Showing 150001 words to 153000 words out of 236327 words
ma rasa inda zata sanƴa kanta tayi, sosai ta kasa zaune ta kasa tashi, sai kai komo take duk dan ganin komai yayi steady yadda ake buƙata.
6angaren JALILAH cike take da wata iriyar tsantsar farin ciki, she can't believe mafarkin ta na zama matar ZEEYAD zai zamto gaskiya, dan kuwa koh da da wasa bata ta6a zaton zai sota har ma yace zai aure ta ba.
Zaune take gaban mirror tana cancaɗawa kanta ado, dan kuwa bata tunanin zata sake yarda da wata baiwa ta sake shirya ta, dukda kuwa ido rufe take neman su Kiki da take zargin su suka aikata abincan.
Sosai tasha ado cikin Maroon ɗin gown mai matuƙar kyau da tsada.
Tashi tayi tsaye tana jujjuyawa cikin shigar tata dan kuwa ba ƙaramar kyau tayi ba.
Tana cikin haka ne ta hango mahaifin ta tsaye ta cikin mirror, hakan ya sanƴa ta saurin dakatawa da abinda takeyi tana juyawa ta kalle shi tare da shan dukkanin jinin jikin ta sakamakon irin kallon da yake aika mata.
Takowa yayi ya shigo cikin ɗakin hannayen sa ɗaure a bayan sa, yana ƙare mata kallo from head to toe, kafin ya fara magana cikin tsare gida "Seems like kina cikin farin ciki sabida burin ki ya kusa cika koh?, amma ga chan ɗan uwanki kulle kamar ƙasƙantaccen bawa ke nan koh a kwalar rigar ki, sai ma farin ciki da kike da hakan, i have never seen a worst sister like you wacce ta sanƴa a hukunta ɗan uwanta, kuma dan bakida kunƴa sai ki rasa wanda zaki so kaf duniyar nan sai yaron da ya kasance maƙiyi ga ɗan uwanki, yaron da bashida isasshiyar tarbiyya yake ganin kowa a tsakiyar kansa, yaron da baya mutunta iyayen ki tare da girmama su shi kikeson aura har kuma kike farin ciki da hakan, uhm?" ya ƙarashe yana kallon ta.
Ita dai JALILAH kanta sunkuye a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalli mahaifin nata.
"Fine then, kije kiyi dukkanin abinda kika ga dai-dai ne a gareki, sannan dukkanin abin da ya biyo baya kiyi kuka da kanki, kar ki kuskura kice zaki kawo mana damuwar ki cikin gidan nan, kada kice ban gargaɗe ki ba."
Takawa yayi zuwa bakin ƙofa ya tsaya kafin ya juyo yace "And inason ki sanarwa shi wanda zaki aura ɗin da ya sanƴa a sako min ɗana, idan kuma ba haka ba...kinsan dai nine uba a gurin ki sannan da izini na da kuma amincewa ta za'a ɗaura miki aure koh?" yana faɗin haka ya fice daga ɗakin ba tare da ya kula mahaifiyar JALILAH dake tsaye bakin ƙofa ba.
Da kallo tabi mijin nata kafin ta shigo cikin ɗakin tana kallon ƴar tata tace "Grandma ta aiko a taho dake, suna chan suna jiran ki."
Ɗago da idanun ta da sukayi sha6e-sha6e da hawaye tayi tana kallon mahaifiyar tata da itama bata wani damu da ita ba, kasancewar tsoron mahaifin ta da take bala'in yi.
"Ba...ba zakije bane?."
Shiru mahaifiyar tata tayi tana mai tausayin JALILAH ɗin tare da girgiza mata kai tace "Mahaifin ki bai yarje min naje ba."
"Yanzu kina nufin haka za'a yi liyafar ke bakya wurin?, dan Allah kizo Ummie" ta faɗa cikin hawaye tana riƙo hannun mahaifiyar tata.
"Kada ki damu ai koh banje ba mahaifin ki zai kasance a wurin."
Shiru kawai JALILAH tayi tana share hawayen fuskar ta, bata sake tankawa mahaifiyar tata ba ta tattari dogon gown ɗinta tayi gaba.
*******
"Have you lost your mind ne YAZEED, ace yau zaka gabatar da wacce kakeso a gaban fada, amma kuma ace banida masaniya akan hakan, sai dai naji a bakin mutane, dah ba dan Jakadiya Salima ta kawomin wannan labarin ba kenan kana nufin har aure zakayi ba zan sani ba."
