Showing 147001 words to 150000 words out of 236327 words

Chapter 50 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45305

6ata fuska.

Kallon Umma da ta saki baki da hanci duka tana kallon sa yayi tare da ɗan murmusawa.

"Toh ai gashi nan ma Boy ɗin, yanzu nake shirin kiran ka kazo ka maida ni gida haka nan" cewar Grandma tana sauƙe wayar a kunnen ta.

Kallon Umma ZEEYAD yayi cike da girmamawa ba tare da kuma ya nuna wani abu ba yace "Good day Aunt."

Tashi tsaye Grandma tayi tana kallon Umma da har yanzu mamaki ƙarara kan fuskar ta ta kasa cewa komai tace "Wannan shine Boy ɗin nawa da kukaji na dame ku da maganar sa kullum, shine jika mafi soyuwa a gareni, ɗan albarka ba" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon ZEEYAD.

Umma miƙewa tsaye tayi fuskar ta ƙarara mamaki tace "How is this possible?" tana kallon ZEEYAD ɗin kafin ta kalli DEENAH da tayi kamar bata gansa ba tace "DEENAH?."

Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon Umma ɗin, kafin ta shiga nuna ZEEYAD ɗin da yatsa tace "Is he not..."

"Ofcourse Umma shine" cewar DEENAH ɗin ba tare da ta nuna wani damuwa ba.

Kallon su kawai Grandma keyi kafin ta saki murmushi tace "ZEEYAD kenan, ai jika na ne, kinsan shi ne koh kin ta6a ganin sa a wani wurin, koh da yake ai ba abin mamaki bane, dan kuwa akwai shi da fita ƙasashe daban-daban, tunda koh sati uku mai kyau bai cika da dawowa daga ƙasar taku ba."

"Well Aunt i know you may find this STRANGE but she is actually my Grandmom" ya faɗa yana kallon Umma ɗin.

"But...but how comes, i mean you were homeless back then, sannan bakada wani family, how then is she your Grandma?" cewar Umma ɗin cikin mamakin da har yanzu bata gama fita daga cikin sa ba.

"Umma he would tell us everything soon, probably idan mun bar ƙasar nan tukun."

"Do you know about this?" ta faɗa tana kallon DEENAH.

Kai kawai DEENAH ta jinjina mata kafin tace "listen Umma i know kina da tambayoyi dayawa da zakiyi masa, but he promised to tell us everything soon."

"Meke faruwa ne, mai suke cewa ne?" faɗin Grandma ɗin tana kallon su.

Murmushi ZEEYAD ya ɗanyi kafin yace "The Mom is Surprised to see me."

"Ka san su ne?."

"Probably yes" ya faɗa.

Murmushi Grandma tayi kafin tace "Masha Allah, a'ina ka san su?."

"It's a long story Grandma, but i will tell you everything soon, coz da akwai abubuwan da ban faɗa miki ba."

Kallon sa Grandma keyi kafin tace "Kana nufin kacemin kayi rayuwa dasu lokacin da kaje chan Nigeria ɗin kenan?."

Kai ya jinjina mata alamun Eh, nan tace "Amma kuma shine kacemin bakasan DEENAH ba?."

Shiru ya ɗanyi kafin yace "Grandma, we should discuss this idan mun isa gida please."

Shiru tayi tana kallon DEENAH da Umma dake magana.

Gyaran murya Grandma tayi tace "Toh mu zamu wuce, sai gobe kuma."

Juyowa Umma tayi tana kallon su, babu yabo babu fallasa tace "Alright, Nagode sosai da kulawar ki."

Murmushi Grandma tayi tace "Ai bakomai, you've such a sweet daughter ne shiyasa."

"Muje mu ɗan nan, dan kuwa na fara jin bacci" cewar Grandma tana kallon ZEEYAD da idanun sa ke kan DEENAH.

Kai ya jinjina kafin ya kalli Umma yace "Good night Aunt."

Kai kawai Umma ta iya jinjinawa tana bin su da kallo har suka fice.

