Showing 87001 words to 90000 words out of 236327 words

Chapter 30 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45339

dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





*CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT,*
*HELIOPOLIS EGYPT*


_____________Ƙarfe takwas ɗin dare su Umma suka sauƙa a ƙasar Egypt, dan haka already akwai masu jiran su wadanda su zasu kai su masauƙin su kasancewar Jafar ya gama yi musu komai ta yadda ba zasu wani sha wahala ba idan sunje.


Hotel ne mai kyau da tsada aka kai su kafin ayi musu iso har zuwa masauƙin su.

Umma dai kallon garin take dan kuwa yanayin ƙasar da garin kaɗai zai tabbatar maka da akwai kwanciyar hankali da daɗin zama.

Kasancewar akwai komai na buƙata a Apartment ɗin hotel ɗin yasa abinci kaɗai aka kawo musu da abin sha.

Ɗan zazzagaye ɗakin Umma tayi Falo ne da ɗakuna guda biyu sai kitchen dama kuma Toilet a kowane ɗaki.

Sosai taji tsarin hotel ɗin yayi mata dan haka toilet ta kai DEENAH tare da yi mata wanka suka fito.

Canza mata kaya tayi zuwa masu ɗan nauyi kasancewar garin akwai ɗan sanƴi-sanƴi, kafin ita ma ta shiga ta watsawa jikin ta ruwa ta fito.

Sallolin ta ta rama kan kuma taci abinci tare da ɗaukar waya ta kira Jafar da sabon layin ta na chan.

Bugu biyu taji Jafar ya ɗaga daga ɗayan gefen tare da yin sallama.

"Wa'alaika Salam, ɗan albarka."

"Umma na, kun bar ni cikin kewa."

"Toh ya muka iya, haka Allah ya ƙaddara."

"Hakane Umma, dafatan kun sauƙa lafiya, Ya DEENAH fah?."

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, yanzu ma zamu kwanta duk da dai ba wata gajiya na kwaso ba, kasan gobe da safe zamu wuce asibiti."

"Hakane Umma, yakamata kam ki huta, ya kikaji yanayin ƙasar?."

"Toh dai gashi nan dai, babu laifi zaiyi daɗin zama daga gani."

"Masha Allah, hakan yayi kyau, gobe da safe wanda zai kai ku asibitin ku haɗu da likitan zai zo shi insha Allah."

"Toh shikenan ai bakomai, Allah ya kaimu, ya wurin su Mami fah?."

"Lafiyan su ƙalau ban daɗe da barin wurin su ba ina gida yanzu."

"Toh masha Allah, zan kira su gobe, yanzu dai bari na kwanta."

"Toh Umma, sai da safe."

"Allah ya tashe mu lafiya."

"Aameen" ya amsa kafin ta datse kiran.


Keken da DEENAH ke kai ta tura zuwa ɗaya daga cikin ɗaku nan, kafin ta kwantar da ita akan bed, addu'a tayi mata tare da rufa mata bargo.

Wutar ɗakin ta kashe kafin ita ma ta sami wuri ta kwanta.


*********************


_________Da misalin takwas na safe wanda zai kaisu asibitin ya iso.

Dan haka shirya DEENAH tayi tare da ɗaukar dukkanin wasu abubuwan buƙata suka kama hanƴar asibitin.


*********************



*AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL*
*CAIRO, EGYPT*



Babban asibitin gwamanti ne wanda ya amsa sunan sa wurin kyawu da haɗuwa, haɗi da ƙwararrun likitoci dama kuma ingantattun kayan aiki.


Kai tsaye amsar DEENAH wasu Nurses sukayi daga hannun Umma aka tura ta zuwa wani ɗaki da ba zan iya fasalta koh wane irin ɗaki bane.

Ba'a bar Umma ta shiga ba sai ma iso da akayi mata zuwa wani ɗakin daban, wanda dai da alamu nan ne wurin zaman jiran patients.