Ta6e baki YAZEED da fuskar sa ke tsuke tunda mahaifiyar tasa tayi kiran sa yayi kafin kuma yace "Well i guess babu wani abin tada hankali anan tunda yanzu kin sani, i was about to call you dan sanar miki sai kuma kika aika a kirawo ni."
"You was about to call me, kana nufin ban isa ka tako da ƙafar ka ka sanar dani ba, sai dai ka kira ni ta waya, what has come over you YAZEED har kanada ikon za6ar wacce kakeson ka aura ba tare da ni mahaifiyar ka nasan da hakan ba, sannan gaka nan koh a jikin ka sai ma farin ciki da kake ciki."
"Ummie please, bakiji excuse ɗin da na baki bane, atleast ai sai kiyimin uzuri koh, introduction ɗinnan sai nan da awa ɗaya za'a fara shi, why not ki jira har sai bayan an gama ban faɗa miki ba sannan kice zaki ɗau mataki, hun for God-sake?."
Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi ganin yadda yakeyi mata kamar wanda shine ya haife ta, hakan ba ƙaramin 6ata mata rai yake ba, yadda YAZEED ke disobeying ɗinta a komai, haka ma kuma baya including ɗinta cikin komai na rayuwar sa.
"Fine then, ka faɗamin ƴar gidan wacce sarki koh mai mulkin zaka aura, nasan ba zaka bani kunƴa ba ta wannan fannin."
Wani irin kallo ya bita dashi kafin yace "What do you mean?."
"Ina nufin da akwai ƴaƴan manƴan masu mulki dayawa a wannan ƙasar, dama wajen ta, nasan tabbas ba zaka auro min wacce iyayen ta ba sanannu bane a duniyar kokuma ƙasar tasu."
Scoffing yayi yana kallon mahaifiyar tasa cike da mamaki yace "Na auro miki as how?."
Rolling idanun ta tayi kafin tace "Koma dai menene ka fahimci abinda nake nufi, ba zan kar6i surukar da ba ƴar gidan kowa bace ba, ɗan sarki kamar ka kamata yayi ace ka auro ƴar gidan sanannu kuma masu ragamar mulki wadanda suke faɗa a ji a ƙasa."
Murmushin takaici ya saki yace "Kinfi son na kawo miki ƴar masu mulki kuma masu faɗa aji a ƙasa, Wow."
Murmushi tayi tace "Kwarai kuwa ɗan albarka, faɗamin ƴar gidan wacece ita?."
"Listen Ummie, wacce nakeso kuma nake da burin aure ba ƴar nan ƙasar bace, sannan kuma ba ƴar masu mulki koh dukiya bace, suna da rufin asiri sosai, look koh da a cikin bayin gidan nan na sami wacce nakeson aura why do you care, ke zaki zauna da ita koh ni?, i guess i have the right to chose whoever i want to marry..."
Dakatar da shi tayi ta hanƴar ɗaga masa hannu tace "Enough, mai kake shirin faɗamin ne haka, yarinƴar ba ƴar ƙasar nan bace, sannan kuma ba ƴar gidan kowa ba, kasan abinda kake faɗa kuwa YAZEED?, ƴar talakawa kakeson ɗauko min a matsayin suruka, a whole me da girma na da daraja ta ka ɗaukomin wata kucaka chan daga wata ƙasar wacce ba ƴar gidan uban kowa ba kace zaka kawomin ita a matsayin suruka, are you insane?."
"Ummie what's wrong with you, maiyasa kike yimin haka ne, duk wani abu da zanyi shikenan ba zan burge ki ba, a komai kinfi son ki ɗaura ni kan abinda ba shine ra'ayi na ba, am a grown up now Ummie and i have the freedom da zan yankewa kaina hukuncin duk wani abu a cikin rayuwa ta, i love DEENAH sannan babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana ni auren ta, so just rest your mind ki zuba ido, idan kina ganin ba zaki iya jurar kallo ba then ba sai kinje wurin ba" yana faɗin haka ya fice a fusace ya bar ɗakin nata.
Da mugun kallo ta bisa tanajin zuciyar ta nayi mata zafi, tabbas YAZEED na neman kaita bango, babu ta yadda za'ayi ta bari ya auri wata ƴar matsiyata ne bayan ga yaran manƴan mutane nan kyawawa kaca-kaca.
******
Kwance yake shi kaɗai cikin ɗakin nasa idanun sa a lumshe kamar mai bacci, sai dai a zahiri ba baccin yake ba.
