Showing 15001 words to 18000 words out of 236327 words
kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
..............Tafiya mai nisan gaske sukayi dan kuwa sun kai awanni huɗu akan hanƴa kafin su iso inda zasu.
Nan duk motocin sukayi Parking kafin a fara bada umarnin fitowa.
Duk mutane ne suka fara fitowa,sai da kowa ya fita kafin ZEEYAD ya fito.
Ƙaton bakin ruwa ne wanda ke ɗauke da manƴan jiragen ruwa dayawa wasu sun fara tafiya wasu kuwa suna zuzzube a bakin ruwan ba'a fara tafiya ba.
Wannan Abokin Abhi ɗinnan ne yayi wa ZEEYAD jagora zuwa wurin wani daban, gefe suka ja suka ɗanyi magana kafin ya haɗa sa da ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo a wannan wuri.
"Yaro wannan mutumin shine zaiyi maka jagora har zuwa inda zaku, duk wata buƙata taka ka tambaye sa zai yi maka ita bakada wata damuwa kaji?, ni zan koma inda na fito yanzu ka kula Allah Ubangiji ya sauƙe ku lafiya."
Kai ZEEYAD ya jinjina tare da furta "Aameen" sannan yabi bayan wannan mutumin nan zuwa cikin wani jirgi.
Ciki chan ƙasa suka shiga inda ya kasance kamar gida ne da ɗakuna a cikin sa harda falo da abubuwan da ba'a rasa ba na cikin manƴan jiragen ruwa.
Wani ɗaki ya kai ZEEYAD yace "Tafiyar nan zata ɗauke mu tsawon makonni biyu, dan haka anan ne zaka dinga kwana sai dai ba kai kaɗai bane da akwai wasu ƴan kwanan ma, idan kana da abin shimfiɗa ka shimfiɗa shi ta gefen chan ka kwanta sannan kuma kayi takatsantsan da jakar ka, idan kana buƙatar wani abu koh ƙarin bayani zaka iya samu na a waje" yana faɗin haka ya juya ya fice.
Da kallo ZEEYAD yabi ɗakin dashi, ɗaki ne shi ba ƙarami ba kuma ba babba ba ɗan madaidaici ne dai, inda kuma akwai tabarmai shimfiɗe wanda da alama akwai masu wurin.
Gefe ɗaya ya samu ya zauna yana rungume jakar sa a jiki, kafin kuma ya shiga tunanin iriyar rayuwar da zaije ya tarar achan wani wurin da koh mafarki da tunanin zuwa bai ta6a ba.
Maganar wannan mutumin da ta ɗansa ne ya faɗo masa rai, nan ya furta "Business?."
Wasu ne suka shigo ɗakin nan ya maida hankalin sa kansu, duk da kallo suka bisa kafin su sami wuri kan wani tabarma su zauna.
Ɗaya daga cikin su ne yace "Wai kowa ma ya waye ya gane da barin ƙasar sa yanzu zuwa wata, kai kuwa ɗan Saurayi mai zakaje yi a Nigeria, kuma daga ina kake?."
Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka musu ba, nan ɗayan yace "Kai ina ruwan ka ne dashi, ka sani koh rayuwa ce tayi masa zafi ya gudo?."
Haka nan suka cigaba da firar su yana jinsu bai tanka musu ba, sai ma ɗaukar jakar sa da yayi ya fice.
Wannan mutumin da ya kawo sa ɗakin ya shiga nema kasancewar da akwai mutane dayawa ya sanƴa sa samun sa da kyar.
ZEEYAD ne yace "Dan Allah, a'ina ne zan sami ruwa da abin sallah?."
Kallon sa mutumin yayi yace "Kana nufin kace bakazo da komai ba?, ai komai na nan wurin na saidawa ne da akwai masu saida duk abinda kakeso har a sauƙa, idanma canjin kuɗaɗen ka kakeso ayi maka zuwa na Nigeria duk akwai wadanda zasuyi maka, kaje ta bayan chan nan ne inda aka ware wurin sallah sannan akwai masu saida ruwa a wurin."
Kai ya jinjina yace "Nagode" kafin ya juya yabi hanƴar da mutumin ya nuna masa.
Wuri ya samu ya zauna sai a sannan ya buɗe jakar da Sadeeq ya basa, kaya ne kala biyu a ciki, sai su bread da biscuits sai kuma ruwan gora, ruwa ɗaya ya ciro kafin ya maida zip ɗin jakar ya rufe.