Juyowa tayi tana kallon DEENAH kafin tace "DEENAH, tell me ya akayi hakan ya faru, maiyasa banga wata damuwa koh farin cikin ganin sa tattare dake ba?."

Kallon Umma tayi kafin tayi murmushi tace "Umma kece baki haɗu dashi ba, amma ni tun satin chan da ya gabata na gansa, tabbas yaya Jafar yayi gaskiya, people change, and sometimes for the worse, i thought koh he still needs me kamar yadda na daɗe ina begen ganin sa, but sam a wurin sa ba hakan bane, he had really moved on Umma and he even have a girlfriend."

"What?" faɗin Umma cike da mamaki kafin DEENAH tace "You remember the girl da tazo ranan da Grandma?."

Kai Umma ta jinjina nan tace "She is his girlfriend Umma, he totally disposed me like i never exist, tabbas naji baƙin cikin hakan but...not anymore Umma."

"DEENAH kina nufin kin haƙura dashi kenan, remember sabida shi kike cikin halin nan."

"A'a Umma, yanzu na fita daga cikin halin nan tunda har na san matsayi na a wurin sa, his Brother likes me doesn't he, then i will date his brother..."

"What, ɗan uwan sa fah, no i can't let you do that DEENAH, that won't make any sense."

"Ofcourse it would, tunda har shi ya iya soyayya da wata then menene a ciki dan ni naso ɗan uwansa, am doing this ne kawai so that i will make him regret what he did."

Kallon ta kawai Umma keyi, nan ta juyo tana kallon ta tace "Kada ki wani ji damuwa Umma, ni DEENAH have moved on since ranar da na gano matsayi na a wurin sa, daga yanzu kuma babu wani abinda zai sake samuna, haka ma kuma ba zan sanƴa damuwar abinda ba zanci ribar sa a cikin zuciya ta ba, zan kar6i soyayyar ɗan uwansa ne so that i will show him what he really missed."


********************



*TWO DAYS AFTER*


____________"Bro what are you saying ne, it's time da yakamata ace kun haɗu kun gaisa, why are you avoiding ɗin duk wani request da na kawo maka na meeting ɗinta, remember she accepts my love and they are living zuwa country ɗinsu jibi, yakamata ace zuwa yanzu kun san juna da ita, right?."

Kallon YAZEED dake ta damunsa da batun yaje yaga DEENAH su gaisa tun ba yau ba yayi, kafin ya sauƙe kafarsa dake ɗaure kan ɗaya yana gyara zama yace "They are living next tomorrow?."

Zama YAZEED ɗin yayi yana fuskantar sa kafin yace "Yeah, wannan ne dalilin da ya sanƴa nake damunka tun ba yau ba akan you should meet her ku gaisa, remember baka ta6a zuwa duba jikin ta ba."

Murmushin ƙarfin hali ZEEYAD yayi kafin kuma yace "Alright, i will do so, muje mu yau da dare."

Wani irin farin ciki ne ya turnuƙe zuciyar YAZEED nan yace "Yo, koh kaifa?, and you know what?."

Kai ZEEYAD ya jinjina masa idanun sa kan system ɗin gaban sa.

Gyara zama YAZEED yayi yace "Why don't we take them out on a date tomorrow night, i mean that would make sense, right?."

Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, kafin yace "On a date?."

"Yeah, i mean idan ma hakan ba zaiyiwu ba we should invite her to our house sannan mu gabatar da ita gun mai Martaba, i mean na gabatar da ita gun mai Martaba as yarinƴar da nakeso, kai kuma ka gabatar da Jalilah as taka yarinƴar, kaga gara su san da cewa muna da wadanda muke so ba wai su haɗa mu da wasu ƴaƴan sarakuna chan ba kamar wadanda suka rasa mashinshina."

Murmushin maganar tasa ZEEYAD yayi kafin yace "Do you think that would work out?."

"Yeah, kana kokonta ne?."

Kai ya girgiza kafin yace "I mean ka tabbata Ummien ka bata yi maka mata ba?."