Umma kam da kallo take bin koh ina, hankalin ta duk ya koma kan inda aka kai DEENAH.

Batayi awanni biyu masu kyau da zama ba wadannan nurses ɗin suka dawo.

Ganin su ya sanƴa Umma tashi daga zaunen da take tana tambayar su lafiyar DEENAH.

Cikin turanci suka ce da ita "Kece Mahaifiyar MADEENAH ABDULSALAM?."

Kai Umma ta jinjina tace "Eh, Nice."

"Alright, Likita na buƙatar ganawa dake, biyo ni muje."


Ficewa sukayi daga ɗakin zuwa ofishin likitan.

Kansa a ƙasa yana wasu ƴan rubuce-rubuce suka shigo da sallama a bakin su.


Cikin harshen larabci Nurse ɗin tace dashi "Sir, ga nan mahaifiyar patient ɗin da aka kawo ɗazun."


Ɗagowa yayi ya kalli nurse ɗin tare da jinjina mata kai yana ajiye biron hannun sa.

"Bismillah, zaki iya zama" ta faɗa tana nunawa Umma kujera.

Zama Umma tayi kafin nurse ɗin ta ɗauki wasu files akan table ɗin Likitan ta fice.

Kallon Umma yayi yace "Good Afternoon Ma'am."

"Afternoon doctor, how is work?."

"Alhamdulillah" ya amsa.

"Kasa a kirawo ni."

"Kwarai kuwa, kune wadanda Doctor Sagir ya turo daga chan Nigeria, right?."

Kai ta jinjina masa nan yace "Well, lucky you da kuka zo akan lokaci, but dukda haka bakuyi escaping risk ɗin faɗawar ta memory loss ba."

"What..ban fahimce ka ba likita, Memory loss kamarya?."


"Actually Ma'am, am sorry to utter this out but ƴarki tayi losing memory ɗinta."


"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, mai kake faɗa min haka, amma ai basu ta6a sanar damu labarin nan a chan Nigeria ba sai kai kuma zaka zo ka faɗamin hakan yanzu."


"Sorry Ma'am, dalilin da ya sanƴa suka turo ku nan kenan, but don't worry insha Allah, just keep praying ta samu lafiyar fitowa daga stroke, da zaran hakan ya faru kuma abu mai sauƙi ne tayi recovering memory ɗinta, zamu cigaba da bata kulawa ta musamman insha Allah ƴar ki zata samu lafiya."

Goge hawayen da suka zubo mata Umma tayi tace "Toh shikenan, bakomai Allah ya bata lafiya, amma sam banji daɗin wannan labarin naka ba, kana nufin kenan fah ƴar da na haifa da ciki na nunawa zatayi bata sanni ba."

"Kiyi haƙuri Ma'am, wuyar ta shine dama tayi recovering daga stroke, amma zata iya recovering memory ɗinta wurin nuna mata iriyar rayuwar da tayi a baya da makamancin su."

"Toh ya na iya, mai zanyi idan ba haƙurin ba dama?, Allah ya baki lafiya Auta, haƙika nayi kewar ki sosai yarinƴar kirki, ƴar albarka, zan iya ganin ta yanzu?."


"Yeah sure" ya faɗa yana miƙewa daga zaunen da yake.

"This way" ya faɗa yana nunawa Umma hanƴa suka fice daga ofishin.

Sun ɗanyi tafiya kafin su iso wani ward, shiru kamar babu kowa haka arear wurin yake, a cikin jerin ɗakunan wurin mai lamba ta 25 ya buɗe suka shiga, da alamu dai ɗakunan VIP rooms ne.

Ɗaki ne babba mai ɗan girma, Bed guda biyu ne a ciki na marar lafiya dama kuma na mai jinƴa, sai wasu ƴan madaidaitan couches guda biyu daga gefe, Fridge sai kuma wata ƴar madaidaiciyar closet daga gefe, sai kuma bathroom da Valcony.

