAH keyi ba tare da ta iya bashi amsar tambayoyin sa, maida kanta yayi ya rungume a ƙirjin shi tare da lumshe idanun sa yanajin kukan nata na ratsa duk wani 6argo na jikin sa.

Sosai kowa na wurin ya cika da mamakin ganin su a hakan, inda kuma murmuring ɗin mutane ya fara tashi ƙasa-ƙasa.

Sarauniya Hafeezah, Nazeerah, dama kuma Naseeba duk sakin baki sukayi suna kallon su, hatta mutanen dake zagaye dasu baki ɗaya, haka ma JALILAH da Sadeeq dake tsaye a bayan su.

Bai sake ta ba har sai da yaji ta tsagaita da kukan nata tukun ya ɗago ta tare da cupping fuskar ta yana kallon ta.

"DEENAH, tell me wa ya sanƴa ki kuka, and where is YAZEED, who the hell have the gut to make you shed tears like this?."

Cikin muryar sabon kukan dake zuwa mata tace "Kada kaga laifin sa, ma...mahaifiyar sa ce tace zata tsine masa muddin yayi yunƙurin tankawa."

Ɗago da jajayen idanun sa dake nuna tsantsar 6acin rai yayi yana sauƙe su kan Sarauniya Hafeezah dake tsaye tana kallon su.

"Mai tayi miki?" ya faɗa yana kallon DEENAH ɗin.

Kuka kawai take ta kasa basa amsa, koh ba'a ce masa komai ba yasan tayi humiliating ɗinta ne gaban mutane.
Kauda idanun ta tayi daga kallon da yakeyi mata, janƴe DEENAH yayi daga jikin sa yana ƙarasowa gaban ta tare da nuna ta da yatsa yace "You..." shiru yayi yana sauƙe hannun sa tunawa da yayi ita ɗin mahaifiyar YAZEED ce, komin munin halin da zata nuna, dole ya ɗaga mata ƙafa albarkacin ɗan uwan shi.

Juyawa yayi a fusace ba tare da yabi ta kan kowa ba yana riƙo hannun DEENAH ɗin ya jata suka fice daga cikin fadar.

Wata iriyar 6oyayyiyar ajiyar zuciya Sarauniya Hafeezah ta sauƙe tana bin inda suka bi da kallo.

"What the hell nake gani cikin idanu na haka?" cewar Kiki tana kallon Sarauniya Naseeba da mamaki ya gama shanƴe ta ta kasa koh da ƙifta idanun ta ne daga bin inda suka bi da kallo.

"Ban fah gane ba, he became so mad and angry da ganin hawaye kan fuskar yarinƴar nan, meke faruwa ne?" faɗin Kiki ɗin cikin nazari.

Barin fadar Sarauniya Naseeba tayi inda Kiki ɗin tayi saurin mara mata baya.

JALILAH ji tayi jikin ta yayi sanƴi, zuciyar ta fal cike da tunanin abinda ya faru anan.

Sadeeq kuwa jan jikin sa shima yayi ya bar cikin fadar, he can't believe wauta irin na ZEEYAD da DEENAH, yanzu dole zuƙatan mutane dayawa ya cika da zargi kala-kala.


*****************

______"It's alright DEENAH, stop crying please" ya faɗa idanun sa kan fuskar ta da ta kasa barin kukan har yanzu.

"Just...just ka kaini wurin Umma ta, where is she?."

"I guess tana tare da Grandma a part ɗinta."

"Take me to her, i don't wanna stay here any longer" ta faɗa cikin goge hawayen fuskar tata.

Kallon ta kawai ZEEYAD yake cike da tausaya mata, yasan halin Sarauniya Hafeezah zatayi fiye da abinda tayi wa DEENAH a yanzun, but ta wani 6angaren kuma zuciyar sa cike take da haushin YAZEED da ya bari mahaifiyar sa ta ciwa DEENAH mutunci a gaban ɗumbin jama'a.

Cupping fuskar ta yayi yana share mata hawayen yace "Stop crying DEENAH."

Cire hannun nasa tayi daga riƙon fuskar ta da yayi tana faɗin "Ka kaini wurin Umma ta."

"Listen am sorry for not been around lokacin da ake ci miki zarafin nan."

Kallon sa tayi tace "Koh kana nan ɗinma what can you do, is she not your Mom?, you can't do anything."

Kallon ta yake yadda take maganar cikin kuka tana share hawayen ta.
Ɗan murmusawa yayi kafin yace "No she isn't my Mom."

Tsagaitawa tayi da goge hawayen nata tana kallon sa.

"She is YAZEED's Mom and my Stepmom" ya sake faɗa.

"Where...where is your Mom then?."

Shiru yayi yana kallon ta kafin ya ɗan kauda fuskar sa yana cize lips nasa.

"Tell me" ta sake faɗa tana kallon sa.

"I only have my Grandma and... Dad maybe."

Ji tayi jikin ta yayi bala'in sanƴi, cikin calm voice tace "Am so sorry for your lost..."

"Don't be sorry please, nobody is meant to stay in this world permanently, just pray for her."

Kai ta jinjina masa tace "Allah yasa tana makoma mai kyau."

Kai ya jinjina mata kawai cikin murmushi.

"We should go to your Mom" ya faɗa yana buɗe murfin motar da suke ciki.

Saurin riƙo hannun sa tayi, hakan ya sanƴa shi tsayawa kallon ta, maido ƙofar yayi ya rufe.

Kai ta girgiza masa tace "Tell me more about you, i need to know who you really are, and how you end up being a homeless person back then, and how you turned to be so rich and Famous like this."

Murmushi yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login