Wani irin tsuke fuska YAZEED yayi kafin yace "No, only i have the right ɗin chosing matar da nakeson rayuwa da ita ba wata ba, whether she likes DEENAH or not that won't stop me from marrying her, sai dai idan Allah ne baiyi cewar zata zamto matata ba."

Kallon sa ZEEYAD keyi har ya idda maganar tasa kafin kuma yace "Alright then, ka faɗawa Grandma?."

"Grandma bata da matsala, she would support this 100% dearly."

"And ita yarinƴar taka, do you think zata yarda tazo nan?."

Shiru YAZEED ya ɗanyi kafin yace "Zan faɗawa Grandma ta shawo mana kansu daga ita har Ummien ta, i know zasu zo."

Shiru kawai ZEEYAD yayi yana jinjina kai kafin kuma daga bisani yace "So yanzu mu bari sai goben kawai idan sun zo, right?."

"No, you should be ready by anjima zamuje mu."

Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "Alright, see you then, i need some rest i guess" ya faɗa yana tashi tsaye tare da tattara abubuwan sa.

Miƙewa YAZEED ma yayi suka jera inda kowannen su ya wuce nasa part ɗin, kan anjima zasu sake haɗuwa suje gun DEENAH.

ZEEYAD part ɗinsa ya dawo inda ya ajiye system ɗinsa da sauran abubuwa ya wuce bedroom.

Zama yayi kan bed yana riƙe kansa da hannaye duka biyu, it's so hard for him yaga DEENAH tare da wani, ji yake kamar zuciyar sa zatayi bombing ta faso waje, and now ya jawowa kansa abinda ba zai iya kaiwa ƙarshe ba, baya tunanin zai iya jurar ganin DEENAH da YAZEED a matsayin masoya, shiyasa yake dukkanin ƙoƙarin sa na ganin ya toshe hanƴar faruwar hakan, and gobe kuma yake shirin inviting ɗinta zuwa ganin family ya kuma gabatar da ita matsayin yarinƴar da yakeso, baya tunanin zuciyar sa zata iya jurar ganin hakan.

Kwanciya yayi fuskar sa na kallon sama, sosai ya rasa sukuni ya kuma rasa abinda keyi masa daɗi, bai ta6a tunanin haka hukuncin da ya yanke zata zo tayi turning tana bibiyar sa tare da azabtar masa da zuciya ba.

Idanun sa ya lumshe yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa tana beating really fast, huci mai zafi ya furzar yana miƙewa zaune, kafin kuma ya tashi ya hau zagaye ɗakin zuciyar sa a matuƙar cunkushe.


*********************


_______Da dare kamar yadda suka shirya hakan ce ta faru, kaya iri ɗaya suka sanƴa shi da YAZEED, kafin su ɗau wata zazzafar mota daga cikin na Masarautar su nufi asibitin.


DEENAH dake ta faman shirye-shirye sosai ta haɗe cikin riga da skirt ɗinkin atamfa, wanda yayi mata ɗass a jiki, batayi kwalliya ba koh kaɗan face lip-gloss ɗin Umma da ta shafa a bakin ta sai kuma kwalli, sai dai irin kyawun da tayi ba'a magana sai wanda ya gani kawai.

Ita dai Umma da kallo kawai take bin ta, dan kuwa itama rabon da taga DEENAH cikin wannan shiga mai kyau haka ta manta tun kafin ta kwanta rashin lafiya, kuma da yake ita ɗin gwana ce wurin son ƙananun kaya shiyasa duk ranar da ta sanƴa atamfa take yi mata bala'in kyau.

Ɗagowa DEENAH da sai zuba ƙamshi take tayi tace "Umma wallahi kinyi dabara da kika ɗauko min wannan kayan atamfar kamar kinsa kuwa zan buƙace ta."

Murmushi kawai Umma tayi tana kallon ta kafin tace "Yanzu shi wannan wankan duk na YAZEED ɗin ne koh na ZEEYAD?."

