Showing 204001 words to 207000 words out of 236327 words

Chapter 69 - ZEEYAD The Abandoned Prince complete hausa novel

JIDDAH   

17 Oct 2024

45311

ta6a yarje miki ba, koh da mata sun ƙare a duniya bana tunanin zai tsaya ya kalle ki sabida babu wani abin burgewa da ɗaukar hankali tattare dake."

"Oh come!, how do you expect ke6ewar mace da namiji wuri ɗaya kuma ki tabbatar da cewa mai afkuwa bata afku tsakanin su ba, i know ba zai faɗa muku gaskiya ba, but he did get intimate with me" ta ƙarashe cikin shu'umin murmushi.

Gum ɗin bakin ta Grandma ta maida tana faɗin "Non of your tricks can work on me Naseeba, you just wait and see how i teach you a lesson" ta faɗa tana dube-dube cikin ɗakin kafin kuma tayi saurin ficewa.

Kallon ta Nazeerah tayi tare da sakin murmushi tace "What a shame Naseeba, i told you didn't i?, i told you to stay away from the Boy but kince bakiji ba, so dama baki tanadi zuwan wannan ranar bane kike ta shuka tsiya, you think asirin ki ba zai ta6a tonuwa bane komiye?, kinga shiyasa ban ɗau damuwar komai na ɗaurawa kaina ba, Allah ya bani ƴaƴa mata na aurar dasu da mutuncin su da komai banga abinda zai sanƴa ni tada hankali na kan wani abu da nasan ba zan ta6a mulkar sa ba, koh da bakiji tsoron Allah ba ai kyaji tsoron zuwan ranar tonon asirin ki, who even cares da wani abin duniya, kinga wannan bakin nawa sam baya magana muddin ba'a gayyato sa bane ba, yaushe nake da lokacin 6atawa ina shirme, kinga gulma ta a ciki na take ƙarewa bata fita koh ina, na baiwa kunnuwa na da idanu na abinci ya isheni nishaɗin gidan duniya, but kinga yadda rayuwar ki ta kasance, kada kiso kiga yadda ran mai Martaba ya 6aci, na tabbata ba zai ɗaga miki ƙafa ba, dan kuwa har Jakadiyar ki Kiki aka kama yanzu haka an kaɗa ƙeyar ta izuwa ƙauyen da kakar tata take, nasan yanzu haka ma sunyi nisa da tafiyar."

Murmuring Naseeba ta fara tana jijjiga kujerar da take kai, ba'a jima ba Grandma ta shigo hannun ta riƙe da hockey stick, kallon Naseeba tayi tace "Ba zan bar ki ki tafi haka banza ba ba tare da nima na huce takaici na akanki ba, you must suffer today" ta faɗa kafin ta shiga zabga mata sandar hannun nata.

Sosai Naseeba ke jin azaba sai dai babu bakin magana kasancewa bakin a toshe ga hannaye duk a ɗaure babu damar kwacewa.

Sosai Grandma ta bubbuge ta iya son ranta har sai da ta gaji ta bari tana zama bakin bed kafin ta shiga sauƙe ajiyar zuciya akai-akai.

Sosai Naseeba takejin idan ta kwace babu abinda zai hana ta aika Grandma lahira.

"So now nayi miki nawa hukuncin, yanzu sai ki jira kuma na mai Martaba, kema dai kinsan hukuncin ki ba sai an faɗa miki ba, ke abin naki ma yayi yawa ga laifin aiki da asiri ga kuma laifin neman ɗan mijin ki, na tabbata binne ki kawai za'ayi a rami a bar ƙatoton kanki a waje a kuma tara yara suyi ta wulli har sai sun gaji kafin kuma a ɗauko takobi a yanke ɗan iska."

Suna haka Guards suka faɗo cikin ɗakin, kallon Naseeba dake a ɗaure ta waro idanun ta kamar zasu faɗo waje sukayi kafin su kalli Grandma suce "Mai Martaba ya umarce mu da mu kai Sarauniya Naseeba izuwa fadar sa, sannan kuma yana buƙatar ganin ku anan wurin."