DEENAH ce kwance kan bed ɗin an jona mata wasu na'urori, sai dai wannan karon idanun ta a rufe suke kamar mai bacci.

Da sauri Umma ta ƙarasa wurin ta tana faɗin "Likita, ta motsa ne?."


Kai ya jinjina mata alamun "Eh."

"Toh amma maiyasa baku kira ni ba, ya zakuyi min haka?."


"Ai koh da mun kira ki ɗin ba zata san kina wurin ba, alama ne na ta ɗan fara recovering kaɗan-kaɗan."

Shafa kan DEENAH dake kwance kamar mai bacci tayi tace "Allah ya tashi kafaɗun ki ƴar albarka."

"Ni zan wuce, da akwai Nurses biyu da zan turo, sune zasu cigaba da kula da ita yadda yakamata har ta samu sauƙi."

"Toh shikenan Doctor, Thank you so much."

"You're welcome, Allah ya bata lafiya."

"Aameen" ta amsa kafin kuma ya fice daga ɗakin.


Waya ta ciro a cikin jakar ta, missed call ɗin Jafar ta gani dana su Mami dan haka Jafar ta fara kira.

Sai da suka gaisa kafin ta koro masa bayanin yadda sukayi da likita, sai dai bata faɗa masa cewar DEENAH tayi losing memory ɗinta ba, sosai Jafar yaji farin cikin jin DEENAH ta fara samun ɗan sauƙi, bayan sun gama waya da Jafar ne kuma ta kira su Mami suka gaggaisa dasu Anty Khadija duka.


**********************


*THE PALACE*


_________Kasancewar ya saba zuwa kullum duba jikin mai Martaba yasa ba tare da wani bincike ba ake barin sa ya shiga.

Kai tsaye har uwar ɗakar mai Martaba ya nufa.


Zaune yake akan kujera cikin shigar sa ta alfarma, kamar kullum ya sanƴa hoton matar sa a gaba yana kallo, yayin da kuma hawayen nadama basu ta6a ƙaura daga idanun sa ba.

Ganin kamar baisan da shigowar Sadeeq ɗin bane yasa shi yin gyaran murya.


Dawowa yayi daga duniyar tunanin da ya faɗa, kafin a hankali ya juyo da kujerar da yake kai yana fuskantar Sadeeq, sosai ya manƴan ta sai dai dukda haka kamannin ZEEYAD basu 6ace akan fuskar sa ba, kamar kullum fuskar sa a murtuƙe take babu fara'a akanta koh kaɗan.

Gaida shi Sadeeq yayi ba tare da ya amsa ba ya ɗaga masa hannu kawai.

"Ayi haƙuri ranka ya daɗe, yau ban ƙaraso da wuri ba, a gafarce ni nayi sabbin patients ne daga wasu ƙasan."

Kai ya jinjina cikin muryar sa da tayi rauni alamun marar lafiya yace "Bakomai."

Murmushi Sadeeq yayi yace "Your Highness dafatan dai ka sha maganin naka?."

Kai ya jinjina masa kafin ya ɗaura da faɗin "YAZEED yazo ya bani maganin, sai da ya tabbatar da nasha kafin ya tafi."

"Masha Allah, hakan yayi kyau sosai."

Gwaje-gwaje ya sake yiwa mai Martaba kafin yace "Your Highness, har yanzu kaƙi ka daina barin tunanin nan, kullum BP ɗinka na ƙara sauƙa ne."

"Kwanaki na na ƙara ja kuma har yanzu Yarima ZEEYAD yaƙi ya dawo gare ni, tayaya kake tunanin hankali na zai kwanta bayan ban san inda ɗa mafi soyuwa a gare ni yake ba, bansan koh yana a raye koh a mace ba, tayaya hankali na zai kwanta bayan iriyar rayuwar da na taso dashi akai wanda ya sanƴa shi guduwa da ƙafafuwan sa, tayaya hankali na zai kwanta bayan ban san koh ya yafe min koh bai yafe min ba, banason na mutu wani ya gaji gadon masarautar nan idan ba Yarima ZEEYAD ba."