Sosai ya luma duniyar tunanin DEENAH, wanda tun jiya da dare da ya ganta, dama kuma yadda sukeyi da YAZEED ya kasa samun kyakkywar bacci bale sukuni tattare dashi, he was very disturbed ganin kamar ya 6allowa kansa ruwa, and yau DEENAH zata shigo MASARAUTAR su a matsayin matar da ɗan uwan sa zai aura while shi kuma an barsa da JALILAH, yeah chosing JALILAH a matsayin matar aure is not a big deal, tunda the girl is cool and decent, but dukkanin zuciyar sa ta karkata ne zuwa ga DEENAH, he just couldn't believe iriyar wautar da yayi.
Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofar ɗakin nasa ne ya katse masa tunanin sa, dan haka miƙewa yayi yaje ya buɗe nan yaga YAZEED tsaye cikin shigar sa ta alfarma, sosai yasha kyau kamar mai zuwa gasar kyau ta maza.
Murmushi ZEEYAD ya saki na ganin ɗan uwan nasa, shigowa YAZEED yayi ɗakin yana bin ZEEYAD da koh alamun shiryawa bai fara ba.
"What is this bro, baka shirya ba, abin nan is less than 30mins yanzu a fara."
Zama ZEEYAD yayi akan couch ɗin dake ajiye a ɗakin yace "Yeah i know, yanzu zan shirya."
"And munyi waya da DEENAH tacemin sun shirya so na aika driver su ɗauko su, you should get ready too, and you know what?."
Girgiza kai ZEEYAD yayi nan YAZEED yace "I saw your JALILAH, she looks so takeaway."
Murmushi ZEEYAD yayi kawai ba tare da yace komai ba.
"You should get ready please."
"Yeah" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Ni zanje na dawo" cewar YAZEED yana ficewa daga ɗakin.
Da kallo ZEEYAD ya bisa kafin shima yayi shirin wanka.
******
"Toh dai gashi yau ZEEYAD ɗinki ke shirin gabatar da JALILAH a matsayin wacce zai aura, bakya tunanin mu ɗau wani mataki ne?."
Wani irin mugun kallo ta watsawa Kiki kafin tace "Rufemin baki chan sakarya kawai, na baki aiki kiyi wancan karon banga kyakkyawar result ba sai yanzu zaki wani dameni da batun mai za'ayi, koh da zan bada aiki ba zan sake baki ba sabida shirme kawai zakije kiyimin."
Sunkuyar da kai Kiki tayi tare da faɗin "Afuwan ranki shi daɗe, yanzu kina nufin kice kin samu mai yi miki wani aikin ne kokuwa?."
"Koh ma dai menene, kedai naki ido" ta faɗa cikin murmushin mugunta.
******************
Sosai aka ƙawata cikin fadar tayi kyau, duk wani lungu da saƙo da zakabi gauraye take da hasken kwan fitila haka ma mutane ke ta kai komo kowa na harkar abinda aka sanƴa shi.
Tundaga layin mashigar MASARAUTAR dake gauraye da hasken kwan fitila DEENAH da Umma suka saki baki suna kallon Aljannar duniyar dake gaban su, ganin irin ƙatuwar faffaɗar MASARUTAR dake gaban su ya sanƴa ta kallon driver mai jan nasu tace "Bawan Allah, anƴa ka tabbata nan aka ce ka kawo mu kuwa?" dan kuwa ita duk ta tsorata haka ma DEENAH dake ta wuwwula manƴan idanun ta dan kuwa sun fara zargin idan ba sayar dasu driver ɗin ke son yi ba.
"Nan ne ranki shi daɗe, babbar MASARAUTAR CAIRO kenan, koh ba kune wadanda Yarima YAZEED ya sanƴa na ɗauko ba?."
Kallon juna Umma da DEENAH sukayi a mamakin ce jin abinda ya faɗa "Yarima YAZEED kuma, kodai Doctor YAZEED?."
Dariya driver yayi yace "Ai duk shi ɗin ne, shi ɗin ɗan sarki ne haka ma ɗan uwansa ZEEYAD da ya dawo bayan shekaru goma da 6atar sa" ya faɗa daidai lokacin da aka ɗaga buɗe musu ƙofar MASARAUTAR suna shigewa.
Baki, hanci duk Umma da DEENAH suka saki jin abin kamar almara, kenan hakan na nufin su ɗin ƴaƴan sarki ne komiye?, shine tambayar da kowannen su ke buƙatar sanin amsa.