Miƙewa Grandma tayi tace "Masha Allah, ai dama abinda nake ta jira kenan, yau dai duhun ki ya cika Naseeba, sai dai kuma uwarki ta haifo wata idan tana haihuwar kenan, Allah sarki sai kuma aje a haɗu da hukuncin da ba'a ta6a ganin irin sa a duniya ba wato hukuncin Allah, ai tunda kika nuna bakiji tsoron sa da kunƴar sa ba toh wallahi sai kin kunƴata duniya da lahira, ku ɗauke ta kuje gamu nan biye daku."

Ƙarasawa sukayi tare da sunce ta daga jikin kujerar da take ɗaure kafin su riƙe ta su fitar.

Kallon Nazeerah Grandma tayi tace "Toh ke kam dai ba zance kina burge ni ba, dan kuwa kema bansan koh kina da wata sharrin a ƙasa ba, amma dai mungode da ba da ke ba ai da ba zamu san da wata Keke koh ya sunan nata yake ne ma, muje mu dan kuwa nasan ba zaki so kallon abinda zai faru a fada ya bar ki ba."

Murmushi Nazeerah tayi tana marawa Grandma baya suka fice.


******************

_______Time to time yake duba agogon dake maƙale jikin tsintsiyar hannun sa, sosai yake cike da damuwa sam baya ganin gudun motar tasu duk da kuwa irin gudun da YAZEED keyi mata.

Ɗan kallon sa YAZEED yayi yace "Don't panic please, am sure zamuyi arriving before time ɗin yayi."

"We've almost 4hrs kafin mu ƙarasa and it's 4pm now, GOD knows what will happen to DEENAH idan bamu ƙarasa dawuri ba" ya faɗa cike da damuwa.

Wayar YAZEED dake silent ne ta sake kawo wuta a karo na ba adadi, tsaki yaja ganin dai mahaifiyar sa ce ke kira, daga baya ma katse kiran yayi yana switching ɗin wayar off.

ZEEYAD dai bai kula shi ba dan kuwa tashin hankalin da yake ciki kaɗai ya ishe sa.


***************************


_________Daf da Magrib suka ƙarasa wannan ƙauyen da bai wuci wani 6angare cikin MASARAUTAR su ba.

Da kaga mutanen ƙauyen ma kansu kasan yin asiri gadon ta sukayi.

Duk firfitowa sukayi inda kowa ya fara shigewa gidan sa yana rufowa ganin guards ɗin MASARAUTA koh ta ina.

Kiki ce tayi musu jagora har izuwa gidan kakar tata, koh da zuwan su basu same ta ba, sai wata mata suka samu inda take shaida musu cewa Kiki ta ɗau DEENAH sun fice.

"Find her, ku dubo kowane lungu da saƙo har sai kun gano inda take don't let her escape" cewar YAZEED cikin ɗagun murya.

Nan fah duk suka dunguma izuwa neman wannan tsohuwar, kallon Kiki ZEEYAD yayi yace "You know where we will find her don't you?, tell me dan nasan ba zaki rasa masaniya kan inda take kai ran mutane ta sadaukar ba."

"Wallahi ranka ya daɗe bansan komai ba, nayi maka alƙawari wallahi bansan komai ba."

"Damn" ya faɗa a hankali.

YAZEED ne yace "We must find her, ina ne babban kogi koh ruwa a wannan ƙauyen, maybe idan muka bi nan zamu same su."

Wannan matar ce tace "Yallabai."

Duk kallon ta sukayi nan tace "Zan faɗa muku inda ta kaita amma nima kuyimin alƙawarin zaku cece ni daga hannun ta, dan kuwa so take ta hallaka cikin dake jiki na, sannan Kiki ƙarya takeyi muku babu abinda bata sani game da kakar tata ba."

Duk irin idon da Kiki keyi mata bai hana ta magana ba, kallon Kiki ZEEYAD yayi a tsawace yace "You lied to me."

Batasan sadda ta zube ƙasa tsabar ruɗewa ba tana riƙo kafafun sa, janƴe ƙafar sa yayi yana wani irin ball da ita cike da tsantsar 6acin ran da yake ciki kafin ya kalli matar yace "Take us there."

Kai ta jinjina kafin ta shige gaba suna mara mata baya, inda wasu daga cikin guards ɗin suka garƙame Kiki.