Tsayawa tayi tana kallon Umma kafin kuma ta ɗaga kafaɗa alamun bata sani ba.

Kai kawai Umma ta girgiza tare da faɗin "Allah ya kyauta."

Murmushi DEENAH tayi tana jujjuyawa tace "Umma nayi kyau sosai, koh na canza?."

Kallon ta Umma keyi tace "Kinyi kyau sosai amma matsalar ai babu mayafi bamu taho dashi ba, idan kuma zaki sanƴa Hijabin ne gashi chan ki ɗauka ki saka."

Shiru tayi tana kallon Umma kafin tace "Umma idan na sanƴa Hijabin tayaya zai ga wankan nawa yaji kishi da haushi?."

"Shi wa?" cewar Umma.

Ɗan turo baki tayi kafin tace "Ni koma waye a cikin su."

Murmushi kawai Umma tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.

Zuwa DEENAH tayi ta zauna bakin bed ɗin tana jiran isowar su, dan kuwa tunda YAZEED yace mata tare suke da ZEEYAD ya sanƴa ta ɗaukar alwashin ƙunsa masa baƙin ciki tare da sanƴa sa nadamar sadaukar da ita da yayi mawa wani.

After kamar 20mins suna zaune da Umma ta suka jiyo knocking a ƙofar.

Kallon juna sukayi ita da Umma kafin kuma ta miƙe a hankali cikin takun ta mai ɗaukar hankali ta isa ga bakin ƙofar.

Juyowa tayi tana kallon Umma sakamakon zuciyar ta da taji tana bugu, ɗauke kai Umma tayi kafin kuma ta murɗa handle ɗin ƙofar tana buɗewa.

Idanun ta ne suka sauƙa kan YAZEED dake tsaye saitin ƙofar, wani irin tsadaddan murmushi ta sakar masa tana basa hanƴa.

Kallon ZEEYAD dake controlling kansa yayi tare da faɗin "Come on dude."

Bin bayan sa ZEEYAD yayi suka shigo cikin ɗakin bakin su ɗauke da sallama.

Da kallo DEENAH tabi bayan su ganin duk sun wani sanƴa kaya iri ɗaya babu ta yadda za'ayi ka gane wanene wannan a cikin su indai har ba sun juyo bane.

Murmushi Umma ta sakar musu suna samun kan couch su zauna kafin su shiga gaisawa da ita.

Tashi tayi ta basu wuri tana ficewa daga cikin ɗakin.

Ƙarasowa DEENAH tayi tana zama facing ɗinsu fuskar ta ɗauke da murmushi ta shiga gaida su.

YAZEED da yakejin sa a sararin samaniya tsabar farin ciki ne yace "Hi DEENAH, you look..." shiru yayi ya kasa iddawa sabida sam baisan da wace iriyar kalma zai misalta kyawun da tayi ba.

Murmushi DEENAH tayi tana sunkuyar da kai kafin ta tsinkayo muryar sa yana faɗin "What kind of dress is this, is it your traditional attire?."

Kai ta jinjina masa tace "Yeah , do you like it?."

"Yeah, it's pretty Wow, i mean you look so gorgeous in it, right bro?" ya faɗa yana ɗan bugun ZEEYAD da ya kasa ɗagowa ya kalli DEENAH ɗin tunda suka shigo da kafaɗun sa.

Ɗago da idanu yayi yana sauƙe su kan DEENAH dake zaune fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon YAZEED.

Sosai ya shagala da kallon ta, sabida wani irin kyawu da yaga tayi masa, har sai da YAZEED ya sake ta6a sa kafin ya dawo hayyacin sa yana wani irin mugun haɗe rai yawa wanda yaci guna.

Murmushi YAZEED yayi yace "Look he couldn't get his eyes off you, i told you kinyi kyau sosai, he is my brother ZEEYAD meet him."

Kallon sa DEENAH tayi tare da faɗin "Hi, nice meeting you ZEEYAD."

