Showing 177001 words to 180000 words out of 236327 words
fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*
_07084653262_
***************************
*CIGABA...*
________Zaune suke kowa jugum, daga mai naɗaɗɗen baki, sai mai dogon baki, kowannen su zaune yake gefe ɗaya da iyalan sa haka kuma kowanne a cikin su da ka ganshi zaka hango iriyar tsantsar rawar kan dake tattare dasu musamman ma ga samarin dake wannan wurin.
Abdulhakeem na hango da family ɗinsa, kallo ɗaya zakayi wa Sooraj ka hango iriyar 6acin ran da yake ciki wanda dai da alama ba'a daɗe da fitowa dashi daga kullen da akayi masa ba, babu abinda yake sai wani irin cika yana batsewa wannan daga gani ƙiris yake a ta6a sa ya fashe.
JALILAH kuwa zaune take kusa da mahaifiyar ta, haka kurum takejin gaban ta na faɗuwa na tara su anan da mai Martaba yayi.
Ayaan da Rahinah suma duk zaune suke kusa da mahaifiyar su, kallo daya zakayi wa Ayaan ɗin shima ka gane a wuya yake.
Sarauniya Nazeerah ita ma wasu ƴan mata kyawawa biyu ne kusa da ita, wanda dai da alamu ƴaƴan ta ne, daga gefe kuma Yara Uku ne maza biyu sai mace ɗaya wanda dai da alamu Jikokin Sarauniya Nazeerah ne.
Naseeba kuwa zaune tayi ita kaɗai yayin da kowane motsin ZEEYAD idanun ta na akan sa tamkar ta ɗauke sa ta cinƴe.
Grandma na hango a gefe haƙimce akan kujera ita ma.
Sai kuma wasu wadanda bansan dasu koh su wanene ba wanda dai da alamu suma Family ne.
Mai Martaba dake zaune gefe da gefen sa YAZEED da ZEEYAD ne yayi gyaran murya tare da karanto addu'o'i kafin ya ɗaura da faɗin "Na san zakuyi mamakin tara ku anan da nayi duka, we're all family here, idan akace Family ana nufin an zama ɗaya babu wani bambanci koh warayya, sannan ansan Family da haɗin kai dama kuma kasancewa da juna a dukkanin wasu al'amura, ba sai na tsaya dogon surutu ba zan wuce kai tsaye ne ga abinda ya sanƴa ni tara ku duka anan wurin, Yarima ZEEYAD ɗana ne haka kuma gudan jini na ne shi, kamar yadda na zanta da dukkanin ministoci na yau suka shaida ina son kuma ku shaida cewa daga yau Ni Sarki Abbas Ibn Hakim na naɗa Yarima ZEEYAD a matsayin magaji na sannan kuma future King na wannan MASARAUTA..."
Abdulhakeem ji yayi kamar ya wantsilo daga kan kujerar da yake da jin abinda mai Martaba ya furta wanda baisan sadda ma ya buɗe idanun sa dake runtse ya saki baki yana Kallon mai Martaba ɗin ba.
Sarauniya Hafeezah ji tayi kanta yayi wani irin gudun fanka wanda ya sanƴa ta ganin mutanen wurin bibbiyu na wasu ƴan lokuta zuciyar ta na mugun bugu da tafarfasa kamar zai wantsalo waje.
Kallon ZEEYAD YAZEED yayi tare da sakar masa murmushi yana yi masa alamun Kudos da yatsar sa, murmushi shima ZEEYAD ɗin ya maida masa yanajin ƙaunar ɗan uwan nasa sosai cikin zuciyar sa.
Grandma ji tayi wani irin farin ciki ya lullu6e ta, jin Boy ɗinta ya kusa zama sarki, hawayen farin ciki ta share, sai dai gefe guda na zuciyar ta na matuƙar tsoron kasancewar sa sarki ɗin wanda batasan dalilin hakan ba.
JALILAH da mahaifiyar tama murmushi suka saki sa6anin Sooraj dama kuma sauran mutanen dake cikin falon gaba ɗaya.
"A King?" cewar Abdulhakeem yana kallon mai Martaba ɗin.
Ba tare da mai Martaba ya amsa shi ba ya cigaba da faɗin "Sannan zai gudanar da mulkin sa ne ƙarƙashin dokokin tsohon Sarki wato Kakana marigayi Sarki ZAYYAD ABDULHAKEEM."
Abdulhakeem bai san sadda ya miƙe tsaye daga zaunen da yake ba, yana bin mai Martaba da kallo, a hankali ya furta "Sarki Zayyad?."