Tafiya mai nisan gaske sukayi, babu abinda suke ratsawa sai jeji a hanƴar tafiyar su ne take faɗa musu cewa "Kiki tana amfani ne da tsafi wurin kawar da hankalin mutum sannan ta asirce shi yadda zaiyi dukkanin wani abu da ta umarce sa, zata sadaukar da ran wanda taso ga aljanun ruwa sabida samun ɗaukaka a duniyar matsafa ya zamto babu matsafi koh matsafiyar da ta kaita ƙarfi, koh yanzu sai munyi a hankali, dan kuwa muddin tasan da zuwar mu babu abinda zai hana ta ganin bayan mu, da akwai wani sanda a hannun ta dashi ne dukkanin wani ƙarfin tsafin ta yake ciki, muddin muka sami damar ɗaukar sandar nan toh babu abinda kuma zata iya, koh da ta karanto makaran tsafi, dan kuwa muddin sandar ya shiga hannun wani toh tsafin ta ya karye kenan, shiyasa a kullum sandar ke tare da ita, koh da da wasa bata rabuwa dashi."

Shi dai ZEEYAD jinta kawai yake but dukkanin hankalin sa na kan DEENAH ganin har yanzu basu isa bane ya sanƴa shi faɗin "How far is the place?."

"Mun kusa ƙarasawa sai dai ni zan ɗan dakata daga gaba kaɗan ku ku ƙarasa, koh dan lafiyar abin dake cikin ciki na."

Kai YAZEED ya jinjina mata, har sai da ta kai su wurin wani dutse kafin tace dasu" ku bi wannan hanƴar sai dai ku sani dole sai kun haɗa da addu'a, sabida akwai hatsari sosai muddin mutum ya wuce wannan dutsen shiyasa ni zan barku daga nan."

YAZEED ne yace "But aren't you afraid to go back alone?."

Kai ta girgiza masa cikin murmushi tace "Koh kaɗan bana tsoro indai har ba wai na wuce dutsen gaban nan bane, nan ne abin tsoron yake, ni zan koma ku ku wuce tun kafin Kiki ta gama aiwatar da ƙudirin ta, ni kaina kun cece ni, dan kuwa nice target ɗinta ta gaba dukda kuwa matsayi na na matar jikan ta sai dai tayi alwashin sadaukar da abin dake ciki na, nayi dukkanin yadda zanyi dan tseratar da raina amma abin yaci tura, kuje ku kada na 6ata muku lokaci."

"Mungode" YAZEED ya faɗa yana saurin marawa ZEEYAD da ya riga da yayi gaba baya.

Sosai dajin ke cike da duhuwa babu abinda kake ji sai ƙarar kukan mujiya da ma kuma wasu mugayen tsuntsayen.

Wayar sa YAZEED ya kunna yana haska musu ganin yadda duhu ya mamaye wurin.

Dukkanin su babu abinda sukeyi sai karanto addu'o'in neman tsari daga sharri, a haka har suka ƙaraso wani fili sai a sannan suka samu ganin sararin samaniya da tayi haske da ita sakamakon hasken farin watar da ya gauraye ilahirin wurin baki ɗaya, daga gaban sa chan kuwa wani ƙaton tekun ne inda suka hango wannan tsohuwar nan hannayen ta riƙe da na DEENAH cikin tsakiyar ruwan.

"DEENAH..." cewar ZEEYAD bai ƙarasa ba YAZEED yayi saurin toshe masa baki yana riƙo shi.

A hankali yake faɗin "This is our only chance, kada muyi wasa dashi, remember what that lady told us, that stick" ya faɗa yana nuna sandar ta dake ajiye a gefe.

Kallon sandar ZEEYAD yayi nan YAZEED ya cigaba da faɗin "Damar mu shine mu samu mu ɗauke sandar kafin mu tunkare ta."

"But DEENAH..."

"We will deal with her later, let's find a way to get her distracted first."

"But how?" ya faɗa.

"Like this" cewar YAZEED yana tura shi kafin shi kuma yayi saurin la6ewa.

Da sauri ta juyo tana kallon ZEEYAD da idanun ta da suka canza, tana sakin hannun DEENAH tare da fitowa daga cikin ruwan tana faɗin "Waye kai, mai kakeyi anan?."

Surrending ZEEYAD yayi da hannu idanun sa kan DEENAH da tayi tsaye cikin ruwan kamar wata gunki, a hankali ya fara waina tsohuwar yana faɗin "I...i...i was just passing by and i thought i should say hello."