Wani irin mugun haushi ne ya mamaye masa zuci yana mimmicking yadda tayi maganar a zuciyar sa, wato kar dai har ta fara jin daɗin soyayya da YAZEED ta fara zuba sa kwandon shara?, shine tunanin da yakeyi a ransa.

Maida kansa kawai yayi yana haɗe rai, sosai wani irin bala'in kishi ke taso masa, bai ta6a ganin tayi kyau kamar na yau ba, she is just perfect a komai, baikamata ace tayi disposing body structure ɗinta a wani haka ba.
_"So waye wanin anan yanzu, nine or YAZEED?"_ ya faɗi hakan a ransa fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure.

Shiru yayi yanajin yadda suke hira tsakanin su, kamar ba wannan DEENAH ɗin da ya sani ba, ɗago da idon sa yayi yana kallon ta ganin yadda take yiwa YAZEED ɗin magana cike da shagwa6a shi kuma yana biye mata.

Ji yayi ba zai iya jurar ganin su hakan a tare ba, miƙewa yayi daga zaunen da yake yace "Idan ka gama ina Mota" yana faɗin haka yayi gaba ba tare da ya jira yi cewar YAZEED ɗin ba.

Da kallon gefen ido ta bisa, tasan koh bakomai ta ƙunsa masa kishi da baƙin ciki ne ya sanƴa shi tashi ya fice, but bai ma ga komai ba tukun tunda hakan yaso.

Kusan almost 20mins ya ɗauka a mota yana jiran fitowar YAZEED amma yaji shiru, inda tsaki kuwa yaja ta yafi sau miliyan a zaman nasa.

Hango su da yayi tafe ne ya sashi kafa mata idanun sa daga cikin motar yana bin duk wani motsi da surar jikinta da kallo.

Wani irin zazzafar huci ya fesar ganin ta haɗa komai da ake buƙata wurin cikakkiyar ƴa mace tattare da ita, babu abinda yafi ɗauke masa hankali a jikin ta kamar waist ɗin ta.
Tsaki yaja a karo na barkatai ganin yadda suke wani taku kamar ba zasu taka ƙasar ba, ga kuma wani irin nonnoƙe kai da takeyi da alamu dai shagwa6a take zuba masa.

Har suka ƙaraso wurin idanun sa akan DEENAH, buɗe wurin mai zaman banza YAZEED yayi ya shiga tare da rufo murfin motar yana sauƙe glass ɗin.

Wani irin haushi ne ya turnuƙe ZEEYAD nan yace "Aren't you guys done?."

"1 minute please" ya faɗa yana masa nuni da hannu ba tare da ya juyo ya kalli ZEEYAD ɗin ba.

Sako kanta tayi ta cikin window ɗin motar tace "Bye take care of yourself."

"Sure" faɗin YAZEED ɗin cikin murmushi kafin tayi masa waving tana sakar masa murmushi tare da barin jikin motar.

Maida glass ɗin motar yayi ya rufe, kafin ya kalli ZEEYAD da saura ƙiris ya fashe tare da sosa kai yace "Sorry bro i kept you waiting."

ZEEYAD bai kula shi ba haka ma bai tanka masa ba yaja motar a mugun tsiyace suka bar cikin asibitin.

Murmushi DEENAH ta sakar tare da bin motar da kallo tace "Let this serve as a lesson to you Abyad, this is just the BEGINNING."






*Yawan Comment, Yawan Typing*





*MHIZZ JIDDHERR..................✍🏽*
[8/12, 1:27 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*



*040...*


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



________Liyafa ce mai rai da lafiya ake shiryawa cikin MASARAUTAR a yau, kasancewar the princes zasu gabatar da wacce suke so yau a gaban fada.

Da kaga fuskar mai Martaba washe take da iriyar tsantsar farin cikin da yake ciki, kasancewar girma dama kuma ƙimar sa zai daɗa ƙaruwa a idanun ɗumbin jama'a, tunda har ya iya ajiye gwarzayen samari biyu da zai aurar.

Grandma kuwa tsabar farin ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login