Wurin da aka ware kamar banɗaki ya gani nan yaje yayo tsarki kafin ya dawo ya ɗaura alwala sannan yayi sallah, Hannun sa ya ɗaga sama tare da kwararo addu'o'i sosai sannan ya miƙe ya ɗau jakar sa ya koma ciki inda ya fito.
Matashi yayi da jakar tasa ya kwanta, dan kuwa ba ƙaramin bacci yakeji ba, da tunanen da bai san ranar yankewar su ba bacci ta kwashe shi.
*************
..........Bai farka ba sai da rana tayi lokacin kuwa har jirgin ya tashi yayi nesa da fara tafiya, fita ya sakeyi yayi alwala yayi sallah.
Bai komo ciki ba sai ma samun ƙarafunan jirgin da yayi ya riƙe yana kallon ƙatuwar ruwan dama kuma yadda jirgin ke zuba uban gudu a kanta.
Ya jima sosai anan har akayi sallahr La'asar yayi, a takaice dai anan wurin ya wuni har dare kafin ya koma cikin ɗaki.
Kasancewar ya fara jin ƴunwa ya sashi buɗe jakar sa ya ɗauko biscuit guda ɗaya ya buɗe ta ya fara ci,sannan ya kora da ruwa a kai.
He was so very emotional and lonely hakan yasa wasu hawayen da bai san da zuwar su ba shiga sauƙo masa, kansa ya sunkuyar ba tare da ya iya controlling hawayen nasa ba, babu abinda yake tunawa sai mahaifiyar sa dama kuma irin rayuwar da sukayi a baya harda Abhi ɗinsa dake tsananin ƙaunar sa amma daga baya kuma shine wanda yafi tsana wanda har ganin sa baya son yi.
"Kai ɗan saurayi" yaji an faɗi hakan.
Ɗagowa yayi nan yaji ɗaya yace "Ka dame mu fah da shessheƙa bakaga bacci muke yi bane?."
"Kuyi haƙuri" kawai ya faɗa yana maida kansa.
Sati ɗaya ya wuce sai dai har yanzu basu iso inda zasu ɗin ba, inda kowa da ka gani a cikin wannan jirgi toh fah rayuwar sa yake cikin kwanciyar hankali sa6anin ZEEYAD da kullum yake cikin ƙunci tare da rashin walwala, ga kuma kayan abincin sa da ya fara ƙarewa inda sau ɗaya kawai yake ci a rana ba zai sake ci ba sai washe gari duk dan gudun kada ta ƙare ya rasa na ci wataran, ga kuma yanayin yadda yaga mutanen cikin jirgin kowa na harkar gaban sa ne, babu wanda yakeyi wa ɗan uwan sa tayin abin ci koh sha, kowa rayuwar sa yake.
A haka rayuwa ta cigaba wa ZEEYAD a cikin wannan jirgi, yau lafiya gobe babu lafiya har Allah yasa suka iso ƙasar Nigeria.
Mutane ne yaji sun fara shewar "an iso, an iso, kowa ya adana kayan sa sannan ya 6oye kuɗaɗen sa."
ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo babu abinda ya fahimta, tafiya kaɗan jirgin tayi ta sauƙa a bakin ƙaton tekun ɗin.
Mintina goma da tsayuwar ta mutane suka fara kokuwar fitowa sai a sannan yaga adadin cunkoson mutanen dake cikin wannan jirgi.
"Kowa ya kula da dukiyar sa" yaji ana faɗa hakan yasa shi damƙe jakar sa a hammata.
Sosai ya zama soko a wannan wuri inda kowa sai bangaje shi yake yana ficewar sa.
A haka shima ya samu ya kutsa kansa cikin mutanen dukda kuwa irin ture sa da akeyi, a hankali yaji kamar ana jan jakar hannun sa ta baya, mamaki ne ya cika shi nan ya sake damƙe ta a hannu.
Ihun wata tsohuwa ya jiyo tana faɗin an kwace mata jakar kuɗin ta, babu wanda ya kula ta sai ma baki da kowa ke turowa yana yin gaba abinsa.
Ratsawa yayi cikin mutane zuwa gun wannan tsohuwa ganin mutane sun jefar ta sai tattaka ta akeyi.