Haka nan aka isa har gaban fada dasu yayi parking ya juyo ya kallesu yace "Mun iso ranki ya daɗe, wannan ita ce ƙofar shiga fada, sannan anan za'ayi taron."
Umma da ta sha adon ta cikin Lace ɗinkin bubu ne ta kalli DEENAH da duk jikin ta ya gama sanƴi tace "Amshi wayar ki kira sa kice mun iso" ta faɗa tana miƙa mata wayar.
Amsar wayar DEENAH tayi tare da ƴan danna kiran lambar YAZEED ɗin, har ya tsinke bai ɗaga ba tana shirin sake ƙira taga nasa kiran na shigowa.
Ɗagawa tayi tare da sanar dashi cewar sun iso.
Driver ta miƙawa wayar kamar yadda ya faɗa, bayan sunyi waya da driver ɗinne kuma ya maida mata wayar ta kafin yaja motar su bar wurin.
"Toh, ina kuma zamu yanzun?" cewar Umma.
Yace na kaiku chan 6angaren "Hajiya Babba, wato Grandma."
Sauƙe ajiyar zuciya Umma tayi tana jin hankalin ta na ɗan kwanciya.
Sauƙe su yayi a gaban wani babban part, suna zuwa suka hango YAZEED ɗin da Grandma tsaye suna jiran isowar su.
Da sauri Grandma ta ƙaraso tana buɗe 6angaren da Umma take tana yi musu maraba da zuwa.
Runguma ta baiwa Umma cikin jindaɗin ganin ta, kafin tayi saurin ƙarasawa wurin DEENAH da ta haɗe cikin baby pink ɗin gown ɗin da ta tilastawa Umma saya mata shi tana rungumo ta haɗi da manna mata kiss a ƙunci tana yi mata barka da zuwa.
Murmushi DEENAH ta saki tana maida duban ta kan YAZEED dake kallon ta yana murmushi.
"Hi" tace masa.
Maida mata martanin murmushin yayi yace "I can't take my eyes off you."
Murmushi DEENAH ta saki tana sunkuyar da kai ƙasa, Grandma ce tace "Toh ya isa haka nan, muje daga ciki ayi komai a gama dawuri."
Duk jerawa sukayi suka shiga ciki duk wayewar Umma da DEENAH wannan MASARAUTA bata ishe su da kallo ba.
JALILAH ce tazo cikin ɗan gudu gown ɗinta dake ɗan jan ƙasa a hannun ta.
"Welcome Aunt" ta faɗa cikin murmushi tana kallon Umma.
Murmushi Umma ta maida mata tace "Thank you dear."
Kallon DEENAH tayi tare da sakin baki kafin tace "Wow" tana ƙarasawa wurin ta ta riƙo ta.
"You look good" cewar DEENAH tana kallon ta cikin murmushin yaƙe dan kuwa itace ta kwace mata Abyad ɗinta.
"Thank you, sai dai ban kai ki ba" cewar Jalilah ɗin.
Murmushi DEENAH tayi a zuciyar ta tana faɗin _"Uhm tunda har ya iya ganin ki kika ɗauke masa hankali wa yafi haɗuwa cikin mu kenan?"_
"I like this your head tie, ya akeyin sa?" cewar JALILAH tana kallon ɗaurin dake kan DEENAH.
Baƙin dogon gashin ta da ya sha gyara ya sauƙa mata har gadon bayan ta kanta babu ɗankwali DEENAH tabi da kallo a zuciyar ta tana mamakin yadda basu cika son rufe gashin nasu ba, nan tace "Kina so ne kema, sai nayi miki."
"Yeah, ofcourse amma dai ba yau ba tukun" ta faɗa cikin ɗan dariya.
Murmushi DEENAH tayi kawai zuciyar ta fal mamaki ba tare da tace komai ba.
Kallon su Grandma tayi tare da yin murmushi tace "Tabarakallah Masha Allah ƴaƴan nan ba ƙaramin kyau kukayi ba a tare, ina roƙon Allah yasa zumuncin ku tayi kyau fiye da yadda kukayi kyau a yanzun.
Ita dai DEENAH Grandma ba ƙaramin mamaki take bata ba da wannan surutun da ba'a tambaye ta, wai ita nan har ta gama yankewa ita YAZEED zata aura JALILAH kuma ZEEYAD.
"Kuje ku sami wurin zama kafin mazajen naku su ƙaraso koh" cewar Grandma.
_"Mazaje?"_ faɗin DEENAH cikin ranta tana mai samun wuri ta zauna.