"Abdulhakeem, ka sami wuri ka zauna ban gama ba tukun."
"This is totally against the law of this Kingdom your Highness, ba zaiyiwu ZEEYAD ya mulke mu ba har sai ya kai shekaru talatin da biyar da haihuwa" cewar ɗaya daga cikin family members ɗin.
Ba tare da mai Martaba ya kallesa ba yace "Bakomai ne sai anbi tsarin doka ba, wasu lokutan wasu abubuwan kama wa yake ba tare da ka shirya musu ba, so am stepping down and ZEEYAD will be the King."
"This can't be possible, indai har sauƙa ɗin kakeson yi why not ba zaka bani matsayin sarkin ba, tunda har ni ƙani ne a gareka sabida ɗan ka bai kai shekarun zama sarki ba tukun" faɗin Abdulhakeem cikin 6acin ran da ta fara zuwan masa.
"I said sit, Abdulhakeem" cewar mai Martaba.
Zama yayi zuciyar sa tamkar ana balbala masa ruwan zafi cikin ta.
"ZEEYAD will be the King immediately bayan an ɗaura masa aure da wacce yakeso."
JALILAH ji tayi zuciyar ta ta tsinke, kallon inda ZEEYAD ke zaune tayi taga ma hankalin sa ba'a kanta yake ba.
Kallon ta mahaifiyar ta tayi tare da yin murmishi a hankali tace "Don't panic dear am sure kece zaki zamto Sarauniyar wannan MASARAUTA tunda har yana sonki.
Murmushin yaƙe kawai JALILAH tayi ba tare da ta iya cewa komi ba.
"And kaima YAZEED na san ba zaka rasa wacce kakeso ba, ka faɗi koma wacece idan yaso sai a haɗa bikin ka da na ɗan uwan naka ayi."
Satar kallon mahaifiyar sa YAZEED yayi wacce gabaɗaya hankalin ta baya jikin ta, zai buɗi baki yayi magana Grandma tayi caraff tace "Ofcourse, yana da wacce yakeso ba kowa bace illa JALILAH" Ta ƙarashe cikin murmushin yaƙe.
Duk kallon ta sukayi daga ZEEYAD, YAZEED har JALILAH ɗin cike da mamaki.
Murmushi mai Martaba yayi yace "Masha Allah, hakan yayi matuƙar kyau, nan zuwa makonni biyu masu zuwa za'a ɗaura auren nasu duka, ku kuma ku hau dukkanin wasu shirye-shiryen da ya dace domin tar6ar surukan naku."
Murmushin farin ciki Grandma tayi ba tare da ta kula kallon da su ZEEYAD ke bin ta dashi har yanzun ba.
"Wannan shine dalilin da ya sanƴa ni tara ku anan duka, zaku iya tafiya domin kuwa ina buƙatar hutu."
***********************
"Grandma what have you done?, YAZEED bai ce miki yanason JALILAH ba."
Murmushi Grandma tayi tace "Ina matuƙar ƙaunar yarinƴar nan JALILAH, wacce mahaifiyar sa ke son haɗa sa da ita sam ba ƴar gidan mutunci bace ba, kaga kuwa koh da ace ya aure su su biyu ɗin na tabbata ba zai wofantar da JALILAH ba koh dan kyawawan halayyar ta ma."
Sosai ZEEYAD ya cika da mamakin ta, tsuke bakin sa yayi kawai tare da yin shiru nan tace "Ka kuwa sanar da Ummien DEENAH zasuyi baƙi jibi?."
Kai ya girgiza mata alamun a'a, nan tace "Toh mai kake jira ne, maza ka ɗau waya ka sanar dasu, koh da yike ma ka bar wannan a hannu na ni yakamata na sanar dasu wannan kyakkyawar labarin" ta ƙarashe cikin murmushi kafin ta fara dube-dube tana faɗin "Ina kuma wayar tawa tayi ne?."
Ficewa kawai ZEEYAD yayi ba tare da ya sake bin ta kanta ba, sosai yakejin babu daɗi wa JALILAH but ya ya iya, muddin ya yarda ya aure ta then ba zai wani bata isasshen kulawa kamar yadda zai baiwa DEENAH ba, da wannan tunanin ya ƙarasa part ɗinsa.
*******************
"Ummie can you imagine, ZEEYAD a matsayin sarki, isn't that odd?."