Hannu ya kai da shirin ɗagota, aikuwa caraff ta kamo hannun nasa tana ihun "Ga shi nan ga 6arawon da ya ɗauke min jakar kuɗi ta, yau Allah ya kama ka, dama kune masu yiwa mutane sata ai, Allah ya kama ka yau" ta ƙarashe cikin kuka.
ZEEYAD ba ƙaramin mamaki yaci ba ganin tsohuwar nan na neman ɗaura masa sharri alhalin babu abinda ya aikata.
Fuzge hannun sa yayi daga riƙon da tayi masa ɗin, ganin kowa na wucewa cikin sauri bai saurare ta ba yasa shi shima jan baya da ita yana kallon ta, ƙarshe dai nan ya baro ta sai kukan 6atan kuɗin ta take yayi gaba.
Fitowa yayi daga cikin jirgin inda wani iska mai daɗi ya huro shi wanda ya sanƴa sa lumshe idanun sa, yayin da kuma tsikar jikin sa ya shiga tashi yana feeling so nervous wanda da kyar ya iya taka ƙafarsa ya fara tafiya yana bin mutanen wannan wuri da kallo kamar ɗan ƙauye.
Bakin tekun ɗin haka yake kamar wani kasuwa mutane kala-kala, ga kuma wasu yellow ɗin Vans zuzzube dayawa duk sunji jiki sunji duniya inda kuma suke ta ihun neman passengers ɗinda zasuyi cikin gari dasu.
"Central Market, Central Market, Central Market" shine yaji wani baƙin mutumi yana faɗa, inda ya zamto mummuna a idanun ZEEYAD ya tsaya yana ƙarewa wagegen bakin mutumin dake ta nanata" Central market" kallo dan kuwa karon sa na farko kenan da ya kalli baƙar fata sai dai fah dukda haka yaga na wannan mutumin ya bambamta da na saura, hakan yasa kansa ƙullewa ganin dai gasu nan dukkanin su baƙaƙe za'a kira su amma kowane da kallar baƙin sa masu haske ɗaɗɗaya yake gani.
Kallon ZEEYAD da ya saki idanu yana kallon sa yayi yace "White Broda how far na, where u wan go?."
Kai kawai ZEEYAD ya Jinjina masa dan kuwa idan ba "How far?" ba babu abinda ya gane cikin maganar sa sauran duk baiji ba kasancewar yadda yayi maganar cikin muryar ƴan shaye-shaye.
Gaba yayi yana ta kalle-kalle ba tare da ya san inda yake sanƴa ƙafafuwan sa ba, in banda kallon mutane babu abinda yakeyi.
Ji yayi an bangaje shi ya faɗi, nan ya juya ya kalli lukutar matar da ɗuwawun ta kamar wadanda aka hura musu iska tana sanƴe cikin Mini skirt ɗinda ya tsaya mata a guiwa sai harɗe ƙafafu take tana tafiya, idanu ya zaro waje wondering koh ita ma mutum ce, dan kuwa bai ta6a ganin ƙatuwa irinta ba.
Haka nan ya miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin sa yana kallon matar da tayi nisa sai dai bai bar kallon ta ba har yanzun dan kuwa mamaki yadda take iya tafiya ma yakeyi.
Haka nan ya cigaba da tafiya duk inda ya samu ya jefa ƙafarsa haka ya fito daga cikin mutane.
Nan kuma yaga ƴan acha6a birjik a gefe suma da alamun passengers suke nema.
Ji yayi an riƙo jakar sa ta baya nan yaga ana jansa ana faɗin "Where u wan go?, pay 500 naira i will take you everywhere you want in Lagos." yaji mutumin ya faɗa tare da amsar jakarsa yana Ɗaurawa kan mashin ɗin nasa.
Mamaki ne ya kama ZEEYAD nan yace "No, actually i don't have any money with me."
"Ahh bro u must be joking nah, keep joke aside na, as fine boy as u are, u no get money?" an european boy" ya faɗa yana washe haƙora.
"No am not from Europe" ya faɗa cikin sanƴi yana ƙoƙarin amsar jakar sa.
"Are u waiting for someone to pick u up?, this one that ur body dey fresh like dis i know u must be from a wealthy Family" ya faɗa cikin washe masa haƙora yana maida masa jakar sa.
Shiru kawai ZEEYAD yayi ya amshi abinsa tare da yin gaba, dan kuwa sam baya fahimtar turancin ɗan acha6ar nan.
Tafiya ya cigaba da yi nan yaji ana yi masa horn a bayan sa, ɗan acha6ar nan ne dai ya sake biyo sa,nan yace dashi "Are u a lost, where u wan go?, make i take u for free."