"Ka raina min hankali ne yaro, kana neman wasa da rayuwar ka ne, do you want to die young?."

Ɗan murmusawa yayi yace "What are you saying?, i mean it's just that aikin naki ne ya burge ni, and i thought that you're making alot of money with that, so i decided to confront you..."

"Shut up" ta faɗa a tsawace tana nuna shi da sandar ta.

Shiru yayi still hannayen sa a sama, a hankali ya fara juyawa har ya zama na ita ta zamto tana fuskantar DEENAH, nan shi kuwa YAZEED ya fito daga ma6oyar sa ya shiga takowa cikin sanɗa.

"Please... Please i really want to work with you, i wanted to be your help boy, just don't kill me."

"Don't say another word Young boy, tell me who you are."

Kallon YAZEED dake tsaye a bayan ta yayi kafin yace "Well, maybe you should get to know who he is first."

Juyawa tayi dan ganin waye a bayan nata, juyowar tata ke da wuya YAZEED ya gwara mata kanshi, nan fah ta tafi tangal-tangal, Inda ZEEYAD kuma yayi nasarar kwace sandar hannun ta, kafin ta sake wani yunƙuri tuni YAZEED ya sake ham6arar ta da bayan hannun sa take ta faɗi ƙasa warwas, dama gata ba aukin komai ba.

Duk shewa suka sanƴa suna tafa hannayen su haɗi da rungume juna, juyawa ZEEYAD yayi ga DEENAH da har ruwan ya fara tafiya da ita, cike da tashin hankali ya shiga gudu cikin dukkanin ƙarfin sa yana faɗawa cikin ruwan.

Nutsawa yayi ciki yadda zaiyi saurin tadda ta kasancewar ya iya ruwa ya sanƴa cikin ƙanƙanin lokaci ya lalumo ta a cikin ruwar yana ɗagota.

"DEENAH" ya furta da ƙarfi yana ɗan marin fuskar ta.

Rungume ta yayi sosai a jikin shi kamar wanda za'a kwace masa ita, yayin da yakejin wani irin ƙauna da sonta na ƙara yi masa dirar mikiya tare da ratsa dukkanin wani jijiyoyi da 6argo na zuciya da jinin jikin sa.

Ɗago da fuskar ta yayi yana kallon ta kafin kuma ya haɗe bakin su wuri guda yana sumbata.

"Let's get going Bro" ya tsinkayo muryar YAZEED.

Sakin lips nata yayi kafin kuma ya ɗauke ta a hannu suka fito daga cikin ruwan.

Ƙarasowa inda YAZEED ke tsaye yayi yana kallon sa, murmushi YAZEED ya sakar masa tare da furta "Alhamdulillah."

Murmushi ZEEYAD ya sakar masa tare da faɗin "Let's go home, let's go" ya faɗa yana kallon fuskar DEENAH.

"Is she breathing?" cewar YAZEED yana kallon sa.

Fuskar ta yake bi da kallo kafin yace "I know she is alive, she isn't dead."

"Then we should get going, it's getting late."

Gaba yayi kafin YAZEED ya kalli tsohuwar da har yanzu ke yasha sakamakon bugun da tasha yace "What about her?."

"Leave her there, but come along with the stick" ya faɗa ba tare da ya juyo ba.

Kallon ta YAZEED yayi kafin kuma ya riƙo ƙafafun ta yana janta zuwa bakin ruwan tare da faɗin "Why don't you sacrifice yourself instead" yana faɗin haka ya marawa ZEEYAD da har yayi nisa baya cikin gudu.


*********************

_________Duk tsaye sukayi akan DEENAH da har yanzun bata farka ba, hannun ta kuwa ruwa ne aka jona mata.

Kallon ZEEYAD da ya kasa koh da barin wurin ta Grandma tayi tare da dafa shi tace "Boy kaima yakamata ace ka sami hutu, tun jiya da kuka dawo baka wani sami baccin kirki ba."

"Grandma please, i don't want to leave her, ba zan sake yin nesa da ita ba, what if something bad happens to her again?."

Sauƙe ajiyar zuciya tayi tace "But am here, koh da baccin awa ɗaya ka samu kayi..."

"No Grandma" ya faɗa kai tsaye.