Shiru Sarauniya Hafeezah wacce tun maganar sarki ta kasa furta komai kamar wacce aka ɗauke mata ji da maganar ta tayi tana sauraron Ayaan ɗin.
"Ummie you've to do something akan hakan, why ina magana tunɗazu kuma kinyi min shiru i hate that, and i thought kince Akhi ƴar wurin aminiyar ki zai aura why kuma that Old hag zata kawo maganar wata aba wai Jalilah like tana da wani iko akan sa, after all she is nothing a cikin MASARAUTAR nan, i wonder why take raye har yanzu" ya ƙarashe a hankali yana yatsine fuska.
"Ummie?" ya sake faɗa.
"What kake tunanin zata ce, she have nothing to say" cewar YAZEED da shigowar sa kenan.
Sarauniya Hafeezah kamar jiran shigowar sa take, dan haka kansa tayi a matuƙar haukace tana ɗebe sa da wani irin kyawawan maruka jere kafin ta cakumo kwalar sa cikin azababbiyar 6acin ran da take ciki ta fara faɗin.........
_Ayiriri casss shagali, ZEEYAD fans kuzo mu cashe😂😂💃🏽💃🏽💃🏽, Yanzu dai kafin nace komai wacece zata je cikin gari ta yanko mana Ankon aure?, dan kuwa ba za'a yi babu mu ba, abu namu maganin a kwa6e mu💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽_
*YAWAN COMMENT, YAWAN POSTING*
*MHIZZ JIDDHERR................✍🏽*
[8/23, 10:40 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```
*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*Jinjina ta ban girma gareku my best Commenters😍*
*Sadysglam🌹*
*Mrs Nuruddeen🌷*
*Mrs Kabeer🌺*
*Ice♥️😂*
*Lateefat😍❤️*
*Fatima Bet🥰❤️*
*Ummu Muhseenah🥰*
*Queen Hafsy❣️*
*Haseenerh💞*
*Mom Misrah😍*
*Ammy❤🩹*
*Nana Ruqayyah💕*
*Deejarmerh*💝
*Rafi'at Darajat*💖
*Mum Intisar*💗
*KHADIJA*😍😍
*Asiya Abdulkhadir*🤎
*Meenorrhh❣️*
*Mrs H💛*
*Beebarh♥️*
*Khadija Usman💚*
_Dama dai wadanda banyi mention ɗinsu ba, haƙiƙa ƙaunar ku ta daban ce a cikin zuciya ta, naga comments naku duka kuma alhamdulillah sun nishaɗantar dani sosai, Allah ya dawwamar daku cikin farin ciki na har abada Habibties🤲🏽🥰_
*046...*
_*NOT EDITED*_
________"You are so happy aren't you, you're happy that my plans are backfired aren't you, you're happy for that boy isn't it?, you chose to hurt your mother and make some random boy happy, i wonder if you're even my son, koh kaɗan baka gaji arziki daga gareni ba, i may say that i regret giving birth to you, menene amfanin haifar yaron da ba zai iya sanƴa ka farin ciki ba, ka haɗemin kai da wadancan banzan mutanen da koh kaɗan basu da daraja, all because of you burin da naci alwashin cikawa shekaru da shekaru ya ruguje, giving birth to you is the worst thing da na ta6a fuskanta da nasan haka zaka bani kunƴa ka kuma watsa min ƙasa a ido da babu abinda zai hanani toshe hancin ka ka mutu kawai a jariri, and let me make one thing clear to you, babu kai babu auren JALILAH muddin ina raye koh da kuwa wancan munafukin mahaifin naka ya tilasta ka toh babu abinda zai hana ka haɗa dukkanin su biyu ka aura, and i swear YAZEED... you will regret watsa min ƙasa a ido da kayi" ta ƙarashe cikin tunkuɗa shi baya tana wani irin huci mai cike da 6acin rai da haɗi da tafarfasar da zuciyar ta keyi.
Sosai YAZEED yaji tamkar ya mutu a wannan wurin, sam baiga amfanin rayuwar sa da wannan matar a matsayin mahaifiyar sa ba, babu komai a zuciyar ta sai sharri, zuciyar sa zafi takeyi masa fiye da tunanin mutum, sam babu sukuni tattare da zuciyar sa, kullum cikin fargabar hali irin na mahaifiyar sa yake, baisan yaushe ne zata canza halayen ta ba, ance mata sunfi yawa a wuta tabbas baya cire ran mahaifiyar sa na ɗaya daga ciki, he hate her completely sabida munanan halayen ta.