"For Free?" ZEEYAD ya tambaya yana kallon sa.
"Ehen na, oya be fast oo before dis stupid cops arrived."
Zuwa ZEEYAD yayi inda dakyar ya iya hawa machine ɗin dan kuwa bai saba ba, Hannun sa ya ɗaura a kafaɗar ɗan acha6ar gudun kada ya su6ule ya faɗi, nan ya tada ta suka hau tafiya.
"Broda, where u wan go na?."
"You mean, where i want to go?."
"Yes."
"Actually, i don't know."
Slowing down ɗan acha6ar yayi yace "U don't know?."
"Yes" ya basa amsa.
"Where are you from, which country are you from?."
Shiru yayi kafin kuma a hankali yace "Egypt."
"Ehnn, no wonder u look so handsome and fresh like fresh tomato" ya faɗa cikin dariya.
"So bro where should i take u now?" ɗan acha6ar ya sake faɗa.
"Anywhere" ya faɗa.
Kara gudun mashin ɗin yayi, tafiya mai nisan gaske sukayi kafin su fara shigowa cikin gari, da kallo ZEEYAD ke bin wuraren da kallo, ganin duk tsofaffin gine-gine sunfi yawa ga kuma saman langa-langar su da duk a kokkoɗe sunyi tsatsa, ga kuma wani uban traffic jam da aka haɗa akan hanƴa.
Sosai ɗan acha6ar nan ya cika shi da surutu, har suka iso inda zasuje yayi parking.
"Yauwa kaga nan garage ne na kawo ka, ba zaka rasa wurin kwana ba."
Rungume jakar sa yayi yace "Thank you so very much."
"Don't mind na, it's my pleasure to meet such a handsome guy like u and even have a Conversation with."
Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi ba tare da yace dashi komai ba.
"Alright bro, good luck i pray we met somewhere again" ya faɗa cikin dariya yana jan Babur ɗinsa yayi gaba.
Da kallo ZEEYAD ya bi shi yana mamakin dama akwai mutanen kirki har haka, ya ɗauko shi daga wuri mai nisa sai dai koh biyar bai caje sa ba, inama ya ƙarashe guntun rayuwar sa cikin haɗuwa da ire-iren wannan ɗan acha6ar.
Kallo ya ƙarewa tashar motar , kafin kuma ya samu wuri daga gefe ya zauna yana bin mutane da kallo.
Kowa na harkar gaban sa, yayin da masu sayar da abinci da toye-toye suma na yin nasu.
Hango table ɗin wata inƴamura yayi plate ɗauke a hannun ta tana ɗebo farin shinkafa daga cikin kula sai fitar da tururi yake, ƴawu ya haɗiya lokacin da yaji cikin sa tayi wani irin ƙarar ƴunwa.
Rabon sa da ya sanƴa abinci a bakin sa kwana biyu kenan, miƙewa yayi daga inda yake zaune ya nufi wurin wannan mata.
Hango sa da tayi ne yasa ta washe haƙora tace "Ah ah Customer, welcome, u too fine oo ehnn,welcome" ta faɗa tana kallon sa.
"Hi" yace da ita.
"Hi, have a seat na, what do you want to buy?."
Murmushi yayi yace "Nothing...i...i am hungry pls help me with...."
Ai bai idda ba yaji ta daka masa wani irin tsawar da bai ta6a jinta ba tunda yake a rayuwar sa, hakan yasa shi jan baya da sauri.
"Help?, help my foot, help u with what?, abeg my friend get lost from here, are you the one that gave me the profit to start this business, idiot, abeg move ur dirty body away from here don't come and infect my food,broke white guy mtssswww," ta ƙarashe cikin jan doguwar tsaki kamar bakin ta zai faɗi ƙasa sai masifa take ta zubawa cikin yaren da baya fahimta.
Da sauri ya bar wurin yana danasanin sa na zuwa gashi a banza tayi disgracing ɗinsa gaban mutane kowa ya gane barar abinci yaje yi abinda bai ta6a ba, sosai yaji ciwon hakan, wuri ya samu ya zauna kawai yana cigaba da aikin kalle-kallen sa..............
*******************
.........."Your Highness, we have searched everywhere but the Prince is nowhere to be found" ya faɗa cike da girmamawa kansa duƙe a ƙasa.