Sosai mai Martaba ke baiwa Sadeeq tausayi, a kullum bashi da tunani wanda ya wuce na ZEEYAD, a kullum kalaman sa basu wuce kada ya mutu ba tare da ya sake sanƴa ZEEYAD a idanun sa ba, shi kansa yasan lokaci yayi da za'a ce ZEEYAD ya dawo yanzun, amma baisan maiyasa yaƙi dawowa ba, shi kansa ya gama fidda ran cewa koh ZEEYAD na raye har yanzun, dan kuwa shekaru goma kenan tun ranar da suka rabu bai sake jin ɗoriyar sa ba, he just hope and prayed that ZEEYAD na raye sannan kuma zai dawo ga family ɗinsa soon.

"Your Highness, insha Allah ni nasan Yarima ZEEYAD na raye inaga dai koh akwai lokacin da ya gindayawa kansa na dawowa ne, amma ni inajin a jiki na cewar yana raye sannan zai dawo nan ba da daɗewa ba."

"Allah yasa hakan."

"Aameen, ka kwantar da hankalin ka."


Kai kawai ya jinjina yana juyar da kujerar sa zuwa kan hoton ya cigaba da kallo.


Kai kawai Sadeeq ya girgiza kafin ya ɗau jakar kayan aikin sa ya fice.


*******************



__________Yau Watan su Umma biyu da ƴan kwanaki a asibitin sai dai har yanzun DEENAH bata farko ba.

Umma tun tana yarda da maganar likita har tazo ta daina yarda kuma, sabida kullum maganar sa bai wuce DEENAH ta kusa samun lafiya ba, amma shiru kakeji, duk da kuwa iriyar kulawar da suke bata sosai.


6angaren ZEEYAD kuwa yana dukkanin iya kan ƙoƙarin sa na ganin ya maida hankalin sa kan career ɗin sa sai dai hakan yaci tura, har sai da Daddy ya zaunar dashi yayi masa faɗa sosai tukun kafin ya ajiye batun DEENAH a gefe duk hakan kuwa kullum tana ransa, gashi bayason karya dokar da Umma ta gindaya masa na cewar bata buƙatar ganin sa a chan wurin su.

Yau ma zaune yake a ofishin shi yana zanen wani irin gida da za'a iya cewa hotel ne, ƙofar ce ta buɗu aka shigo.

Secretary ɗinsa ne dan haka cike da girmamawa yace "Sir, Madam tazo neman ka, gata chan sai hayaniya take da guards ɗin da kasa sabida sun hana ta shigowa."

Ɗan ƙaramin tsaki yaja sabida takaicin hali irin na Khairat, duk maitar Surayya bata kamo koh da hannun Khairat bane balle ƙafar ta.

"Sir, mai za'a ce musu, a bar ta ta shigo?" ya faɗa jin ZEEYAD ɗin yayi shiru.

Wani irin mugun kallo ya watsa masa kafin kuma yace "Kace dasu muddin naji koh da muryar ta ne then a bakin aikin su."

Amsawa yayi cike da girmamawa kafin ya fice daga ofishin dan zuwa aiwatar da abinda ya sanƴa su.


"Mayyar yarinƴa kawai" ya faɗa a hankali yana cigaba da zanen sa.


Yatsina fuska yayi yana jin sa so very boring tun bayan tafiyar su DEENAH, gashi ba magana take ba balle yayi waya da ita, a wurin Jafar kaɗai yake samun labarin ta yaji hankalin sa ya ɗan kwanta.


***************

Zaune Umma take akan DEENAH dake kwance ta tafka uban tagumi, sosai ta lula duniyar tunanin halin da DEENAH ke ciki.

Nurses masu kula da ita ne suka shigo kamar kullum dan duba yana yin lafiyar ta.