Juyawa yayi zai fice daga ɗakin tayi saurin dakatar dashi da faɗin "Hold it right there, kaje ka sami mahaifin ka ka sanar dashi da akwai wacce kakeso ba ƴar wurin Abdulhakeem ba, ƙinyin hakan babu abinda zai ja maka sai tsinuwa ta and that girl JALILAH i will make sure i ruin her life forever muddin ka kuskura ka sake aka ɗaura maka aure da ita, and that Old Hag nayi alƙawarin koya mata hankali soon, who is she da har take tunanin yanke wani hukunci cikin rayuwar ka, kayi abinda na umurce ka, ƙin yin hakan dai-dai yake da 6acin ran kowa a wannan MASARAUTAR, get out of my sight."
Ficewa yayi ba tare da ya tanka mata ba.
*********************
_______"I thought cemin kikayi the king to be zaki aura, yaushe kuma kika koma kan ɗan uwan sa?" cewar Abdulhakeem yana kallon JALILAH dake durƙushe a gaban sa tana kuka.
"Abhi bansan ya akayi hakan ba, ni babu komai tsakani na da YAZEED" ta faɗa cikin kuka.
Dariya Abdulhakeem yayi yana kallon Sooraj dake zaune cikin kujerun alfarmar da ya ƙawata falon nasu.
"Abhi daga ita har YAZEED ɗin babu wanda yakeson juna, dan haka hukuncin ta shine ka yarda a aura mata shi let her suffer tamkar yadda tasa wancan ZEEYAD ɗin ya sanƴa a rufe ni for almost 2months a jail, sakarya kawai" cewar Sooraj cikin hargowa kamar ya ɗauke ta da ball.
"Well hakan za'a yi, tunda chan ba son auren nata da wannan marar mutuncin yaron nake ba, but yanzu kin shigo hannu dan kuwa Hafeezah kaɗai ta isheki magani a wannan gidan, da akwai ƴaƴan Sarakuna dayawa da suka nuna interest akanki amma haka kika rufe ido kika ƙi amince musu yayin da nikuma kika watsa min ƙasa a idanu, kika kuma zubar min da mutunci kika ƙeƙashe dake da mahaifiyar ki akan sai ZEEYAD kike so, gashi nan ai wanda kika tsaya jira tsawon shekaru ɗin ya watsa miki ƙasa a ido zai auri wata ba ke ba, na tabbata Kakar sa na ƙaunar ki yasa ta haɗa ki da YAZEED da kuwa haka zaki gama tsofewa a cikin gidan babu aure, kinyi wasting shekaru biyar cikin rayuwar ki waiting for wanda ba zai ta6a sonki ba, na tabbata cikin shekarun da haƙuri kikayi kikayi auren ki da yanzu muna da jikoki, ga kuma arziki da zamu ci mu more, but kin watsa min ƙasa a idanu tare da maida ni ƙaramin mutum a idanun mutanen da suke ganin girma na, koh dan wannan abinda kika aikata min ma ba zai sanƴa na bar ki ki cika burin ki ba, marar mutuncin banza da wofi."
Ita dai JALILAH sosai take kuka da jin abinda mahaifin nata ke faɗa mata, bata ta6a tsanmanin ZEEYAD zai watsa mata ƙasa a ido ya auri wata bayan ita ba, sam bata ƙi ta zamo matar sa ta biyu ba muddin zai aure ta ya kuma nuna mata ƴar kulawar da yake ɗan nuna mata a baya.
Tashi tayi da gudu tana ficewa daga gidan nasu dan kuwa zaman ta anan babu abinda zai ƙara mata sai damuwa da baƙin ciki sabida duk babu mai nuna damuwa koh kulawar sa a gareta bale su kwantar mata da hankali.
Mugun kallo Abdulhakeem ya watsawa Matar sa dake tsaye zuciya babu daɗi tana kallon su nan yace "What are you staring at, faɗa zakiyi min koh duka na zakiyi sabida na ta6a ƴarki?."
Bata tanka masa ba ta juya fusace ta koma ɗakin ta.
***********************
______"Wace iriyar maganar banza ne wannan, i have already annouced batun auren ka da ƴar wurin Abdulhakeem, dan haka babu abinda zai sanƴa ni janƴewa, kai kanka kasan bana magana biyu, batun auren ka da ita kuma babu janƴewa, ita kuma yarinƴar da kacemin kana son nata za6i ya rage gareka either ka haɗa su su biyu kokuma ka kyale ta, but aure da kai da Jalilah babu fashi."