Sosai Ran mai Martaba yayi mummunar 6aci jin labarin da ake kawo masa kullum tsawon sati biyu da 6acewar ZEEYAD.
"It's been two weeks now, sai dai har yanzu no one knows his whereabout, mun samu bayanan cewa tun lokacin da Sooraj ɗan wurin Abdulhakeem yazo da dakarun sa sukayi wa Yarima ZEEYAD dukan mutuwa tundaga ranar kuma ba'a sake ganin sa ba" ya sake faɗa cikin girmamawa.
Tashi tsaye mai Martaba yayi yace "Ku kawomin Abdulhakeem dama kuma Sooraj nan wurin, bama su kaɗai ba da dukkanin wasu dangi ku aika musu da cewa ina buƙatar su a fada yanzun nan, include the QUEEN'S" Ya ƙarashe cikin kakkausar murya idanun sa na yin jaa.
Duƙawa yayi cike da girmamawa sannan ya fice dan zuwa aiwatar da umarnin mai Martaba.
Mintina ashirin mai kyau fada ta cika Family kowanne zaune da iyalan sa a gefe wanda aƙalla zasu kai su biyar.
Da kallo mai Martaba ya bisu dukkanin su kafin kuma yace "Ɗa na Yarima ZEEYAD, yau sati biyu kenan da 6atar sa ba'a gansa ba, sannan rahoto yazo min cewa Sooraj ɗa ga Abdulhakeem shine wanda aka gansu tare ƙarshe ya sanƴa bayi sunyi masa duka, Sooraj" ya kiraye sa da ƙarfi yana aika masa da mugun kallo.
A razane Sooraj ya miƙe tsaye cike da girmamawa ya duƙa yace "Yes your Highness."
Shiru mai Martaba yayi kafin yace "A'ina ka kai min ɗa na?."
Kame-kame ya fara kafin yace "Wallahi ranka shi daɗe, tun lokacin da muka samu sa6ani dashi ban kuma sake sanƴa sa a idanu na ba, sabida na dai san lafiya ƙalau na...na taho na bar sa a wannan wurin" ya ƙarashe yana kallon Mahaifin sa.
Mai Martaba ne yace "Kada ka nemi ka raina min hankali mana, Abdulhakeem koh kasan da abinda ɗan ka ya aikatawa Yarima ZEEYAD?."
Tashi Abdulhakeem yayi yace "Kwarai kuwa ranka ya daɗe, dan kuwa nayi masa faɗa sosai akan hakan kuma yayi nadama yace ba zai sake ba, har ma nace ya koma yaje ya baiwa Yarima ZEEYAD haƙuri amma kuma sai ya dawomin da labarin cewa bai gansa ba ya bar wurin."
"Tayaya zaka yarda da ɗanka bayan kasan muguwar zuciya irin tasa, koh ka sani shine wanda yayi sanadiyyar 6acewar Yarima ZEEYAD sannan kuma ya 6oye maka gaskiya."
Cikin ruɗewa Sooraj ya fara faɗin "Abhi wallahi bansan komai kan 6acewar Yarima ZEEYAD ba, nidai nasan kawai nasa dogarai sunyi masa duka ne amma bayan nan kuma babu abinda ya sake shiga tsakani na dashi."
"Hafeezah!" cewar mai Martaba a tsawace.
Sarauniya Hafeezah da duk hankalin ta yayi gaba jin mai Martaba na kiran ZEEYAD da sunan ɗansa har ma da kiran sa Yarima yasa hankalin ta mugun tashi, a razane kuma ta ɗago tana kallon sa sabida yadda ya kira sunan nata.
"Ina ɗana?" ya faɗa yana kallon ta.
Cikin in-ina take faɗin "Bansaniba, bansan inda yake ba nayi maka rantsuwa da Allah babu abinda na sani game da 6atar sa."
Tsaye ya miƙe yana sarƙe hannaye a baya yace "Na baku nan da kwana ɗaya ku nemo inda ya shige, idan kuma baku aiwatar da hakan ba toh ina mai tabbatar muku da cewa sai kun fuskanci hukunci mai tsananin gaske" yana faɗin haka ya wuce fuuu tare da haurawa sama ya bar su nan zaune kowa da abinda ke gudana cikin zuciyar sa.
Murmushi Sarauniya Nazeerah ta saki dan kuwa ita babu abinda yafi burgeta face taga ana rigima,dan kuwa ita bata tsani kowa ba amma burin ta shine kullum ace rigima