Ba'a jima ba YAZEED da yaje kiran ZEEYAD suka shigo dukkanin su cikin shiga iri ɗaya ta alfarma.
DEENAH idanu ta zuba musu har suka ƙaraso wurin dan kuwa ba ƙaramin burge ta sukayi ba, ganin sun kusa haɗa idanu dashi ne yasa ta saurin kauda kanta zuwa wani wurin pretending bata ganshi ba.
Haka ma 6angaren Umma da mamaki ya jiƙa ta ya shanƴe ke binsu da kallo har ZEEYAD ɗin ya gaida ta cikin girmamawa ta amsa masa.
Kallon kowannen su da ya sha kyau ba'a magana Grandma tayi kafin tace "Masha Allah, yanzu tunda kowannen ku ya halarta anan yanzu duk sai mu lula zuwa chan fadar mai Martaba, nasan yana chan yana jiran isowar surukan nasa.
DEENAH ji tayi gaban ta ya faɗi, anƴa kuwa abin nan da take shirin aikatawa ba kuskure bane, anƴa kuwa ba zata yi wasa da feeling ɗin YAZEED ba?, idan shi ZEEYAD ya yarda yayi sacrificing soyayyar sa then ita kuwa bata tunanin batayi kuskuren amincewa da soyayyar YAZEED ba tunda ba wai tana sonsa bane, idan ta bari wani abu na aure ya ƙullu tsakanin su yanzu then kanta ta cuta kokuma dai ZEEYAD ɗinne ya cuce su baki ɗaya?, da wannan tunanin a ranta take kallon JALILAH da ZEEYAD dake zaune kusa da juna shi kansa a sunkuye yayin da ita kuma take yi masa magana cikin murmushi.
Kauda kanta tayi tana danne abinda ke taso mata cikin zuciya.
"Maza duk ku tashi muje, ga nan motocin sun iso duk ku tashi muje" cewar Grandma tana yi musu magana.
Duk tashi sukayi inda Grandma da Umma suka jera.
YAZEED ne ya ƙaraso wurin DEENAH yace "Lets go princess."
Kallon sa tayi tare da maida masa martanin murmushin kafin ta kalli 6angaren su ZEEYAD dake jiran JALILAH wacce ke gyara ɗaurin igiyar takalmin ta, ganin tana neman 6ata musu lokaci ne ya sanƴa shi durƙusawa ya shiga gyara mata, DEENAH batasan sadda tayi rolling manƴan idanun ta tana wani irin frowning fuska ba.
Kallon ta YAZEED yayi yace "On your lead" ya faɗa yana nuna mata hanƴa.
Murmushi tayi kafin tayi gaba sabida karma zuciyar ta yayi bursting da baƙin ciki yana mara mata baya.
Da kallon gefen ido ZEEYAD dake gyarawa JALILAH takalmi ya bita, dan kuwa shima yau yayi alƙawarin ƙunsa mata kishi da gangan tamkar yadda tayi masa jiya.
Bayan ya gyara mata ne ta tashi tsaye kafin suma su bar cikin part ɗin Grandma.
Duk motoci suka shiga cikin abinda bai fi mintina biyu ba suka iso fadar mai Martaba ɗin.
Duk buɗe musu ƙofa akayi suka fito.
ZEEYAD da zagayowa yayi ta 6angaren JALILAH tare da buɗe mata ƙofar yana miƙa mata hannun sa.
JALILAH da zuciyar ta ke cike taf da farin ciki nata hannun ta basa kafin ya taimaka mata ta fito, hannun ta ɗaya riƙe da gown ɗinta da ta ɗan tattare shi, kallon ta yayi yace "Ina maids naki?."
"I don't need them today, i can manage things on my own."
Kai ya jinjina hannun ta cikin nasa yayi leading ɗinsu zuwa ciki, kasancewar su DEENAH har sun shige.
Shigar su keda wuya aka maida ƙofar fadar aka rufe.
Sosai aka ƙawata faffaɗar fadar da kwalliya da kujera masu kyau da ɗaukar hankali, Umma da DEENAH kam mamakin da suke ciki har yanzu bai gama ficewa daga zucin su ba.
Hango sa tafe riƙe da hannun JALILAH ba ƙaramin ƙona mata rai ba _"Seems like he enjoyed touching girls da ba muharamman sa ba"_ ta faɗi hakan cikin ranta tare da kauda kansa daga garesu.
Sosai mutane suka hallara cikin fadar, inda kowa sai bin DEENAH da