Tunda mai Martaba ya fara magana kan YAZEED ke duƙe a ƙasa, sam mahaifiyar sa ta hana rayuwar sa sukuni, ta wargaza masa tunani da farin ciki, abinda ta damu dashi shine kawai ta ganta cikin farin ciki, bata damu da feelings ɗin wasu ba, gashi yanzu tana neman jefa rayuwar sa cikin sarƙaƙiya, bashi da wani za6i da ya wuce ya amincewa auren ƴar wurin aminiyar ta koh dan kada Jalilah ta shiga ƙunci da ƙiyayyar da zata ke nuna mata.
"Abhi... na amince zan aure su su duka biyu, and i promise to do my best wurin kwatanta adalci a tsakanin su."
Shiru mai Martaba yayi yana kallon YAZEED ɗin da har yanzu bai ɗago ba, cikin kwantar da murya yace "Tell me Son, Hafeezah ce ta tilasta maka auren yarinƴar koh ba haka ba, kai kuma ƴar wurin Abdulhakeem kakeso ita kuma Hafeezah bata ƙaunar ta da kai, hakan ya sanƴa ta tilasta maka wurin auren ƴar aminiyar ta."
A hankali YAZEED ya jinjina masa kai.
"Tell me, mai tace zatayi maka muddin baka auri ƴar wurin aminiyar tata ba?."
Shiru YAZEED yayi ya kasa basa amsa, ajiyar zuciya mai Martaba ya sauƙe yana mai mamakin hali irin na Hafeezah, koh ba'a ce dashi komai ba yasan ta tilastawa ɗan nata tare da ɗaukan masa alwashin wani abu muddin baiyi abinda tace ba.
A hankali ya furta "Alright, you will Marry them all, ka cika alƙawarin ka na ganin cewa ka kwatanta adalci a tsakanin nasu, yin hakan zai sanƴa Allah ya taimake ka ya kuma kawo maka sassauci a rayuwa, kayi ƙoƙarin ganin ka rabu da mahaifiyar ka lafiya wurin yin abunda ta umurce ka muddin ba wai ya sa6awa doka da addini bane."
Kai ya jinjina cikin raunanniyar muryar sa yace "Insha Allah Abhi."
"Kaje ka kira wo ɗan uwanka, da akwai abubuwan da nakeson tattaunawa daku yanzu."
Miƙewa YAZEED yayi daga zaunen da yake cikin girmamawa ya amsa mai Martaba kafin ya fice daga fadar.
**************************
*WASHE GARI*
_______Zaune DEENAH take jugum, tunda taji labarin dangin ZEEYAD na hanƴar zuwa tambayar hand in marriage ɗinta take jin abin kamar almara, she can't believe, dah ace shi ya faɗa musu ba Grandma ba dah ba zata ta6a yarda ba, mamaki take why yake cikin eager ɗin mallakar ta da wuri haka.
Shigowar Jafar ɗakin ya sanƴa ta ɗagowa tana kallon sa har ya ƙaraso kusa da ita ya zauna.
Murmushi yayi mata kafin yace "I thought zan zo na same ki cikin farin ciki, coz mafarkin ki ya kusa zama gaskiya, atlast ZEEYAD is gonna be your Husband, no more cries, no more being depressed, no more over-thinking, sai kice Alhamdulillah."
Rungume sa tayi hawaye na biyo mata ƙunci, sosai takejin ta fara kewar su tun yanzun, sam batason yin nesa da family ɗinta, yanzu kuma fah tafiya zatayi kenan zuwa gidan zaman ta na kanta wanda ita ma zata tara nata future Family ɗin, sosai takejin wani irin kewa na dabaibaye mata zuciya.
Ɗan dariya Jafar yayi yace "Toh tun ma basu ƙaraso anyi maganar ba kike kuka, ranar da zasu tafi dake kuma fah ya zakiyi?."
"Ba sai na fasa bin su ba" ta faɗa cikin muryar shagwa6a.
"Well ai kuma bamu isa mu hana su tafiya dake ba, coz kin riga kin zamto ɗaya daga cikin family ɗinsu."
"Nidai ku kaɗai ne Family ɗina" ta faɗa cikin ɗagowa tana share hawayen ta.
Dariya yayi kafin yace "Yeah koh kin tafi ɗin we will still be family forever."
Murmushi tayi tace "Koh wane sati sai nazo na ganku na tafi."
Idanu ya waro kafin yace "Ai koh gari ɗaya muke ba zaki dinga zuwa bayan sati ba bale kuma chan Egypt."
Baki ta turo