Dube-dube suka fara irin tasu na likitoci yayin da ɗaya ke yin recording a cikin takardar hannun ta.

"Wait...did she just moved her fingers?" cewar mai ɗaukar record ɗin tana kallon DEENAH.

"What, really?" cewar ɗayar duk suna maida duban su gun ta.

Idanu Umma ta zuba musu tana kallo dan kuwa sun ma tare mata DEENAH gashi sam bata fahimci abinda suke cewa ba kasancewar hankalin ta yayi nisa.


DEENAH dake kwance sama-sama takejin maganar su nayi mata yawo cikin kwakwalwa, inda takejin kuma kamar a mafarki take.

A hankali ta shiga motsa nannauyar idanun ta da suka gama jeme wa yayi duhu sosai sabida irin daɗewar da sukayi a rufe tana ƙoƙarin motsa yatsun hannun ta.


Sama-sama haka takejin maganar su har izuwa lokacin da ta gama ware idanun ta akan su sai dai sakamakon duhun da idanun nata sukayi yasa take ganin su dishi-dishi.

"She is awake, call the doctor" haka Umma ta faɗa cikin ruɗewa tana tura su gefe kan kuma ta shiga kiran sunan "DEENAH."

Da gudu nurses ɗin suka fice dan zuwa kiran likita, basu daɗe ba suka dawo tare dashi dan haka wuri Umma ta bashi kafin kuma ya shiga aiwatar da aikin sa cikin kwarewa Nurses ɗin na taya shi.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah Nagode maka, Allah kasa tashin ta kenan daga wannan rashin lafiya, haƙiƙa kai maji roƙon bayin ka ne ya Wahhabu, wanda bai bika ba kuma bai yarda da cewa kaine sarki mai rayawa da kuma kashewa ba kuwa yayi asara duniya da lahira, yaa Zul-arshil majid ka tashi kafaɗun baiwar ka ka bata lafiya mai ɗorewa, Allah Nagode, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" haka Umma ke ta faɗi cikin kukan murna, tare da sa ran DEENAH ta tashi daga rashin lafiyar kenan.


Sun ɗan ɗauki lokaci akanta kafin su samu komai ya daidaita.

Ɗagowa yayi yana sharce gumi tare da kallon Umma yace "Muje Office."

Da sauri ta mara masa baya tana waigawa ta kalli DEENAH da idanun ta ke a rufe nurses ɗin na cigaba da rubuce-rubucen su.


Wuri ta samu ta zauna tana addu'ar samun jin kyakkyawar labari daga bakin likita.

"Likita ka faɗamin meke faruwa, ƴata ta tashi ne koh yaya?."

Murmushi yayi yace "Sunana Sadeeq."

"Toh ni ba wannan ba, yanzu ka faɗamin halin da ƴata ke ciki na roƙe ka."

"Ki kwantar da hankalin ki Ma'am, sannan ki godewa Allah, Alhamdulillah bayan dogon jinƴa ƴar ki ta samu sauƙi daga stroke ɗin da ta faɗa, sannan ta fita daga risk ɗin samun wani cuta makamancin hakan, this is a real miracle ko dayake babu yadda Allah baya yi sannan kuma ba'a mamaki da ikon Allah."

Zubewa Umma tayi a ƙasa tare da yin Sujudu-Shukur tana miƙawa Allah godiyar ta.


Ɗagowa tayi tare da fashewa da kuka sosai wanda ita kanta batasan koh na menene ba.

Sadeeq ne yayi ta rarrashin ta har ya samu ta ɗan tsagaita kafin kuma yace "Amma..."

Kallon da tayi masa ne yasa shi kasa idda maganar.

"Amma mai?."


"But, ba zata iya taka ƙafafun ta ba yanzun, dole ne sai an koya mata yin tafiya, and for that to happen har mu samu tayi recovering memory ɗinta then zaku sake spending like 2-3months under our care."