Shiru Grandma tayi ta kyale sa kawai dan kuwa tunda yace a'a ɗin toh yana nufin a'a ɗin ne.

Kissing hannayen DEENAH dake cikin nashi yayi yana murzawa kafin ya fara faɗin "Am sorry DEENAH, i caused you all this."

"Stop it Boy" cewar Grandma.

"I will never stop feeling guilty until na ganta ta buɗe idanun ta sannan ta kira sunana ta cemin she is Okay."

"Insha Allah hakan zai faru, you know how hard it has been for her, dole she needs more rest zuwa anjima zata iya farkawa."

Kai kawai ya jinjina mata ba tare da yace komai ba.


Ƙarfe sha ɗayan safe ya wuce DEENAH ta farka, ware idanun ta da sukayi mata nauyi tayi tana sake bin ɗakin da kallo.

Da sauri ta miƙe dan kuwa ta zaci koh mafarki take, murza idanun ta tayi nan dai tags ba mafarkin take ba, bin riga da wando na baccin jikin ta tayi kafin kuma ta maida idanun ta gun inda take jiyo motsi.

Fitowa yayi daga ɗakin closet ɗin yana sauƙe idanun sa cikin nata da ta kafe sa dashi.

Da sauri ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta.

Ja da baya tayi dan kuwa bata yarda koh shi ɗin bane ba.

"DEENAH" ya kira sunan ta.

"Don't come close to me" ta faɗa cikin tsoro tana sake ja da baya.

"Babe it's me, not Naseeba."

Shiru tayi tana kallon sa kafin a hankali tace "Abyad?."

Kai ya jinjina mata, rarrafowa tayi da sauri tana shigewa jikin sa tare da sakin kuka.

Rungume ta yayi tightly yana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyar sa.

Sosai ta sha kuka kafin ta ɗago da idanun ta tana kallon sa, hawayen da ya 6ata mata fuska ya share mata, kafin yayi kissing lips nata yace "I miss you."

"You've been living with your step Mom all this while not me, she is evil, they are all evil" ta faɗa cikin kuka kafin kuma ta ɗago hannayen ta dake ɗaure da Bandage sakamakon ciwon da taji sakamakon igiyar da aka ɗaure ta dashi da yayi tighting ɗinta sosai, nan ta cigaba da faɗin "The old woman, where is she?."

"She is dead" ya faɗa yana kallon ta cikin kulawa.

Sake manna kanta tayi a ƙirjin sa kafin tace "What about your step Mom then?."

"She is still alive, ke ake jira ki farka a yanke musu hukunci a gaban ki."

Ɗagowa tayi tana kallon sa, nan ya jinjina mata kai, cikin kuka tace "I don't want to... i don't want to go anywhere, am afraid your PALACE is full of wicked souls, babu wanda yake sona sai kai da Grandma, babu inda zan sake fita."

Cupping fuskar ta yayi yace "Calm down please, kina jin tsoro?."

Kai ta jinjina masa da sauri nan yace "Shiyasa suke samun damar cutar dake coz you're afraid of them and what they can do, just show them cewa ke babu wanda kike tsoro sai Allah and dashi kika dogara, idan kinyi hakan then babu wanda zai sake raina miki hankali wurin kawo miki farmaki sabida kin riga da kinyi musu nisa."

Shiru tayi kawai tana kallon sa, murmushi ya sakar mata yana sake kissing lips ɗinta.

Lamo tayi a jikin sa tana rungume sa so tightly kamar wanda zai gudu ya barta.


**********************


_______Da yamma mutane ne birjik a wani ƙaton fili da alama dai duk sunzo baiwa idanun su abinci ne bisa ga irin hukuncin da za'a yiwa Naseeba da Jakadiyar ta Kiki.

Hannayen su duk a ɗaure yake aka fito dasu daga cikin kurkukun da aka garƙame su guards na biye dasu aka shigo dasu filin kan dakalin da za'a yanke musu hukunci ɗin.

Kallo ɗaya zakayi musu ka hango tsantsar tashin hankali da fargabar da suke ciki.

Miƙewa sarki yayi hakan ya sanƴa ilahirin wurin baki ɗaya ɗaukar tsit.

Cikin mic ya fara magana da cewa "Ance 99days for the thief, one day for the owner, as you can all see here the person i called

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login