"Bakomai wallahi, ai tunda ta warke daga babban ciwon nan na san sauran duk zaizo da sauƙi, zan iya jiran fiye da hakan ma indai ƴata zata samu cikakken lafiya ta dawo kamar bata ta6a ciwon nan ba wannan ba damuwa ta bace, Allah ya bata lafiya kawai."


Murmushi yayi yace "Insha Allah, zata samu sauƙi very soon, yanzu munyi mata allurar bacci da zaran ta farko kuma bamason ayi stressing ɗinta dole ne mu bari kwakwalwar ta huta tukun kafin ki tunkare ta da wata maganar."


"Amma har zuwa yaushe zan jira hakan?."


"Zuwa gobe insha Allah."

Shiru Umma tayi alamun yayi mata nisa kafin kuma tace "Toh bakomai, Allah ya kaimu goben da rai da lafiya."


"Aameen" ya amsa.

Ɗakin Umma ta dawo kafin ta zauna gefen gadon tana kallon fuskar DEENAH da ya zamo so very pale sosai tausayin ta na cika.
"I can't believe zaki tashi amma ba zaki san koh ni wacece ba, ba zaki san wacece Ummar ki da kika saba ra6ar jikin ta kullum ba, am so very sad da jin wannan labarin sai dai na san komai mai wuce wa ne, sannan zaki zo ki warke baki ɗaya ki dawo asalin ke."

Miƙewa tayi tare da tattare kayayyakin ta cikin ɗan madaidaicin jaka, kafin ta fito.

Nurses ɗin ta nema dan haka ce musu tayi zata je ta dawo.

Hotel ɗin Umma ta koma sannan tayi musu wanki sai da ta jira suka bushe ta kwashe su, tare da dafo Black tea a cikin flask ta sake kwaso wasu kayayyakin sannan ta komo asibitin.

Koh da ta dawo tararwa tayi an canzawa DEENAH ɗaki, dan haka iso sukayi mata zuwa cikin ɗakin.

Ɗaki ne mai kyau shima na mutum ɗaya sai dai bai kai na farkon kyau ba.


Jere komai tayi mai kyau kafin ta samu wuri ta zauna.


Wayar ta ta ciro tare da danna kiran Jafar.


"Assalamu Alaikum Umma na."

"Wa'alaika Assalam, kana lafiya?."

"Lafiya ƙalau Umma dafatan kema haka?."

"Alhamdulillah ɗan albarka."

"Ya jikin DEENAH fah?."

"Jiki Alhamdulillah lafiyar ta na ƙara improving kullum sai dai mu godewa Allah, yanzu ma an canza mana ɗaki."

"Umma kenan ta fara samun sauƙi?."


"Sosai ma kuwa."

Cike da murna yace "Alhamdulillah, Yaushe zaku dawo kenan, Umma muyi video call na ganta."

"A'a kai kuwa ba sai ta gama warkewa tass zamu dawo ba, koh zamu zo muyi abinda za'a sake maido ta asibitin ne, kaga ni wannan video call ɗin naku ba gane kansa nake ba, ban iya shi ba."


"Haba Umma kinyi karatu fah, ba abu ne mai wahala ba, toh ki nemi ɗaya daga cikin masu aiki a asibitin su nuna miki."


"Toh shikenan kada ka damu insha Allah zanyi hakan."

"Yauwa Umma na yanzu fah."


"Toh inbanda abin ka Jafar ai basa kusa yanzu sai sun zo tukun."

"Toh shikenan Umma nima yanzu ina wani aiki ne a office, idan na idda zan kira ki."

"Toh shikenan, Allah ya taimaka yayi maka albarka."

"Aameen Umma na."

Yanke kiran tayi tana jin hankalin ta na kwanciya.



*THE NEXT DAY*


A hankali take buɗe idanun ta har ta idda buɗa su duka tarr akan ceiling ɗin ɗakin asibitin da take ciki.

Idanun ta ta shiga wulla wa tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login